SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Ina takure a dakin sai ga su Atika da murja sun shigo shigowan su ya dan sani sakin dan jiki na tsagaita kuka da tunanen ba,a sona da nakeyi.
A haka su manjo mama saude da umma su Atika da sauran suka shigo suna sallama gidan ne da shegen gima haka ya hanamu jin sallaman nasu lokacin.
Da tayake Addah tasan dakin ita ta kawo su inda nake ina ganin su na bata rai na bada baya waini nayi fushi muna cikin har akai sallah da isha,i muna ta hira manjo ke fada min ai nan zasu kwana tare dani.
Naji dadi hakan yasa na saki raina muna tsaka da hirane hjy ta fado dakin daidai an kawo muna abinci suna ci ina rabe gefen Manjo dake cin abinci da kyat.
Eyyah lalai har kunga gidancin abinci ko to ba mamaki andade ba a hadu an samu banza ai dole aci yanzu kamar mayunwata.
Hjy rabi ta karbe to keko anga gidan ci ba dole baje anacin dadi ba dole a baje talauci ba a nan ana kwasan banza.
To ba wanan ba kune matsiyatan yan uwan yarinyar nan ko wa kike da suna koma dai wa kike ke ya shafa.
Yadda kuka shigo gidan nan ku tatara kayan tsiyan ku, ku kwashi munafukan yar ku kubar gidan nan tun muna sheda juna daku a wurin nan.
Amma hajiya wanan kamar ba mutuncin ki bane a baka kuautan dan mutum baki gode muna ba sai ki zo da zancen Allah waddai.
Umman Atika ke fadin hakana daga inda ta kare sallah ke kuma a wa kike idan ma baku sani ba ku sani ni dai na haifi maigidan nan da cikina.
Don haka nace ba zai auri yarku ba indai nono na yasha a duniya aure da ita ya haramta gare shi.
Banga laifin Alh ba daya gargadaki ya nuna maki shi namiji ne aikai sha,anin nan salin alin ba zamu bar gidan nan sai idan shi mijin nata yazo ya koremu da yar tamu zamu fita ko minti daya ba zamu kara ba zamu fice maki gidan dan ki.
Addah ke bata amsa tace aiko zan nuna maki bana magana biyu yau ba sai dana yazo ba zaku kwashi tsiyan ku kubar gidan nan.
Nan suka fara cire gyalen su suna shiri fada kamar an jefo part din yace cikin tsawa haba mama wanan bai dace ba gaskiya.
Tsayawa tayi tana kallo shi kafin tace gara da Allah ya kawo ka yanzu maza ka saki yar kauyen yarinyar nan tun kan na saba maka .
Mama ku fito muje waje muyi magana do Allah tace ba ida zan tafi sai ka sakar masu yarnan yau yau ta koma masu gida.
Ya dukar da kai kafin yace ba zan iya ba mama amana take a gurina kamar yadda nayiwa daddy alkawari tun farko.
Ta juya da sauri wurin ya uwanta tana fadin may na fada maku dama na fada maku maimuna ta shanye shi tun farko.
To kaji da kyau ko ubanta ya baka amana saika saki yar nan yanzu ba ko sai na gusa daga nan ba .
Mama kiyi hakkuri don Allah ba zanyi hakan da kike so ba don wani dalilina .
Babawo kai da bakin ka kake fadawa uwarka hakan a kan wanan matsiyacin yarinyar da aka kwaso aka daura ma wahala.
Mama rabi wanan abinda kukeyi bai da kyau kuna zuga mama tana abinda bai dace ba don Allah kuyi hakkuri ku fita daga waje mayi magana.
Baza a fita nace babawo koni ko ita yau a gidan nan ka zabi daya a wurin nan.
Ba zai zabi kowa ba kawu balarabe ne yake fadin haka daga kofa kawu mustapha yace amma dai jimmai kinji kunya dakin santa.
Kin gama da gidan yarki kinzo nan suma zaki tayar masu da hankali don baki san ciwon kanki ba.
Mama rabi zatai maganaz ya daga mata hannu yana fasin malama ba dake muke magana ba don Allah.
Ku fice gidan nan in ba hala ba yanzu hukuma ta futar muna daku gidan.
