NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Salma bata samu ganin mijin ta ba sai washe gari da baki suka watse a gidan, gidan ya rage sai ita da kawayen ta biyu da suka shigo mata su suka tayata gyara ko ina na gidan bayan tafiyan bakin .
Har suka tafi Ahmed bai shigo gidan ba sai wajajen sha biyu saura na dare tana zaune a dakin ta taji motsin shi ya dawo yana rufe gida.
Dakin shi ya nufa saida ya watsa ruwa ya fito ya dade a falo tana jin motsin shi sai can ya nufo dakin nata.
Kamar yadda yai tsamani zai samay ta hakan ya samay ta kwance a takure a guti daya ya tsaya daga kofa ya karewa yadda take kwance kallo.
Har zai juya ya fita daga dakin ganin tayi motsi yasa shi dan dakatawa yana fadin baki barci ba ke nan ki tashi ina falo ki samay ni.
Ya dan jima da fitowa sai gata ta fito tasha uban kwaliya sosai kallon ta yayi ya kawar da kanshi gefe daya.
Karsowa tayi cikin falon ta dan tsaya nisa dashi kadan ya nuna mata kujera da hannu shi alaman ta zauna.
A takure ta zauna din ya dan dauki lokaci kafin yace salma kike ko don ni kin san ba sanin sunan ku nayi ba sosai musaman yaran dakiku din.
Dago kai tayi tana kallon shi da mamaki yau ita Ahmed zaice bai sani ba mutum da kusan ko wani sati yana gidan su do yin wani abinda ya shafi gidan.
Yace kina mamaki na ko kada kiyi mamakin hakan don ba abin mamaki bane.
Tun lokacin da hjyn ku ta nuna bata sona tare da Alh na tsani duk wani dan dakin naku.
Din na lura kuma baku son kowa ya rabi Alh don wani tunane naku can na daban yanzu dai va wanan ba don kinci albarkacin mai albarka a wurin na.
Ina fatan kin san gidan wanda kika shigo ma,ana kin san ko waye Ahmed dan almajiri kamar yadda hjyn ku take fada ko yaushe.
Kamar yadda kika sani sunana dai Ahmed din idan kinga dama zaki iya kirana da Ado Almajiri kamar yadda kuka saba da shi bai taba damuwana ko kadan.
Don Almajiri ma mutum ne mafi daraja a wurin mutanen da suka san hakan irin su Alh namu don yasan daraja da mutuncin amajiti kai ba almajiri kawai ba Alh yasan darajan dan adam da ace yaran shi zaku kwaso halayen shi da gidan ku ya zama gidan kwatance a gurin tausayi.
Naso ace fatima na aura kamar yadda naso ta tun farkon ganina da ita a gidan Alh badon saboda komai ba don halin mahaifiyar ta dana sani kyawawa.
Hjy maimuna mutum ce da tasan yakamata da badon nasan kan gidan Alh ba sai ince uwa daya uba daya ya haifesu ita da Alh din.
Dago kai tayi ta kalle shi a karo na biyu yace yes nasan zakiji zafin magana na sai dai yana da nasaba da abinda yasa na zaunar dake nan yanzu.
Da farko naso yi watsi da zance auren ki dayazo min a bazata lokacin da nake jinyan rashin fatima a gare ni sai zancen auren ki yazo min kwatsam da rana tsaka banda labarin hakan.
Da ace wurin da zan iya gardama ne da na hutar da hjyn ku da tazo gida tana min cin mutumci data san abinda ke raina da batazo ba a lokacin.
Hawaye ta fara don tasan komay ya fada mata taci hakan agare shi don ita kanta kafin hankali yazo mata hjy tasha turata tai mashi rashin mutunci.
Dan murmushi ya sauke dayaga tana hawaye yace a yanzu kan zaki iya fidda hawaye son ranki sai dai ki kwatar da hankalinki don Ahmed ba maci amana bane ko maimanta alheri don kinci albarkacin Alh da darajan shi a gurina.
Ba zan taba kallo ki da ido cin amana ba saudai ina fada maki abindake zuciyana ne a yanzu don ki fake sharudan da zan fada maki.
Dan sanyi salma taji a ranta don jin kalamshi yace na karshe yace ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada maki idan kin kiyaye mu zauna lafiya idan baki kiyayye ba mu saka kafan.wando daya dake don dai kin san auren mu babu zancen saki a aure mu.
Ns farko dole ne gare ki ki tsabatace gidan nan tunda safe idan gari ya waye haka kuma zaki hada mana abin karyawa kafin in fita karfe tara na safe.
A ka,idan gidana ban daukan yar aiki matata itace zatayi mun komai daya shafi rayuwan mu don ta dorawa yarana tarbiyan daya dace.
Fuska ta bata don antabota soai yayin da tabi fadin gidan da kallo yace yes haka ra,ayina yake don kinsan ni da kauye ne..
