NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Sam basuyi tsamanin shigowan shi ba a lokacin sun zube a falo sai cacakanshi sukeyi ga salma sai kuka take rusa ana mata huduban shedan.
Ganin shi tsaye yana sauraren su yasa aka hau kalon kalon a tsakanin su ashe duk fitsaran hajiya jummai da sauran shakkan shi a zuciyar ta.
Kallon salma yayi yace salma tashi ki shige daga ciki hjy zatai magana ya daga mata tsawa yace nace ki tashi ki shiga daga ciki.
Amma dai Alh kasan wanan abinda ka, , , , hannu ya dagawa hjy rabi data soma magana wace kebiwa hjy jummai gurin haihuwa.
Yace ban yi dake ba rabi ko kina cikin iyalina ne in sani tace banciki amma dalili ya kawo haka ai.
Yace to wanan dalilin ya tsaya iya ku da yar uwan ku banson ina magana da iyalina wani bare na saka min baki ki kiyayye hakan.
Wallahi ba zai yuyu ba hajiya jumai tace tana mikewa an tabamune dolemuyi magana wanan bakin auren wallahi yadda ka daura shi haka zakasa a warware shi yace dakyau.
Ya nuna mata kofan fita tare da fadin magana na yana nan har yanzu ina bisa bakana niko ko ki bar wanan zancen ko ki fice min daga gidan nan.
Hjy rabi tayi caraf tace don gidan ka zata bar maka gidan ka amma ka sani kaida kanka zaka nemay ta ai hjy ce kasan ta .
Suka mike lokaci guda suna fadin don an bar maka gidan sai may dama ai ba a gidan aka haifeta ba diya kuma bada su tazo ba.
Yace ashe kun san da hakan kuke son nuna min yadda zanyi da abina tace ko zan tafi da salma zan tafi bazan barta a nan ba kai mata dole.
Yace kiko tabbatar da idan kin tafi da ita ta tafi ke nan sai dai ki nema mata wani uban bani ba tunda kinfi gareta.
Salma dake saurare daga daki tayi saurin daukan waya ta kira yannen ta tana kuka cikin kashe murya take labarta masu abindake faruwa a gidan.
Kawu ya fice ya barsu a falon hjy rakiya tace lalai anty mutumin nan a shirye yake da ko wani irin mataki zaki dauka akan zancen nan don haka muyi hakkuri ku barshi a yadda yake so daga baya musan shirin da zamuyiwa zancen.
Hjy rabi tace gara mu nuna mashi muma muna da right din mu aiba shi kadai ya haifi yaran ba da yakewa mutane iko dasu.
Ke salma fito muje yayi abinda zaiyi din anty bata kara minti goma cikin gidan nan gidan shi din banza may ya aje a gidan banda tarin matan banza ko a hakan da yake ganin ya gama da ita akwai mai sonta wanda yafishi.
Shi inba ma aure mu kaddari ba har ya isa yace zai auri anty ne bakauyen banza dashi ma.
Ta kara kwalawa salma kira salma taki fitowa har lokacin hjy tace idan baki fito muka wuce ba sai na balbala ki a dakin nan idan na samay ki ciki.
Jin haka da sauri nafisa ta taso ta datse kofan dakin tana fadin kada ki bisu wallahi ba inda zaki tunda su basu ba mama sharawaran alheri.
Ranan salma tasha zagi duka fice suna bambami a kofan gida suka hadu dasu Aliyu da sauri ya fito mota yana fadin mama lafiya don Allah kada ki tafi ki koma daga ciki muyi magana.
Ba inda zan koma ai yunda Alh da bakin sa ya iya fadin in bar maigida yau ko gidan shi ya saura a duniya na barshi ke nan.
Har wanan yar iskan salma wai nace tafito taki fitowa din uban ta yace mama yi hakkuri mu koma amma fir hjy taki bin shawaran dan nata.
Tasa kai suka wuce da yan uwan ta a gaban Aliyu dake masu magiya basu ji ba haka yasa Aliyu din ya kira yan uwanshi yana fadin akwai matsala.
Shi umar har lokacin bai fito ba yana cikin dakin sa na gidan sa kwance ga dan aikin su ya gama abinci kari yana jiran shi har lokacin bai fito ba.
Sai dai ba barci yakeyi ba don basu dade da gama waya da merry ba da take mai korafin yaushe zai dawo ne har yana batun kai one week a wanan kasan mai zafi da sauro.
Shidai murmushi yayi mata yana fadin ai itama saukin abin asalinta ke nan daga kasan take gaba da bayanta .
