NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Kuyi hakkuri wallahi duk kwanakin nan banajin dadin jikinane

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:12 – ????????????: DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI GODIYA DA YABO YA TABBATA GA ALLAH SARKIN BAIWA DA RAHAMAN SA UBANGIJI MUNA ROKON KA KA SADA MU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANAN GOMAN JUL, HAJJIN AMIN ????

Kawu ne zaune a falon shi tare da yaran shi a daren jumma,a kallo daya zakaiwa kowansu kagane halin tashin hankalin da suke ciki lokacin.
Kowa yakasa magana baya sj fahinci dalili kiran da mahaifin nasu yayi masu sai zufa ke ketowa ko wani su a lokacin .
Umar ne yayi karfin halin yin magana a cikin su yace to daddy don wanan ai kowan mu yasan da zancen nan cikin mu.
Dama ka fada muna tun can a waya da sai a turowa mama da kudi ayi duk wani abinda ya kamata ayi .
Cikin farin ciki kawu ya kalli dan nasa yace Allah yayi maku albarka dama nasan ba zaku taba kinyatani a duniya ba .
Gaban habbib ya yafadi dake shirin fadln daddy nifa ban shirya ba sai yaji umar ya ari baki su yaba mahaifin su aamsa da fadin sun amince yana saka masu albarka da godiya tare da yaba masu.
Idan ranshi yayi dubu ya baci a lokacin hakan yasa ya kasa daurewa a ranshi ya dago fuskan shi daya gama nuna tashin hankali a ciki yana masu wani irin kallo.
Kawu yace yaya habbibu ko baka shirya hakan bane kai a wurin ka yace cikin sunkuyar da kai a,a daddy gani nayi dai baka sanar damu zancen da wuri ba sai yanzu muke ji.
Alh yace na isar maku ne yasa hakan sanan kuma daura aure a yanzu ba yana nufin tarewan su bane ranan sai nan da zuwa satin sama mai zuwa kaga zuwa lokacin aika gama wani shirin da duk zakayi.
Umar da takaici ya gama cikawa babu halin nunawa yace sai dai daddy ina ga ni ba zan kai wanan lokacin ba a kasan nan don ina da aikin da zamuyi a hong kong idan na koma.
Alh yace ai shike nan tunda an daura aure zaka iya tafiya da matar ka dama shine wajibin aure ai wanan ba wani matsala bane mai girma.
Takaici da badaman fadin haka ya rufe mai zuciya yace a fili shike nan daddy yadda kace haka za ayi.
Sai Alh yace saidai ina kara rokon wani alfarma a gurin ku don Allah don gujewa rigimar uwar ku kan hakan ina son ku rufe wanan maganan don Allah ba dan niba sai an daura zataji idan zai yuyu.
Kowan su tunane yake a ranshi ta yaya zasu iya boyewa mahaifiyar su wanan maganan mai muhinmanci a garesu haka duk da sun san idan taji ma daga bayan ba,a hutaba.
Sun dan gama tataunawan yace zasu iya tafiya Allah ya kaimu gobe bayan ya mika masu kaya a cikin ledoji dinkaku da zasu saka a ranan.
Haka suka mike suka fice daga falon jikin kowan su babu karfi sai tarin bakin ciki da takaicin dake cin ransu lokacin.
Har sun nufi hanyar part din mahaifiyar su umar ya dakatar dasu yana fadin ina son ku sani yiwa mahaifin mu biyayya ya zama wajibi a gare mu .
Mudin muna son haske a rayuwan mu ya kamata kowan mu yabi umurnin mahaifin namu don mu gama lafiya dashi kamar yadda yake so har ya nuna muna jin dadin shi a fili haka kan yardan namu.
Don haka zuwa gurin mama a wanan lokacin yana nufin rushe farin cikin mahaifin mu ne don babu yadda za yi mu shiga wurin mama yanzu bata fahinci komai ba gare mu.
Don haka ina shawartan ku da ku daure mu kyale mama har sai komai ya kammala kamar yadda daddy ke so damu daga baya koma may zai faru sai ya faru mundai nuna ma daddy mu masu biyayya ne a gare shi .
Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke da tun fara maganan ya kasa furta komai sai lokacin yace nima hakan nake gani don ba komai yasa zan hakkura da hakan da daddy ke so sai do goben mu don muma zamu so diyan mu suyi muna biyayya a gare mu wata rana don tarihi yakan maimaita kanshi akan mutum.
Kayi tunane Aliyu abinda na dade ina faman tunane ke nan a raina yasa nake nuna yarda na, babu gardama ga mahaifin mu don mu rabu lafiya dashi.
Ya dafa kafadan habbib dake cika yana batsewa tsaye gefe daya hannayen shi daye cikin aljihun wandan shi yace be cool bros komai zai zama sauki da yardan Allah.
Kai kawai habbib ya iya kada mai ya juya zuwa hanyar fita gidan hankali a tashe daga haka sukai sallama kowan su ya bar gidan.
Hjy jummai ta aje masu abinci tana jiran shigowan su har goma na dare bataga shigowan su ba yasa ta kira layin Aliyu don shi keda saukin samu a cikin su sai dai waysn tasa a kashe take haka yasa ta gwada na habbib shima hakan.
