NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:16 – ????????????: ALLAH ABIN GODIYA JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI, , , , ,

Ina cikin mota zaune nake barci cike da dinbin mamakin wanan sabuwan rayuwan wahalan dana gani yau a rayuwata.
Wai abin mamaki dan adam ya hana kanshi barci yana rayuwan sharholiya saboda jin dadin duniya da yai mai yawa.
Zakace wurin kasuwa ne har tsofi akwai wurin da yara kanana na goye an hanasu barci suji dadin dare saboda wanan shirmay banza sai ciye ciye kungiya kungiya suke faman yi.
Barci na samu ya dauke ni cikin mamakin ya umar wanda yayi watsi da addinin shi da dabi,un aladanshi akan mace.
Alam din agogona da na saita don jin lokacin sallah karan shi ya tayar dani daga dan barcin dana samuyi.
Da mamakin dana kwanta dashi na falka don sai ince wurin yafi lokacin dana kwanta barci cika.
Tsofine da yara har na goye gasu nan kungiya kungiya sai masha,a da raha akeyi a wurin babu zancen tunanen Allah.
Mamaki kan yau na sha shi wurin kallon abin al,ajabi da mamaki ace mutum mau ilimi irun ya umar ya biyewa wani ikidan banza na mace don dai kawai taji dadin hakan a ranta.
Gashi yazo ya maida kanshi wani kototon katon jahili cikin addinin shi saboda kawai ya dadadawa macen da yake so rai.
Na dade zaune cikin motan ina sake saken zuci ni kadai ina hango su daga inda suke zaune din.
To waini ma a wani matsayi nake a wurun nan don ban fahinci dalilun su na kawo ni wanan wurun haka ba.
Ko wanan ne wayewan da merry take kiran tana son ya kaini makarabtar da ta zaba inyi.
Ko madai ma maynene nabar abin a raina kamar yadda shima din ya barni a rufe nidai burina in samu in kammala karatuna in koma gida wurin a halina.
Saidai nasha alwashi a raina cewa da zaran mun koma gida zan fadawa kawu da Amma irin zaman tanbadan da sukeyi da arniyar matar shi a turai.
Kallon yarinyar dake barci a jikina nayi na dab daga ta a hankali cikin sanyin jiki na bude motar a hankali nafito.
Kara kallon su nayi da wani irin kyama da tsana don sun cutar dani na zuwa wanan wuri dani haka ina zaune kalau abina.
Cikin sanyin jiki da kasala na fara tafiya a hankali zuwa nesa da inda ba mutane sosai na dan tatara hannun rugan sanyun dake jikina a hankali na fara gabatar da alwala don asuba ya gabato sosai a lokacin.
Na kusa kai karshe naji murya a bayana ana fadin hy babbe idan ba damuwa zanso kasancewa dake.
Ko kina tare da wani ne a gurun nan ban dago ba sai kokarin alwala nakeyi har na idar na daga yatsana sama ina hailala ga ubangijina Allah.
Yace Wa, woo, so you are muslims girl baby kinzo da wasu ne ko ke kadaine a gurin nan zaso mu dan kasance tare dake na dan wani lokaci.
Naso yimai rashin mutunci sai ba tuna nan ba Nigeria bane kada yazo ya turani cikin teku ruwa ya wuce da banza ba a san na mutu ba wanan wurin.
Ke idan kin gama abinda kikeyi kizo ki wuce ya umar ne ke magana a bayan mu da sauri na shafa na raba baturen zuciyana yana min kuna da maganganun da ya rabbatamin din.
Wurin motar na nufa ina kokarin tayar da sallah yayin da na barsu can tare da baturen komay yake fada mai oho.
Ganin zanyi sallah ya kyaleni ina kallo shi shima can gefe daya yana sallah a cikin yashin teku.
Ke idan kin idar ki tashi muje yace ni wanan ke din da yaya ke fada min waidai ko baisan sunana bane wai na tambayi kaina ?