Yace shifa yana ganin ma karshen ta Nigeria zai dawo da zama baki daya don ya gaji da zaman turai da yakeyi can tace saidai ya koma shi kadai ita kan bada ita ba.
Yana cikin tunanen hiran nasu ne kiran Aliyu ya shigo yana dauka ko gaisawa basuyi ba Aliyu ke fadin bros babu lafiya fa gida don hjy ta tafi.
A razane yace ta tafi ina kuma ?
Sun samu matsala da daddy ne ta bar gidan itada su Anty rabi innalallahi ya fada a zabure yace yanzu ina suka nufa ?
Ban san inda suka nufa ba a yanzu sun dai tafi yanzun nan yace shi daddy fa yana gidane ?
Ban shiga ciki ba Aliyu ya bashi amsa yace gani tafe idan nayi wanka habbib fa yana inane ?
Yana hotel na barshi yana barci salmace ta kirani tana fada min shine nayi saurin zuwa in hanata tafiya barin zo gidan kajirani a nan ka bugawa habbib waya mu hadu a gidan.
Mikewa yayi ya shiga wanka bai dade ba kamar kullun ya fito a gurguje ya shirya yafito ya samu an hada mai abin karyawa ruwan tea kawai ya iya sha ya fito.
Ya samay su a part din sun jima suna zancen da yan uwan shi inda yanuna bacin ranshi kan yadda yan uwanta basu bata shawaran kwarai kuma mahaifiyar tasu tana dauka.
Sun tabbatar da daddy su baya gidan haka yasa ya mike ya dan leka Amma don shi maganan ma da yan uwan nasa keyi kara bata mai rai yakeyi.
Ya shiga a yadda Amma ta ganshi yasata tambayan shi ko azumi yake ya zauna yana fadin may kika gani Amma tace au baka azumi zancen auren ne yasa ka ramay haka ?
Ko tsoron fadawa matarka an aura maka yar uwarka kakeyi yace tsoro kuma Amma akan may zanji tsoron wace nina ajeta ba ita ta ajeni ba.
Tace haka nake son ji namijin duniya kaida har yanzun kana da daman da zaka kara biyu nan gaba yace kai haba Amma ?
Kamar dai wani injin can may zanyi da mata har hudu haka please ni Amma ba wanan ba tace sai may ?
Kace tafiya zakayi da matar ka dan anajiran ka wurin aiki saudaki don Allah ka rike amanan yar marainiyar nan da aka baka a yanzu baka sanin dadin hakan sai nan gaba dadin hakan yana tafe da yardan Allah.
Naji Amma yace a gagauce yace yanzu Amma abinda su daddy sukeyi da girman nan nasu yayi daidai ke nan ace mama bata taba fita ba gidan nan tunda kurciyar ta sai yanzu da girma ya kama su.
Saudaki ina kake tunanen Amina zata a wanan shekarun nata wace keda kaman ku haka sakwa sakwa wani abu kuma ya rage masu banda hakkuri da junan su.
Amma mama fa bata gidan nan tunda safe wai daddy yace subar mashi gidan shi shine yan uwanta suka zugata suka fice din.
Kaga laifin yan uwan nata da ita dasu waye a gaban haihuwa ya kamata ace jummai tayi watsi da kishi ta kama gidan ta a hannun ta.
Yau da safen nan su suka tayar damu da tankiyar su ba irin zagin da batai muna ba yau ni na hana kowa ya tanka masu a gidan nan.
Kada mu zama daya dasu mu raba abin kunya wa jamma, a kaga koku ba zakuji dadin hakan ba idan mun biye masu.
Wallahi in ba yanzu da kazo kana wanan maganan ba ban san bata gidan nan ba sam don tunda na baro yar nan dana kwana da ita ba lafiya ban lekawaje tinda na dawo shiyan nan.
Bata nan Amma ya fadi cikin wani murya mara dadi yace ni nafi ganin laifin su mama rabi da suka kara zugata basu bata hakkuri ba ta zauna dakin ta.
Basu da laifin don jummai ai babban kantane yanzu wanda ya aje kaman ku mai ya rage mai ba hakkuri ba .
Bai jima ba ya mike yace zai fita tace ance jibi zaku tafi ko yace haka nake so Amma da yardan Allah indai an gama takardun yarinyar nan da wuri don nace Aliyu ya kaita ai mata idan wanda akai masu na umura ba zai fita ba.
Ke nan kai ba zaka tasa matar ka gaba kaje kuyi ba wanan wani haline kamar mutumin da ?
Yace idan kuma nai hakan kuce nayi rashin kunya ko Amma hakan kuma danayi yanzu ma ban tsira ba.
