NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Hjy maryam motar mu na dagawa ta koma part din ta a cikin kunan rai zubewa tayi saman kujera tana haki kafin ta furta shi ke nan.
Yanzu ana nufin yarinyar nan taci gaba ke nan ko may yanzu yaran mu da suke diyan gata an zube muna su nan a wullakance sun kare ga auren yaran shago yar agolan gida ta aure umar.
Alh bai muna adalci ba a rayuwan mu Allah ya cuta ma rayuwan yaran nan da sauri dayan matan tace ki bar fadin hakan ina hanin ki da furta kalami mara kyau ga auren yar ki.
Kinsan abinda gobe zai iya haifarwa gare su shifa ya haifi diyan shi yasan abinda yakeyi ko kin taba ganin inda mutum zai mayar da danshi baya a duniya ya fifita dan wani.
Shiru tayi badon ta yarda da zancen yar nata ba taci gaba da kada kafa Allah kadai yasan irin tunanen da takeyi a ranta.
Wayan ta dake gefe ne yayi kara ta kasa kallon wayan balle ta daga sai sadiyace tace mama wayan ki na kira fa ta juya ta kalli wayan a lalace tana duban sunan dake kiran wayan.
Gani hjy babba a screen din wayan ta fisgi wayan da sauri hannun sadiya tana receiving.
Tana dauka hjy jummai tace maryam kin ban mamaki koda yake ba abin mamaki bane don kishiya tayi farin cikin barin kishiya gidan miji.
Ace wai maryam baki kirani ba tun da nazo nan ke nan kins farin ciki da barina gidan kema dama nasan zakuyi murna na matsa na baku wuri kuyi yadda kuke so a gidan.
Haba yaya wanan abin fa bulalan hanyane fyadi yaro fyedi babba Alh yai muna bake kadai ke cikin wanan hali ba don kowa a gidan nan an fyede shi.
Haka dai nake ji daga baya wai har Ikilima ashe a cikin auren ita kuma wani dan kaddaran ya ba ita don duk wanda ya karbi auren yaran mu akan ganganci ne sai ya sako muna diyan mu.
Daga kai tayi ta kalli yarta dake tsaye suna kallon ta tace uhumm sadiq dai na shagon kware da kika sani.
Hjy tace sadiq sadiq dai wanan miskilin yaron da bai damu da mutane wanan yaron dan jin kai da fadi rai ?
Wallahi shi kuwa yaya shi ya hadata dashi yayi son ranshi ga yaran mu kamar bashi ya haifi abinshi ba.
Amma ita yar son agolan shi ya hadata da danshi inda yasan zata huta yanzun haka mun dawo daga rakiyan sune sun tafi kin san yau suka bar kasan ai.
Wa ya bar kasan kike nufi tace su umar da yar nake nufi mana .
Wai kina nufin dai babawo nawa kowa hjy maryam tace wai baki san da tafiyan su bane ko may cab ai sukan yanzu hakama jirgin su ya daga yabar kasan nan watakila.
Dif taji ta kashe waya bata kara kallon wayan ba ta wurga gefen kujera tana cewa yannen ta ashe uwar ma bata san da tafiyan su yau ba ke nan ?
Ni dai ina horon ki da kikama bakin ki mijin ku kin san yayi kokarin kan yaran nan don ba duka maza zasu tsare maka haka ba maryam.
In kinyi duba mutumin nan fa gata yayiwa yaran shi a fakaice a yanzu baku gane hakan gare ku sai nan gaba halin dattakone iri na mutanen da kega maigidan ku wanda mutanen yanzu ke ganin shi wani abu na daban.
Uba ko ince iyayye sukeda hakkin zabawa diyan su abokan rayuwa na gari amma boko da zamani ya sauya muna al,adan hakan.
Inda ada can baya ne ko kaka yana iyayiwa jikokin shi hakan ko wani daga cikin yan uwan shi yai bugun gaba ya aiwatar da hakan kuma a zauna lafiya babu mai korafi kan hakan.
Amma yanzu shida abinshi kuna son nuna mai ba isa da kayan shi ba shi kuma ya nuna maku ya isa da gidan shi.
Kuma yayi dacen samun diya na gari daga mazan har matan ba wanda ya musa mai kan hakan.
Har ita agolan nashi da kuke ganin yaiwa gata kunsan yanayin da uwarta take ji ne kan hakan babu wata uwa a zamanin nan da za ai mata haka da yarta taso a ranta.
Amma da yake tanada wayau bata nuna hakan yai mata zafi ba ta dake ta daure rabar abin a ranta kinga kenan darajanta saiya hauhafa a gare shi.
Shine kema nake nuna maki hakan don ba karamin daraja zakuyi a idon shi ba ya sakaku kun bi umurnin shi.