Mota muka shiga muna baya da yarsu har lokacin tana barcin ta sai gyara kwanciyan da tayi saman jikina tana dunkulewa a wuri daya.
Ba kan garin na sani ba don haka ban san titin dayake bi damu ba a lokacin nidai tun muna tafiyan arziki har yakai nagaji ina dan jan tsukin dana dauka a zuciya na nakeyi.
Merry ce ta fara juyowa inda nake zaune tana fadin kingaji ko sorry fatema kin tayani zuwa eather da abokaina da yanuwa da abokan arzikina naji dadin hakan da kukai min ke da dan uwan ki.
Magana take tana murmushi cikin nuna fari ciki irin na wanda yaji dadin abu yayin da idanuwanta ke kaina a kafe.
Da murmushin yake na kakaro a fuskana ina jin ta dan juya ta kalli mijin tana fadin taji dadin wanan kasancewan da yayi dasu harda sister din shi.
Mun iso gidan sai lokacin na fahinci inda mukazo shiya zagayo ya dauki yarinyar a wurina ya sabata zuwa ciki,
A falon mukaya da zango kallona yayi yana fadin zaki iya shiga wanan dakin da kika taba zama yana nan babu kowa a cikin sa.
Jin haka yasa na mike da sauri don duk a matse nake a gurin damaina shiga nayi ban daki na hada ruwan dumi masu zafi na gasa jikina dashi.
Alwala na dauro na fito cike da tunanen a raina na kayan da zan saka inyi sallah sai ina ganin zuwa wurin yasa tufafi na basu da tsarki yanzu kuma.
Naji mamakin ganin kaya saman gadon an aje min na dan tsaya ina karewa kayan kallo kafin in karasa zuwa wurin da sauri hannun kayan na fara dubawa idan ba yar shimi bane.
Dogon rigane irin na matan turai yana da yan hannuwa ba wani dogo sosai ba da ganin kayan zai bi jikin mutum ya lafe mai a jiki.
Dayan kuma kamar abayane sai dai yana da shape shima ba irn na matan larabawa bane ganin idan na gama ramuwan barci zanyi yasa na saka na farkon a jikina.
Dan gyale na dauko ina takaicin barin hijab dina danayi gida banzo da shiba don sallah to mutum kawai yace ka shirya ba tare da fada ma komai ba ina zan tsaya shirin kwarai lokacin.
Allah ya isa nayi ta ja a raina zuwa nan inda suka kwasoni ba don na sani ba wurin wullakanta kai da kiman mutum.
Tun inda na idar da sallah na fara gyangyadi na mike da kyat zuwa bakin gadon nan nahaye na yada kaina sama sai barci.
Barci sosai nake a kife a dakin sai dai ya umar da ya fito ya shigo yana dubani yakai sau uku har lokacin yana samuna ina barci.
Har mamaki yayi wanan wani irin barcine haka don yasan cikina akwai yunwa ban ci wani abin kirki ba tun jiya din koma dai yaya ne yasan yunwa zai tayar dani ai.
A razane na mike kan gadon gami da salati a zato har lokacin rana ne ban jima ina barci ba.
Duban lokaci nayi nayi na lumshe ido da sauri ina mamaki na zabura nayi bandakin na wanko bakina gami da alwala na fito na tayar da sallah don har isha,i ya wuce lokacin.
Banji nauyi ko kunya ba yadda nake jin cikina a lokacin firowa nayi neman abinda zanci tunda dai gidan ba bakona bane yanzu.
Ganin abinci a saman dining din na nufi can saida na bubude naga abinda zan iya ci na zuba nayi dik na kora ruwa nayi hamdala.
Sai lokacin na kula da irin kwalliyan da akaiwa gidan irin nasu na chirstoci idan suna shagalin su ba buki.
Ikon Allah na fadi a fili ina mamaki tare da tunanen ko dai ya umar din ya canza shekane basaja yake wa mutane.
