NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:21 – ????????????: BISSIMILLAHI RAMANIN RAHIM ALHAMDU,LILLAHI RABIL ALAMIN, , , , , ,

Nikan dai ranan naga abin mamaki a gidan cike da tunane da fargaban merry na kwana a rayuwata da safe dai fashin sallah nakeyi don haka na tsabtace jikina tare da shirya har tsoron fitowa waje nake daga dakina a yadda nake tsoron dan giya a rayuwata yadda muke kyamatan su nan gida Nigeria.
Kwance nake na lafe saman gado ina rub da ciki naji shigowan yaya dakin ban juyo na fuskance shi ba ya kuma san ba barci nake ba a lokacin.
Ki tashi muje asibiti mu duba queen sai lokacin na dan juyo na fuskance shi kindai ji abindaya faru dasu don itama merry din tana asibitin sun mayar da ita saboda ta bugu a hannun ta sosai.
Har lokacin banyi magana ba shi kuma yana tsaye tsakiyan dakin saida yaga na yunkura zan tashi yabar dakin da sauri nikan kayana gaba daya na hada don a ranan nake son komawa gidana ba zan yarda yar giya ta illantani ga banza ba don harga Allah tsoron merry ya kamani har cikin raina.
Ina gama hada komai nawa na fito na samu baya falon dan zaman jiran shi nayi na dan lokaci sai gashi ya fito da alama wanka yayi ya sauya kayan jikin shi sai kamshin da yakeyi lokacin.
Ban tsaya jiran yace wani abuba na mike da sauri ya dan kalleni don ganin jakkar kayana dana dauko lokacin.
Bai min magana ba illa kitchen danaga ya nufa wurin masu aiki duk na kagu ya fito mu tafi lokacin.
Sai gashi ya fito masu aiki na biye dashi da abinci a zato asibitin za aikai abincin sai naga sun nufi dining da abincin.
Sai da suka gama jerawa ya nufi wurin ya zauna ya juyo yana kallona tare da fadin ba zaki zauna kici abinci ba.
Nace na koshi wani tsareni yayi da idanun shi saida tsorata dashi a hankali na tako zuwa dining din dake da dan tazara daga inda nake tsaye kamar ina jiran umurni.
Ina karaso naja kujera zan zauna naji yace may kikaci jiya da dare bayan kina daki kina fushin banza da mutane.
Dan kunkuni nayi ban fitar da maganan a fili ba yana kallona na dibi abincin maimakon in zauna sai na daga zan bar wurin.
Maza ki zauna nan kici yace kamar ya samu yarshi dama kuma ai yar tashi nake don da uwata suka taso dashima mace ce da yanzu kila yana da sa,ata.
Sannu a hankali nake kai abincin bakina duk a kyamace don sai ban yarda da yan aikin ba ga baki dayan su.
Zakici abincin ko sai raki ya baci yanzu naji muryan shi yana fada min nayi firgigit na tsakuro abincin zuwa bakina yaci gaba da fadin.
Ba zai yuyu kina zama da yunwa ba wani abu yaje can ya samay ki ace gidana akwai yunwa ki bata min suna ga banza.
Nace bashi nazo yi bani ga dai may shirin bata ma suna nan tana abinda taga dama har dasu shan giya da auren ka.
A natse naga yayi murmushi maimakon yai fushi kan maganan dana fada mai mai zafi sai naji yace ai ba gidan ki bane gidanane kuma matatace a haka nake son zama da abina.
Nace da wani yace maka shi matarkace kaje kaita zama da ita ko da zindir zatayi yawo mana.
Ban iya fadi kalaman sosai a fili ba sai na dadi ciki ciki ina murguda baki banyi aune ba sai ganin shi nayi gabana ya cafki bakina dana murguda mai yana fadin mara kunyar banza wace bata san rarashi ba .
Wai may yasa ku mata baku san ya kamata ba sai anyi tsiya daku ko wani lokaci wai harda ke wanan karamar yarinyar kin iya takon tsiya wa maza ko ?
Dan ja nayi baya ina fadin nika sake min bakina mutum da baki shi a hana shi magana na fada ina kwace kaina daga rike baki dayayi min.