Yanzu ita hjy data bijire masa mai hakan ya haifar gareta gashi anyi din kuma bata gidan ita da kanta ta dabama cikin ta yuka duniya sukaji ta.
Da tabishi a sannu sai ayi abin salin alim ba wanda yasan abinda dake gudana a tsakanin su amma yanzu mai hakan ya haifar a gareta ?
Danka har yabar kasa da matarshi ke uwa baki da labarin hakan yanzu ai duk inda take wanan labarin tafiyan da taji tana can hankali a tashe.
Don haka ki natsu kiwa kanki fada tun baki barar da darajan ki da yake gani a idon shi ba har wani dadi kikaji wurinta da zata wani neme shiri dake don kawai ta dinga jin sirin gidan a bakin ki.
Idan magana ya fito kiji kunya ya dauka kina ha,intar shine da iyalin shi kece ke kawo rashin zaman lafiya gidan tunda keke tsegunta mata komai.
Sauran sukace wallahi hakan ne zai faru shiru tayi tana nazarin maganan da suke fada mata.

Hjy jummai tana jin abinda hjy maryam tace ta kashe wayan zabura tayi zuwa falo suka hadu da yayan ta yake fadin lafiya dai maryam tace yaya ni yaran nan zasuyiwa haka ?
Sai ta fashe da kuka ta kasa magana hakan yayi daidai da shigowan su hjy rabi a lokacin don nasu iya zama a gidajen su saboda abinda suke kullawa a tsakanin su na ala dole sai sin raba aurarakin nan don manufan su ya cika.
Da mamaki suka karaso falon suna tambayan abinda ke faruwa ta kasa fada sai kuka take tana aikawa umar zagi da kyat ta iya buda baki tana labarta masu abindake faruwa.
Murya sukaji daga bayan su ana fadin kwarai nine nan na tursasa ma yaron wucewa a yau don wanan irin shiririta naki da hauka da kikeyi.
In banda lalace da maida kai baya kin taba jin wanan haukan da kukayi jiya uwa ta dauki kafanta zuwa gidan auren yayanta tace wai sai an sakar mata diyanta ko sarakuwanta ?
Jummai na rasa inda hankalin ki da wayauki ya shiga a yanzu yara suna iya kokarin su suga kun zauna lafiya da mahaifin su amma ke kina kokarin kara bata abu.
Yaran nan don farin cikin ki a gidan uban su suke wanan abin don sharudan da mahaifin su ya kindaya maki.
Amma ke tunanen ki da hankalin ki ya kasa gano hakan jiya suna gidana da dare ni nan da yayan ki gashi nan muka tilas ta mai ya dauki matarshi su bar kasan nan suje nesa dake inda ba zakiji duriyan su ba har zuwa lokacin da hankalin ki zai dawo gareki.
Umar dane na gari don a daren jiya yayi niyar sakin yar nan idan haka kike so shiya saba da ubansh.
Mu muka hana su yin hakan don barin su aikata hakan abinda zai haifar yafi wanan haukan da kikeyi yanzu karshenta ma ku rasa Alh ga baki daya kinga waya kashe shi bakin cikin ki dake da yaran ki ya kashe masu uba.
Kina ganin yaya zasu daukeki daga baya idan haka ya faru dasu bafa zasu yafe maki ba jummai don diya ma suna da hakki akan iyayyen su suma.
Don haka nina tilasta mai dole a yau ya bar kasan nan tunda dama komai na yarinyar a kammale yake mahaifin shi ya gama shirin tafiyan su kafin ya aiwatar da komai.
Don haka ina rokon ki jummai ki bi abin nan a sannu kada rabo ya kashe ki idan ya rantse don idan kin matsa da wanan fitinan Allah na iya daukanki cikin wanan halin kowa ya huta.
Dago kai tayi ta kalle shi tun lokacin daya fara magana a falon yace kwarai kuwa rabo yana kashewa yana rayawa idan ya ratse.
Allah ana mashi dolene kamar fa kina jayaya da hukuncin ubangiji ne hakan da kikeyi.
Kince baza ayi ba anyi din da ranki da lafiyan ki kin gani kuma ba yadda zakiyi.
Kawu tana da yadda zatayi kan tunda ita ta haifi diyan ta ba shi kadai keda iko da su ba ai hjy rabi tace mai.
Rufa min baki mara kunya dama zan dawo gareku ai duk wanan abin dake faruwa da jummai da zugin ku takeyin shi.
Yar uwarku na cikin wani hali mara kyau maimakon ku bata shawaran kwarai a zauna lafiya sai ku buge da zugata ta bar dakinta ku kuna zaune naku dakunan kalau.
