SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:14 – ????????????: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI, , , , , ,
Wasa wasa na share kusan sati shidda banji duriyan kowa daga wani bangare ba gashi banda lamban kowa ko waya babu a hannu na na koma kamar marainiya a ari mutanen da banda uwa banda uba balle wasu yan uwa najini a tare dani.
Yau na dawo a daidai lokacin da nake shigowa gidan sai dai abinda ya ban mamaki tun daga waje shine ganin sayun shigan mota a gidan.
Da mamaki na karasa ciki sai dai gidan yana a kulle kamar yadda na barshi sai mamakina bai kare ba lokacin da nayi arba da wasu takardu a saman table din falon .
Ban bi ta kan takardun ba ciki na shiga da sauri in duba ko an min sata a gidan na samu kayana tsab ba abinda aka taba min.
Sai na sauke numfashi na aje jakkan dake hannuna saman gado na numfi bandaki don in kewaya.
Alaman wanka naga anyi a bandakin ruwa a ko ina bai gama bushewa ba gurin a tsorace nayi abinda zanyi na fito ina mamakin waya shigo gidan bana nan ?
Wake da key din gidan bayan ni haka na kwana tsorace ga yunwa ga tunane saida safe na dan dafa shayi nasha na fita zuwa school.
Inda yanzu na fara fahintar komai banda matsalan karatu komai na zama min a kaina idan na dauka.
Duk da rayuwan London yana cike da abubuwan mamaki da debe kewa na zamani da debe kewa sai dai duk basu a gabana a wanan lokacin.
Na zama kamar kanwar the guy wanda yanzu anfi sanin shi da Yusuf bin Abdoulah shi kadai nake gani inga kamar naga wani na gida nawa.
A hutun farko da muka samu bayan share watani uku muna daukan kararu mukaje hutun karshen zago.
Sai lokacin na shiga damuwa sosai ni kadai a gidan ba fita ko ina daga inyi wanka inci abinci inbi lafiyan gado in kwanta ko in kunna kallo ko kuma indan fito wajen gidan ina kallo abubuwan ban mamaki.
Ina zaune a falo bayan na gaji da barci na fito don in samu abinda naci jin kara bude daya kofan dakin yasa da sauri na dago kai na kalli kofan.
Ya umar nagani ya fito yana saye da yan kananan kaya waya a hannun shi yanayi ya nufo falon gidan a inda nake a zaune.
Ido na zuba mai da mamaki har ya karaso falon ya zauna da hannu yai min alaman in kawo mai ruwa har lokacin bai bar wayan da yakeyi ba din.
A cikkn sayin jiki na mike zuwa kitchen don na dauko mai goran ruwa na fito daga kitchen din duk da ina gida ni kadai ne hakan bai hanani dan saka kaya mara kyau a jikina ba don ma dai din banda shi a gidan ko banza duk kayan dake gareni na kwarai ne tun zuwana garin.
Ya zuba min ido yana wayan kamar mai kallon style din jikin rigan dake jikina din tunda na sanyo kai falon gaba daya ya tsura min idanuwan shi har saida na tsargu da kallon da yake min din.
Nazo gaban shi na aje goran ruwa da cup saman table din na juya zan bar wurun sai lokacin naji yai magana a cikin wani yanayi daba zan iya fassarawa ba lokacin tsawa ne ko lalama oho ?
Wa zai zuba min ruwa da kika aje min haka ya fadi yayin da yaci gaba da wayan shi hankali kwance.
Hakan yasa nazo gaban shi na dan duka na tsiyaya mai ruwan cikin cup na aje a gaban shi ina zubawa na mike na bar wurin.
Kai ya dago ya bini da kallon mamaki tankar wani wanda yaga abin mamaki a tare dani kitchen na nufa dama yunwa ya fito dani falin na zauna kuma ina tunane ?
Ina cikin tunanen abinda zan dan dafa inci naji muryan shi daga kofan kitchen din yana fadin watau haka kike zama da yunwa don lalaci ba zaki dafa abinda zakici ba ?
