NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA

NOVEL DIN KUDINE DON ALLAH KI KIYAYI SHIGA HAKKIN WANI YAR UWA
16/11/2021, 23:24 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM IYYAKA NA ABBUDDU WA IYYAKA NAS,TA,IN, , , ,

Tun lokacin daya fahinci barci ya dauki ni yayi ajiyan zuciya tare da kallon yadda nake sauke numfashina a wahalce har lokacin a tsorace nake da abinda ya faru tsakani dashi din a wanan daren.
Jin ajiyan zuciyana a cikin barci yasa ya dan rungumay ni zuwa jikinshi yana sauke ajiyan zuciya a hankali tare da fadi a cikin ranshi.
Zarah kin shayar dani mamaki a rayuwata dama hausawa sunce samun abin kwarai wahala gare shi.
Wahalan da yasha da zuciyar shi da tashin hankalin mutane da dama daga ahalin shi ma duk akan cikan wanan burine na mahaufin shi.
Lalai hausawa sunce abinda babba ya hango yaro yaro ko yahau tsauni ba zai taba hango shi ba tabbas daddy yayi gaskiya wurin dawo da rayuwan shi ta asali.
Tabbas ance kowa yabar gida gida ta barshi duk daba wai ya taba wani abin asha ba a rayuwan shi saita hanyar sunna.
Zai iya cewa matan hausawa daban suke ashe ko ta jinsin su yau sai yake ganin kamar farkon shiga jikin wata mace ya fara a rayuwan shi don irin ganima da ni,ima da natsuwan daya diba a jikin yarinyar daya raina da farko.
A fili ya furta Allah ka yafe min daddy na tuba nayi kuskure ka yafe min daddy naso in yaudari kaina in yaudare ka.
Ashe ba zabin banza kai muna ba daddy ka fimu sanin abinda bamu sani ba a rayuwan mu yau da nabi ra,ayin mama na bijirewa daddy da na yaudari kaina ashe.
Da kyat ya samu ya dan runtsa idon shi barci ya dan daukeshi kadan da asuba alarm din wayan shi ya tayar dashi don sallah.
Firgigi ya falka yana kallona har lokacin barci nake ina sauke ajiyan zuciya saboda kukan dana sha.
Ya mike yana tunane a ranshi kodai zalaman shi yasa yajinwa yar mutane ciwo bai sani ba in ma zalaman ne yasan yayi mata haka kanta daren jiya zai iya cewa matsuwan shice ta ja mai yin hakan don a matse yake a yan watannin nan yana bukace da bukatan shi.
Har yakai bandakin ya shiga don yin wanka yaga wurin a tsabtace kamar inda ba,a amfani dashi ko yaushe komai na gidan yana nan tsab dashi don tsabta zarah badai tsabta ba .
Duk tsaba da kulawan shi saida ya yabawa tsabta irin na zarah a rayuwan shi yarinyace zarah karama amma tarbiya data samu a gida yasa ya fara kwadaituwa da halaiyan ta.
Don irin yadda ta iya boye sirin su tsawon shekara biyu da rabi ba wanda yasan alakan auratayan dake tsakanin don dokan daya saka mata kawai.
Tasan idan yana gidanta ta ciyar dashi yadda ya kamata sai dan gyaran da yai mata kadan wanan kuma yasan karancin shekarunta ne ya hana ta gane hakan.
Har ya fito daga wankan bayan ya hada ruwa masu zafi a ciki har lokacin ina kwance ina batcin wahala.
Sallah ya tayar a kada ya makara yana idarwa ya nufo gadon ya ya dan kira sunana a hankali haka yasa na dan motsa ganin da yayi ban da niyar tashi yasa shi sukutana a cikin barcin na danyi kara ina fadin a wahalce don Allah yaya kayi hakkuri na dauka wani abin zai kara yi min kuma.
Saida ya tabbatar da na zaunu da kyau a cikin ruwan dumin ya bar ban dakin zuciyar shi cike da tausayina a lokacin don kawai baida zabi ne har hakan ya faru tsakanin mu.
Don saboda da shakuwan da mukayi a dan zaman tare sai yake jina wani bangare na zuciyar shi yanzu.
Sauka yayi zuwa kitchen ya hada min tea mai zafi da kauri tare da dauko magani a dakin shi ya nufo dakina har lokacin ina zaune na kasa anyanawa kaina komai a bandakin sai kukan da nake wanda ba sauti ciki.
Muryan shi naji yana fadin ba zaki fito hakana ba lokacin sallah yana shigewa ko sai nazo nayi maki da kaina.
Jin hakan nasan yanzu ba karamin aiki bane gare shi don zai iya yin hakan tunda ya furta hakan a fili.
Da sauri na dan cudanya jikina yadda addini ya koyar damuyi ji nayi ba zan iya kara sanya zanin dana kwanta dashi ba na dan leko kai daga ban dakin sai na ganshi a tsaye ya ban baya kafita in dauki zanina don Allah na iya fadi a lokacin.
