NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Zan iya cewa ranan mama hadiye da yaranta ne suka kwana cikin farin ciki a gidan bayan su ko wani part a ciki tashin hankali suke.
Part din hjy jummai ke asibiti da ita inda yaranta gaba dayan su suna asibitin sun zagaye ta cikin tashin hankali fuskan kowan su babu walwala a cikin sa ranan.
Sai shaga da fice suke a dakin zuwa office din likita uwa ke nan mai yafi uwa dadi a duniya.
Alh sani ma da yan uwan shi da farko sun dauki abin kamar wasa sai da sukaje suka iske halin da take ciki ne suka gaskanta girman maganan nata.
Zagi da diban albarka ga auren an shashi ga bakin yan uwan hjy jummai ranan duk wanda yazo da irin abinda ake fada saida wani baba a gare su da kawun su suka tsawata masu aka koma yi a boye.
Kawun yace may kuke nufi da zagin bawan Allah nan da kukeyi dashi da yayan shi zaku hanashi yin iko da abinsa ne ?
Wani irin mulki da nuna isa ne jummai batayi a gidan Alh sani ba har mutane na ganin ta koma miji shi ya koma mata sai yau da yafito ya nunawa duniya ya isa da gidan sa yanzu shine zaku zageshi.
A lokacin da yar uwarku take nata mulkin da nuna isa may yasa baku zage ta ba sai shi dayayi abinsa bisa kan ka,ida zaku saka shi gaba da zagi haka ?
May ye laifin Alh sani cikin yiwa yaran sa gata dayayi wanda ku duk nan baku sanda hakan ba sai gaba.
Ya fiku hange da tunanen nesa don yasan abinda yakeyi lokacin da dan ku ya dauko maku maidan buje may ye nan baku fada ba ga hakan ?
Sai yanzu da yake son nunawa duniya shidin mutum ne wanda ya isa da iyalin shi kuke kokarin hurewa yar uwan ku kunne ?
Shiru sukayi har su Aliyun su uku dake tsaye daga gefen gadon suna jin batacin da sukewa mahaifin su da sunan son yar uwarsu gare su.
Ya juya wurin su Aliyu yana fadin kunyi daidai don ku ba mata bane ubangiji Allah yai maku albarka ya kawo haske ga lamarin ku yaba abinda zaku kula da iyalan ku ta hanyar halal ya baku zuria dayyaba masu albarka.
Idon ko wanin su yayi ja don tashin hankali da fitina tsohon yace kunyi daidai kun nunawa duniya iyayye suna gaba da komai wayewan ido ba shine sanin duniya ba bin iyayye shine alheri.
Sannan ku idan kun san ba zaku taushe yar uwarku ba na rokeku Allah ku bar kysantan ta a wanan halin sai idan komai ya lafa.
Yana mai hade hannaye shi guri daya yake wanan maganan tare da bin kowa dake dakin da ido cikin bacin rai da kunan zuciya.

Ban garen hjy maryam ma yan uwa sai da suka taru suka taushe ta da kyat aka ciwo kanta ta hakkura tabar kukan da takeyi.

Ikilima ma kusan halin da nake ciki itama ta kwana ranan don su ko mijin ma ba wanda ya sani don koda suka tambaya akace masu sunan mijin dai nata Abubakar .
Ba wanda yasan wani Abubakar ne don Alh baya cikin hankalin shi ranan ba wanda yaga fuskan shi balle a zauna maganan.

A ranan su baffa suka koma bayan sun kara ganawa da Alh ya sanar dasu ba zamu kai lokacin daya diba na shagalin bukin da mata zasuyi ba don mijina yace yana da aikin yi can zai koma da wuri.
Don haka masu zuwa zasu iya zuwa gobe ko jibi za ai yinin bukin gaba daya a huta tunda komai da za a tanada dama an gama shiryawa.
Da wanan bayanin suka koma gida bayan ya kara bin su da alherin dayace angone da kansa yace a basu su kara namai a motar su.
Kowansu ya koma misau ciki da farin ciki da al,ajabin karamcin irin na Alh sani a zukatan su har suka kai suna hiran irin hayan wanan mutumin.
Mamu da su mama hadiye sunje asibiti duba hjy a cikin daren ta barmu da Amma dake zaune damu a part din yayin da ni ban san inda kaina yake ba saboda narcin da nakeyi.
Ba wani tarbon arzikin da suka samu don yan uwan hjy ne maza da mata tab a dakin gaida ita sukayi inda bayan hakan ba wanda ya kara bi ta kansu kuma.
Sun dan tsaya sukayi masu Allah ya sauwaka suka fito daga dakin a haraban asubiti suka hadu da yaran sun fito sallah isha,i suka tsaya suna masu yaya jiki.