Sallon daddy yace na kawo ki garin mutane na bar mashi ke da yunwa ko ?
Idon daya kashe ni dashi lokacin yasani saurin dukar da kaina kasa har lokacin ban iya koda gaida shi ba.
Ganin banda niyar magana ya juya ya fita na dauka ya tafi ke nan don ni fanin shi bayan mamaki sai tsoran shi ya kamani don ina mamaki yaya yashigo min gida bada masaniyata ba haka ?
Na dora ruwa ina kokarin ciro nodles in bare sai naji shigowan shi gidan again leda ya aje min tare da fadin ki fito ki zuba min nawa don yunwa nake ji kada ki bata min lokaci.
Nazo a hankali na dauki ledan na koma kitchen dashi na bude bread din alkama ne irin wanda ake ci da source a kasan.
Na dan dade tsaye ina kallon bread din don ban taba kokarin cinshi ba asalima nafi bukatan in dafa da kaina inci saboda tsaron addini na kada inzo inci abinda ba halal ba.
Na dauko plate masu kyau na shirya masa nasa na nufo falon dashi yana zaune hankalin shi a sytem din shi kamar wani mayen na,ura.
Naso in share shi in aje kawai in wuce sai dai dana aje na dan tsugunna daga gefe nace ya sannu da zuwa ina kwana.
Da kai kawai ya amsa min da uhumm na juya zan shige inda na fito naji muryan shi yana fadin wani yaro ne kike yawan tsayawa dashi a school din ku wani lokaci ?
Cikin mamaki na dago kai da sauri na dan kalleshi ganin niya tsurawa ido yasa na dukar da kaina da sauri ba tare dana bashi amsa ba.
Ya sake fadin bakiji bane na tambaye ki sai da na tsaya nadan yi dan tunane don ni na manta da zancen yusuf a raina sam.
Ya fadi a tsawace nace wani yaro ne wanan ya zubo min idanu sai kace wani tsohon zaki can dashi.
Nace ni ban san wani wanda nake kulawa ba a school din mu sai dai idan sheri za ai min yace sheri cikin mamaki sheri fa ?
Wa zai maki sheri ni ko wa zai maki sheri zaki fada mi ko sai na bata maki rai a gurin nan ?
Innalillahi nace a fili wallahi yaya ban san wanda kake magana a kanshi ba asalima niko kawa mace banda ita a makarantan balle wani na miji can .
Wa ya baki coffee da kika fito sallah ranan gabana yai mugun faduwa na dago kai da sauri nace yusuf ne .
Dan makarantar mu ne tun a Nigeria shine muka hadu dashi a nan yana daukana tankar kanwar ce a nan ko magana bama yi dashi.
Asalima ranan na samu sun sayane sai gani ya miko min sai nayi shiru yace da yake ke mabukaciyace lalaci ya hanaki ki girka a gida kika fita da yunwa ko ?
Nace a cikin laushin murya idan hakan ya bata ma rai kayi hakkuri ba zan sake ba in sha Allahu.
Kasa magana yayi duk wani fadan daya kulla zai mun sai kuma na bashi tausayi don bai tsamaci karaya haka da sauri a gurina ba a yadda ya sanni fitsarariya.
Bread din da baici ba ke nan ya mike cikin fushi ya bar falon ina jin tayar da motar shi ya bar gidan ban damu ba tunda nasan banyi komai da yake zargina ba akai.
Zama nayi inda ya tashi na fara cin bread da source din daya bari gurin rana banci abinci ba sai ruwa danayi ta sha ranan sai yamma na girka abinci naci.
Tun wanan ranan na gane wanan bread na alkama ban yarda in rabu dashi a gidan dama na gane masuyi din musulmai ne yan pakistan sai na kara mayar da hankali gutin cin sa sosai sai ya kosar dani har yamma.
Ranan na dauka zai dawo sai dai ban sake sa shi a ido ba nima hakan bai damay ni ba ko kadan.