Yana sake min yayi gaba tare da fadin in kingama ki samay ni waje ban tsayaba na mike tare da mara mai baya kusan a tare muka fita daga gidan dashi.
Motar ya bude min na shiga da kayana sai lokacin yake fadin wanan kayan fa ina zaki dasu haka banji komai a rainaba nace gida zan koma yau ni.
Wanan ba gida bane shi ko wani ya takurawa rayuwan kine a nan sallon kiji dadin fita yawo kice zaman kadaici ya isheki a can ko ?
Ni dai gida zan koma daga asibitin na kara bashi amsa baiyi magana ba ya zagaya ya shiga motar muka dauki hanyar asibiti kai tsaye.
Asibitin babba ne sosao mai benaye da abin hawa saida muka shiga lifter ya kaimu sama dakin yar shi muka fara zuwa tana kwance an daure mata kafa har cinya da plaster hakama hannun wata na barin hagu da kafan shima a daure yake an rataye kafan a jikin wani karfe kafan yana lilo.
Sannu mukai mata mun samay ta tare da wata dadtijuwar mace matar tana saye da wando da rigan t,shirt kanta babu gashi ko kadan an aske ga makeup tasha a fuskan ta bakar fatace matar wuluk da ita.
Bayan mun kare gaida yarinyar na dan rike mata hannun dayan dake da lafiya ta sake tiedy din dake rike a hannun ta ta rike hannun nawa.
Matar ce ta tambaya wanan ce kanwar taka dake karatu a nan a cikin daure fuska naji ya bata amsa da eh itace.
Wani kallo tayi man kamar wace taga abokin gaban ta saita kawar da kai daga kallona da tayi bani kadai naga wanan kallon ba har shi yaga irin kallon da taimun da idon shi.
Oya les pray yace wa yarinyar tare da juyowa gareni yana fadin ki muna addu,a ban samu bashi amsa ba naji yana cewa yar komai taji ya fada itama ta amsa da Amin tace Ameen yace No say Amin
Ya juyo ya dan kalleni sai na daburce na rasa abinda zan karanta a lokacin fatiha na fara jerowa kafin in dora da adduan .
Sai cewa suke Amin yana hadawa da ya Allah jin yadda yake kiran Allah yasa hankalin dattijuwar matan ya tashi gaba daya har ta kasa boye yananin ta a dakin.
Mun gama ya dan zauna yana hira da yar shi ina gefe daya a takure ina kallon su sai matar ta fita ya juyo yana fadin bayan fitanta wanan itace uwar merry.
Da mamaki nace wanan din subbahanallahi ke may ye haka yace mun nayi saurin dukar da kai ina ci gaba da mamakin abindana gani.
Watau ita merry daga gurin uwarta ta gaji katon kafircinta don da ganin matar katuntumar kafira ce gata ta tsufa amma bata bar kwalliyan iya shege ba nace.
Ga abin bada labari ina gani a gidan yaya sai dai babu wanda zan ba labarin sai ni kadai zance ke cina a zuciya.
A raina nace wanan da kawu zai ganta a haka nasa babu abinda zai hana shi daukan mataki a kan umar din.
Don wanan hada zuri,a dasu ai banar sunane sai natuna da addu,a da sauri nace idan suna da rabon shiryuwa Allah ya shiryesu.
Na dago kai naga yadda yakai kwance saman gadon suna duban waya da yarshi cikin kwanciyar hankali abinsu dan tsuki naja da bansan lokacin daya fito min fili ba.
May ya faru kuma ya dago yana tambayana na girgiza kai kawai tare da dukar da kaina daga kallon su sai daya dan kara bata lokaci dakin kafin ya mike yana fadin ki kula da kanki ki dinga fadin Allah Allah dana fada maki ta gada kai.
Yace bakicewa anty bye bata dan dago min hannu alaman bye take min na karasa wurin ta nace Allah ya bata lafiya.
A zatona ba asibiti daya suke da uwarta ba sai na dauka tafiya zamuyi lokacin sai naga ya nufi hanyar wani ward na daban sai da muka kai kofan dakin na fahinci inda muke.