Tayi tunanen kiran umar sai dai tasan tunda yakai wanan lokacin bai shigo ba tasan ba zai shigo din bane don baikai karfe tara ma a gidan shi.
Haka taita gwada layukan nasu baya shiga dole ta hakkura da rashin samun su din ta kwata da tunanen ina suka shiga haka basu fada mata ba don tasan komai under control din ta sukeyin shi.
Ba zasu iya yin wani abu kai tsaye ba indan suna garin kai koma basu garin hakan kamar ya zamo masu jiki sai sun sanar da ita dan dama umar da ya fara girma ya fara yarda wanan akidar tasu na yan dakin nata.
Don haka ne wanan damuwan nata a ranan yai yawa rashin jin yaran nata ko washe gari haka ta aje abinci ba wanda ya shigo daga cikin su dan dama Aliyu ya dan leko a gurguje daukan abu salma ta ganshi yace tace yana zuwa suna wani aiki ne yasa bai samu lokacin shigowa ba.
Taje ta fadawa uwar tasu kafin ta fito ya fita yabar gidan bata samu ganin shi ba ya wuce ko da saurin shi.
Karfe biyu daidai A massalacin dake unguwan an tashi daga sallah jumma,a aka sanar da daurin auren wanda ranan mafi yawan bakine suka halarci masalacin daga cikin su harda su baffa da sukazo daga misau a ciki da sauran abokan daddy da suka samu labari a kuraren lokaci.
Wanda hakan yaba mutane mamaki da dama hjy jummai da bata san abinda akeyi ba tana can tana sheka barcin ta a dakin ta ta saka wayan ta a silent don tana son ta huta haka yasa kira da yawa na masu son cinta tara yai ta shigo mata bata sani ba.
Hjy maryam data tsuncin labarin daga sama shiganta uku wurinta tana samun tana barci ga tsegumin haka yana cinta dole ta hakkura har ta tashi taji kwam.
Sai bayan anci an sude kanen ta da suka zo a fusace don jin yaya harkan ya faru basu da labari su bayan ko jiya da yamma suna tare da ita bata fada masu ba.
Ta daiyi masu korafin ya kira yara ba tare da ya sanar da ita zasu zo ba bata kuma san dalilinn shi nayin hakan ba ya kyale yaran a cikin damuwa .
Cikin barci taji bugun kofa a tashin hankali ta farka a razane tana kallon kofan tare da fadin wai waye ne don Allah ke damuna.
Turo kofan sukayi suka shigo kallon yanayin fuskan su kawai ya nuna ba lafiya ba a rude take tambayan su lafiya ta gansu haka hankali tashe ?
Kallon juna sukayi tare da samun wuri suka zauna ba wanda ya iya magana a cikin su kara tambaya ta maimaita masu may ke faruwane wai na ganku haka kamar a rude ?
Anty Alh yayi maki bayani ko a rikice tace wani Alh bayani akan mau kuma don Allah ku fada min abinda ke faruwa kun barni a duhu ?
Kara kallon juna sukayi sai babba daga cikin su tace bai maki bayanin kan auren yaran nan da aka daura yau ba bayan sallah jumma,a harda na salma aciki ?
A rude take fadi tana nuna kanta tana fadin yarana harda salma wace salma wai kuke magana ne ?
Salma dai nake dasu babawo yau an daura masu aure yanzun nan ma har gida ya fara cika da jamma,a.
Ta sake nuna kanta tana fadin ni ni Amina ni din nan Alh zaiwa sheri a idon, , , bata iya karasawa ba sai ta tafisu ta fadi a sumay.
Ihu suka saka suna kiran sunan ta ina bataji tayi suman gaskiya a lokacin don bata san wanda ke kanta ba.
Hjy maryam dake jiran taji kwam sai ganin yan uwanta tayi maza suna shigowa wurin ta da kwandunan goro da minti dasu chewing gun.
Tana kallon su da mamaki ta karaso falon tana fadin yaya kune tafe ashe ai wanan kwandunan ba a nan za a kawo suba don na yan shiyan hajiyace kayan .
Yayan su babba yace wanan na nan shiyan ne don kayan daurin auren ikilima ne da sadakinta yanzu aka bamu don karramawa mu shigo maki dasu nan.
Ikilima kuma yaya ta tambaya da sauri cikin tsure su da ido tana kallon su eh yanzu aka daura masu aure harda ita ciki ai.
Yau da safen nan yaje ya fada muna muma haka mukaji zancen daga sama wallahi shiyasa bamu tsaya neman ki ba don ba lokaci kamar yadda yai muna bayani din.
Ni ni Alh zaiwa haka ya tozartani a idon duniya maina aje yanzu na auren ikilima har nawa ikilima take ne wai da zai daura mata aure ban sani ba.
Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi a lokaci guda suka shiga bata hakkuri a wurin.
Sallah na idar naji ina bukatan kwanciya a kasan don yanayin jikina dake min ciwo a lokacin yasa na dan kwanta in huta.