Hukuma ai nafi son kuje ga hukuma ayita ta kare ba aamuje ko ina ba dole ki fita kibar gidan nan yanzu in ba haka ba zakiga ba daidai ba yanzu kin dai sanni ki san halina.
Sanin waye kawu balarabe tace kuzo mu tafi ai zamu hadu ku rubuta ku aje sai yar na tabar gidan nan.
Kamar yadda mutuwan auren ta yake daidai da mutuwan naki auren ba ke baki da wayau wallahi suka fita suna cacan baki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:13 – ????????????: ALHAMDULLAHI ALA QULLI HALIM, , , ,
Jirgin da nake mafalkin shiga yau gani cikin sa saidai bada dadin rai ba don da kunci da takura nake zaune a jirgin.
Kujeran mu daya dashi sai dai tun shigan mu jirgin danaji yayi ajiyan zuciya bai waigo inda nake zaune ba a hankali ina tunane da kewan gida bansan lokacin da barci ya dauke ni ba.
Barci nake sosai har bansan lokacin da na rankwafo kaina gare shi ba barin abinda yakeyi yayi ya waigo kadan yana kallo mm a gani yayi barci nake kaina a saman kafadan shi.
Baison ya tayar dani yasa ya aje wayan hannun shi ya barni ina barcin tare da sauraren saukan numfashi a cikin kunne shi a hankali.
Idanuwan shi ya lumshe a hankali tunanen abubuwan da suka faru a gida suna dawo mashi a rai daya baya daya.
Ido ya bude tare da danke hannunshi guri daya ba komai yasa shi haka ba sai tuna kalamin kowa a kansa kowa zaiyi magana sai ya furta umar ka rike amanan yar marainiyar Allah.
Ido ya kara runtsewa a ranshi yace may yasa suke daureni akan wanan yarinyar hakane ?
Shi wani amana a yanzu zai iya rikewa na wani yaro wanan ai wani sabo aiki daddy ya hadashi dashi ga yarinya karama haka under etheety.
Wani aure zaizo nan yayi da ita kawai daddy yace rainon ta ya bashi yau daba don daddy bane ba wani mahalukin daya isa ya dora mai wanan nauyin haka a kansa shida ko yarsa mimi bai tsaya ya kula da ita ba yaushe ne zai tsaya duba wata babba can.
Shi dai zaiyi kokari yaga ko yaya ya inganta rayuwan yarinyar kamar yadda daddy su ke son yayi din don alkawari ya daukanwa daddy.
Dan tabanin da naji anayine yasa na bude idona da sauri dan bansan na dauki awani haka ina barci ba lokacin.
Ba tare daya kalleni ba yace ki tashi mun kawo idan zamu sauka sai mun huta zamuci gaba da sauri nayi yunkurin tashi sai lokacin na farga a yadda muke.
Ganin ya tashi ya dauki yar jakkarshi yasa nima tashi nabi bayan shi muka sauko daga jirgin binshi kawai nake a baya don ya fini sauri banda lakkan da zan iya jerawama dashi lokacin.
Tsuki naji yayi lokacin da yake jan yar jakka na da mamu ta lodamin kayan amfanina a ciki wanda a lokacin ban san may ye acikin jakka bama.
Wani guri muka shiga bayan mun fito daga cikin haraban wurin inda naga dakuna a jere ya bude wani daki yace in shiga dakine mai nuna wurin hutawa gado da yan abubuwan bukatan daki.
Na zauna a bakin gadon tare da bin dakin da kallo aje jakkana yayi ya fice daga dakin har yakai kofa ya juyo yana fadin zaki iya watsa ruwa idan kina so ki dan huta.
Bayan fitan shi na mike tare da duban lokaci nayi ganin lokacin sallah yayi na shiga duk da bansan lokacin da kasan ke sallah ba.
Na dai gabatar da sallah azahar bayan na watsa ruwa a jikina sai dai ban sauya kayan jikina ba a daidai lokacin naji ana nocking din kofan dakin wani farin bature na gani tsaya yana dauke da abinci yace miss fatema na gyada mai kai ya shigo da abincin .
Bayan fitan shi na kalli abincin ba wani abincin dana sani bane saidai shinkaface kadan sai yawan ganye da tarkace a cikin sa wanda ban taba ganin irin su ba.