A nan gurin da ita da mahaifin merry din ne da gani rayukan su a bace yake jin budan kofan mu ya dawo da hankalin su ga kofan suna kallon mai shigowa dakin.
Uban yana ganin mu ya wani hade rai lokaci guda yana hadiyan malolon bakin ciki tare da kawar da kanshi gare mu.
Shikan yaya ya fahinci may sukeyi ni daice ban fahincesu ba lokacin sai ma kokatin gaidasu danayi lokaci guda.
Na juya wurin merry ina mata yaya jikin ta wani ya mutse fuska kafin ta ban amsa na samu wuri gefe na tsaya abina ina kallon su.
Umar ya karasa bakin gadon ya tambayan yadda jikin nata yake yanzu ta amsa mai a gyatsire wai ita ranta ya baci da zancen da uwar tazo masu dashi.
Look Omar na fadama ban son wanan akidan addinin ka da kake koyawa Faith rikici sukayi sosai a wurin zaman iyayyen nata a gurin bai hanashi fada mata bakaken maganganu ba har mahaifin yaso yasa baki ta daga mai hannu tace ba maganan shi bane wanan.
Bayan ya gama fada mata zataga matakin da zai dauka kan abubuwan da take mai tace she will see nothing in her life dama ku musulmai haka kuke da baki ai.
Nikan ganin sun kaure da fada na bar dakin zuwa waje inda naga kujeru na zauna ina dakon fitowan shi daga dakin .
Ya fito raibace ya dan kalleni yace mu tafi da sauri na mike muka bar asibitin ya fisgi motar shi bamu bar asibitin da wasu yan mintina ba sai ga abokin shi ya kirashi Deved yana mai korafin merry ta kira shi rai bace tana kuka sun samu sabani Farget about that Lady Deved ya bashi amsa ya kashe wayan shi.
Maimakon inga ya dauki hanyar da mukazo sai naga sabanin hakan wani hanya muka bi nidai ido na zuba mai kawai.
Mun danyi nisa ya juyo yana fadin may kike saukewa ajiyan zuciya tun dazun ?
Ban taba tunanen akwai irin wanan rayuwan haka ba a duniya kuma ga bakar fata wai irin mu gaskiya ni ha zan sake zuwa wani guri ba daga yau.
Ya juyo a fusace yace kina nufin niba musulmi bane ko may ko ban san abinda nakeyi ba kike daukana.
Ki tuna fa a guri daya aka bamu tarbiya dani dake karki tsamani ko ki daukeni wani jahili Qur,ani da hadisi babu ayan da bazan kawo maki ban fasara shi ba da kai.
Rasa kalman da zan fada mai nayi don ya fahinci inda maganata tadosa akan fadan su da merry ne da iyayyen merry din.
Ba wanda ya kara magana a motar har ya shiga wani unguwa daban taba sani bama ni a gaban wani gida ya Parker motar shi.
Banda niyar fita don ban san inda kuma ya kawo ni ba again fita yayi daga motan ya zagayo ya bude min gefena kallon shi na yi yayi tsaye kimkam ba tare da yayimin magana ba.
Ganin ba zan fito ba ya daka min wani uban tsawa dole na sauko daga motar da sauri na.
Fara tafiya yayi ya barni a baya ina karewa ginan kallo a raina nace nan kuma ko inane oho ?
Bell ya danna dan jimawa kadan sai ga wani bakin mutum ya bude kofan yace a cikin fara,a kace yau nayi babban bako a gudan kenan cikin harshen hausa.
Sai daga baya ya kula dani tafe yace kai mutumina kace da bakuwa kake tafe mana ka barni ina zuba surutu haka ?
Madam tana ciki ya tambayi mutumin yace tana nan kasan ai hutu ake yanzu ko ina fara gaida mutumin nayi bayan na karaso gaf dasu.
A cikin hausa ya amsa min yana amsa ya juya zuwa ciki yana kiran Halima halima fito ga bakuwa munyi.
Daga ciki ina jin muryanta tana fadin bakuwa daga ina babban Nasma ?
