SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:18 – ????????????: ASSALAMU ALAIKUM WARAMATULLAH, , , , , ,
Washe gari bayan na gama komai har nayi wanka na shirya banji duriyan ya umar ba gidan.
Har nakai kofa zan fita na dawo don in sallamay shi kamar yadda anty farida ta fada min in dingayi idan yana gida.
Na tura kofan a rufe yake sai mamakin hakan ya kamani don bai faye rufe kofan shi ba idan yana gidan.
Juyowa nayi da niyar in wuce takardan dana hango ne saman dining table aje yasa na sauko da sauri na isa gurin na dauka ina dubawa.
Fatima nayi tafiya ban sani ba ko in dauki lokaci ban dawo ba komai da zaki bukata na amfanin gida na tanadar maki shi a store da fatan zaki kula da kan ki daga yayan ki umar.
Kamar ba school zanje ba a lokacin sai naga nz kai zaune ina faman tunane a raina gabin zan batawa kaina lokaci yasa na mike na rufo gidan na tafi.
Da kyat na samu mota don bus sun dan wuwuce saboda sakkon da mutane keyi zuwa wurin aiyukan su na yau da kullun.
Na kusa makara don ina shiga mai koya muna na shigowa lokacin haka akai lecture rabin hankalina yana ga tunanen ina yaya ya tafi.
Karfe daya saura muka fito daga daukan darasi don yin break da sallah a ka,idan makarantan kamar kullun duk wanda zaka hadu dashi a irin wanan gurin muke haduwa din girman makarantar ya baci department ne kala kala gasunan sai inda idon ka ya tsaya.
As usual mun san inda muke zama mu hadu a kullun a gurin na samu anty farida tana waya samun wuri nayi na zauna ina dakon ta mu gaisa jin da hausa take wayan ya fahintar dani a gida Nigeria take yin wayan lokacin .
Tun ina sauraren ta har na fara tunane sai can naji muryan ta kamar a mafalki tana fadin waiko yau lafiya kike yar gidan ya umar kamar yadda nake kiran shi a gaban ta idan wani magana ya taso itama haka ta fada min.
Na dawo cikin hayacina ina dan murmushi nace anty mun wuni lafiya yaya jama,an gidan ki cikin kako murmushin dole nake maganan.
Ta amsa da duk suna lafiya sai dai yau yanayin ki ya nuna kamar kina cikin tunane da damuwa sister ?
Bakomai bane anty na fada ina bude jakkata da nake amfani dashi a school din na dauko wayana dake cikin zip din ciki.
Ta kara fadin ko yau da kewan yaya ki kika tashi ne hakan na dan dago kai ina dariya tare da fadin kai anty yau yaya din ai a gidana ya kwana sai dai da safen nan ne naga takarda daya bar min wai tafiya ya kamashi ya tafi bai tasheni ba .
Amma dai wana yayan naki da yawan tafiya yake fatima kamar agogo ko yaushe yana saman hanya shi ?
Ai dama nasan kina kewan shi ne tunda mutum kike ba dabba ba duk mace mai lafiya da jini a jika ai zatayi kewan mijin ta na sunna ko ?
Haba anty har wani sabawa nayi da yaya umar ni na fada ina kokarin hade abinda nake ji a raina.
Tace da sannu zaku saba ai ki barshi kawai ya gama iskancin shi da iya shegen su na maza shi da kansa zai kawo kanshi inda kike sister.
Nace jiya yazo min da wata magana sai daga karshe yake fada min wai April full yayi min da sauri tace wani irin April full kuma ana April full sau biyu ne a shekara ?
Da sauri na dago nace na shiga uku anty watau yaya wayau ke nan yayi min ashe da gaske yake zancen ciwon kawu ganin hankalina ya tashi yasa yace mi wai april full yayi min.
Take idanuwana suka fara tsiyayan ruwa hankalinta ne ya tashi a rude take fadin maynene haka sister zaki jawo hankalin mutane gare mu kuma ?
Cikin dan rage sautin muryana nake fadin watau da gaske yaya keyi kawuna baida lafiya ganin hankalina ya tashi shine yace min wai wasa ne.
Kinga ki kwatar da hankalun ki kimin bayani yadda zan fahince ki mu san mafita tace dani.
Da kyat na hade kuka nayi mata bayanin komai tana saurarena sai dana gama tace banda abinki sister ai ciwo na Allahne.
