SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Kada ki tura min novel waje idan kin turawa wata ubangiji yabi mun hakkina a kanki yar uwa ma hadu ranan nadama ga bawa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:24 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM MALIK YUMUDEEN, , , , ,
Har wayewan gari bai sake runtsawa ba don yana barin dakin dakin shi ya koma yayi wankan tsarki ya tada sallah.
Ya dade zaune a inda yai sallah yana addua tare da rokon Allah gafara kan kurakuran shi daya tafka a rayuwan shi.
Ya dade a gurin yana jero addu,oi sai zuwa can ya mike ya nufi gado don babu abinda yake so a lokacin sai kwanciya ko zai samu natsuwa.
Ido rufe ya kwanta sai dai barci yaki daukan shi ya sake bude ido a hankali don surana dake mashi gizo a cikin idon shi a lokacin.
A sannu ya kara lumshe ido yana tuna kalamaina a gare shi wanda yake jinsu tankar zuban wuta a zuciyar shi.
Anyway zarah kina da gaskiyan ki cin fuska da tozarcin mama a gare ki keda mahaifiyar ki.
Dolene su zanci hakan sai dai ba zai danganta hakan da tayi da wani ya zugata tai mashi rashin kunya ba.
Don ranan yaji wayan da tayi da mahaifiyar ta kaf a kunnen shi inda uwar bata yarda ta furta komai daga bangaren ta ba, don ta hana yar magana sai huduban da tayi mata kanzaman hakkuri duk yana ji ya gani a cct camera din gidan wanda bai yarda kowa yasan dashi a gidan ba.
Yakan tara abinda ya faru a gidan bayanan idan ya dawo cikin dare yake kallon komai dana gudanar a falon da wasu sasana gidan banda dakin kwanana kadai.
Dan murmushi yayi a fuskanshi kafin yace da sannu zaki saba da halina zarah.
Ada ina tausaya maki da wasu dalilai nawa a yanzu ko na watsar da shakkan komai a raina zan rugumi aurena tsakani da Allah kamar kowa a duniyan nan.
Shirun da yaji baiji motsin fitowana ba daga daki ga rana har ya haska a ko ina yasa shi mikewa wanka yayi ya shirya ya sauko ya shiga dakin da yake motsa jikin duk safe rana yayi yau sosai don haka bai wani dade don baiyi komai ba a falo ya yada zango ya dade zaune a gurin kadan kadan yake dago kai ya dubi lokaci.
Har lokacin ba dalilin fitowana daga dakin balle in hada muna abin karyawa da zamuyi break dashi.
Lazy girl ya fada a fili yana mikewa ya nufi kofan nawa ya samu a rufe sai ya juya ya shiga daki shi gado ya koma ya kwanta zuciyan shi cike da tunanen abinda ya faru a dare jiya tsakani mu.
A tsorace na falka daga barcin inda dan hasken rana ya hasko inda nake kwance daga waje da kyat na iya bude idanuwana da sukai min nauyi saboda kukan dana sha daren jiya din.
Sannu a hankali abinda ya faru dani yake dawo min a rai idanu na runtse ido sai ga hawaye na silalo min a fuskana.
Idon na bude ina bin gadon da yake yamutse da kallo da sauri na daga don tuna irin abinda ya yi din saman gadon dani.
A cikin fushi na mike tare da dukawa na sukkuci zanin gaba daya na yaye shi daga saman gadon a fili nake fadi cikin kuka bazan kara amfani da wanan bedsheets din ba a tayuwa ta.
Wanka nayi na darje jikina dakyau har lokacin kirji yayi min wani irin tsami sai zafi da suke min na dan gargasu a gurguje na fito bayin.
Saida na shirya tsab dani, na gyara gadon dakin dana yaye zanin kai inda nake aje kayan wankina na tara don naso inyi wanki a ranan.
Sanin yana gida na fasa fita zuwa lanudry din mu nayi zama a dakin saidai hankalina yana falo ga yunwa ga gyaran gidan dana san yana jirana komai dare.
Jin ba motsin sa yasa na mike na sauko daga saman gadon a hankali na bude kofa ina dan lekawa kadan har lokacin gidan tsit take babu motsin kowa.
Cikin rashin daga kafa na sauko babu kowa a falon har lokacin kallon falon nayi na gane ya fito da safe kilama ya fitane tun lokacin nace a raina.
