NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Kuyi manaji dashi don Allah da kyat na iya rubuta makushi wallahi ban ma san abinda nake rubutawa ba karshe.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:16 – ????????????: DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAIIII,

A gida Nigeria kawu yana gama waya da dan shi cikin murmushi ya dago kai ya kalli Amma data matsa sai an kiramu anji lafiyan mu.
Za ace yara tun tafiyan su ba,a kirasu anji lafiyan su ba ai hakan bai dace ba.
Itama Amman murmushi ta sauke cikin jin dadi da kwanciyan hankali tana sauke ajiyan zuciya don ko ba komau yanzu hankalin su zai kara kwantawa tunda sun tabbatar da muna lafiya.
Karewama gashi ana tambayana ya mika min waya mu gaisa lalai hakan ya nina muna zaune lafiya ke nan.
Nan Amma ta shiga bada labari ga duk wanda yazo ta bangaren ta tana fadin ita kan wanan hadin yayi mata dadi sosai umar ya rike amana yar marainiyar Allah da aka dora mai a kai.

Sai dai ni a nawa ban garen ranan ban yi barcin kirki ba ina tuno mutanen gida da kewan su a rains harma da wa yanda ban shiri dasu ranan naji kewan su sosai a raina.
Ance inda kake nan aka sanka gani a garin mutane ba fada ba girma da arziki da kowa a garin ba zancen wance na sona wance bata sona duka dai gashi na rasa hakan yanzu a tare dani.
Na juya ina mamakin irin karyan da yaya umar yayi a gabana kan wai muna tare ko wani lokaci su barima ya bani waya mu gaisa ai.
Tabe baki nayi na sake juyawa tunanen mamu da hjy jummai na fara ina anyana ko wani hali suke ciki bayan mu barsu a can ?
Ko yanzu hjy su yaya umar ta saduda tabar zancen raba auren da tace muddin tana raye sai taga bayan wanan bakin auren namu.
Da za acema zataci nasaran rabawan a yanzu da sai nafi kowa farin cikin hakan matsala ta daya shine karatuna da zai iya samun cikas.
Wani shawara ne yazo min in jure in kara hakkuri akan wanda nake na zaman kadaici ni kadai a katon gidan nan har lokacin da burina dana iyayyena zai cika gareni na kammala karatuna.
Don yanzu komai ina fahinta ga kayan koyan komai a wadace banda matsala ta ko ina indai kan karatuna ne.
Tausayin mahaifiya ta dana baro a cikin wani hali duk da bata nunawa tana kokarin boyewa nasan wanan abin ba karamin taba mata rayuwa yayi ba.
Don na fahinci mamu na tausaya min tana matukan son ganin rayuwana ya inganta a duniyan nan.

Ban san yadda akayi ba ana saura sati mu koma karatun mu ne ranan ya shigo gidan kamar an jefo shi ina zaune ina kallon wani shiri na musulunci a tv mai suna women in hijjab.
Kafana suna mike saman dan center table ina tauna dan porncorn din daya zama min dabi,an ci koda yaushe.
Ganin shigowan shi yasa na dan rude na mike tsaye ina mashi sannu da zuwa ya amsa min kamar dai kullun ya nufi hanyar sama har ya fara hawa ya juyo yana fadin ki shirya nan da minti talatin kafin in fito.
Haka kawai ya fadi yasa kai ya haye saman abinshi binshi nayi da kallo ina tnane wani irin shiri yake magana ke nan ?
Hakana na mike na shiga daki sai kuma na rasa wani irin shiri zanyi a dakin lokacin ba wasu kaya sai dogayen riguna dole daya na zaba har kasa wani mai adon ja da bakin jan maron colour da adon baki gaban rigan gyalen da zai shiga da kayan na yafa na rufe daga kaina zuwa wuya duk da haka ina jin kaina kamar a tsirara ne duk da rigan ya rufe min ko ina.