Fito ki ganta yar uwam mu ce bahausa itama matar na fitowa taja tayi turus tana fadin ikon Allah a cikin fara,a wanan bakuwan kan ta gidace daga ganin shigarta ya banbanta dana yan kasan nan.
Sannu ki da zuwa tace min na amsa mata cikin fara,a kamar yadda tayi min fara,a itama.
Ki zauna ga wuri sannun ku da zuwa tana ta jin dadin zuwan mu gidan nasu sai na samu kaina nima da jin dadi a raina sosai ba kamar yadda naji a gidan merry ba.
Sai gasu sun shigo falon shida maigidan matar ta kawo muna abinsha da ci ta aje a gaban mu aka kara sabon gaisuwa tsakani mu dasu .
Mijin ne ya kalli matar tashi yace ai sai ku shiga ciki kuyi halin ku na mata ko da kuka saba idan an hadu.
Tana dariya ta jani tana fadin taso kanwata mu basu guri sun kore mu da wayau ne kawai dai.
Wani dan karamin falo na kara gani ta nuna min kujera tace in zauna a kawo maki abinsha ne naga baki sha wancan dana kai maku ba matar tace.
No nagode na bata amsa dashi haba ki saki jikin nan kamar gida kika zo ai ban san dai yaya kuke da enginer ba amma ai aminin maigidanane sosai duk da kasan nan suka hadu amma suna amintaka sosai da junan su.
Yayanane na ba amsa dashi tace ikon Allah yayan ki na jini ko may nace eh gidan mu daya dashi karatu nazo yi nan ni.
Au wallahi har na fara muna ina zaton ko yayi aure ne ai ya rabu da wanan arniyar matar tasa daya aura nan.
In fada maki maigidana baiso auren su ba amma saboda nacewan wanan arniyar saida tasan yadda ta auri dan uwan nan naki.
Abu kamar aikin asiri tun wanan lokacin zumuncin su da maigidana yayi rauni suka rage arkalla da juna kamar farko.
Don matar bata son kowa ya mami mijinta daga ita sai yan uwan shi Allahne ma ya kwato shi har ya waiwaiyi gida daga bayan nan nasan karfin adduan iyayyene yai aiki a kasa.
Murmushi nayi kawai don jin abinda ta fada nace ai mu duk da muka taso bamu san yaya umar ba sai zuwan shi daya yan shekarun da suka wuce muna dai jin labarin sa kawai a gidan mu.
Gaskiya ba zaku sanshi ba kan don ina ga ai ko ashrin baki rufe bama ko ta fada tana kallona nidai dariyan kawai nayi mata ban bata amsa ba.
Hiran yanayin garin ta dauki min da al,adun su sai kewan gida da mutum kanji farkon zuwan shi idan bai ganin na gida a kusa dashi.
Har ta kai ga tambayana a gidan shi nake zaune nace a,a ina wani gidane dake kusa da school din mu don yafi mun kusa.
Tace sau daya nasa wancan gidan nasa muntafi ganin amarya a lokacin akace bata nan tana America ne da zama.
Naji dadin kasancewa a gidan Yusuf baba yola do matar tana da dadin hira sosai ban dai yarda na buga komai a gidan ba sai dare yaya yace in fito mu tafi.
Haka muka rabu da sunan watarana zan sake kawo masu ziyara a gidan da zan tafi taimin kyauta na bajinta da ba zan manta da shi ba don har da kayan abincin mu na gargaji ta bani da turare da sauran tarkace.
A waje muka samay su sai maigidan nata ke fadin to amarya munyi murna sosai da wanan auren ubangiji yasa wa aure albarka.
Kallon juna mukayi nida halima danace wa shi yayanane da farko tace wai kana nufin matarshi ce ita din yace wallahi ai Umar baya da kirki ashe aure ya kara har kusan shekara biyu ke nan bai fadawa kowa ba.
Sai yau yake fada min nima na sani tace amma yanzu take fada min shi din yayantane gidan su daya karatu tazo yi nan London.
Mungun yace ta fadi hakan ga kowa daya tambaye ta yaya suke umar ai yakai mugu wallahi.
Amma ko dana sani ai daba hakan ba dana baki tsaraban ma,aurata don ni ina samun su koda yaushe ana kawo mun.