Kyaman ci naji da kyat na daure nakai cibi daya a bakina babu test din irin abincin mu na gida haka yasa na ture abincin gefe nasha lemo kawai na dan kwanta har lokacin banjin dadin jikina.
Wani barcin na danyi sai zuwa yamma muka bar kasan lokacin dare ya soma haka yasa na gyara kwanciyana a jirginn har ban san lokacin da aka tsaya ba.
Wani farar fatan mutum ne yazo taron mu da fara,a a fuskokin su suka shaking din hannu tare da dan ruguman hannun baya sun gama gaisawa da ya umar din sai mutumin ya juyo inda nake yana murmushi ya miko min hannun wai mu gaisa.
Hannun nasa nabi da kallo kafin in dago ina girgiza mashi kai nabi ya umar da dan kallo naji yayi saurin fadin oh Alex meet my sister fatema .
Yace kasa mu a al,adan mu bamu gaisawa haka da fata haramun ne yin hakan gare mu.
Juyawa nayi ina fadin kaga min dan iskan mutum kawai nayima kama da yan iska ne da zaka miko min hannu.
In kin gama kunkunin kizo mu bar wurin nan yace dani wanan mutumin ya saka kayana a mota don shi dagashi sai yar jakkar dake rataye a kafadan shi yake.
Bayan mun shiga motan ne yace dani a harshen hausa zaki nunawa kowa ke kanwatace a nan don su nan basu san matsayin mata biyu ba a wuri su.
Ina fatan kin fahinci magana har merry a matsayin kanwata zaki zo mata don a haka tasanki da farko.
Ina fatan kin fahince ni cikin dan basarwa nace naji ba tare dana kalli inda yake zaune ba na bashi amsa a takaice nima.
Jefi jefi suke kira da mutumin inda hankalina baya gurin su ina can ina kallon gine ginen da bantaba ganiba na ban mamaki.
Cikin wani unguwa motar ta dosa da kusan ginan gurin iri dayane ba zaka iya banbantasu sin tsaru wurin kyau kamar ba hannu ya kera ginan ba.
Ga furannin da suka kara kawata ginan duk wurin kamar babu kasa titine da grass carpet ko ina sai dogayen itatuwa masu tsawo da suka kara kawata gurin kamar kurmi.
Kofan wani gina motar ta tsaya nan naga suna kokarin fita daga motan haka yasani mayar da hankalina garesu daga kallon da nakeyi,
Kofan da nake gefen shi ya bude hakan yasa ni dauko dan handbag dina na fito daga cikin motar nima.
Kofan gidan naga ya nufa ya danna bell bayan dan wani lokaci sai ga wata mata ta bude kofan dan dukawa tayi cikin girmamawa tana gaishe shi ya amsa mata a daure yadda yake.
Ya dan taka ya juyo yana fadin oh sorry Greco meet my sister fatema zata zauna damu na dan wani lokaci a nan.
Wace ya kira da Greco ta juyo tana kallona tare dan fara, a a fuskan ta tana min sannu da zuwa .
A cikin girmamawa na amsa mata ta karbi kaya a hannun Alex ta fara ja muryan merry ce dake saukowa take mashi sannu da zuwa.
What sister in law in this house ta fada a cikkn mamaki bayan munyi arba da juna da dan saurin ta ta karaso gareni tana rungumay ni.
Nima rungumay ta nayi yayin da ta sake ni ta juya gare shi tana fadin wani abin mamaki kai mun hakan a bazata.
A daidai lokacin ta sake ni naji tace let me guest you name tana tunane sai can tace fatem yeah fatema am i right ?
Tana dan dariya yayin da naga ta mikawa Alex hannu kamar yadda ya bukata dani da farko suka gaisa.
Yace cikin dakewa she is here for schooling wow sister inlaw will stay here with us ?
Bai bata amsa ba ya wuce naga ya nufi hanyan hawa sama ina tsaye ina binsu da kallo mutumin nan ne yace kinsan Omar suna da kyau family su sosai ganin sister din shi na gane hakan dariya tayi naji ta kwalawa wanan matan na farko kira sai gata ta fito da sauri wani hanya tace take her to her room .
Matar ta juyo gare ni tana murmushi tace muje ta nuna min dakin da zan zauna .