Damu dake da lafiyan bamu fishi ga Allah ba sai kiga mai lafiyan ya tafi ya bar masu lafiya a jika shi lamarin Allah idan ya taso addua ake so bawa yayi don yanzu adduan mu yafi bukata ba wanan kukan da kikeyi ba.
Mijin ki yayi maki wayau manyane ya wuce ya barki don kada ki daga mai hankali idan kin matsa sai kin bishi can zuwan may zai karaki dashi ?
Ai addu,an ki kawai kawun ki yafi bukata gareki ki kwantar da hankalin ki Allah yasa mijin ki yayi farar tafiya ya tad kafadan kawu lafiya.
Cikin murya mai kama da rada na amsa mata da amin anty ina kada kaina ina fadin amin anty cikin damuwa.
KANO
Ba wanda yasan da zuwan shi suna zaune cikin halin damu har lokacin ga fargaban halin ciwon da maigidan ke ciki ga kuma kishin da ba,a daina shiba har lokacin.
Sallaman shi yasa su gaba daya dago kai suna amsa mai mai a yanayin yadda ya shigo cikin damuwa ganin su ya kara sa hankalin shi tashi tun bai gamsu ba.
Hjy jummai tunda tayi arba da dan nata tayi saurin kawar da kai daga kallon shi.
Yanzu idan zata kirga shekara daya da rabi kenan rabon data ganshi tunzuwan da yayi ya samay ta gidan wanta sai wanan ganin da tayi mai.
Ga al,adan bahaushe girmamawa gana gaba duk da fadin da malaimai keyi baida kyau malam bshaushe bai yarda ya yar da wanan al,adan na tsugunawa gaida mahaifanshi ba wani lokacin.
Shima Umar hakan yayi don bai gaida kowa ba duk da sannu da zuwan da suke mai sai daya samu wuri ya dan rage tsawo ya gaida su a cikin jimmila ga baki daya wanda ke gurin.
Su mama hadiye sukace ashe kun samu labari rashin lafiyan yace eh gwaggo Aliyu ya kirani yake gaya min abinda ke faruwa naso tasowa saidai hakan bai samu ba saboda wani dalili.
Yau ai jikin nasa da dama sosai don yana dan motsa idanun shi kadan kadan hakan yasa hankalin su ya dan fara kwanci.
Yai masu yaya mai jiki duk a cikin jam,i ya mike tare da tambayan wanda ke cikin dakin a lokacin suka bashi amsa kusana tare banda mamu da hjy su da suka kawar da ido daga kalo shi.
Dakin ya shiga su kawu balarabe ne da kawu mustapha a cikin dakin zaune sun tsura mashi ido a cikin tashin hankali.
Jin an turo kofa yasa suka juyo lokaci daya suna kallon kofan don sin hana kowa shiga saboda rikicin dayaso tashi tsakanin hjy jummai da hjy maryam wurin jinyan.
Yasa suka hana kowa shiga a yadda sukaga dama da farko an rabawa kowa lokacin zuwa saidai hjy jummai tace basu isa ba zata zo a duk lokacin da taga damane ita.
Yasa suka kasa suka tsare don sanin halinta suna jinyar dan uwan nasu da kansu wanda hakan yasa duk wanda yazo saidai ya tsaya daga waje inda kowa yake sai idan suna bukatan wani abin zasu kira wacce keda duty a lokacin tazo ta taimaka masu da wani abin.
Ganin ya umar yasa su sauke a jiyan zuciya suna fadin umar ka taso ke nan ga Alh nan jikin yaki har wanan lokacin.
Direct wurin gadon da mahaifin nasa yake ya nufa kai tsaye ya dan tsaya a kansa ya tsura mai idanu .
Can ya juyo yana fadin likita yayi bayanin akan matsalan dake damun shi ?
Kawu balarabe yace eh to yayi bayanin don sunce akwai hawan jini da sugar sune mu sabbabi matsalan duka.
Ya umar yace zanso mu fita dashi waje don zaman shi a hakan ba ba dadi gaskiya tunda an gwada na nan ba aci nasara ba har yanzu.
Allah sarki mukan ai munga sauki yanzudon yau ma an samu cigaban samun lafiya sosai don yana bude idanun shi lokaci lokaci.