Yana fadin haka ya fita dama maganan ya ishe shi sun aje dasu Aliyu idan sun san inda mahaifiyar su take zasu je in ya dawo.
Ina nan kwance rijib sai ga Nafisa ta shigo part din mu tana wani daure fuska tace maman Fauziya wai Fatima ta shiya ta fito yaya Aliyu yana jiran ta a waje.
Ina zasu ta wani ya tsune baki tare da fadin ban sani ba yadaice in fada mata hakan, daki mamu ta shigo ina barci saman gadon ta taba jikina taji yayi sanyi.
Jin an tabani cikin barci na bude idanuna a hankali mamu nagani a tsaye kaina tace zaki iya tashi ga Nafisa nan wai Aliyu yana jiran ki a waje.
Nace a shagwabe mamu banda lafiya tace daure ki fita kiji may ke tafe dashi don ban son Nafisa ta gane komai.
Tana fadin haka tasa kai ta fita daga dakin ashe fadawa Nafisa tayi ina zuwa.
Ta dawo dakin dauke kaya a hannun ta tashi ki shiga ki gyara jikin ki da kyau ki kula ko yaushe banda zama babu kamahi sayadi kada ki bari wani yaji wari a jikin ki duk da nasan kinayi yanzu ya zama dole ki kara don kinga yanzu kina da miji.
Ina cije baki na tashi da kyat don bin umurnin mahaifiyata dake tsaye a kaina tace banda sanyin jiki ko yaushe ki kwanta wai ke baki da lafiya ko kina ciwo idan ba yakai intaha ba ki daure kinawa mijin ki aiyukan daya dace kiyi.
Ni dai ban tsaya ba na shiga bandaki naji muryanta tana fadin akwai humran wanka yana nan ida kin fito ki murza tundaga can ko ina a jikin kuma kiyi sauri kada ki saba da barin namiji yana jiran ki idan zaku fita.
Ni dai ban kula abinda take fadi ba na shiga nayi yadda tace ban dade ba na fito tana zaune tana mun kallon tausayi zuciyan ta ba dadi har na shirya ita da kanta ta rakoni daga kofan falon ta tsaya shi kuma yana cikin motar Umar zaune ina tafiya ina layi alaman dai banda lafiya har na karaso wajen motan na tsaya nisa kadan dashi.
Ya sauke glass din motan yana fadin ba saceki zanyi ba amarya angon ki ne yace a kaiki wurin pasphot yanzu.
A raina nace don pasphot aka tayar dani daga barci paspho din may kuma may zaiyi da pasphot dina ?
Bude min gefen shi yayi na shiga na zauna ina gaida shi ya amsa tare da tayar da mota muka fice daga gidan.
Ina jin shi na kifa kaina ga hannu na na hago fuskana na kallon window din motan yana canza kira,an dake cikin motan nasan neman waka yake ko wani abu.
Can yayi tsuki yana fadin mijin ki fa kamar ustazu yake shi bai damu da kida ba ko kadan tun farko haka rayuwan shi take.
Ajiyan zuciya na sauke na dan kalle shi ta gefe bance komai ba yace kinyi dace da miji mai hakkuri a rayuwan ki mudin zaki bi umurnin shi babu mai jin ku a duniyan nan.
Bros yafimu hakkuri sosai duk dakin mu yafi kowa saukin kai da hakkuri da mama don haka ina baki shawaran da ki bi mijin ki ki watsar da duk wani fitina da akayi a nan zakiji dadin shi sosai.
Shi mutum ne mai saukin kai maiba na tare dashi hakkin shi baida rowa sam sai dai matsalan shi shi bai son yawan surutu.
Zan baki shawara duk yadda ya nuna yana son zaman ku ki daure ki bishi a hakana don Allah zaki ji dadin hakan a gaba.
Ba ruwan ki da merry idan bai fada mata matsayin ki ba kada ki yarda ki fadawa merry komai a gamay dake har zuwa lokacin da zata gane.
Jin yayi shiru yana fakin yasa nace nagode yaya Aliyu yace ba komai ake kanwar muce ba zamu so muga wani abu ya samay ki ba kuma ki bashi girman shi sosai duk abinda ya hana ki kada ki yarda ki maimaita abin nan.
Daga haka ya bude mota yana fadi fito mu shiga ciki har lokacin ina tunanen a raina ashe haka yake in hakane itama Aisha ta dace da miji ke nan kamar yadda shima yake yabon dan uwan shi.
Office ne wurin kala kala ba zuwan mu na farko ke nan bax don mun gama school muje da daddy yace zamu raka Amma umurah kuma Allah bai nufa tafiyan yayi ba.
