SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

AMERICA
Yana zaune ya mayar da hankalin shi ga computer shi yana aiki so yake ya gama aiki dake gaban shi wani aiki ne daya kawo shi kasan daga england duk da ya kusa kammala aikin kuma akwai sauran kwana uku da yake son karawa garin kafin ya wuce.
Wayan shice tayi kara har tana batu tsukewa bai daga ba sai can ya daga wayan ya duba sunan kanin shi ya gani rubuce a fuskan wayan.
Receive ya danna kada wayan ya katse tare da fadin habbib ya kayi ne cikin muryan shi dake nuna gajiya da natsuwa.
Habbib din yacd haba bros ka shige kwana biyu ko labarin ka ba aji wanan ai sai hankalin mu ya tashi.
Yanzun ma hajjaju ne ta kirani tana fada wai kwana biyu ta nemi layinka bata samu ba shine hankalin ta ya tashi.
Sai da ya shafa goshin shi ba don zufa ba sai dai don gajiya da aikin da yasa a gaban shi yace wallahi habbib na danyi tafiya ina America sati biyu ke nan nazo wani aiki ne daga ma,aikatar mu.
Bros shine babu sanarwa kasa hankalin mum ya tashi kasan fa halin mum a kan mu yace wallahi zan kirata I will call her leter.
Gaskiya ya kama don hankalinta ya tashi sosai wallahi kasan kuma ga matsalan gidan nan yanzu dad ya birkice mata sai korafi take min ko yaushe ta rasa gane kan dad a kwanakin nan.
For what reson may ke faruwa a gidan ne wani abu ya hada su yana tambaya cikin nuna damuwa.
Wai fa akan wanan matar daya aura ne fa yake kokarin juyawa hajiya baya kaji mun dad fa duk yadda suke da mum yanzu akan wata zai juya mata baya.
Nasan duk wanan abin ba sherin kowa bane sai , , , , kai habbib mind you togue ka daina shiga zancen mata da miji don Allah.
Duk abin dad nasan ba zai taba juyawa hajiya baya ba akan wata matar diba ga yadda shakuwan su yake kai ma wai baka san halin mata bane idan an masu kishiya.
Ka daina shiga irin wanan maganan kai na miji ne idan kaji ka bata hakkuri ka kwantar mata da hankali shi yafi.
Yace ni wallahi shi yasa ban son wanan auren da dad ya kara ba tun farko don , , , ,
Kai ni ba wanan ba na fada ma ka daina shiga harkan mata don Allah zan turo maka da kudi ka tura masi gobe ita da dad din kodaya yake ma barshi dai zan turawa dad nasa da kaina .
Daga haka ya kashe wayan yana girgiza kai alaman kai mata halin su daya a gurin kishi ba yara ba ba manya ba indai har kan kishine.
Shi yama manta da kamanin wanan matar da ake cewa yar uwan su ce dad din nasu ya aura sai kuma ya ja tsuki don bai son abinda zai dagawa mahaifiyar tasu hankali ko kadan don yadda take son su haka suma suke son mahaifiyar tasu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:37 – ????????????: YA ALLAH MUNA ROKON KA KA AZA MU HANYAR TSIRA KABAMU IKON TSARKAKE IMANI DA BAUTA A GARE KA TSARKAKKE YA ALLAH MUNA ROKON CIKAWA DA IMANIN KA A LOKACIN KOMAWAN MU GARE KA AMIN YA HAYYU YA KAIYUMU.
Alh sani yana kishingide yana kallon labaran NTA na kasa gefen shi hjy maimuna ce a zaune wacce hankalin ta baya kan tv ita.
Jin tsukin da yaja ne yasa ta daina latsan wayan hannjn ta da take yi ta kallo shi tare da fadin lafiya ko ?
A rayuwana na kijinin hurda da arnakun nan sai dai yanzun boko da wayenwan kai yasa komai zakayi a duniyan nan sai tare da su muddin kabar kasan hausan nan to ka rabu da akidar hausawa ke nan .
Shiyasa nake fadawa hajiya yaron nan ya dawo gida hakana tunda ya gama abinda ya kai shi can yau shekara nawa da kare karatun shi.
Zaman da yake can kwata kwata bai kwanta min a rai ba na fi son su dawo gida kusa dani idan ma aiki ne akwai ire iren aiyukan su a nan gida nigeria ai.