Wata zuciya tace min ko da asubah baki ganshi yana sallah bane da zaki masa sheri to amma abun yai yawa mana nace a raina.
Banji fitowa shi ba sai dai ganin mutum nayi a gabana haka kawai naji gabana yana faduwa .
Cikin dan i,iniya na fara gaida shi kamar yadda ya saba amsawa a dake hakan ya amsa min gaisuwan wanan karon ma.
Wanan kallon wullakancin nasa ya jefo min yana fadin kin ga dama kin tashi kin wani kwanta kamar wace tayi wani aikin dake ?
Yana waso min idanuwan shi masu kama dana mayau dari da naki jini tun a gida kamar yana jin tsoron kallon mata yakeyi.
A takaice na bashi amsa da dama aikin nayi ai zaifi min wanan zaman.
Ni kaina amsan yazo min a bakine don bansan lokacin dana fadi ba don takaicin shi da nake ji din.
Kallona yayi ya girgiza kai cikin mamakina kamar zaiyi magana sai kuma ya wace ga yar shi data fito tana kiran daddy daddy.
Mikewa nayi zan tashi in bar wurin naji muryan shi yana fadin ina son ki kula min da yata don yau muna da baki a gidan.
Cikin kunkuni nace ni ina ruwa da baki ku da zaka mayar dani yar raino na juya naji yarinyar na fadi cikin turanci daddy na manta da sunan ta ya dago ya dan kalleni yace mata fatima.
Sai ta girgiza kai yace oh sorry aunt fatima tace yes that’s her name ta juyo tana fadin tana wani kada idon kinibibi zaki wasa dani ?
Na nuna kaina nace wasa ta langabe kai tace mummy bata da time dina iam lone now ta kuma bata rai kamar wata babba.
Yayin da shi kuma ya wani kasheni da ido kamar yana son jin amsan da zan ba yarinyar.
Jin nayi ahiru yasa ta kara maimaita maganan a dan shagwabe na riko hannunta ina fadun dare yayi yanzu lokacun barci ne ai.
Tace No no tana dan bubuga kafanta irin na shagwaba tare da fadin mummy tace zamuje wurin prayers ne yanzu and I don’t want to go with her.
Jin hakan yasa na kama hannunta muka nufi dakin da nake muka barshi tsaye yana bin mu da kallo har muka shige ciki.
Muna shiga dakin ta fada saman gado tare da fadin ina wayana muyi game dan jin nayi sai can nace mata ai banda waya ni.
Mikewa naga tayi ta fita da sauri ashe zuwa tayi wurin baban ta tace ya bamu waya zamuyi game dani da ita nace banda wayani.
Can sai gata tadawo da gudu tana dan ihu tana fadin daddy give us his phone tana hawowa gadon.
Kallon ta nayi naga da gaske wayan ya ba yar tashi kuwa ta zauna tana dan danne danne a cikin wayan jin nayi shiru.
Ta dan juyo tana fadin sunayen game din dake wayan hankalina baya wurinta a lokacin.
Aunt may samayki kike tunane tace tana hawowa inda nake kwance a ringigine din.
Ajiyan zuciya na sauke nasa hannu na rugumay ta zuwa jikina nace mata ina tuna mamace dake gida da yan uwana.
Fuska ta bata tace kema kina da mama ne ?
Na shafa mata kai nace baby girl kin taba ganin wanda baida mama a duniya ?
Ta dan rage sautin muryan ta tace harda daddy ta yana da mama ta dago kai tana kallona taji abinda zan fada mata din.
Mamaki yarinyar tabani don tayi kankanta da wanan tambayan idanun ta har lokacin suna a kaina tana jiran amsa taji.
Shiru na sake yi na dan lokaci can a hankali nace yes yana da mama da baba har da grany tace har da brothers ?
Tana watso min idanuwanta masu girma kamar na ubanta gasu dal kamar hasken kwan lantarki.