Kwance yake mike saman dogon kujeran dake karamin falon su yana nazarin wasu jirage da suke so gyarawa a kasan Dubai.
Sai dai yanayin kwanciyar nasa yana nuna akwai damuwa sosai a tare dashi ya mika hannu ya dauki wayan shi dake gefe a je ya sake dialing din nomban merry din karo na barkatai ke nan tun dawowan shi london din.
Kamar yadda computer ta saba mai babatu wanan karon ma itace ta soma zancen cikin sanar dashi layin baya shiga.
Karan kararawan shigowa falon kamar ba zai dago kai ya duba ba yadan share don ya dauka cikin yan aikin gidan nasa ne ke masa sallama.
Merry tace ta shigo falon cikin shigar wani dogon riga da cinyan shi yake bude har kasa rigar mai hannu kamar dan shimin mata sai yarta dake dauke hannun mai aikin su ta daukota tana barci.
Dan peck takai mai daga inda yake kwance din hakan yasa shi mikewa zaune tare da rike mata hannun yana fadin yanzu ya gama trying din layinta yana rufe.
Merry bata amsa ba illa amsar yarta datayi a hannun mai aikin tana kokarin kwatar da ita saman kujeran daya tashi akai.
Itama taka zaune tana kokarin cire takalman kafanta masu tsinin gaske kafin ta juyo gurin shi tana sauke ajiyan zuciya.
Mai aikin cikin gidan su ce ta shigo dauke da abinsha tana kokatin ajewa a gaban ta kallon kayan yayi yace Greco na hana a kawo min wanan abin a gidana kin sani.
Yaya akayi ya shigo min gida ya fada tare da hade fuskan shi a lokaci guda yana kalli merry din rai bace kamar bashi bane ya gama fara,a yanzu ba.
Tace commo dear cikin dan marairaice murya tana fadin iam testing let me have some please you know we are in long joining.
Ya kalleta da idanuwan shi da suka kada sukai ja a lokaci guda sun sauya kala ya nunawa Greco hanyar fita da kayan da sauri ta dauke kwalban giyan zuwa waje.
Hakan yasa merry din tashi ta barshi a gurin tana fada a fili ya bita da kallo mai kama da harara kafin ya juyo ya mayar da kallon shi zuwa ga yarsu dake barci hankali kwance.
Wani irin tausayin yarinyar yaji ya darsu mashi a ranshi ya kai zaune a hankali yana dan shafan kan yarinyar tare da runtse idanuwan shi.
Lalai duk abinda babba ya hango yaro baya hango shi don sai yanzu bayan auren su ne yake sanin wasu munanan halaya na merry data boye mai a baya daya dauka ba dabi,un ta bane.
Ta boye mashi wasu abubuwa da dama daga cikin dabiun nata da sai yanzu ne yake gano hakan bayan haihuwan yarsu mm a farko ta fitar fili.
Wani irin ajiyan zuciya ya sauke tsoro da nadama auren merry ya darsu mashi a zuciyar shi.
Tsoron ingancin addinin shi da abinda addini ya shari,anta yana zo mai a rai take tsoron kada Allah ya kamashi da laifin daba nasa ba yazo mai a rai.
Take tunanen yar mutane da ya kawo kasan ya rabota da kowa nata ya darsu a zuciyar shi lokaci guda.
Idan wani abu ya samu yar mutane a inda ya watsar da ita da sunan karatu mai zace ma iyayyen su a gida ya samay ta ko basu tambaya ba ai Allah yana ganin shi.
Shine mafarin zuwa ranan ya dubani dayayi bayan ya saka wanda zai dinga kulla da duk wani movement dina a school din ba tare dana sani ba ya fara zuwa guri shi ya tambaye shi yace mai ina nan lafiya sai dai yana ganin ina yawan tsayawa da wani yaro dan Africa ne shima.
Tun wanan ranan idan ya dauki fushi da merrey yake zuwa nan ya huta ba tare da na sani ba idan ya gama abinda yakeyi ya wuce abinshi tunda dai yasan ina lafiya.