Ajiyan zuciya ya sauke don jin bayani su ya juya yana kurawa mahaifin nasa idanu mai nuna zallan tausayi a gare shi .
Ya kara takun shi zuwa wurin gadon ya tsurawa kawu idanu kamar yasan shine a gurin sai ya bude idanun shi a daidai lokacin ya kafe umar din da idanuwa kamar yana kokarin sheda ko waye a gaban shi lokaci.
Daddy sannu umar din yace mai sai ya lumshe idanuwan shi a hankali dan dukawa umar din yayi daidai saitin kan mahaifin nasa yana mashi adduan samun sauki daga Allah.
Yakai wani lokaci a hakan kafin ya dago daga dukawan da yayi din ya juya zai fita daga daki nmuryan kawu balarabe ne ya tsayar dashi.
Zaifi kyau ko zaka fita dashi a bari har ya kara samun lafiya zaifi tau baba Allah ya tada kafa dan shi yaba daddy lafiya suka amsa da amin.
Ya fito da sararen gwiwa don yadda yaga daddyn nasu a lokacin rai a hannun Allah.
Jin kara bude kofan yasa na wajen juyowa suna kallon mai fitowa daga dakin .
Umar ka fito mama hadiye tace dashi yace a wani yanayi na nuna rashin jin dadin shi ga ganin mahaifin nasa.
Ya dan samu wuri ya jingina bayan shi ga bango tare da harde kafan shi daya a cikin daya.
Ya lumshe idanuwan shi muryan mama hadiye ne ke fadin kaje gida wurin hajiya ka huta don da alama isowan ka ke nan daga airport ka nufo nan.
Bude idanuwan nasa yayi tare da sauke ajiyan zuciya yace Amman tana gidane mama tace eh dazun nan ta koma tazo taga jikin yaya din.
Yaya su Fatima dasu Amina sarka sarkin rikici duk suna lafiya ?
Ajiyan zuciya ya sauke kafin yace suna lafiya na barta saboda karatun ta da ya fara nisa yanzu,
Dago kai hjy jummai tayi ta watsa mashi wani kallon takaici ta kawar da fuska a gurin su.
Wasu daga wurin sunga abinda ya faru sai dai basuyi magana ba ya dan busar da iska yana fadin zan dan je naga likitan dake kulla da daddy din .
Suka amsa mai ya tafi ko juyowa baiyi inda suke zaune din zuciyan shi cike da damuwa ko kallon yanayin nasa yaje gurin likitan sun dan dade a office din kafin ya fito kai tsaye gidan mahaifin shi ya nufa wurin Amma.
Kamar a mafaki tagan shi falon nata sadauki kaine rafe ashe kana da labarin abinda ya faru da mahaifin naku ?
Ya kai zaune tana kokarin tashi da kyat yace ina kuma zaki Amma tace wai in kawo ma abun sanyi ka sha ko ta fada tana kallon fuskan shi.
Yace barshi kawai Amma ya mike ya nufi wurun fridgen din nata da kanshi ya bude ledan ruwa da sauran tarkace yagani yadai dauko ruwan ya dawo ya zauna a inda ya tashi da farko.
Tace tana kallon shi kai kadaine tafe wai banga mutumiyar tawa ba tashigo.
Ya kalle ta da idanuwan shi da sukai mai ja yace banzo da ita ba ni kadai nazo sai wani jikon zan shigo da ita wanan tafiyan bana hankali kwance bane.
A ikon Allah zan so ganin mutumiyar tawa inga yadda ta koma yanxu.
Ya dan tabe baki tare da fadin tana nan yadda kika santa sai karatun ta da yanzu yayi nisa sosai.
Mikewa yayi yace zanje in dran, huta na dan wani lokaxi tun yanzu baka ko huta ba ?
Yace eh nazo dai kawai in ganki ne yace yana kokarin fita daga falon nata kai tsaye sai dai cikin ran shi yana mamakin halin mahaifiyar su.
Don dai irin kallin da rake jifan shi dashi yasare masa gwiwa sosai do yasan tana cike dashi sai dai ba zaice ga laifin da yayi ba lokacin .
Sai ba bayan azahar ya falka wanka yayi yafito yayi sallah kai tsaye asibuti ya nufa.
Wanan karon iya hjy maryam ya sama a asibitin wurin mahaifin nasu itace keda zaman rana a wurin shi karfe shidda mamu zata karba ita kuma ta koma gida.