Sukan sun amsa masu a cikin kulawa da nuna su nasune tare da tambayan ya akaji da taron jamma, a kuma dan dama habbib wanda tunda ya gaisa dasu ya koma daga baya kadan ya tsaya yana dakilan wayan shi.
A hankali kamar baya sauraren su har suka gama gaisawa suka tafi Aliyu ne ya fara magana gaskiya maimunan nan tafi mun hjy maryam mamace dai kawai bata son a fada.
Diba yanzu duk irin halin da ake ciki saida matar nan ta tako kafanta asibitin nan kai ma da ganin ta kasa akwai damuwa a tare da ita wallahi.
Humm ka manta mutumiyar mama ne sosai har dinki mama take muna tare da muna yara takance batayiwa bros kaya ba tare da hussainar shi ba.
Sai lokacin ya dan saki murmushi a gefen fuskan shi yana fadin daddy da mama sun raba wanan tagwaicin yanzu maimuna sarakuwanace can you imagine wai yau nine da auren yar maimuna ta cikin ta fa ?
Wata kanwar hjy ce ta katse masu dan hiran rahan da sukeyi ta fito tana fadin wai a kawowa hjy ruwa masu zafi daga gida yanzu.
Likita yace idan ruwan hannunta sun kare ta dan watsa ruwa ko jiki zai kara sake mata dan haka ne su Aliyu da habbib suka nufi hanyar gidan a wurin packing din motocine suka samu su mamu da motar mama hadiye yaki tashi suna fama da ita dole suka tsaya suka duba masu motar kusan a tare suka iso gidan.
Sai a lokacin suka tuna da babu kowa a part din sai kuma suka rasa yadda zasuyi dole gurin mamu suka nufa ta samasu shi da sauri tare da bada babban ktele din ta akai don bukata haka suka wuce suna zancen a mota.
Koda suka dawo sun samu hjy a zaune ana jiran dawowan su suna zuwa aka juye mata ta watsa sai data fito ne tana zaune ana zancen dora wani ruwan zafin ta kyala idon ta ga kytele din mamu tayi saurin gane shi don sunyi sababin don may aka sayo mata shi lokacin haihuwan twis da tayi a asibiti tace don may Alh zai saiwa maimuna electric ita kadai a lokacin.
Sai ga shi yanzu ktelee din yai mata rana itama bata damu da halin da take ciki ba ta lailayo ashar tana fadi ubanwa ya kawo wanan electric din nan, nan ?
Wani electric kike magana wanan ai su Aliyu suka zo dashi da aka bukaci ruwan zafi fada take sosai kannen ta suna bata hakkuri a daidai lokacin suka shigo dakin tako hausu da sababi tana fadin don may suka dauko mata kayan makiyiyar ta.
Tsayawa sukayi suna kallon ta da mamaki don basu san aka abinda takewa fadan ba haka sai daga baya suka fahinci abinda takewa fadan .
Bayani sukai mata tace da ba kowa a gidan ba sai kuje wani gun ba ku karbo min Ammani ko kayan maryam ba zanyi amfani dashi ba balle na maimuna.
Haba mama matan nan fa har rawan jiki take da sauri ta sa ruwa na don a kawo maki kuma har asibitin nan take wurin gaida ke.
A zabure tace makira algunguma tazo ganin halin da nake ciki ko don ta gani ko na kusa mutuwa ko yaya ance mata na fadi kasa warwas shine ta kwaso kafa tazo gani.
Aiko do wanan yarinyar bazan mutu yanzu ba don kawai inga bayan ta gobe dole ne babawo ya sake mata shegiyar yarta don duk bala,in da za ayi dole ne auren salma dana babawo ya mutu a goben nan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:12 – ????????????: YAHHAYU YA KAIYUMU BI RAHAMATILLAHI YA ASTAGIS

Dakin yai shiru ana sauraren ta kafin ta dago kai tace dawani sakaran mara hankali ya samu yaba salma shi don sai mara hankali zaiyarda da aure yata ba tare da sanina ba wanan wani dan iskan nemawai ?
Kowa ya kasa fada mata sai habbib ne yaja dogon numfashi kafin yace ba wani bane fa mama Ahmad ne yaron daddy.
Tayi saurin fadin wa iye tare da sakin wani uwar ashar kafin tace Ahmad, Ahmad dai almajirin mu kowa ?
Yace almajiri kuma mama Ahmad ai ya wuce a kirasa almajiri kuma yanzu.
Mikewa tayi tsaye lokaci daya tana fadin yanzu na gane kuskurena na auren Alh don wallahi Alh ya nuna baya kaunana ko kadan.
Amma zai gane kuren shi nayin hakan gare ni na fahinci nema yake ya tozartani a idon duniya kai yama gama tozartani din yanzu.
Saidai wallahi yayi karya don wanan auren basu dauro ba kamar an warware shi angama a wurina.