Nifa ba mijina bane na fada ina daure fuska a matsayin yayana yake kuma kawuna na fada na bata rai.
Dariya naga miji da matar sun kwashe dashi tace ba laifi zamu kara haduwa da yardan Allah nan bada dadewa ba tunda har kunzo gidan mu muma muna nan kawo maku ziyara watarana.
Mukai sallama suna tsaye har motar mu ya daga ba wanda yai magana daga cikin mu har tsawon wani lokaci.
Na cika nayi fam har muka kai gida ba wanda yayi magana a cikin mu ina ganin street din mu na sauke ajiyan zuciya sai lokacin ya dan kalloni kadan ya kawar da kanshi.
Ban tsaya ya zagaya ya bude min ba nayi wuf na fito daga motar ina sauke ajiyan zuciya a fili na nufi hanyar shiga gidan sai dai key din gidan yana hannun shi dole na jira ya gama rufe motar ya nufo ya bude gidan zuwa lokacin kankara ya fara sauka a ginin gidaje da motoci yana rufewa .
Ban tsaya kallon wanan ba Allah Allah nake ya bude in shiga gidan don zuwa lokacin a matse nake sosai don fashin sallah da nakeyi lokacin.
Yana budewa har ina bugeshi wurin shiga na haura sama da sauri tare da bude dakina jakata na wurgar saman gado na nufi bandaki don kintsa kaina .
Ruwa na hada masu zafi da zasu isheni na dade a bayin ina gasa jikina kafin in fito rigar barci kawai na saka naje na rufe kofa na haye gadona.
Washegarima ban fito da wuriba don ban falka da wuri ba dana tashi kuma sai dana tsaya na kintsa jikina kafin in fito.
Abinda ban sani ba shine zuwan mu gidan abokin shi ba ziyara mukakai na Allah da Annabi ba shawara abinda zai fitar shi yaje nema gurin Yusuf yola din kamar yadda yake kiranshi.
Bayan sun sallame mu zuwa ciki ya dubi Umar din yace abokina lafiya kuwa na ganka haka ?
Umar yace ina cikin matsala abokina Yusuf yace subbahanallahi may ke faruwane haka duk yanayin ka ya nuna kana da matsala.
Nan ya kwashe yanayin zaman su da merry sauyawan ta gaba daya da komai yana fada mashi.
Yusuf din yace kaga abinda nake hango maka tun farko mutumina wa yan nan mutane ba abin yarda bane sam.
Yaya mazon SAW zai magana a kansu maganan ya tashi daga baya tun farko na fada maka auren wanan matar matsalane gare ka kana dan bahaushe musulmin asali kajawa kanka wanan nauyin.
Ansan idan mace tayi jahadi tsakani da Allah har ta yarda zata musulunta wanan baida illan komai kasan son tsakani da Allah take maka.
Amma ni yadda iyayyenta suka kafa sharudan su kai kuma ka yarda dashi kana ganin zaka iya juyata daga baya ne ?
Ba yau irin hakan ya fara faruwa ba muna gani wasu ma da farko zasu yarda su musulunta sai daga baya su koma akidarsu ta kiristanci don yaudara.
Wasu ko har bayan rai suna cikin islama ba zasu canza ba irin merry yana da wuya ta canza farat daya idan ka tsaya tun farko kayi nazarin waye ita din.
Yana da wuya merry ta iya canza addinin ta farat daya idan kayi la,akari da irin kungiyan su datake bi tun muna karatu.
Godiyana ga Allah shine da Allah ya kwato muna kai hankalin ka har ya koma gida tun lokacin nasan kana da rabo mai karfi.
Ai yadda ta biyo maka ta baya ta cuce ka haka kaima zakayi ka nuna mata namjin duniya kake na gaske.
Fita batun da yar insha Allahu yarinyar tana girma ita da kanta zata neme ka ai ya katse a bokin nashi da fadin Yusuf ina tsoron queen ta taso cikin addinin uwarta mai zurfi.
Don tun yanzu duk akidar yarinyar irin dabu,un su ne takeyi don merry bata yarda sam yarinyar ta mamay ni ko wani nawa takima fada mata komai a gamay dani.
