SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Tun dawowa na na kasa sukuta komai a rayuwana sai faman tunanen da nakeyi ni kadai zaune a falo ina yawan kallon kofa da wayana na dake gefena aje ina sa ran kiran yaya umar a lokacin.
Saidai har dare gashi bai kirani ba balle inji idan Nageria ya tafi a ban wani na gida muyi magana dasu.
Saidai bai kira ba har lokacin da nagaji na mike na kashe komai na shuga dakin kwanana na kwanta da kyat na samu barci ya zo mi lokaci.
Waahe gari ma haka na daure zuwa daukan karatu don fita zamuuyi yin pratical da malamin mu .
Ban yarda mun hadu da anty farida ranan don kada ta gane ina cikin damuwa tai min wani fassara na daban.
Gashi har lokacin ya umar baibugo min waya ba ni kuma banda layin kowa na gidan namu.
An shigaKwana uku shiru ba wayan ya umar ba dalilin kiran shi hakan ya kara tayar min da hankalina sosai.
Haka yasa na fara zargin ko dai wanu a babu ya faru da kawun ne hae ya saka ya umar ya tafi .
Gabana ne ya fadi sosai a lokacin take na shuga share kwallan da ya zubu min a idanuwana daka ganni kasan akwai damuwa a tare dani lokacin
A rana na biyar ne ina zaune nayi tagumi sai ga wayana yana ringin na dauka ina dubawa ya umar dinne ke kiran layina.
Da sauri na dauki wayan ina kokarin karawa a kunne na da sallama ya amsa min da kyat tare da fadin kina nan kin saka kanki cikin damuwa ko ?
Nace ya don Allah ka fada min idan wani abu ya faru da kawuna ne in sani yace ba na fada maki baida lafiya bane ?
Yaya kayi hakkuri ban son in rasa kawune yanzu ke kina masa fatan mutuwa ne ko may da kike fadin wanan magana ?
Kukan dana fara yasa ya kashe wayan gaba daya haushin kaina naji dana kasa controling din kaina a lokacin balle inji halin da kawu ke ciki lokacin.
Daga lokacin bai kara kirana a waya ba duk zaman garin ya isheni ban san ko ina ba daga gida sai school saboda sabon da mukayi tun a gida da rashin fita ko ina yasa ko a nan ma wanan halin ya bini hakana.
Na ramay na lalace ko wani gyara duk na daina karatuma kamar ya zama min dole nakeyin shi ban san ina son kawuna haka ba saida hakan ya kasance dani yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:19 – ????????????: SALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI, , , , , ,
Wasa wasa saida ya share fiye da wata daya a gida duk da banda wani matsala a bangarena ko na abinci dana wurin karatuna ga baki daya.
Tun ina tunane har na gaji na fawwala al,amarin ga Allah ranan da kadaici ya isheni anty ta karbi wayana ta bude min whatsfapp naji dadin hakan sosai don ranan wuni nayi ina kallon yan makarantar mu da nake da layin wayan su.
Wani dp na saka inda mukayi da wasu coursemate dina nice a tsakiya sun rugumoni su biyun muna saye da labcoath a jiki mu cikin nishadi.
Tsananin hasken fatana na daya karu yanzu yasa mun saje da su dan banbancin dai kadan ne dasu a photon.
Son da nakewa photon yasa na saka shi don sune kawayen da nayi na kut da kut da muke karatu dasu.
Munyi photon a cikin farin ciki da so da kaunan juna a tsakanin mu don hakane na zabi wanan photon a matsayin dp din wayana.
Zaune nake saman dogon kujeran falon na mike kafafuwana ina kallon tv dake aiki sai corn dake hannu na ina ci a hankali ga waya da na mayar da hankali muna hira da anty farida cikin harshen hausa.
Nigeria Kano
Ya dawo asibiti gurin daddy da yanzu akafara ganin sauki gareshi sosai yasa hankalin iyali ya fara kwantawa .
Ya umar ne ya shigo falon shi a lokacin tun safe da ya fita zuwa asibitin yana can gurin daddy shida yan uwan shi sun kewaye mahaifin nasu a nan su salma da mazajen su suka samay su aka cika taro dasu har wani lokaci suna gurun Alh a zaune sai matan ne suka dan fita daga dakin zuwa inda uwayen su mata suke zaune.