Haka kuma ya zama wajibi gareki ki kare min mutuncin ki yayin da zaki fita ko wani bakon namiji zai shigo a gidan nan ko wanene kuwa.
Yasan halinta na rashin son saka sutura masu rufe tsiraici yace wana ke nan ki sani ba a fita ba tare da izinina ba ko nan da kofan gidane.
Ki tabbatar da bakin da bn aminta dasu ba kada in gansu a gidan nan don ban zama mutumin banza a gari.
Ban son barnan abinci zaki iya dafa duk abinda zuciyar ki ke so a gidan nan muci haka kuma idan kina da ra,ayin wani abu zaki iya fada min kafin lokacin fitana ban son sai abu ya kare ace za a fada min.
Ban yarda da yada sirin gidana a gurin wani na wajeba ko waye sirin mu sirin mune iyamu duk ranan da naji wani zance gidan nan a waje ki kuka da kanki don banda dadi idan an taka min doka.
Idan kinbi tsarina mu zauna lafiya dake a gidan nan zaki iya zuwa ki kwata don dare yayi yanzu Allah ya bamu alheri ya mike yana kokarin kashe kayan wutan dake falon.

Gidan ikilima yan uwa da abokan arziki sun watse kamar yadda al,adan buki ya tanada gida ya rage saura ita da kanwar ta.
Ana sallamay isha,i abokan nan shi suka rako shi gidan sun samay su a falo suna hira don ba wani wayewa sukayi dashi ba sosai.
Daki suka koma da sukaji hayaniyar su tafe shida kanshi ya shiga ya kira su don suyi sallama da abokan shi dake son ganin ta.
Ba laifi don ta dauki dan haske kawu sun dan masu nasiha da shawarwari yadda ya dace da zasu tafi suka aje mata alherin da sukazo mata dashi.
Mikewa sadiya tayi tace itama zata tafi yace su sauke ta a gidan su ya dan jima bai shigo ba sai can ya shigo ya rufe gidan.
Ledadojin daya shigo dasu ya mika mata fuskanshi a daure tamau don shi mutumne da baida fara,a ko kadan baida yawan surutu.
Yana mika mata ya fice dakin tun lokacin bata kara ganin sa ba sai safe da zai tafi masalaci ya tayar da ita ta hanyar bubuga mata kofa.
Ya wuce bai shiga gidan ba sai dai har ya dawo baiga alaman ta tashi tayi sallah ba balle ta fito gyara gidan .
Har karfe takwas saura ya nufi dakin ya buga ta taso da kyar tana ya mutsa fuska ta bude kofan shi ta gani tsaye ciki hade fuska yace ke kinyi sallah kuwa ?
Bansan gari ya waye haka ba ta bashi amsa cikin rashin damuwa da abinda ta fada yace a dan hasale ke wata irin mara hankali ne ?
Sallah asuba kice baki san lokacin yinsa yayi ba bari kiji ban daukan wanan shashan a gidan nan ya zama maki na karshe duk lokacin sallah yayi bakiyi sa a lokaci ba sai na saba maki.
Ki shige kije kiyi sallah tun kan na saba maki ya juya yana tunane a ranshi lalai mahaifinsu ya fadi gaskiya suna da aiki sosai a gare su gamay da amaren nasu.
Bai yarda ya sake mata fuska ba ko kadan hakan yasa ta shiga tsoron shi don umurni yake bata gashi gidan shiru ita data saba da yawan surutu a part din su suna hayaniya da uwarsu da yan uwanta ko yaushe.
Wanan zaman shiru din ya fara damuwan ta da zaran ya shigo zata fito daga dakinta tazo ta zauna falon saidai suyi zama kaman kuramay ita dashi bai mata maganan komai har sai ta gaji tayi magana ya basar da ita ba amsa don haka halin shi yake shi a rayuwan shi.

Gida;rakiya da habbib an gama komai kamar yadda ya dace gidan ya koma shiru dama shi bawai yasan rakiya bane don da dare suka taba haduwa da daddy ya matsa masu sai sunje sun gana din.
Ko yanzu a gajiye ya shigo gidan ga haushin da takaicin abubuwan dake faruwa a tsakanin iyayyen nasu a lokacin tare da tunanen wai yau shine da aje macen da baiso a gidan shi.
Ya shigo ba tare da sallama ba don gidan ba kowa ita kadaice a zaune a falo tana kallo cike da tsoro don babu alaman motsin kowa a gidan.
Ganin shi tayi murtun da fuska haka ta daure tare da dan mikewa tsaye tana fadin sannu da zuwa yaya tana dan dariyan yake .
A dakile ya kalle ta sai dai bai taba tsamanin haka rakiyan take ba a fili yadda ya ganta yanzu tasha kwalliya kyawon ta na diya mace ya fito sosai a fili.