Umm,humm yaya sai nake ganin yanzu umar ba yaro bane ai don akwai sa,annin shi da sukai aure da iyali , kaga wanda ya kai munzalin rikon iyali ai ba za,a ce zaiyi wani abin asha ba yanzu.
Kai dai kawai ka bisu da addua a duk inda suke ubangiji ya tsare muna su tare da sauran yan uwa musulmai.
Ko banza indai umar ba ya canza bane kaf yaran gidan nan yafi su natsuwa da sanin ya kamata a iya sanin da nai masa a baya.
Murmushi jin dadin yabon danshi da tayi yayi tare da fadin Umar kan akwai natsuwa da tausayi wanan haka yake ba karya kika fada ba ga halin sa.
Jin shigowan mutum kamar daga sama falon yasa suka daga fuskokin su dauke da murmushi kan maganan da sukeyi na dan Alh din.
Kallo daya kowan su yai mata ya hango fitinan kishi a tare da ita gama ga yadda ta samay su a zaune din.
Kusan hjy maimuna rabin jikin ta na ga jikin mijin nasu wanda take kokarin bawa juice din shi na zalla diyan icce da yake sha duk dare kafin ya kwanta a matsayin abincin daren shi.
Da zaran ya dawo da yamma ya ci abinci ba zai kara cin wani abin ba sai yayan icen don tsaron lafiyan shi da yake yi din wanda har ya saba da hankan yanzu.
Sai da hjy jummai ta samu wuri ta zauna kafin ta fara magana da miji nata gani haka yasa hjy maimuna azaman fita daga falon mijin nasu.
Ina kuma zaki baki gama dani ba cewan Alh sanin yana mai kallon hjy maimun duk da yasan shigowan uwar gidan nasu yasa zata basu wuri su gana.
Kamar ba shi yai magana ba sai kuma ya juya inda hjy jummai take zaune yana fadin kin gan munan yanzu haka maganan umar muke kika samay mu.
Uumm, tace dashi ba tare da ta fadi komai sai dai a can cikin ranta fada take da maigidan nasu akan may zai zauna yana maganan danta da wata mace a gidan nan mafarin ya sake masu siri ke nan kuma ko.
Juyowa tayi inda suke da hjy maimuna yana fadin baida sanyi dai sosai ko cewa da juice din data kara daukowa zata zuba mashi din.
May umar din yayi kuma har kake maganan shi da wata a yanzu irin haka ai kamar wani abin ne ko ?
Wani abu kuma hjy ba zanyi maganan dana duk lokacin dana so ba sai dake ke nan, wai may yasa ku mata kuke da karamin tunane ko wani lokaci.
Kai tsaye tace maganan da na ni da kai ya shafa bada wani ba a gidan nan ko cikin yan uwa bada wani bare ba can daban.
Maimunan ce bare Jummai ?
Ta dago kanta da sauri don jin kiran da yai mata ta dan kalle shi jin sunan ta da ya kira ba sakaye don haka tasan ranshi ya baci ke nan.
Yaci gaba da fadin idan ma kina tamtamane to ki bari don maimuna ta wuce bare a gurin diyana kin fi kowa da sanin hakan kuma.
Ban san da hakan vmba sai dai idan yanzu kike kokarin raba hakan a tsakanin diyan ki da yan uwana.
To sanun sarkin yan uwa dadin abin dai kowa nada nasa yan uwan a duniya balle ai min gorin yan uwa a gidan nidai nace al,amarin diyana ni ya shafa a gidan ni kadai.
Yace haka kika dai fadi sai dai ni kuma ban lamunce da hakan ba don ba ke kadai kika haifi yaran ba.
Ummummm ashe manufar ki ke nan da kike kokarin nisanta yaran ki da kowa to bari kiji kowa yasan ni yasan ni mutum ne mai son raya zumunci.
Ganin zasu rikice a falo yasa hjy maimuna bari falon ba tare da Alh sani ya farga da fitanta ba nan dai ta barsu suna kwama rikici a tsakanin su.
Part din ta koma ta gyara yaran ta zuwa wurin gwagon su hadiya dake zaune tare dasu a gidan don idan tana da girki tun zuwan hadiye gidan a gurin su take kai yaran su kwana ita kuma taji da dawainiya da maigidan.
Yanzun ma data shigo ta samu har yaran sunyi barci a falo inda ta barsu suna cin abinci kafin ta fita zuwa sashen maigidan don gabatar da hidimomin shi na yau da kullun da suke may kafin shiga barcin shi.