Karfe hudu ya baro asibitin zuwa gida sai da ya zauna yaci abincin da mai aikin shi ya girka mai yaci don bai tsaya karyawa da safe ba ya fita .
Ya gama a wurin yai zaune tare da balance saman kujeran da yake zaune a kai ba gwanin shiga whatsf bane shi amma ranan sai yaga ya shiga don duba sakonne kamar yadda yakeyi idan sun taru.
Ya gama komai kamar ance ya duba sunana daya rubutawa kaddara sai yaganni a online da alama ina saman interneat a lokacin da sauri yace kai , tare da dan zabura da mamaki.
Da sauri ya tura sako ke may kike a nan ?
Waya bude maki wanan abin kike yi ?
Jin sako ya shigo min a jere lokaci guda yasa na aje corn din dake hannuna ina kallon waya da mamaki.
Baki na mere ni kadai a gida ina jan tsoki tare da fadin dan rainin wayau kawai so kake in mutu a garin mutane saboda bakin halin ka.
Ban bashi amsa ba sai ma sauka danayi ga baki daya na mike tare da kashe komai na falon na hau sama na kwanta.
Ina tsaka da addu,an shiga barci waya ya dauki rurin kira a lokacin dubawa nayi ya umar ne yake kirana .
Kallon wayan nakeyi ba tare da na dauka ba har ya gaji ya katse ban daga ba sai can naji sako ya shigo min again share shi nayi sai can na duba sakon naga ya rubuta ke ki dauki waya nace.
Kaci min mutunci daga can ko ka raina min hankali tunda har yanzu na goye kake kallona a idon ka kin dauka nayi na share shi barci yayi gaba dani a gurin.
Shiko yana can yana cika yana batsewa har akai magariba yana jin kamar yai tsutsu ya ganshi a London ya makeni.
Kallin dp din dayayi zooming a wayan shi yayi mun fito shar damu a photon da kayan gwaji a jikin mu inda nau,in jikin mu ya nuna mabanbantan kasa muka fito gaba dayan mu.
Kiran sallah yasa shi mikewa ya nufi ciki alwala ya dauro ya fita daga gidan a gaugauce kada ya rasa jam,in sallah magariba na lokacin.
Yana fitowa ya nufi family house din su kai tsaye wurin hjyn su ya nufa duk da hattaran shi da uwar keyi tun zuwan shi kasan .
Sai yake nuna baima sam tanayi ba don zai shigo ya zauna dukda nuna mai kin kulawan da take sai yayi zaune yana bata lokaci da waya a hannun shi.
Sai idan su Aliyu sun shigo ne suke dan zama suyi hira wani lokaci kuma su kwasa su fice zuwa asibiti.
Har yau hjy saboda bakin ciki ta kasa bude baki tayi mai magana ko ta tambayi iyalin shi ga baki daya batayi ba.
Yau ya shigo babu kowa a falon sai tv dake aiki yayi sallama ya shiga kai tsaye ya samu wuri ya zauna shi kadai a falon.
Nafisa ne ta fito jin sallaman shi tana amsa mashi sallaman nasa tare da fadin ya umar ashe ka shigo.
Yace ummm a dakile tace yaya in kawo maka abin karyawa ne duk da tasan ba zaici ba halin sa ne wanan tun lokacin da ya tare a gidan shi bai damu dayaci abinci a gidan ba.
Ta samu wuri ta zauna tana fadin ni yaya wai yaya A ruwa ban samu tambayan ka ita ba tunda kazo ?
Dan dago kai yayi yakale ta yace tana lafiya karatu ya hana inzo da ita daka koma da ita inda ka dauko ta.
Muryan hjy mahaifiyar su ne, dake fitowa take magana tare da hararan shi dan murmushi ya sake yana fadin barka da fitowa mama.
Ya dan zamo daga inda yake zaune yana gaida ita da kwana bata amsa mai ba sai cewan da tayi kana zaton na janye maganata akan auren wanan makiran yarinyar da kakeyi.
Idan sun mallake ka sun mallake ubanka ni basu mallakeni ba ni ba kuma ba zasu iya mallakeni ba yadda suke so.
Har yanzu ina kan bakana sai ka saki wanan yarinyar don ba zan hada iri da irin matsiyata ba a zuri,a ta.
Ayi hakkuri hjy lokaci na zuwa da hakan zai faru ina wanan abin ne saboda ke da daddy mu.
