SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Umar yana zaune yayi wani irin zabura wani tunane yayi a zuciyan shi nayin gangancin ba mamu layi na kai tsaye ba tare da yayi worning dina ba kada in fada mata komai gamay da zaman mu.
Yana zabura ya duba agogon hannun shi da sauri sai ya mike tsaye don yasan lokacin daya ba mamu na kirana yayi don haka tana iya kirana in tona mashi asiri don ba wayau ke gareni ba.
Waje ya fita duk da likitana ciki yana duban yanayin daddyn su lokacin sai dai hakan bai hanna shi fita da sauri daga dakin ba .
Can dan nesa da mutane ya nufa ya kira layina lokacin ina zaune na saka abincin a gaba ina kallon na kasa ci sai tunane da nakeyi.
Wayana dake aje saman table din yayi kara da sauri na kalla a zato mamuce ke kiran layina lokacin.
Ya umar na gani wanan karon da sauri na dauki wayan ina mai sallama ya amsa min yadda yake karbawa nice nayi mai ya jikin kawu yace da sauki a takaice.
Zan kara magana ya tareni yana fadin ke naba maman ki layin wayan ki nasan zuwa anjima zata kiraki don haka saura ki mata shirmay da kika saba idan ta kira.
Don kika kuskura kika fada mata wani abu gamay dani ranki zai baci sosai wallahi idan na dawo garin nan don na kusa dawowa kwanan nan insha Allahu.
Shiru nayi ina sauraren shi har sai da naji yayi shiru nace wai mamu kake magana ai ta kirani ko tun rana mukai magana da ita.
Da dan karfi a razane yace what ?
Nace eh ina mai jin haushin shi a raina cewan da yayi min shirmay nake dashi a raina.
Yace makika fada mata data kira ki nace kamar ya magana tsakanina da mahaifiyata kuma saina fada ?.
Yace ke ni kike fadawa wanan maganan don rashin kunya ko may nace ni ban maka rashin kunya ba ai na daiga uwatace ta kirani ai.
Ke may kika fada mata nace kin tsaya kina min maganan banza da ina kusa dake dana doke wanan bakin mai maganan banza.
Ni zaki nunawa maimuna mahaifiyar ki ce ko mai na mayi regret din bata layin ki danayi tun farko don ba hankaline dake ba nasani.
Duk naji wani maganan da kika fada wanda bai dace ba a garin nan sai na saba maki sosai idan na dawo .
Jin yana magana kamar tababe yasa na kashe wayan da mamakin shi a raina ina tunanen may yake nufin zan fadawa mamu bayan alherin da yake min a nan din ga karatuna iba yi hankali kwance.
Matsalata daya shine kewan gida dake addabata ko yaushe bayan wanan wani hali yake zaton zan fada a gida dayake min din.
A bangaren shi kuwa yana kashe wayan Aliyu ne ta gani tsaye a bayan shi da alama duk maganan da yake fadamin Aliyun yaji shi lokacin.
Yana juyowa sukai arba da Aliyu din wani irin gilty ya kamashi lokaci guda ya daure fuska yana fadin kai kuma maynene hakan kazo ka tsaya mun a kai ina waya.
Dan murmushi Aliyu yayi, yana fadin cool down bros likita ne yace a kiraka ciki haka ya wuce dan uwan ba tare da ya amsa mashi ba.
Aliyu ya bishi da kallon maki yana girgiza kanshi cikin takaici yabi bayan shi zuwa ciki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:19 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , ,
Mamakin kalamin ya umar na kwana dashi a raina duk da kurciya ya hanani gano inda maganan shi ta dosa a lokacin.
Amma zuciyata bata hanani hangon ma,anan maganan tasaba sai dai bankai can inda tashi manufan ya dosa ba.
Washegari mun shiga karatun mu lafiya ban nemi anty ba don nasa yanzu ita karatun su yayi nisa tana gab da gamawane lokacin.