Dan gyare gyrare na hauyi yayun da na saka abincin jiya a ovon ina dumamawa in karya dashi har lokacin ina yi ina waigen bayana.
Saida falon ya koma tsab kamar yadda nake son shi na saka kamshi ko ina na gudan ya amsa na zauna ina cin abincin dana debo.
Na kusan kammalawa naji karan budan kofanshi bayan ya gama kallin abinda nake a gidan tun fitowana daga dakina a camera.
Duk da naji takon shi gaba na yana faduwa ga kunya da nauyi ya sakani gaba alokacin jin ya matso inda nake yasa na dago kaina a hankali.
Na dan dago kaina a firgice ina fadin ina kwana fuska a daure sai yanzu kika fito saboda lalaci daga an dan tabaki kadan matsoraciyar banza da wofi sai bakin tsiya.
Ban iya dago kaina na kalleshi ba har ya gama yana fadin ki zubo min abincin in karya kuma ki godewa Allah da jiya kina on da nayi maganin wanan bakin mai bakar magana gidan nan.
Sai lokacin na tuna da period dinane yaceceni a gurin shi ashe don kaina bai kawo wutan hakan ba sam.
Na mike na bi gefe na wuce kaina kasa har lokacin ban iya bashi sa ba abincin yayi kamar yanzu aka dafa shi sai kamshi ke tashi ko ina ma jera mashi har ruwa na aje mai da zai sha.
Ya tako a hankali zuwa dining din ya zauna na juya naba da baya naji yace waike a gida baki koyi bawa miji abinci bane ?
Jin kalamin shi yasa na dan jiyo da zuman bakar magana saidai na kasa daga idona in kalleshi har lokacin saboda kunyar da nakeji lokacin nasa.
Kizo ki zauna ki zubamin saina gama kuma zaki bar gurin nasu.
na dago a hankali don jin sharudan da yake kidanya min lokacin kamar wasu ma,auratan dake da kusanci a tsakanin su.
Yadda na kalleshi zaka gane da magana a bakina lokacin saidai ban furta shi a fili ba.
Na juya tare da takowa kamar yadda ya umurceni in mai din na bude abincin na fara zuba mai cikin plate din dake gefen shi.
Na gama zubawa ya nuna min kujeran dake kusa dashi in zauna saida na dan kalli kujeran kafin injashi baya ina kaiwa zaune zuciyana ciki da tunanen may wanan ke nufi danine sallon wani yaudaran yazo min dashi kuma nake fadi a cikin raina.
A hankali ya mika hannun shi fari sol ya kara matso da plate din gaban shi ina jin yana bissimillah kafin yakai abincin ga bakin shi.
Cibi biyu yaci ya dago kai ba kunya yace wai kwana nawa kike wanan abin nakune ?
Yi nayi kamar banji shi ba na share shi ya kara kai cibi abinci a bakin shi saida ya hade ya kara kallo inda nake yace bakiji bane a tambayan ki ?
Ni ban san abinda kake tambaya a kanshi ba ai na fada ina ya mutse fuskana kamar raina a bace yake a lokacin.
Ai dole ki fada yarinya don wasan boye ya kare a tsakanin mu yanzu auren mu zamu inganta a gidan mu ta hanyar da zamu kai ga gina rayuwa da samun zuri,a masu albarka a duniya.
Jin abinda ya fada yasani na dago na tsare shi da idanuwa na da mamaki waini yau yaya ya zaunar yake min wanan maganan haka.
Nace yaya nice fa a gaban ka yarinyar da aikai maka dole a kanta, fatiman da hajiyan ku tace bata kaunar hada zuria da ita don ba, a san asalin uwata ba nice dai din yar agolan gidan ku abin kyamar kowa da, , , ,
Ke ya isheki haka don Allah wanan wani irin aibanta kanki kikeyi haka da bakin ki kin taba jin wani ya fadi wanan kalman a gaban ki ?
Ai ba karya na fadaba don a gabana ansha min gorin hakan don hajiyan su salma ma enough enough zarah.
Ya fada cikin tsawa tare da buga table din daning har plate din abincin na rawa kamar zai fado ya fashe.
Ita din sa,arkice da kike danganta maganar ta da namu yanzu ko wuyan ki ya isa yankane da har zaki zagan min mahaifiya a gaba ke nan rashin kunyar da ake maki kirari har yakai can ban sani ba ?