Gyara yaran tayi kamar yadda ta saba yi kullun sai ta shirya su tsab tare da kayan bukatan su takan goya daya a bayan ta ta rugumay dayan ita kuma mama ta rike mata hannu zuwa part din hadiye dake hade da gwagon ta sarakuwan su ke nan.
Suna zaune a falon su suna hira ta shigo da sallama suka amsa mata Amma dake taunan goro kafin shiga kwana tace yanzun nake maganan ku a raina banga an kawo min mazaje na tun dazun nace ko basuyi barci bane.
Kamar kullun sai da tayi halin nata watau murmushi a fuskanta tace ina gwago aikin san hali su basu kai tara basuyi barci ba.
Yabzu ma na san shiga hadama baban su shan shine na dawo na samu wai har sunyi barci a inda na barsu suna ci abinci.
Ba magana yara kamar kasa a gurin barci hadiye kama mata na hannun nata mana taji dadin sauke na bayan ta wa yan nan manyan diya haka tubarkallah dasu kamar su kadai ubansu yake ciyarwa a gidan nan.
Amma ta tabe baki tare da fadin ke kama bakin ki kar kisa a saka masu ido kuma a lalata min kimar yara ba,a fada ba sun tsone ido inaga an fada din kuma.
Hadiye dake shimfide yaron saman kujera tace yaya ko zasuyi dasu sai gani sai hangeb don Allah ya riga da yayi ikom shi.
Da jummai tasan yadda zata kawar dasu tun suna jarire aida ta kawar dasu a gidan nan don wanan matar kishin ta sai ita.
Maimuna tace yanzun ma ita tasa na fito suna can suna kwasa da yaya a falon shi daga magana ta hau fadar bakaken magana don kawai Alh yace yanzun ko maganan Umar muke yi dashi shike nan ta hau fada don may zaiyi maganan diyan ta da bare.
Da sauri Amma dake ta ya tsunan fuska tace waye bare a gidan nan banda ita da maryama kaji min mata da fada karya rikicin Jummai wani lokacin kamar mai motsi a kai.
Tayi ta gama don yanzu na kula shima yayan hali nata ya fara fita kanshi don ya fara gane halin ta ko kuma abinda akai may ne ya fita kan shi ba.
Amma ta karasa fadi cikin kunan rai da halin rikici iri na hjy jummai wanda ba gaira ba dalili takeyin shi a kan dan abinda bai kai ya kawo ba a gidan.
Sun dan zauna sun taba hira a part din sai lokacin da ta kwatanci hjy jummmai ta bar gurin Alh ta mike tana fadin barin leka wurin maigidan ko sun gama badakalar su.
Jummai mai rikicin gangan fada ba naki ba ya zama naki ni har mamaki halin mulkin ta ke bani ko ance mata samun wuri haukane ?
Ita dai hjy maimuna bata kara tsunkawa ba don bata faye son maganan kishiyoyin nata ba a gurin kowa, takan ce daukan nauyi ne hakan.
Har ta gama shirin ta ta rufo part din ta zuwa sashen maigidan hankalin ta yana ga maganan hjy jummai da tace mata wai ita din bare ne gun yayan mijin su da yake wa a gurin ta.
Ba abinda ta tsana kamar mutum ya ci mata fuska irin haka don muzantawa ne ba kadan ba.
Ta koma ta samay shi har ya gama abinda yake ya kwanta ta shigo dakin sai da ta tsaya ta kashe kayan wutan dake aiki a falon ta karasa uwar dakin shi.
Zaune yake saman sallaya da alama shafa,i da wutiri ya gabatar a lokacin yake addu,a ta shigo dan dago kai yayi ya kalle ta tare da fadin kin rufe kofa da wutan falon ta bashi amsa da eh tunda ban gan ka ba a falo na san ka shige ke nan .
Ai tun fitan wanan mara hankalin na shigo daki, mata kamar wata mai kwankwamai a kai ban gane ma Jummai ba a gidan nan tunda na auri maryam halin jummai ya sake baki daya a gidan nan.
Yaya laifi fa kayi mata kuna zaman ku na dadi rai daga kai sai ita da yan yaran ku, ka karo mata iyali a gidan don may ba zatai fitina ba da kai ?
Ku mata shine matsalan ku ai kada dai na miji yace daku zai kara aure yanzun komai dadin ku da mutum za a jiku da
shi.