Bayan mun taso sai ga kiranta a wayana tana fada min ta tafi don yaronta da baida lafiya ranan.
Nayi mata Allah ya sauwaka muka kashe wayan bayan na dawo gida abinci kawai naci naga ya dace in leka gidan anty farida a karo na farko duk zaman mu tare ban san gidan ta ba ban ma taba zuwa ko layin nasu ba a rayuwana.
Shiryawa nayi duk da yamma yayi sosai na fito tare da rufe gidana na nemi taxi ta hanyan fada mai layin duk da ba nisa sai daya dan kalleni.
Ban damu da hakan ba duk da nasan manufan dan taxis din lokacin ganin yayi inda zamu a unguwar muke sanin ban san gurin ba ya hanani damuwa a lokacin.
Sunan layin da nomban gidan na fada mai sai gashi cikin dan kankanin lokaci ya ajeni a kofan gidan na biyashi kudin shi ya tafi.
Tsayawa nayi ina karewa unguwar kallon mamaki a raina duk kusan ginan iri dayane sai dai bai kai wanda nake girma ba da komai nan na gane ba cikin karamin gida nake ba ashe.
Na taka a hankali zuwa kofan na danna bell din sallaman dana gani a gidan ringing biyu aka bude kofan wata yar matashiyar budurwa ce a kofan tsaye tana min kallon mamaki.
Dan murmushi na sake a fuskana tare da fadin zainab ko don yawan kiran sunan ta da anty keyi kanwar mijin ta da sukazo da ita don kula da yaran su.
Itama murmushin ta mayar min a fuskanta tare da fadin kina neman wani ne a cikin harshen turanci tayi magana nace eh da hausa don ta gane nima ba hausace yar uwanta.
Juyawa tayi tana fadin anty farida ga wata bahaushiya yar uwan mu tana neman ki a kofa tare da kokarin jaye min daga hanyar shi don taban guri don in shiga .
Lah ikon Allah ashe kina hanya baki fada min ba fatima dan juyowa zainab tayi ta kalleni tare da mamaki a fuskan ta tace anty wanan dince fatiman dama ?
Anty tace itace Fatiman zainab yau dai kinganta a gidan mu ko ciwon daddy ya jawo muna ita zuwa gidan nan.
Zama mukayi muna gaisawa tare da tambayan ta jikin yarin nata da baida lafiya ta nuna min shi kwance saman kujera tare da fadin gashi nan yaji dama sosai na samu Abban su ya kaishi asibiti sun karbo magani.
Ban zauna ba na nufi gurin yaron tare da fadin babana ya jikin naka ina kokarin taba lafiyan jikin inji yadda yake.
Yaron ya dan dago kai tare da fadin naji sauki a hankali abinda na zo mai dashi na ciro a jaka na mika mai cikin kayan makulashen da yaya ya tara mu a gida wasu ban ma san dadin su ba har lokacin.
Yaron yai zubur ya mike tare da fadin nagode ya karbi ledan ya fara budewa a hankali ya dago kai ya kara fadin nagode anty.
Zainab ce ta matso inda muke tana fadin yau dai ciwo ya warke ke nan gidan nan tunda ga kayan kwadai an samu tana kokarin karban ledan a hannun yaron ya kabe mata hannu da sauri yana fadawa uwar.
Oya zainab dauki diyan ki zuwa ciki anty tace tana kallin zainab din a lokacin har budurwan ta mike tsaye taja hannun yaron zuwa ciki .
Sai lokacin nake tambayan ta yarta guda tace tana ciki tana barci ruwan da ke gaba ta kalla tare da fadin baki sha ruwa ba ko a kawo maki abinci ne don an kare ko ?
Nace banda yunwa yanzu gaskiya anty sai dai zuwa an jima wata kila zan dan taba na fada mata hankane don ta saki rai dani.