Wai baki gama shitin bane ya fada a dan hasale da sauri na dauko dan jakkana na fito daga daki ina fadin na gama.
Kallona yayi daga samana har kasa ya kawar da kai ga kallona tare da fara tafiys na biyo bayan shi daga can cikin motan yace wa zai kulle maki gidan ?
Jikina na rawa na koma na dauko key inda nake ajewa nazo na kulle gidan na nufo wurin motan don tsoron shi da nake ji na takure a wuri daya zan shiga bayan motan.
Wani harara da tsawa yai min sai ganina nayi a gaban motan zaune ya bar gidan sosai yake gudu da motan .
Ni dai ban san inda muka nufa ba don ba garin na sani ba kaina a duke don nagaji da kalle kallen abin mamaki a idona ga tafiyan mai nisa sosai da alama.
Don tun da rana har wani lokaci muka isa gurin
Jin hayaniyan mutane yasani dago kai a hankali wani signboard na gani anyi rubutu manya a cikin style welcome to CUMBRIA PICNICK LAKE WINDERMERRE, , , ,
Bayan motar ya bude ya miko min wani bakin coat na mata kallon rigan nayi yace ki saka in ba haka ba sanyi ya illanta ki a nan.
Da sauri na karba na saka sai ga rigan yazo min har iya gwiwa na sai dogon rigan dake jikina ya koma kamar buje .
Waya yayi banji may akace ba naji yace muje don Allah bin bayan shi nayi ina fadin mutum haka komai a hasale yakeyin shi ?
Zaune suke duk da duhun dake gurin sun saka wuta a tsakiya wasu na kwallo wasuna shaye shaye wasu a kwance .
Hi Omar we are here muryan merry naji sun sauka a kunnuwa na lokaci guda da sauri na dan kalli wurin na karasa ta hanyan bin bayan shi zuwa inda suke zaune a cikin yashin teko da wasu mutanen da kusan rabin jikin su duk tsirara ne.
Unbelieveble wa nake gani nan kamar fatema ta fada tana kokarin tasowa daga inda take zaune din .
Haka yasa wa yanda suke tare a zaune suka juyo suna kallon mu tasowa tayi sukai dan wani musayan gaisuwa na gefen mumuke.
Nidai ina tsaye ina kallon ikon Allah ta barshi zuwa wurina taimin irin wanan gaisuwa hannunta yana rike a cikin nawa take tambayana yaya karatu ?
Nace da ita Alhamdullahi dan bubuga min baya tayi tare da jan hannu na zuwa wurin mutanen da ke zaune tare da ita tana fadin.
Meet Omar sister Fatema tana karatu ne a nan kasa tazo daga nigeria ne itama suka kara kallona suna fadin she is so beutiful.
Tare da tambayan merry din yaushe nazo basu sani ba tana fada masune hankalina yaje gurin yaya umar dake rungumay da yarshi zaune a cikin kasa suna hira cikin kwantar da murya yana rungumar yarinyar .
Cewan da merry tayi ga abokanta mu gaisa ya dawo da hankalina inda suke hannu suke kokarin miko min nayi saurin masu jam,i ga baki daya na gaida su.
Don nasan ko mazan zasuyi kokarin miko min hannunnsu hakan gareni wanda nasan sai dai in ba merry din kunya don bazan karba masu ba.
Merry tayi saurin cewa halan ba al,adan mu bane mun rike addinin mu sama ga komai don haka mijin ta yake shima.
Sai suka sa dariya a tare lokaci guda kamar yasan may sukeyi yace kezo nan zakace badani yake magana ba.
Ganin ni kadai ke jin hausa a gurin nasan dani yake magana na juya a hankali zuwa inda suke dashi da yar shi din ya rungumay ta wanan karon.
Ki zauna yace dani da yana nuna min wurin zama da hannun shi haka yasa da sauri nayi abinda yace din .
Na kai zaune saman yashin a kusa dasu na zauna tare da dan takurewa a guri daya.