Sabodani ta fada da dan mamaki tana kallin shi tare da kada kai tace ka dauka zaka iya yaudarata ne babawo ?
May ka mayar dani ne wai kana nufin zaka zauna da yarinyar da baka so har tsawon shekara daya da rabi da ita kana kallon ta ?
Wani irin dagowa yayi yana kallon mahaifiyar tasu da mamakin kalamin ta gare shi tace kai waliyi ne ko shehi da zaka zurawa mace haka idanu kana kallon ta ?
Kiyi hakkuri mama ba hakan nake nufi ba wanan yarinyar karatu take yanzu haka a can sune dalilin da kikaga ban dauki wani mataki akanta ba har zuwa wanan lokacin.
Aliyu ne yayi sallama ya shigo kallon yanayin zaman su ya fara sai kuma ya juya wurin mahaifiyar su yana gaida ita da kwana kafin ya juya wurin dan uwan yana fadin bros ashe kana nan gidan ka na fito yanzu daga can nake nayo nan.
Yace na shigo ingaida su da kwana don in na tafi asibiti ba zan fito da wuri ba yana nan yana karanta min hauka don ya daukeni mara hankali.
May kuma akayi mama yana kallon dan uwan nasa ta tabe baki tana kawar da kai daga kallon shi.
Umar da dama yake neman hanyar gudu daga wurinta yayi saurin mikewa tsaye yace barin leko Amma mu gaisa in zo mu wuce.
Zaka dawo ka samay ni ai hjy tace tana hararan shi shidai ya fice ya barsu da Aliyu a falon zaune.
Ya samu Amma tare da mamu a part din mamu tana ganin shi nauyi da kunya ya kamata lokaci guda ta shiga dan kamay kamay taga surikin ta wai.
Gaida su yayi a daidai lokacin da mamu ke mikewa tace gwaggo zan tafi sai dai idan na dawo ke nan kuma.
A,a kardai ince yanzu kuma kunyar Sadauki kike ji kuma maimuna ta fada tana kallin mamu din da dan murmushi a fuskanta.
Mamu tace kai haba gwaggo kunyanshi kuma tana kokarin fita daga falon yace naso tunda nazo in baki layin wayan ta sai dai bamu samu kebewa da ke b.
Jin hakan yasa mamu ta dan tsaya daga tafiyan da takeyi din tace badai tana lafiya ba ?
Lafiya take yace yana kokarin ciro wayan shi a cikin aljinhun shi yana duba lamban na.
Mamu da za,a bude zuciyar ta a lokacin aga farin cikin da take ciki a lokacin bai musultuwa .
Yace saidai ba a samun ta sai weekend ko bayan karfe biyar a daidai lokacin tana gida ke nan don shine lokacin da ake samun ta kawai.
Ya karanto mata lamban ta loda a wayan ta cikin farin ciki tare da fadin na gode tana shirin juyawa Amma tace ni ina ta jiran ace muzo gashin cibiya sai naji shiru?
Dan kallon Amma yayi ya kawar da kai ba tare daya iya furta komai ba a wurin Amma taci gaba da fadin gashi yan uwanta wasun su suna da ciki yanzu.
Amma kin dai san ita karatu takeyi yanzu ko idan tayi ciki yanzu wa zai taimaka mata da raino da sauran su don gudun kada Amma ta gano komai.
Tace may ye aikina a nan ko aikin kakarta dake bukatan taimako sai ni in hakkura wanan boyar Allahn ta tafi don matar tana bukatan kulawa sosai.
Wata mace kuma kike magana yanzu kuma Amma ko har kin fara rudun tsufan ne hakan yanzu ?
Tace a dan maraice wanan mahaifiyar uban yar nan nake zance don tsakanin ta da A ruwa sai Allah .
Shiru yayi bai tanka mata ba sai can ya mike ya kalli Amma dake masa hiran da bai saurare yace zai tafi asibiti ya duba mahaifin shi dake can.
Amma tace ni kan ban gane wanan abin ba da na dauko maka zancen matar ka sai ka gudu ka barni anya kuwa sadauki kana kula da hakkin yarinyar nan yadda ya dace a can ?
Da sauri yaja ya tsaya guri daya yana kallon Amma kafin yace ko kinji wani abune gamay da zamana da ita ?