Haba mama ki kwantar da hankalin ki don Allah har ki samu lafiya mu yanzu lafiyan ki shine a gaban mu umar da tun shigowa shi kamar baya dakin yai magana cikin zafin rai ga mahaifiyar tasu a laron farko tunda ta tashi tana haukanta yana zaune yana dakilan wayan shi.
Cikin wani tsawa tace rufa min baki don na fuskanci baka son laifin mahaifin ku a fakaice idan ayi magana ka wani nuna damuwanka a kanshi duk zaku gane kuren ku na yarda da wanan bakin hadin da kuka bari akai maku.
Zaiyi magana habbib ya daga mai hannu tare da fadin bros mu tafi idan yin biyayyan data koya muna muyiwa mahaifin mu ya zama laifi a gare mu yanzu.
Yana fadin haka ya juya yabar dakin cikin zafin rai Aliyu bai tsayaba ya mara masa baya umar suka bari zaune ranshi inyai dubu ranan duk a bace suke mai.
Katashi kabi su kaima don banga abinda kake muna a nan ba tunda bakin ku daya da mahaifin ku na sani.
Umar ya sake dago kai ya dan kalleta kamar zaiyi magana sai kuma ya mike ya kalli yan uwanta dake tsaye cirko cirko suna kallon yace mama zan tafi sai da safen ku ya juya wuri ta yace Allah ya baki lafiya mama daga haka ya fice dakin shima.
Yana fita ta fashe da wani irin kuka Asma,u ta kalleta tace haba yaya bai kamata ki fito masu ta wanan hanyan ba gaskiya.
Ki tuna yaran nan suna maki matukar biyayya duk inda kika dorasu basu ketare wurin yanzu suwa mahaifin su bore a fili kike so may ye laifin yaran nan cikin maganan nan don Allah ?
Asma,u barni naji da abinda ke damuna Alh rayuwata yake nema tace koma dai may ye anty munsan irin halinda kike ciki don dukkan mu nan muna jin zafi amma yaran nan yadda kikai masu ne bai dace ba.
Tun dafa aka kawo ki nan bansa wanin su yasha ko ruwa da dadi ba yaya kike son suyi da ransu bafa don Allah ya dora mu akansu yace muyi masu yadda mukaga dama da rayuwan su ba.
Sai ki bisu a sannu tunda suma baki san kudiri su ba gagawa fa motar shedan ne anty.
Ta jefawa Asmau wani harara tare da fadin ke kika damu da hakan yanzu ban tausayin su tunda da sukazo nuna min sukayi basu san komai ba ai.
Asmau na jin hakan ta mike tana kallon agogon wayan ta tana fadin dare yayi anty mu zamu gida saidai da safe mu sake shigowa Allah ya baki lafiya.
Babu wanda ya tankata cikin su uku dake dakin ta mike ta fita abinta tana fita dayan tace ita asamau dama haka take a kan yara bata son ran daya baci.
Mikewa hjy jummai tayi tana fadin ni yanzu zaman may nake a nan yashe ga aiki nan ja a gabana ai banga zaman asibiti ba tunda naji sauki.
Ki dai bari zuwa safe sai a kara ganin yadda bp din naki yake kinga sai a neme sallama wirin likita zaifi.
Da kyat ta yarda da shawaran su sai zuwa safe zataga likita ya sallamay ta takoma gida da safe tunkan likita ya bata sallama ta salami kanta tana idar da sallah din.
Ita ta buga gida maigadi maigadi da bai dade da dawowa daga masalci ba ya bude masu kofa ta shigo da jidalin ta tana fadin.
Ina munafukan banza da wofin gidan nan ban mutu ba na taso do a hada baki aga bayana maiganin bayana sai Allah.
Yanzun za,a fara wasan tsakanina daku tunda haka kuke so duk wani tsohon banzan gidan nan da baiba da shawaran alheri na daina shayin maishi daga yau din nan.
Jin hakan da mama hadiye tayi yasa ta bude kofan part din su ta fito tana fadin tsofin banza na gwale kin barsu Amina .
Indai wanan ne ba a son ki ba a son ki din Amma dake zaune a kaina tun kare sallah na tana ban baki taji muryan mama hadiye tafito tace.
Hadiya idan nina haife ki ban yafe ki kara tankawa duk haukan da jummai zatayi a gidan nan ba.
Haka yasa mama hadiye komawa badon taso ba don ta shirya su cashe juna ranan da hjyn a gidan.
Kawu da bai dade dawowa daga masalaci ba yana dakin shi sama sallaya yana karatu yaji wanan hayaniyar nata zai fito ne yaji abinda Amma tacewa mama hadiye haka yasa ya koma bai fito ba.