Har yanzun dai maigidan ki bai dawo ba kasan nan ba fatima tana kallona take maganan na dan duka ina tsiyaya ruwan dake gabana nace.
Bai dawo ba anty sai dau munyi waya ga jiya dashi har da mama ya bata layina ta kirani .
Kai amma ko ya kyau ta gaskiya dama abinda nake son tambaya ke nan yanzu ai.
Nace sai dai anty kamar an tursasa shi ya bata layina don daga baya ya kira yana min fada nan dai na kwashe yadda mukayi na fada mata komai .
Sai dan murmushi naga ta sake a fuskanta tare da girgiza kai tana fadin barazan banza ke nan yasan yana jin tsoron mahaifan sa amma baya jin na Allah dake kallon shi .
Amma ai anty yana kula dani tunda ya tsaya min a karatu gashi babu abinda na nema na rasa a rayuwata matsalata daya shine rashin yan uwa a kusa dani.
Wanan kuma nasan na dan lokaci kadan ne da zaran na gama kararuna zan koma gare su ne ba shike nan ba anty.
Ido ta zuba min tun lokacin dana fara maganata babu ko kyatawa har na kare .
Naji rata wani dogon tsuki tana fadin Fatima kin ko san may aure yake nufi a rayuwan ki ?
Mijin kine fa na sunan ma,aiki kina zuwa makaranta a gida malaman kun suna koyar daku abinda aure ya kunsa a addinance kin sani ?
Shi kansa yana tauyewa kansa hakkine akanki kuma ke kanki yana cutar da rayuwan ki ta fanni daban daban fatima.
Ke bari dai in fada maki gaskiya ki sani rashin tararyan da baiyi dake na aura taiyya yana cutar dake sosai fatima sosai.
Iyayyen ku bawai sunyi wanan hadin bane a tsakanin ku don kizo nan kiyi karatu kawai ko ya zuba maki ido haka yadda yake kallon ki.
Shin fatima ke ba mace bace baliga mai jini a jiki da zaki kwana gida daya da mijin sunan ki baki ji komai a rayuwan ki ba.
Ruwa na dauka na sake kurbawa a hankali idona suna a kanta na aje kofin a hankali nace, ko daya anty don ni a matsayin dan uwa na jini nake kallon shi .
Ko kadan ban taba mashi kallon miji a gareni ba sains yan uwan taka har matar shi duk basu gabana wallahi .
Ni dai burina kawai in ga na hada karatuna na koma gida gurin iyayyena na kai masu kwalin sun gani.
Kai amma sai kuma tace wai fatima in tambaye ki man ?
Yanzu shekara nawa kile ne nace cikin dariya sha takwasa nake yanzu zan shiga na sha tara koda nazo nan ina da shekara sha bakwai cif anty.
Gaskiya wanan dan uwan naki bai dace dake ba wallahi cutar yayi yawa wallahi .
Shiru tayi kamar may tunane kafin can tace kina jina shin wai sharan dana baki a baya kina amfani dashi fatima ?
Ta tsareni da ido tana son jin amsa daga bakina a lokacin na dan kai bayana ga makarin kujeran da nake zaune a kai nace ina wasu ban wasu gaskiya.
Yau she ma na ganshi a gidan har zan tsaya mai wani kwarkwasa ko shagwaba can anty ?.
Mutumin da zai shigo gida a takure kamar wanda yazo bakunta a kullun fuska a daure ns dan ja tsuki tare da fadin bari kawai mu tafi a hankan dashi anty.
Ba zan bariba Fatima ta fada a tsawace kamar mai maganan bacin rai a lokacin da wani tace kin san kuwa irin cutar kanku da kukeyi daga ke har shi din yanzun haka fatima ?
Wallahi da ace nasan ainihin iyayyen ku da nakai karan ku gaba daya gurin su don hakan ne baya son kiyi hurda da kowa a garin nan.