Fuskokin mu yana facing din ruwan sake iska keta kadawa a lokacin mutane wuri ba adadi kowa da abinda yakeyi a furin ba wanda ya damu da wani.
Ina can ina kalle kalle naji muryan shi yana fadin ke yar nan nake son ki rike min kada ki bari tana bin wa yancan ya nuna su ba tare daya daga hannu ko kai ba.
Da dan mamaki na dan kalle shi yace eh nasan yarinyar tana da sabo zata saba dake idan kin nuna mata kulawa daya dace.
Yana fadin hakan ya mike ya barmu da yarinyar zaune tare dan hannu na mika mata sai ko tazo gurina yayin da hankalina yake gare shi ina kallon inda zai tafi.
Muryan yar yarinyar ya dawo da hankalina gare ta kallonta nayi naga ta bata rai tana fadin i want to sleep now.
Yanayin maganan ta ya ban sha,awa ganin tayi karanta sosai da zuwa irin gurararen nan haka.
Fuskana take kallo take maganan na dan sakar mata murmushi kadan ce tazo ta kwanta a jikina bata ki ba sai ta matsa inda nake zaune.
Zaune muke kafafuwan mu a cikin ruwan lake din na rugumay ta sai lokaxin tunanen kanne na yadda nakeyi dasu a hankali nakai hannuna saman kanta dake da kitso hudu na kalaba yaji dauri da ribon masu kyau.
Ina dan bin zanen kitson da hannuna naji yadda take sauke ajiyan zuciya a hankali alama barci na zuwa mata a lokacin.
Tace my mum sing for me idan ina jin barci duk dare na dan kalle ta ikin kamilaliyan fuska nace ban iya irin wankan da maman ki ke yi ba ni ai.
Tace kiyi ko wani iri kika iya na dan yi tunane kadan sai na fara karanto mata fatiha har zuwa karshen shi.
Nakai aya nayi shiru don na dauka tayi barci saboda yadda ta lafe a jikin nawa lokacin sai kawai naga ta dago kai ta kalle ni tana fadin may yasa na bari kuma taji dadin wankan sosai ci gaba nayi da maimaita mata karatun ina dan taba mata kai a hankali.
Yanayin da nake ciki yasa na zarce da karatuna a cikin zazzakan murya ba tare da nasan ina daga murya sosai ba a lokacin.
Sannu a hankali suke taruwa suna kallon yadda nake karatun su basu raina abin kallo a wurin su hakan ya jawo hankalin su merry gare mu ta tako har zuwa inda muke zaune din .
Hannu ta mika tana fadin tana baki wahala ko fatema a daidai lokacin da take mika hannu don daukan yarinyar a jikina tana fadin ina Dad din ta ne ya barki da ita haka ?
Abin mamaki ga yarunyar da tayi nisa a barci sama jikina uwar na tabata da niyar ta dauke ta saman jikina di don ta fahinci abinda nake karantawa yarinyar nata a lokacin.
Uwar na daga yarinyar sai ta zabura ta kankamay min a jiki tana girgiza kai tare da fadin no no zan tsaya a wurin wanan aunti din .
Daga bayan ta taji muryan mijin yana fadin ki kyale su tare ko kin manta da alakana da yarinyar ne ?
Yana gama fadin haka yarinyar tace thank you dad ta mayar da kanta saman jikina kamar ta koma barci lokacin.
Ina mamaki a raina don kalman godiyan da ta jefawa uban tana a lokacin yana nuna taji dadin hukuncin daya yanke a kanta ke nan na hana uwar ta dauketa wurina.
Can na dauka tayi barci ne saboda irin lafewan datayi saman jikina din lokacin sai naji muryanta tana fadin.
Whats your name please ta fada tana dago kai tare da duban fuskana dake manne a jikin ta lokacin.
Kallon ta nadan yi nace fatima sai naga ta girgiza kanta tana fadin okey i will called you anty fatima na danyi shiru ina mamakin wayau karaman yarinyar haka.