Tace ko daya yo a ina zanji labarin ku a gurin ka ya kamata muji komai gamay da yar nan saidai tun zuwan ka ba wanda kaiwa zancen ta a gidan nan kaf.
Hakan yasa nake zargin irin zaman da kukeyi a can da ita don yar nan Amana take a gutin ka kasani.
Ki bari in dawo indai zancen ta kike son ji zakiji komai idan na dawo shike nan ko ?
Ya fada yana kokatin fita yayin da Amma ta tsare shi dz ido tana zargin shi.
Luckyly ranan ina gida ban fita ba sai after two zamuyi pratical don haka na tsaya dan gyare gyaren gidan.
Mamu ta kasa hakkutin kirana har yamma gwada lauin daya bata take ta faman bin nombobin da kallo tayi a wayanta sai ko ya shiga.
Daga inda nake tsaye naji waya na ruri a raina na dauka anty Farida ce don nasan ba zai kirani ba shi a wanan lokacin.
Haka yasa na isa gurin don daukan wayan saidai ganin nomban Nageria yasa na tsaya wasiwasin daukan wayan ina kallon nomban karshen lamban yasa na gane layin mamu ne da don dama sauran nomban na biyun karshe ne ban haddace ba.
Da sallama a bakina na daga yayin data karba min ta bangaren ta ihu na saka sai kuma na sa kuka ina fadin mamu kukane yazo min lokaci guda.
Dan murmushi naji tayi ba tare da ta ban amsa ba har na saida taji banda niyat tsahaitawa tayi magana.
Sayadi don na kiraki kike wanan kukan hakan komay ashe dana sani da ban kira layin ki ba na barki.
Da sauri nace mamu ina kewan ku ina kewan kowa a gida nan banda kowa a nan sai Allah sai anty farida dana hadu da ita a school din mi ta zamay min kamar yar uwa.
Tace dama aure haka ya gada Sayadi idan kaji shiru lafiyace inji ba haushe muma muna kewan ki sosai kin sani a kullun sai gwaggon ki da kawun ki sunyi maganan ki hakama kannen ki.
Nace mamu bandake ke nan ko dan murmushi tayi tana fadin har yanzu dai kina da sauran wauta ashe ?
Na zunburo baki kamar tana ganina nace mamu ni yanzu banda wautan komai ni kadai fa nake rayuwana a gidana sai idan ya umar yana gidan nake tare da wani.
Dama ai idan ka auri mai mata Sayadi hakan ne ke faruwa don ba kullun yake tare da kaiba sai lokacin ka ai.
Duk da ban fahinci may take nufi ba nace mamu da gaskiyane kawu baida lafiya ?
Ta katse da fadin amma ya samu lafiya sosai yanzu don mijinki bai nisa da juyowa gare ku ai.
Yaya wurin su merry da yar ta suna lafiya nace banda labatin su mamu don ba gida daya muke zaune da su tsakanin akwai dan tazara so sai.
Sai dai wani lokaci nakan tafi inda suke amma yanzu na dade banje ba a cikin hikima da basira irin ta manya mamu ke min tambaya ina bata amsa ba tare da komai ba sai dai bata tambayeni irin zaman da nake da yaya umar ba nima ban fada mata ba.
Na tambayeta labarin amma da manjo da su Aisha ta dan ban amsa a gurguje akan suna lafiya Aisha nan haihuwa ko yau ko gobe ma .
Dan ihu murna nayi jin hakan tace salma da ikilima sun haihu wata biyu daya wuce nace ikon Allah.
Tambayan karshe da tayi mun ne yazo min a bazata tace ke yaya labarin haihuwa wurin ki ko har yanzu baki samu komai bane ?
Wani iri naji a raina na canza fuskana a lokaci daya tare da fadin mamu kin san ina karatune yanzu fa .
Sayadi ke nan karatun ki shi zai hana wani abu kardai kice min kuna wanan planning din banzanne kuma.
Ban san may planning ke nufi ba na hau yi mata shirmay sai dai abin yaro da babba a cikin shirmay na ta fahinci akwai matsala a zaman mu mukayi sallama tace idan taje asibiti zata ba kawuna waya mu gaisa.
Mukai sallama a cikin so da kauna irin ta uwa da yarta ta barni ina kewan ta ina hawaye ni kadai a gidan ina jin kamar in bude idanu in ganni a gaban mahaifiyata.