Yanzun kuma sai gashi na sake dawowa ke nan dai ina da rabon shiga jirgin ke nan harwa yau.
Anyi mun komai yadda ya dace muka fito muna shiga mota wayan shi na ringing ya dauka naji yana fadin gamu mun fito an gama komai sunce in dawo zuwa gobe da rana.
Yana aje wayan ya kecewa mijin kine yaga mun dade kila sai kuma yace yaya nagan ki haka kuma ko baki da lafiya ne ?
Banda lafiyane yaya na bashi amsa ina dora kaina a window mota har lokacin yace subbahanallahi may ke damun ki ko kema irin na mamane kan auren kike ciwon ?
Dan murmushi maganan shi ya sakani nayi murmushi kawai ba tare da nayi magana ba.
Maimako muje gida sai baga ya dauki hanyar gidan yaya umar din dan juyowa nayi ina kallon shi yace kada ki damu kanwata nasan abinda nake ai ba kaiki zanyi ba dauko shi zamuyi fita zamuyi tare.
Idan mun tsaya sai ki koma bay ina fatan bamu takura maki ba dai nace babu komai yaya nagode ya dan juyo yana fadin da may kuma ?
Ban iya bashi amsa ba har ya fita daga motar ya shiga gidan nikuma na fito na koma baya na zauna.
Ina nan zaune na hango su sun fito suna magana kamar kullun yau ma yana saye da kananan kaya a jikin shi bakar rigace da anini daidai damtsen hannun sai farin wando daga ksa da bakaken takalma.
Kodai ban sanshi ba da sosai zan iya cewa naga ya fada sosai ya danyi duhu kaina na kawar daga kallo su har suka karaso bakin motar.
Tun daga nesa ya ya kalli Aliyu yace yaya haka kuma baka kaita gida bane ko yaya yace na ratsene mu dauke ka sai mu wuce idan mun sauke ta.
Daga haka baiyi magana ba muna karya kwanan gidan muka hango motar daddy a wajen gidan.
Daddy ya dawo gida ke nan yace a waje Aliyu ya tsaya da mota na fito na barsu ciki bayan fitana Aliyu yace yarinyar nan bata da lafiya fa.
Yana magana ya balle mota ya fito ba tare da yayi magana ba sai daya dira kasa yace fito mu shiga muga daddy kafin mu wuce.
Koda nashiga su hajita maryam nagani ta rako wasu kawayen ta zasu tafi suka tsuro min idanuwan su na shige ba tare da na gaidasu ba don nasan gulmana akeyi.
Shigowa su ne ya hana suyi maganana kallon ya koma gare su ikon Allah shi wanan ma badamu ba uwarshi na can tana ciwo don auren shi .
Shi yana nan yana yawo da amaryan shi a gari lalai zamani kuwa maganan uwarshi ne an gama dashi sannu kawai sukace masu suka shige kai folon mahaifin su kai tsaye.
Sun samay shi yana shirin fita kuma yana ganin su suka tsayar dashi dole ya zauna suma suka samu wuri suka zauna a kasa.
Dan shiru ne kafin umar din yace daddy munji abinda ya faru tsakanin ka da mama da safe ya sai ya kara sunkuyar da kai cikin ladabi yace don Allah daddy kayi hakkuri mama ta dawo dakin ta.
Ya dubeshi da mamaki yace umar ai ban koreta ba zabi na bata kuma taga hakan yafi mata don haka ko jummai zata dawo gidan nan sai ta gane kuren ta tayi nadama.
Ku kankuma sai kunyi min alkawarin amincewa da zabina gare ku ba zaku watsa min kasa a idon duniya ba.
Zaku riki matayen ku bisa amana ba zaku wullakanta diyan mutane ba kamar yadda suma iyayyen su sukaga mutuncina suka bada su Amana.
Umar yace daddy ai kasan bamu taba maka musu ba ga duk abindaka umurcemu muyi yace na sani umar sai dai mahaifiyar ku tasha alwashin sai ta raba wanan auren danaku dana salma ga baki daya.
Har tana ikirari salma tafito su tafi da ita na nuna idan salma tabisu bani ba ita a duniyan nan.
Aliyu yai saurin fadin daddy abin baikai can ba ai su salma sun mayar muna da yadda akayi adaiyi hakkuri daddy don Allah.
Sun dan kara bashi hakkuri yace sai yayi shawara nan yake fada masu zancen tarewan matan su gobe don ba za a tsaya jiran komai ba.
Sun mai godiyan dole kafin su fito zuwa gidan da mahaifiyar su take itama su bata hakkuri kamar yadda suka ba mahaifin su din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button