Ko ranan danaje gaidashi ai nasan sai daya titsiyeki da tambayan ina kika sanni ko ba ai hakan ba don yadda naji ya kiraki ranan nasan da akwai maganan da yayi maki akaina ?
Kawai dai tambayana yayi a ina ba sanki na fada mai shine yace baison yawa kwashe kwashen mutane ya fada min tun farko.
You see dama ai na fada a raina don hakane bai son yaga kina hurda da kowa fatima don kads a fahintar dake abinda baki sani ba ki bitkice mai lissafi.
Ya kamata ki natsu ki san may aure yake nufi Fatima kema fa mutum ce kuma aure ne ya haife ki ba a aure ayi tararya da namiji aka haife mu mu ?
Don hakan ki canza ki nuna mashi ke din kin san abinda kikeyi bawai ina nufin ki bayar da kanki gare shi ba lokaci guda a,a .
A cikin hikima da basira zaki fito mai may kika rasa wanda ake nema a jikin mace Fatima ke zaki iya fitowa gasa sarauniyar kyau wallahi kici aduk inda kike.
Ya kamata ki canza idan mune yau bamune gobe ba don yanzu haka in ance yan uwan auren ki sun haihu ko suna da ciki ba abin mamaki bane ga al,adan muna hausa.
Mun dade gurin tana min maganan jan hankali akan aure na wani in fahinci may take nufi wani kuma ba ganewa nake yi ba sai da mijin ta ya dawo ne muka kalli lokaci muka gane dare yayi ko sallah bamuyi ba a lokacin.
Gaidashi nayi ya amsa min a cikin fara,a tare da fadin kardai ince wanan dince fatiman da ake damun mu akanta kuun tace ka canka daidai honny .
Yau dadi ya jawo muna ita gidan nan da ba don babanta bane ke ciwo nasan ba zata zo ba wanan mai kama da kifin rijiyan .
Dan dariya nayi a cikin kunya nace kai haba anty zanzo mana don rashin sanin gurine dama ya sa ban zuwa.
Sai mamakin yadda naga sunayi a gabana babu ko tar din kunya a idon su biyun lokacin wai don ina zaune suji raban idona basuji ba.
Mikewa nayi ina fadin zan tafi nikan anty don dare yayi ashe ina nan dan magana naga tayi mai kamar mai rada sai yace ok ba matsala muje a sauke ta.
Tare muka fito suna gaba ina bayan motar na fada mai layin gidan da zai sauke ni ba wani tafiya mai nisa bane tsakani sai gamu a gidan .
Nace wancan gidan ne ya dan kalli matar da mamaki tare da fadin wanan ai gidan wani dan kano ne ai something sani wudil ko ?
Wai kardai kice min wanan kanwan shice ko may ashe yar gidan manyace ita din ya fada da dan mamaki har lokacin a fuskan shi.
Yana daya daga cikin ma,aikatan mai da jirage da kasan nan keji dashi sosai ai sai dai miskilin gaske ne shi din shiyasa ba wanda ke kula harkan shi .
Koda yake kiyi hakkuri fa ina fadin halin dan uwanki a gaban ki hakan ko ya fada yana kallon matar shi.
Tace yaushe kuma baya ka gama honny ?
No gaskiya nake fada matar shi ma yar Nigeria ce sai dai wata arniya yake aure ai nake gani tsayawan da motar tayi ne yasa ina kokarin bude motar tare da fadin na gode fa zan fita.
Ya danna gurin bude motar tayi dan kara na bude sai lokacin anty tace dani tau Fatima mun gode da wanan ziyaran sai mun hadu school monday ke nan Allah ya kaimu nace tare da kara mata godiya sai da naga dagawan su na juya zuwa ciki.
Ranan ban yi barci sosai ba ina ta juya maganganun mu a raina har lokacin ban samu mafita ba ga zancen anty din nace idan ma cutarwa ne yake min kanshi ya cuta bani ba ai.