Duk da haka yayi kokarin hade mamakin shi wurin amsa mata ciki ciki ya nufi hanyar daki shi ta bishi da dan kallo tana murmushi kasa kasa don tasan abinda suka shirya da mahaifiyar ta.
Ya jima a dakin shi tana zaune bata shiga daga ciki ba sai can gashi ya fito da alama wanka yayi duk dadewan da yayi a dakin.
Yana saye da three quater wanda da yar riga armless yayi mamakin ganin ta a inda ya barta zaune har lokacin.
Yana fitowa ta sake fadin barka da fitowa yaya ya gajiyan taro wanan karon da mamaki ya amsa mata rashin zuciya irin nata.
Zama sukayi gaba daya falon ba wanda yai magana a cikin su sai habbib da yazaro wayan shi yana kiran dan uwan shi yaji ko sun sauka lafiya ?
Sai dai layin bai shiga ba a lokacin haka yasa shi jan guntun tsuki yana wani layin ya kira saidai wanan karon mace ce yakira da wayan nasa.
A yadda take jin suna magana cikin tausassa murya ta fahinci akwai soyayya duk da da harshen turanci suke magana.
Rakiya dake zaune duk da taji haushin cin fuskan dayai mata din bata yarda ta nuna hakan ba gare shi.
Tasan dama don ya musguna matane yake waya da wata mace a gabanta don taji haushi kuma gurin shi ya cika taji haushin saidai ta yi kokarin shanyewa.
Sai da ta bari ya gama ya dauki remote yana chanza chanel ta kalle shi ta mike tana fadin sai da safe yaya .
Ya kalle ta cike da gadara yace ke a gidan ku ba a koya maki tarbiyan ba miji ko ruwa bane ?
Ta dan murmusa tana gyara gyalen ta kamar bata damu ba tace kayi hakkuri yaya na dauka ai ba zaka sha ruwa yanzu da dare bane ?.
Cikin takama yace kinga inba zaki debo min ba kada ki cikani da surutun tsiya don Allah doluwa kawai dakikiya .
Allah ya baka hakkuri tace ta nufi gurin da fridge din yake ta dauko goran ruwan da yayi raba har ya gaji don sanyi tare cup a saman fridge din ta kawo mashi.
Kallon cup din yayi yace ashe ke sokuwace kasheni kike so yi tun yanzu ba zaki dauraye kofin kafin ki bani ba don cuta zaki bani shi a haka da datti ?
Dauka tayi ta nufi kitchen ta dauraye saida ya tsane ta fito ta kawo mashi ya dauka yana wani juya cup din a yatsune ya tsiyaya dan ruwa kadan ya kurba ya aje da gani dama ba shan ruwan zaiyi ba.
Dauka tayi zata mayar bayan ya gama habbib ya kalleta cikin kallon tsana yace wama sunan ki kamar wata tsohuwa da suna mutanen da can.
Tace sunan kakan mu aka saka min amaryan Amma ance bata taba haihuwa ba har ta rasu ban tabaye ki jin tarihi ba.
Idan ina son ji ba kece zaki fada min ba don Amma na da ranta a gurin ta zan iya jin komai ya fada yana mata kallon mugunta.
Kina son zama dani a gidan nan ya fada cikin tsare ta da idanuwan shi masu bata tsoro ta bude baki da kyat tace.
Yaya kaman yaya ina son zama dakai bayan kuma kaga gani gidan a yanzu tunda , , ,
Ke ki bani amsa tambayan ki nayi kin amince da wanan hadin da akai muna na aurena dake ?
Ta danyi murmushi kafin tace mai zai hana yaya tunda kana dan uwana kuma musulmi kuma iyayyen mu sukai wanan hadin don cikan wani burin su .
Tunda ba mu kadai akaiwa wanan hadin ba kowa kuma ya hakkura sai mune zamu nuna masu gazawan su.
Ya kura mata ido yana kallon yadda take fitar da lafuza a bakinta karamar yarinya da ita ta iya kinibibi yace a ranshi.
Amma a fili sai data gama magana yace good yana kallon ta tare da kasheta da ido saida ta dukar da kanta kasa.
To tunda hakane ina son ki sani kin shigo gidan da sai kinyi hakkuri da zaki zauna a gidan nan tare dani don kin taro wa kanki kunci da bakin ciki a rayuwan ki yarinya habbib ba mijin mace bakauya irin ki bane .
Yana fadin haka ya mike ta bishi da kallon mamaki ta juya ta mayar da ruwan ta shige dakin ta take ta kira uwarta ta labarta mata abinda ya faru a tsakanin su.
Uwar tayi dariya tace haka yace tace wallahi mama tace ki barshi baisan shi karamin dan iska bane sai ya shigo hannu zai gane kuren sa.
Shiko daki ya koma yana cika yana batsewa har ya kwanta yana tunanen irin ukuban da zai gana mata a gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button