Umar wai ka manta da rijejeniyar kune danasa ka saka cewa zaka iya kara aure aduk sanda ta sauya wani al,ada daga rijejeniyar ku.
Ban manta ba umar din ya bashi amsa sai dai ina tunanen sheri irin nasu do hakane kaga yanzu komai nawa yana zuwa gida ina kokarin ganin komai nawa ya koma gida ga baki daya.
Merry tasa da wanan shirin naka ya girgizawa Yusuf din kai yace bata san komai nawa ba tun farko don ban yarda da hakan ba ban shi harka sana,anta itama haka bata shiga nawa.
Kayi dabara Yusuf yace, yadan kada kafafuwan shi na dan lokaci yace da umar din da yai shiru yana tunane.
Umar ka tuna shekarun ka suna korawa fa a yanzu girma yana dada shigan mu ga al,adan mu da iyayyen mu suka koyar damu iyali shine alfari mutum koda yabar duniyar nan muddin kana da diya masu albarka tankar baka barta bane.
Sai nake ganin idan ka tsaya ka dogara da merry da yarta tankar kaida kanka ka dabawa cikin ka yukane ka kashe kanka.
Kowa yana alfarin zama waje ne na dan lokaci idan ka gama tara abinda kazo nema sai a koma gida ayi rayuwa cikin yan uwa da abokan arziki.
Yau idan haka ya kasance dakai umar damay zakai alfahari baka da mata bakaga yarka ko ta canza ra,ayi zata kara haihuwane yanzu.
Umar yace ba alaman hakan a tare da ita don kullun ikirarin ta queen ta ishe mu rayuwa do haihuwa akwai wahala ba zata yarda ta sake ba.
You see abinda nake hango maka ke nan tun farko abokina nu sai nake ganin ka kara aure kawai shine mafita gare ka hakan zai sa merry ta shiga hankakin ka in har tana son ka.
Aure kan ai na dade da karashi yacewa abikin nasa da sauri Yusuf ya dago kai yana kallon shi yace yes almost to two years ke nan ina da aure Yusuf.
Sai dai ban ba auren nawa wani muhinmanci ba sosai don aure da iyayye suka daura a bisa kaddara don karamar yarinyar nan daka gani yanzu matatace ita.
Saidai muna zuwa nan na canza akalan zancen ta koma yar uwata yanzu haka karatu takeyi a nan tun bayan zuwan mu na sakata a makaranta.
Tunda ya dauko chapter dina Yusuf din ya kura mai idanu yana kallon shi da mamaki sosai a fuskan shi sai da yaji yakai aya yace.
How comes Umar bansan wanan zancen ba yace laifinane abokina nan dai ya kwashe duk yadda auren ya kullu har irin zaman da yakeyi dani ya fada mai.
Yusuf yace lalai Umar kakai namijin gaske kana sa kamar wanan yarinyar a gida may zakayi da wata merry can data dade da shan ruwa tun baka aure ta ga daya sharrr.
Wai dakata umar kai baka tsoron Allah ya kamaka da wanan hakkin yarinya karama da kake tauyewa ?
Baka tsoron alhakin mahaifin ka yabika ko da akan yayan ka ko wani kaddaran ka ?
Umar ka tuba kaji tsoron Allah wanan alhakin yayi yawa ina zaka dashi shawarata ka rungumi matar ka hannu bibiyu kaida kanka zaka dawo ka bani labari.
Yusuf na fada ma matsalan da auren yarinyar nan ya jawo min nida mahaifiyata fa sunna ka raya fa umar ba zina kayo ba.
Yarinyar nan watarana abin alfahari ne a gare ka ta bangare da dama ka godewa Allah daya baka mahaifi mai hangen nesa.
Shiru umar yayi tun lokacin da yusuf ambaci tauye hakki gare shi don shi tausayina yake ji sai yake ganin ban isa aure va sai zuwa lokacin daya kare tsare tsaren shi kafin yasa mafita dani.
Sun dade suna tataunawa da abokin nasa mumuna ciki bamu sam anyi hakan ba muna can muna tamu hiran a ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button