Ashe wanan zumuncin munafuncin zamu samay shi a cikin zurianmu kawu kamar yaya munafunci ya dakatar da ita cikin daka mata tsawa yana fadin ke rabi ki fice min daga ido har yanzu ina nan ga Adon da kika sannin a baya.
In ba munafunci ba da wani manufa naki zakiga yar uwarki na aikata ba daidai ba ki kara zugata yanzu da tazo ta zauna nan gidan dan uwanku shima so kuke ku kashe mashi nashi auran.
Tun wuri jummai kiwa kanki fada ki koma dakin ki kibar biyewa rabi da wanan mai kamar sunlobiya suna kara rikitaki don kyashi da hassada da ta dora a zuciyar ta.
Don haka yau din nan zamu je mu zauna da Alh sani yayi hakkuri ki koma dakin ki zuwa dare kuma kada naji kin muda mashi kan wanan zancen kuma.
Yaran ki sun san abinda sukeyi kuma suna da biyayya kwarai don sun zabi farin cikin ki sama da nasu ke kinfi kowa sani badon sharadin Alh ba gareki ba babu yadda za,ayi su karbi auren da basu shirya ba.
Yayan musa yace kwarai kuwa kawu don kawai suga iyayyen su a tare kowan su ya hakkure ya rugumi kadda ke kanki kin sa da ba haka ba umar da habbin ba akai masu can ba don taurin kan su ke baki la,akari da hakan.
Shine har zaki zauna kina shirin yiwa diyan ki baki akan sun zabi farin cikin ki a zauna lafiya su da mahaifi su ?
Kiyiwa kanki adalci da yaran ki idan kin masu baki suka lalace kanki kika zalunta jummai ba wani ba don kowa albarka yake sakawa nasa kullun da fatan gamawa da duniya lafiya.
Kawu yace fada mata dai dan albarka yayan yace ku kuma kada kuce ko bamu gane manufan ku bane kallon ku mukeyi sarai.
Munki magana ne muna kallon ko zaki gano manufarsu a kan diyan ki ki barsu sai dai kassh baki da niyar gano hakan har yanzu.
Nikan yaya kun tsaneni akan zancen nan wani manufa nake dashi akan antyn mu yace ki cusa yarki ga umar ko habbib dasu basu san kina yi ba har uwarsu din.
Kukan munafunci ta fashe dashi tana fadin an mata kage indai haka suke dauka tabar zancen koma tayi hakan ai ba laifin bane ta karasa fadi tana mikewa tabar falon.
Kawun yayi murmushi yace kingani rabi bata da gaskiya harke Rakiya kin san komai amma kika kasa haskawa yar uwarki hanya.
Shin in kun rabata da dakinta ko iyalinta ta zauna muna haka a gida riban mai zakuci in yar ku ta kaso auren ta da girmanta ta dawo gida ta zauna muna.
Hjy rakiya tace kawu ba haka bane ni naga ai duk gidane wa zanki wazan bari a cikin su amma Rakiya baku kyauta min ba hjy tace.
Ku barni inji da abinda ke damuna mana yake gabana mana na fada maku hakan bamai yuyuwa bane tun farko da kuka nuna min hakan ai.
Yanzu dai kyawa kanki fada Asma,u karamace a cikin ku amma ta fiku wayau da sanin ya kamata.
Don da ita muke komai a tsanake tun tasowan wanan magana itace tsaye ta bangaren ki ita taje ta zauna da yaran nan a madadin ki gidan.
Hawaye ta soma tana fadin da wani zanji yanzu da yaran da na kasa fahintar su ko da Alh da ya nuna min dani da babu duk dayane a gidan sa ko da abinda ku yan uwana kukai min ?
Yanzun dai a bar wanan zancen mu samu ki koma dakin ki ki zauna cikin iyalin ki shine mafita a garemu yanzu.
Ita gurin ta yanzu bai wuce taga ta koma dakin ta ba kamar yadda kawun nasu ya fada in yaso daga baya sai ta san inda ta bulowa zancen.
Don har yanzu bawai ta yarda da auren umar da salma bane a cikin ranta don ba zata yarda ta hada zuri,a da fakirai ba tana ji tana gani.
In ma auren zaiwa salma ai bata rasa masu sonta ba da aure amma ace wai yau almajirin su shine a matsayin surukin ta haba dai damay duniya yai kama ?
Hakama ba zata taba yarda da saka fatima a cikin dakinta ba nan gaba ta zamo mata annoba kamar yadda uwarta ta zamo masu yanzu.
Yadda kawun nasu yace haka ya faru sun samu Alh da sun bashi hakkuri yace shi baida matsala fa indai ta amince da bukatan shi a zauna lafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button