Ranan bayan ya bar gidana ya koma gida ya samu itama bata kwana a gida ba sai yarsu kawai ya samu a wurin Greco tana rainon ta .
Bayan ya gama duba yar ya shige dakin kwanan su a hankali yake bin dakin da kallo ido ya lumshe take mahaifin shi ya fado mai a rai lokaci guda.
A hankali ya kai kwance saman gadon dakin ya rasa abinda ke mai dadi a rayuwan shi wanan wani al,amarine da bai taba zaton zai iya faruwa dashi ba yake cin ranshi.
Duk wani tunane nasa yau ya dunkule a wuri daya yana hango zancen daddy su a lokaci guda tun farkom ganin shi da merry da daddy ke fadin su din basu da tabbas domin munafukai ne.
Bai taba tunane merry zata iya sauyawa daga irin sharudan da suka sakawa junan su tun kafin suyi aure da yake gani a nasa tunanen ta rike don son da take mashi din bayi zaton zata iya karya alkawari ba hakan
Can a cikin barcin gajiyan da yakeyi don idan ya dawo aiki yakan zauna a gida ya sauke gajiyan shi na yan kwanaki kafin a nemay su kuma .
Jin dararakun nasu harda kamar maza a cikin su yasa shi saukowa kasa bai shiya ba a hankali yake takowa daga steps din tsayawa yayi yana kare masu kallo su hudu ne mata uku sai namiji daya dake ta shafan macen guda a falon.
Wani tsawa ya daka masu tun daga saman inda yake tsaye duk suka juyo a firgice suna kallon shi da mamaki.
Ya tako inda suke ba tare da yayi magana ba ya nuna masu hanyar fita daga gidanshi kallon mamaki suke mai har lokacin rai bace yace merry may kike so mayar mun da gidane wai ?
Tace no no bamuyi haka dakai ba dear kada ka fara korar min abokai a gidan nan don ni ban kori naka ko daya ba.
Wani kallo yai mata ya juya ya shiga daki sai gashi ya fito rike da key di motar shi ya wuce su ya bar gidan.
Ina gidan zaune a cikin kadaicin da yanzu ya zama min jiki saye a cikin doguwar rigar kirar Oman baka a jikina naji ana lwankwasa kofa da farko naji tsoron hakan sai daga baya na daure ina tambayan waye ?
Yace ki bude nine gabana ya fadi na bude a hankali naja baya don in bashi hanya.
Ya shigo rike da ledodi da da jakkar laptop din shi a hannu bai tsaya min magana ba ya haye saman benen na bishi da kallo kafin in rufo kofan.
Tun da ya shige dayan dakin ya rufo ban kara jin duriyan shi ba har safe na dauka ko baya gidan ma don har lokacin muna hutu ban fita ko ina.
Har na gaji da kwanci na taso in sama ma cikina abinda zanci a lokacin naji karan budan kofan shi.
Daga kofan kitchen din ya tsaya yana fadin daddy ina kusa da ita yanzun hakan ko a bata ku gaisa ne.
Da sauri na juyo don jin abinda ya fadi ina kallon shi miko min wayan yayi da sauri na karaso inda yake na karbi wayan .
Sai dana share hawayen daya gangaro min a fuska a lokacin na iya cewa naam kawu yace hasbunallahu wani,imal wakeel yata nake ji haka radau a waya ?
Sai da na hade wani abu daya tokaro min zuciya na amsa mai da lafiya lau muke kawu yaya su Amma da mamu da sauran mutanen gida?
Yana tsaye ya tsare ni da ido yana sauraren yadda muke wayan da kawu a lokacin hakan ya hanani yin wani motsi mai karfi.
Bayan min gama gaisawa ya miko min hannu ya karbi wayan shi ya fara tafiya ina jin yana fadin tana karatu sosai daddy.
Lokaci guda hankalina ya tashi a wurin daya barni na rushe da wani itin kuka mai tsuma rai sosai bai kara shigowa gidan ba haka ya barni cikin kewan gida don jin muryan kawu danayi ranan.