Nan aka barta tana ta zage zage ita da yan uwanta a tsakar gida ba wanda ma ya bude part din shi ya kula da abinda takeyi kowa nasa ya ishe shi a gidan.
Ta kare da fadin duk uban daya daura aure diyan ta shi zai koma ya warware shi don ba wanda ya haifa mata diyan balle yai masu auren dole don an raina ta.
Alh dake daki ranshi ya gama baci yana son fitowa kalamin mahaifiyar shi ya hana ya fito sai mamakin irin kalamin da take sake mai shida yan uwanshi harda mahaifiyar su.
Hakana ya daure ya kyale ta saida ta shiga part din ta ita da yan uwanta ya tashi yai wanka ya shirya ya fara shiga wurin hjy maryam dake tare da yaran ta da wasu tsofi gudu biyu yan uwanta da suka kwana suna tausanta.
Sun gaisa dashi a ciki mutunci inda hjy maryam dataci kuka har ta gode tana zaune a kasan kafet ta dukar da kai.
Zai fita yace babba gobe idan Allah ya kaimu ne yaran nan zasu tare a dakunan nasu da naso sai satin sama ayi buki amma yanzu saboda wasu dalili an fasa haka gobe ne tarewan nasu.
Wani kuka hjy maryam ta sake maicin rai tana fadin ita bata aje komai ba bataba wani ajiya ba zai sa mata buki bata shirya yinsa ba.
Ya kalleta yai murmushi tare da fadin ina dai nine mahaifin wanan yaran ni kuma nasa bukina to ku barni da dabarana ku gani.
Tsohuwa guda tace Alh mu damuwan mu shine yarinyar nan tace bata san wanda aka daura ma yar nan aure dashi ba shine damuwan nata.
Yace babba wanan ba matsala bane don ni nasan wanda na zabawa diyana da kaina kuma haka tsarina yake idan an kaita zaku sanshi ai.
Allah ya kyauta matar tace yace amin ya fice abinshi ya barsu ta sake barkewa da wani kuka daga ita har ikilima din.
Part din mamu ya shiga ya samaysu falo zaune tare da Amma ya dan sake fuska saidai hakan bai boye mashi damuwan dake tare dashi ba har lokacin.
Kasa ya zube yana gaida mahaifiyar tasa ta amsa itama cikin yanayin damuwa a tare da ita take tambayan shi yaya gajiyan jamma,a yace Alhamdullahi.
Ya dago yana fadin hajiya gobe in Allah ya kaimu yaran nan zasu tare a dakunan su don na gama shirin komai saboda umar yace yana son zaikoma nan da jibi bakin aikinsa.
Haka yasa na mayar da tarewan nasu gobe idan Allah ya kaimu don haka nake son idan da wani shiri a bangaren mata sai ai min lissafi na bada komai ayi yadda ya dace din.
Tace gobe goben nan aiko dai kamar yayi kusa yace baiyi ba hjy idan kinyi la,akari da haukan da jummai ke nunawa gara ayi a kare komai kowa ya huta hakana.
Allah yasa hakan shi yafi alheri mamu da taji maganan kamar daga samane ta fashe da kuka da bata iya cewa na maynene ?
Kallon ta sukayi yana fadin ke kuma may ye abin kuka anan zaki sarewa yarinyar nan zuciya ne ko may kukanki yake nufi yanzu ?
Cikin karfin hali tace yaya naga komai fa bamu shirya ba kan tarewan nasu a bangaren mu yanzun kuma za,a ce wai gobe gobe ?
Wani shiri ne zakuyi ina ita fatima ba ko garin nan zasu zauna ba tafiya zasuyi don gudun hakane gaba dayan su nace su tare ga goben ai.
Nagaji da wanan tashin hankalin naku da kowa ke mun abinda taga dama a cikin gida kuna son daukana mutumin banza.
Ammace ta bashi hakkuri har ya bar part di mamu bata daina kukan da takeyi ba saida ya fita Amma tace gaskitan yayanku ne ai kukan ki yana nufin kina sarewa yarnan gwiwa ne.
Ki bata kwarin gwiwa da hikimomi muna mata da zai amfane ta don yanzu ba abinda ya rage tunda an daura aure ko.
Gwaggo har nawa sayadi take da za a dauke ta a wanan hali zuwa wani kasa mutumin nan bafa so yarinyar nan yake yi ba wani fuskan tausayi bai taba shiga tsakani su ba har yau.
Ahir din ki maimuna nace ahir din ki da furta wanan kalami ga yarki na karajin wanan a bakin ki nida kaina zan saba maki a gidan nan .
Ganin irin fushin da Amma tayi yasa ta fara bata hakkuri kan kuskuren datayi din nan dai amma ta kara sata a hanya daga haka ta mike tana fadin zama ba namu bane yanzu tunda tafiya ta canza sallo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button