Ko kina nufin don aurataya ua shiga tsakanin mu har zaki iya kallin tsaban idona kina fadin magana gamay da mahaifiyata.
Yaja wani huci kafin ya mike tsaye yana fadin na dauka ai ko ban auren ki zaki iya mutunta iyayyen a ko ina kika tsunci kanki don kema taki mahaifiyar tana da kima a idon mu.
Sannan kuma har inkin san darajan aure ba zaki yarda ki fadi wani mugun abu na mahaifiyata a gabana ba don darajan kawin ki da aure da ya shiga tsakanin mu daku.
Na dauka wanan kin sanshi tun gida duk wani mutuntawa ga miji shine ka mutunta iyayyen shi ko yan uwan shi.
Ko may mama tayi maki a zaman ku tare na dauka zata samu albarkacina ki manta da komai yanzu tunda kina gidan dan ta zaune.
Nace ni ba zagin ta nayi ba kuma ba zan taba zagin taba ko bayan idanun ku tun farko kawai dai na tunatar da kaine furcin ta gare mu ai.
Do haka ban taba raina hjyn su salma bam kuma fadi wani abu yanzu wanda yake raini a gare ta ba don nima ba zanso a fadawa uwata wani magana mara dadi ba.
Baki dauka hakan ba aida ba zaki ta kawo min maganan hajiya a gabana ba ko yaushe magana ya taso tsakanin mu.
Idan ma tace bata yarda ta hada zuria dake ba nimai aure naji na gani na yarda in hada mahaifina kuma ya yarda da hakan sai ki barni da ita ai mahaifiyatace ba naki ba ko ?
Tunda kin kasa manta abubuwan da suka faru a baya tsakani ku a hakan zamu zauna dake kike tunane a kullu kina kulleda mahaifiyata a ranki ?
Ko maimuna da kike fadin muna rainata ita ta taba fada maki akwai raini a tsakanin mu da ita a gidan mu in baki sani bama ki sani yau munfi ganin darajanta bisa ga maman su ikilima a idon mu don har yau bamuji wani abin assha da tayiwa hajiyan mu na rashin mutunci ba a gidan.
Na fada maki mu maza zamu iya juyewa a ko wani lokaci daga wani matsayi zuwa wani don haka daga yau bakinki yasan abin fada don ba zan lamunci jin hakan ba a gare ki na fada maki.
Yana fadin haka ya ja iska ya fice daga gidan ya barni zaune a inda nake na rike kaina don yau naga bacin rai sosai a idon shi kan maganan dana furta na mahaifiyar shi a gaban shi.
Tun ranan sai da muka jera kwanaki kowa harkan gaban shi yakeyi ga matsanancin sanyin da akeyi a kasan kamar zai illanta mutum.
Sati daya tsakani ina kitchen ina aikin abinci fitowa na kenan daga daki sai kamshi ke tashi ajikina lokacin ina saye da daya daga cikin tsaraban malasiya daya zo min dashi.
Hankalina yana gu abinda nakeyi ban san shigowan shi kitchen din ba a lokacin sai ji nayi an rikeni daga baya an rungumay .
Dan firgita nayi don bansan ko waye ba dukda mu kaidaine a gidan dagani saishi daga baya na nasa hakan a raina.
Daskarewa nayi a gurin tsaye kamar mutum mutumi ya dan kwanto da kanshi gefen kunnena kamar mai rada yana fadin.
Kinyi wankan ke nan kin fara sallah zuwa yanzu yayi magana kamar yana rada kada wani yaji mai yake fadi a lokacin.
Shiru nayi ban motsa daga yadda nake ba ban kuma yi magana ba ya kara kwanto da kanshi yana matseni a jikin shi ya kara fadin.
Bakiji abindana tambaye ki bane zarah bana son ina magana ana kyaleni hakan zai hadani dake matukar ina magana baki ban amsa.
Tambayan ki nayi kinyi wankan hailan ki nace a dan tsorace sai nan gaba har yanzu yana nan bai dauke ba.
Dan murmushi naji ya sake kafin ya kara manna jikin shi sosai da nawa kamar zai ballani yace tun bakizo duniya ba nasan wanan babin yarinya .