Da sauri ya juyo don jin abindana fada yana fadin a ina zanin yake in miko maki nidai ka fita don Allah in dauka da kaina nace cikin dan muryan da bai fita.
Baiyi magana ba sai naji ya juya ya fita da sauri na fito na dauki zani na daura na saka hijjab din sallahta na tayar ina idar a lokacin kuma abinda ya faru tsakanin mu ya dawo min a raina tiryan tiryan wasu hawayene suka ziyarci idanuna bal,bal,bal lokaci guda.
Kuka sosai na zauna nayi ni kadai a dakin mai faruwa ya riga daya faru a daren jiyan saura in tsura ido inga sakamakon da zai biyo bayan abinda ya faru din tsakanina da yaya yanzu.
Tun da har mahaifiyata ta kasa ban zabin kaina na matakin dana dauka da nake ganin zai fitar damu daga manufan su maganan ta kullun nakira ko takira shine inbi umurnin mijina in mashi biyyaya ma,ana dai in mika kaina a gareshi a fakaice .
Nasan yanzu sunana karamar bazawace a gurin shi kai ba wurin shi bama a gutin kowa dana sani don ba yadda za ayi indai ba hjyn su ce ta janye maganan ta akan mu ba ya zauna dani har madi.
Tau yau dai na mika saura mamu da kawu dasu amma su saurari hukuncin abinda zai biyo bayan umurnin su yanzu gareni.
Haka na zauna ban iya tashi a gurin ba balle duk motsi sai na runtse idanuna don ciwo da nake ji a karkashina har a cikin raina nake jin shi lokacin.
Ina zaune ina ta sake sake a raina in kulla wanan in warware ni kadai a dakin na kudundune kaina da gwiwa na.
Muryan shi danaji yasani razana da sauri na dago kaina fuska shabe shabe da hawaye ido ya kurawa yanayina ido a hankali ya kai tdugunne a idana nake zaune.
Dan rungumoni zuwa jikin shi yana fadin oh sorry zarah don’t cry again don wanan abin ya faru tsakanin mu kike zubar da hawaye haka ?
Makin ki godewa Allah da ya tsareki ya baki ikon sadaukawa dan uwan ki da wanan abin mafi daraja ga mace.
Don’t cry again kukan nan naki yana taba min zuciya matuka ba sai kinyi kuka zan gane abinda nai maki bada sin ranki ba and kuma wanan kukan yana nuna min irin kiyayyan da kike mun a filine zarah.
Ban iya magana ba ban kuma dago kai na kalleshi ba jin nayi shiru ba amsa ya mike tsaye a hankali ya dagoni daga inda nake zaune a takure.
Bakin gadona ya kaini ya zaunar dani a hankali ya mika hannu ya dauko flask din shayin daya hado min ina kallo ya tsiyaya a cup ya miko mi yana fadin karbi kisha sai kisha magani don jikin ya rage maki tsami.
Da kyat na iya bude baki nace dashi na koshi cikin muryan kuka kin koshi damay yaci yana kallona .
Maza karbi nan ki shanye in baki magani ko kuma ranki yanzu ya baci a dakin nan jin yadda yake magana fuska a daure yasa na mika hannu da sauri na karbi kofin shayin na fara kurba kadan kadan saboda banjin dadin shi ko kadan a bakina.
Yana tsaye ya dora hannayen shi saman kunkurun shi ya rike da hannu biyu haka yasa corth din jikin shi fara dan dagawa daga baya ta yadda zaki iya hango zanzaron shi da farar rigar shi ta ciki.
May zakiyi yace yana kallo na fuska na yamutse nace nakoshi yace kina wasa da nine zarah ki shaye nace sai ki sha magani fuskan shi a daure.
Don dole na mayar da cup din a bakina ina kurban shayin a hankali yana tsaye ya kura mi idanu kadan na rage cikin cup din na aje saida ya kalla yace wanan fa na maiye kika rage.
Da kyat na iya budan baki nace mai wanda zan sha maganin dashine sai naga ya juya zuwa inda ya dauko flask din magani ya dauko yana barewa kwara uku buyu iri daya guda daya kalan shi daban ya miko min na amsa ina juya kafin in watsa baki ina bata fuska don dole na hade da kyat.
Ko ke fa yarinya da raki haka don’t be lazy don mijin ki jarumi ne shi don haka ban son mata ragguwa daga dan tabaki kike wanan rakin haka.
Aini ba yar iska bace nace a hankali yace niko dan iskane amma fa da matana don haka saiki shirya koyon iskanci daga yau.
Zaki iya kwanta ki huta zan dan fita in samo muna abinda za a ci anjima yace ba tare da ya tsaya jin mai zance ba ya fice daga dakin.
Nabi bayan shi da kallo ina maida kaina ga filon dana jawo a kusa dani don ban son yin dogon motsi a lokaci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button