Na kalle ta nace ba kince kina jin barci ba da farko kiyi barcin ki tunda daddy yace a barki a nan gurina.
Ajiyan zuciya naji ta sauke tana sone kanta da kyau saman kirjina a hankali.
Merry dake rungumay da hannayen ta tana tsaye da kawayen da duk bakaken fatane suna tambayan ta yaya muke da mijin nata.
Sai da ta sauke ajiyan zuciya tace kaunar shi ce wata ta jefo mata tambaya da fadin uwa daya uba daya ?
Tace yar step mum din shine mahaifi suka hada dashi kawai tace tana kokarin tafiya wurin mijin ta .
Amma kyan yarinyar yayi yawa ya nuna kamae ba jinin su daya ba wani fannin sai dai kama na fari da suke dashi kawai don wanan tana da zubin yan arab sosai.
Bata juyo ba ta dai wuce shi yana tsaye yana kallon ruwa babu komai a ranshi sai tunane karfin hali kawai yake da tsayuwa a wurun taron nasu.
Yayi kokatin mata kara ne kawai dan taya ta bukin da zasuyi na Esther da ya gabato ko wani shekara wanan dalilin yasa ya dauko ni don manufa biyu.
Na farko nazo don yar shi sai na biyu yasan zan danji dadin zuwa cikin mutane dana kwana biyu a zaune a gida ban fita ko ina.
Karatun da yaji ina wa yarshi ne ya kara daga mai hankali abinda ya dace ace shiya fara tunanen koya mata hakan sai gashi yaji ya gani da idon shi nayi hikimar koyawa yatinyar karatun addinin mu lokaci guda.
Hakan yayi mai dadi sosai a zuciyar shi har ya saka shi tunanen wani abinda yasan ba zai yuyu ba ga yar nashi sai a cikin hikima da basira.
Jin hannun merry dayayi saman jikin shi tana kokarin rungumay shi ne yasa shi sauke ajiyan zuciya a hankali.
Ya juyo da ita zuwa gaban shi goshinta ya hada da nasa kafin ya hade da jikjnta ya rugumay ta yana dan sakin murmushi wanda hakan ne halin shi idan yana cikin yanayin jin dadi.
Daga inda nake zaune na mike da yarinyar a saman jikina da kyar ina dube duben inda zanga iyayyen nata don sallah dana tuna banyi ba a lokacin ina son samun kebeben wuri da zan gabatar da sallah din.
Hango su nayi a inda suke tsaye rungumay da junan su wurin su na nufa a hankali ina fadin lokacin sallah yayi zan shimfide ta inyi sallah ne.
Don har azahar ban samu yi ba a lokacin ba tare da ya sake merry a jikin shi ba kuma baiyi magana ya bani amsa ba ya juya ya fara tafiya .
Nidai na gyara yarinyar da nauyin ta ya cika min hannu sosai a lokacin nabi bayan su muka jera har zuwa gurin motar su dake can aje dan nisa kadan da inda muke din.
Bude motar yayi ya juyo ya karbi yarinya tare da fadin sannu da kokari kamar ba dani yake magana ba zakace.
Nima ban amsa ba amsan yarinyar yayi ya ahimfide ta a bayan motan dan hakan na juya zuwa bakin ruwan dake ta feso muna ina kokarin tattare hannun rigana don yin alwala .
Na fara naga shima yazo yana alwalan a can dan nesa da inda nake ina idarwa na hango ya shimfida muna abin sallah gurin motar shi kusan tare mukai sallolin da ake bin mu din don shi ya jamu sallah lokacin.
Sai bayan mun idar ne naga merry tana fito da kayan abinci a bayan motan tashi yayi ya taimaka mata suka jera kayan a gurin .
Shi yati min basimilla nace a koshe nake bana jin yunwa dan kallona yayi a dake yana fadin may kikaci fun dazun muka bar gida don haka ki zoba abinda ranki ke so a nan kici.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button