Don haka koya dauke ko bai dauke ba a yau din nan zan karbi hakkina gareki gabanane ya fadi na tsorata da jin kalaman shi da kuma abinda hannayen shi ke mun a jikina.
Cikin wani irin murya da tsorata dan hawaye yazo min a lokacin nace don Allah yaya ka barni kabani salama a rayuwata na rokeka.
No no no zarah kiyi hakkuri yau ki ban hakkina hakkurina ya kare a kanki zuwa wanan lokaci ki tausaya ki daure in karbi hakkina a gutin ki hakana ?
Ina kokarin kwatar kaina daga irin rikon da yai min a lokacin naji yayi murmushi naji ba zan so in tilastaki in maki dole ba .
Tunda na rigada na gane baki da niyar bani a cikin sauki kamar yadda nake son bi dake a cikin lumana baki da tauayine zarah a ranki ?
Ya tambayeni a lokacin da yake dan dago kanshi daga kafada na da yake kwance kin san ban tare da merry a kasan nan balle ta kawar min da abinda nakeji a yanzu.
Kaina na kawar gefe gefe nace idan wane neni banda matsala daku zaka iya binta kasan da take ai ba don ni kake zaune a nan ba dama.
Anyway komai zaki iya fada a yanzu do ina neman hakkina a gutin ki yanzu saidai ki sani ba zai yuyu in zuba maki ido hakaba muna zaune a gida daya in takurawa kaina tunda sadakina ya bani hakkin yi hakan a tare dake.
Da farko naso mu fahinci juna dani dake ki gane hakan da kanki amma sai naga ke wanan baya gaban ki ko kadan .
Don haka zan karbi abina nawane bana wani ba aduk lokacin danaso kuma naga dama a wurin ki in yaso daga baya sai ki dauki wanan akidar da kikasa a zuciyar ki ki yafawa kanki kuma don kina ganin in anyi hakan abubuwa zasu biyo baya a zaton ki .
Ganin maganan shi da gaske yakeyi ba gudu baja da baya gaskiyar zuciyar shi yake fadi a lokacin don ya koma min kamar wani zarare dashi nake gani ba kunya ko shayi ko kadan a idon shi namiji ke nan.
Ganin da nayi shifa da gaske yake bada wasa bs yasa na sake kokarin yunkurin kwatar kaina daga rikon da yai min a lokacin.
Saboda na firgita ainun da abinda yake fadi a lokacin don ba wasa ko kadan a fuskan shi lokacin.
Don Allah yaya kayi hakkuri ka barni kada ka rabani da daraja ka wullakantamin rayuwa kazo ka kini daga baya in zama abin dariya a gurin mutane nasan bani kake so ba rashin matar ka yasaka zuwa gareni yanzun din.
Ban an kara ba naji ya matseni sosai a jikin shi yana aika mi sakkoni a dukka sasan jikina kuka na fara masa ina magiya ina hadashi da Allah.
Amma shi ko a jiki shi lokacin yayi nisa baijin kira saida ya gaji don kansa ya janye daga jikina yana maida numfashi idanuwan shina runtse.
Ina jin ya sake ni na fito daga kitchen din da sauri na har ina tuntube da kafet din kofan kitchen din na rugada gudu zuwa dakina.
Ina fita ya jingina bayan shi da carvenet din kitchen din yana jin wani irin shauki a tare dashi don bai taba zaton jin gamsuwa a jikin wanan yarinyar yadda yaji ba.
Yarinyar daya raina yake mata kallon karamar alhaki sai gashi tun farko taba jikin ta ya shiga wani yanayi daya kasa control din kanshi akanta tun lokacin.
Taushi da kamshi jikinta zuwa dukiya kirjin ta ya sa ya raja,a daya kasa kama kanshi akanta yanzu yanzu ya gaskanta maganan Yusuf yola da yake fadin kai kake daukata yarinya.
Ita mace bata da kankanta ai yadda ka rainata saita baka mamaki idan kaje gareta sai ka raina kanka.
A da yasa a ransa zai daure dukda babu soyayyanta a gare shi zai daure ya sauke nauyin daya rataya akanta shiyasa ya fara tilastawa zuciyar shi zama da ita koda ita din bata da ra,ayin hakan dashi.
Da kyat ya iya daga kafa yabar kitchen din cikin dayi jiki ya nufi dakin shi gadon shi ya hau ya kwanta rub da ciki ya rintse idanuwan shi babu abinda yake gani sai suran fatima zarah aruwa sayadin mamu a lokacin.