Rugumay ni tayi tana shige min jiki ta marairaice murya tana fadin can you take me to them ?
I want to see them aunt ta fadi a dan maraice take naji wani tausayin yarinyar da sonta yana kamani lokaci daya.
Murya ta ne take fadin tasan uncle joshua tasan anty linda da grandmun da dad ashe tana da wasu yan uwa kuma na daddy su.
Shiru dukkan mu mukayi da hakan har barci ya dauke mu bamu sani ba muna lake da junan mu don har uwar tazo daukan ta don zasu can church sai dare sosai zasu dawo.
Samun yanayin data gamu yasa taji bata son tayar da diyar nata a lokacin ta fito rana fada mai ta samu munyi barci dukkan mu don haka zata tafi ita kadai.
Sai cikin dare na falka naga yadda muke kwance ta yarda wayan can gefe daya ta make a jikina gyara mata kwanciya nayi da kyau na kashe wutan dakin.
Washe gari ma tunda asuba ina sallah uwar ne ta shigo dakin a uzurce ta samu na tashi ina saman salaya take fadin tazo daukan faith ne zasu tafi wurin ibada yau special day ne na addua a gare su.
Haka ta kinkimi yarinyar tana barci suka fice a dakin kallon tausayi nabi yarinyar dashi har suka bace min na sauke ajiyan zuciya a hankali naci gaba da abinda nakeyi
Nikan tunda nayi sallah ban fito ba kuma banyi barci ba sai faman tunanen da nake a cikin dakin yayin da kamshi ke ziyartan hancina ta ko ina na girgi.
Fitowa shi ke nan daga daki da tunda ya dawo motsa jiki yayi wanka ya kwanta bai fito ba shima wanan zaman gidan ya damay shi a lokacin don dai kawai ya bama iyalin shi lokaci yake zaune gida tare dasu din ana shagalin esther dashi.
Yanayin data zo mai yasa ya gane tans dauke da magana a bakinta a lokacin.
Wuri ta samu takai zaune tana fadin your sister want to creat a sin to us why zata fadawa faith about your parents.
Alhalin tasan bata san da zancen su ba zata dauko muna wahala kasan halin faith da rigima fa yanzu gashi ta damay ni tana son tasan su ita.
Murmushin takaici ya sake yace Okey ke kuma baki son ta san dasu ko ya fada yana duban fuskanta .
Yarinyar ne ta zo ta rabe a jikin shi yadan rungumo ta yana fadin Queen what’s your problem tell me about it.
Ta bata rai kafin tace is aunt thinking about her parents na tambaye ta tace min akwai dad da mum da grany da ban sani ba.
Yace Oh realy tace aunt tana tunanen gida sosai daddy nima ina son sanin mutanen da take tunane din.
Merry tace you see na fada ma zata kawo muna matsala fa idan tana irin wanan maganan.
Kare mata kallo yayi da kyau kafin yace may wanan maganan naki yake nufi merry kina nufin yata ba zataje gurin iyayyena ba komay ?
Nan suka fara musayan baki tana fadi a hasale yarta va zataje inda ake kyaman su ba ko ita yaya ta kare balle yarta dasu.
Wanan maganan ya kawo muna matsala da merry ta fara canza mi fuska tana dadaure mun fuska ban gane zaman gidan ba ga baki daya ga wanda ya kawo ni ma ba kula nake samu ba gurin shi.
Na fara ganewa ta hanyar hana yarta ta kusance ni da zaran taga tazo inda nake yanzu zata zo ta cajata idan kuma na fito tana waje sai ta tashi ta shige ciki.
Ranan kawai tun safe na shiya suna barci na bar gidan don dama nagaji da zaman gidan sosai Allah ya taimakeni katina na shiga jirgin kasa yana cikin yar jakkar dana dauko.
Na sulale na tafi abina don nasan yadda ake shiga jirgin kasa din zuwa lokacin cikin ikon Allah na kawo kaina gidana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button