Na soma barci naji murya kamar na baffa na suna gaisawa da mamu zubur na mike zaune ina kokarin tashi naji mamu na fadin yaya ashe kun iso ko ?
Yace eh maimuna mun shigo makare yasa muka wuce wurin daura auren baki daya don mota ya dan bamu matsala a hanya ne .
An daura yanzu alhamdullahi Alh yayi kokari har yara goma maza biyar mata biyar sai addua ake masa a gurin taron.
Tsaye nake na kasa karasowa gurin don jin maganan da sukeyi sai dai gaba ya fara faduwa ganin har da baban Atika a cikin falon da sauran fuskokin da ban iya shedawa a lokacin.
Baffa yana fadin banda abinda zancewa Alh sai godiya don har surukin namu an kirashi mun gaisa yanzu yaron kirki kamili mai mutunci baban su Atika ke fadi.
Huce na ke wanda ban san daga in yake zo min ba kafin na fara kuka in kai kasa a wurin jin faduwa na ya jawo hankalin su a inda nake suna fadin subahanallahi ku kamata.
Da sauri mamu ta isa gurin da mama suwaiba da ban san zuwan ta gidan ba suna fadin yaya haka kuma wani irin mika nayi na sake ihu mai karfi daya gigita kowa a falon take gurin ya rude.
Baffa yace subbahanallahi wanan matsalan ya taso ke nan na yatinyar nan wai dama haka abubuwan nan suke damun fatima ne yanzu ?
Wasu abubuwa kuma yaya mamu data gigice take tambaya tare da fadin bata da matsalan komai dama yau dai ne na fara ganin haka a gare ta ai.
Wanan matsalan ko a misau ya taso mata haka akasha fama da ita ranan har dare ana abu daya da yarinyar nan a gurin.
Mamu tace tau walllahi bata taba yin haka a nan ba gaskiya tunda tazo garin nan sai yau din nan na fara ganin haka gare ta.
Murde ni ake ana wani irin lankwasa ni da juyani guri daya sai mai kallona ya dauka bazan iya more jikina ba kuma a rayuna.
Fita tayi da sauri zuwa part din Amma suna zazaune ana mayarda yadda abubuwa suka tafi kamar yadda kawu da yan uwan shi suka tsara komai sai ganin mamu hankali tashe sukayi tana fadin gwaggo kizo ki duba sayadi halin da take ciki.
Gaba daya su mama hadiye suka mike suna tambaya ta kasa fada masu komai don hankalin ta dake tashe a lokacin.
Suna shiga falon mamu kowa ya tsaya da mamakin yana kallon ikon Allah abinda ke faruwa a falon lokacin salati Amma ta fara tana tafa hannayen ta a cikkn mamaki tana fadin.
Yar nan dama tana tare da mutantanin nan ne haka ba a sani ba sai yau ranan auren ta suka taka haka a kanta ?
Kowa na tsaye yana kallon ikon Allah shigowan kawu sani ya ce kawu balarabe ya kai su baffa masauki suci abinci kafin su juya.
Waya ya dauko yayi kiran wani layi baifi mintina ba wani mutum ya shigo saye da jallabiya fara a jikin shi .
Tunda ya tun karo inda nake wa yan nan abubuwan ya kura min ido har lokacin daya tsugunna daidai inda nake din kwance yace assalamu alaikum idan musulmine su amsa min muyi magana.
Sai shiru ba magana kusan biyu suka zagayo suna nasu sallon sai can akaiwa malam din sallama kamar ba muryana ba.
Ya amsa tare da fadin may ke tafe daku mai zaisa kuzo mata yau ranan farin ciki a gare ta kuma zumunci ya kawo yaran mu wurin ta don su nuna mata farin ciki.
Yace amma ai ba haka ya kamata ku nuna farin cikin ku ba gare ta ko yace kasan yaran zamani ba jin magana sukeyi ba sai dai nima nazo ne don in fadakar daku akan wanan baiwar Allah.
Tana tare da makiya a ko ina mun dade a tare da ita bama yarda wani ya cutawa rayuwan ta da can munsata rashin ji sosai da wasu abubuwa na yarinta.
Sai dai yanzu zan fada maku duk lokacin da kuka ganmu ku sani wani abin cutarwa ne yake harinta zamu taka duk wanda ya nufeta da sheri komai kankantan shi.
Dan murmushi malamin yayi yace Allah ne kadai ya isa ya kare bawan shi ga komai sai yayi dariyan manya tare da fadin ka manta Allah na sanadin sa ta ko ina a cikin wanan sanadin muna daga ckin kaddaran ta .
To idan ku musulmine don Allah ku bar boyar Allah nan ta zauna lafiya kunga yanzu tana gap da shiga sabon rayuwa ne .
Ya tare malam da fadin saboda hakan ne muke yawan biyanta wanan lokacin domin sihirin da ake kokarin aikowa gare ta .
Da kyat dai bayan sun gama kwasa da malam tare da jin abubuwa daga bakin su suka fita kaina tun lokacin na kwanta wani barci mai nauyi ban kara sanin inda kaina yake ba saida Amma har mamu suna kaina ranan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button