A dakina ina shiga na rufo da zumar murza key a kofan sai dai babu shi babu alamashi gutin haka yasa na rufo kofan da karfi na nufi gado na fada zuciyana cike da tsoro da fargaban yaya da wanan sabon yanayin da yazo min dashi yanzu.
Sam ban kawo rashin ganin key dina a lokacin yana da nasaba da yaya ba don ba mutum bane daya kula da shiga min daki babu dalili tun zuwa na gidan key din yana makale a jikin kofan.
Na dade kwance a dakin can na tuna da girkin dana dora a gas da sauri na yunkura cikin sanda na nufi kitchen ban ganshi a falon ba na shiga kitchen din na samu ya rage min karfin gas din.
Sauri nayi na kammala na gyara gurin don kada ya dawo ya riskeni ciki ranan a dakina naci abinci nayi sallah ina gamawa hutu muke na danyi karatu na shiga nayi wanka don akidanane yin hakan ban iya kwanciya banyi wanka ba tun a gida na saba da wanan wankan daren.
Na fito har lokacin jikina bai sake ba a gidan tunda nasan yana gidan lokacin don ba inda zai tafi din yanayin sanyin da kasan ke ciki mutane in ha dole ba basu faye zirga zirga zuwa ko ina ba.
Bayan na kammala shirina na kwanta har barci ya fara zo min sai lokacin na tuna da ban rufe kofa ba don gujewa yaya ranan don a da haka nake barin kofan koda baya gidan ma.
Tashi nayi na fara tunanen ina key din kofan ya shiga duk iya neman da nayi mai ban iya ganin sa ba a dakin.
Haka na koma na kwanta jiki a sabule naja bargo na rufe jikina dashi har kai sannu a hankali barci ya fara daukata.
Banji shigowan shi dakin ba don barci ya fara daukana a lokacin ya shigo dakin ya tsaya yana kallon yanayin dana kwanta din a tsorace nake da alama.
Fitalan dakin ya kunna haske ya gauraye dakin ga baki daya zubur na bude idona daga barcin daya fara fisgata na bude idona na sauke a kanshi.
Yana tsaye ya harde hannayen shi ya zubamin idanu akaina ba wasa ko wani sayina fuskan shi yace ki tashi kiyi alwala sallah zamuyi.
Banga fuskan yin musu ba a lokacin na tashi kamar yadda ya umurceni ina tafiya kamar zan fadi don tsoro a lokacin.
Sai dana dan bata lokaci zuciyana cike da tsoron abinda zai faru a kaina wanda ban sani ban taba zaton haka zaizo min ba.
Har na fito na samay shi a tsaye a tsakar dakin nawa ya kurawa wuri daya ido kamar mai tunanen wani abu a ranshi jin karan budan kofana bai tsaya ba naga ya nufi saman sallayata.
Jiki ba kwari na fara neman abin sallahna na saka lokacin naji ya tayar da sallah ko.
Raka biyu mukayi saidai don dogon surar da yaja muna a lokacin yasa muka dan dauki lokaci muna sallah.
Mun idar ya tsaya addua a baiyyane godiya ga Allah da neman zaman lafiya da zuri, a masu albarka ya shafa nima na shafa.
Naji ya ambaci sunana a hankali haka yasa na dago kaina na dan kalleshi kafin yace zarah ki kwantar da hankalin ki ba ha,intarki zanyi ko wani abu ba idan nayi hakan na zalunci kaina na zalunceki riban mai zan samu a yin hakan.
Ki tashi mu kwanta ba komai zan maki ba kwanciya kawai nake son muyi tare har zuwa ranan da zaki bukaci ban hakkina da kanki.
Kuka na soma yi sosai a lokacin ya dago tare da dafa min kafadana ya kara matsowa gaf dani har ina juyo numfashin shi a lokacin.
Kidimaiwa nayi lokaci guda don gaba daya ya juye min daga yaya ya koma min wani abin tsoro yanzu s rayuwana.
Ban san lokacin dana kai kaina a kadan shiba ina kuka ya dade zaune yana sauraren kukan nawa bai hanani ba.
Harsai da yaji na sau#uta kukan ya mike ya dauke ni sai saman gado tare da kashe fitilan dakin yana sauke numfshi a hankali.