SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Bayan ya fitane ya duba motar shi idan tana fita ganin kankaran ma kara rufe motar yayi lokacin yasa ya hakkuri ya tare taxi zuwa inda ya nufa.
Barci nayi sosai daga kwanciya na don haka bansan lokacin daya dauka bai gidan ba sai wajajen la,asar ya dawo har lokacin ina barci.
Tayar dani yayi inyi sallah lokaci ya kure ban koyi azahar ba haka na daure na tashi na shiga bandaki ruwa masu zafi kwarai na hada na kara shiga sai naji dadin jikin nawa a lokacin na dan dade zaune a ciki kafin in fita in daura alwala na fito naji dadin jikin nawa ba laifi don ya rage min yadda nake jin shi da farko.
Yana fita falo ya koma yaci abinci sai kuma ya zauna waya da wata kawar merry data kirashi tana tambayan dalilin daukewa merry da yarta kafa da yayi ?
Don merry taki kiranshi don tasan shi da kansa zai nemai ta idan yana da bukatanta duk zai kare fushin shine su dawo daidai don bai iya broke da ita.
Bai fada mata komai saicewa da yayi is a family issue don haka ba maganan su bane.
Yana gamawa ya aje wayan yana juyawa sai wayan ya dauki wani kiran kuma ya dauka itace sai ya dauko da zuman cewa ta barshi kada ta kara kiran layin shi.
Saidai baikai ga hade fushin shi ba mamaki ya kamashi ganin sunan mai kiran shi a fili ya furta mama ya dauki wayan.
Gaisawa sukayi a mutumce da farko kafin dan shiru ya biyo baya sai can hjyn ta kawar da shirun ta hanyar tambayan shi yaya iyali ya amsa da suna lafiya mama tace kadai ki kawo min takwarana har wanan lokacin in gane ta.
Yace zamu zo mama in Allah ya yarda har lokacin yana mamakin kiran mahaifiyar tasu a yau.
Baza kuzo ba don kada na tursasa ma ka saki wanan yar banzan yarinyar daka lakawa kanka na fadama ba zan hada zuria da wanan iri tsiya ba a jinina .
Haba mama kiyi hakkuri ki bar wanan maganan haka ki barwa Allah dalilin shi nayin haka a kan mu.
Rufa min baki mara kunyar banza duk bare baren da kakeyi na na sani bawai ban sani bane don magana bai biyuwa a gidan nan.
Uwarta ta mayar dakai saniyar tatsa yanzu sun samu wurin ci tunda na ubanku ya kare yanzu shi yasa tun farko naki wanan abin don nasan idan sun samu namiji ya zama bawan su.
Mama akan mai zanyi wani bare bare matar nan fa yarta na a hannuna akwai nauyi a tsakanin mu yanzu fiye da da can baya tunda ina auren yarta.
Yarta na gidana zaman matana ace kuma ko gausuwa ba zamuyi ba da ita ai abinda nauyi mama danne hakkin yayi yawa mama.
Babawo kasan mai wanan furcin nake yake sakani yanzu a gaba har zaka iya kiran wanan yar da wai matar ka ?
Da kasan yadda naji a yanzu da wanan kalamin naka haka da baka furta min ba har yaushe ta zama matar taka kuma ?
Ina kace min ba a gari daya kuke da ita ba ba ruwanka da ita rufa ido kawai kake ma mahaifin ku kadai sanyata karatune kawai.
Mama amma ai na baro gida da itane da sunan aure ko in banda ke ai ba wanda na fadawa gaskiyar zancen.
At list ko bata karu dani da komai ta karu dani da karatun da takeyi don fushin daddy ya rage a kaina sai ya dauka laifinsu ne.
Kai babawo kana jina ka turo masu yarsu gida nake bukata yadda suke bakanta min rai a nan da uwarta da duk wani dangin Alh suma suji a jikin su.
Yace mama ai saura dan lokaci kadan ta karasa karatun ta gaba daya kinga sai na tarkatota in turo ta gida zuwa lokacin.
Amma yanzu tunda bata kare karatun ta ba ai kinga dawo min da ita za ayi nan kuma zaune bai kare muna ba ke nan kuma.
Babawo bakan yadda na tsani wanan yar ba a rayuwata naki jinin wa yan nan mutane wallahi balle har in hada iri dasu kai ni wanan matar takama tafi soyo min a rai bisa ga yarinyar nan Fatima.
Mama na gane mai kike nufi ai ki dan ban lokaci kadan ya rage komai yazo daidai ai naji tace cikin isa tare da fasin matsiyata ai ko banza saida suka karu damu da wanan karatun daka sakata yi.
Ba komai mama kiyi hakkuri komai zaizo daidai a daidai lokacin ya dago kai mukai arba duk da fitowana ke nan daga dakin bai hana in fahunci da mahaifiyar shi suke magana ba lokacin don jin karashen maganan su.
Ya samu ya lalabata ta yadda ba zan iya fahintar komai ba lokacin sai bayan ya kashe waya ya dago yana fadin ki sauko mana kinja kin tsaya kuma nan.
Kamar in juya in koma saidai da ya riga da ya ganni a lokacin don haka banda zabi na tako a hankali ina saukowa daga saman benen.
Nazo na samu wuri na zauna dan nesa kadan dashi zuciya ta sai fadi nake shike nan ta faru ta kare dama hjyan su ce ta matsa ya lalatani ya sako ni ashe ?
Ya jikin naki maganar shi yasani dagowa firgigit daga tunanen da nakeyi a lokacin nace a hankali da sauki .
Zaki iya tashi ki zuba abinci ko na zubo maki zan iya nace mai ina kokarin tashi ina cije baki ya bini da kallo kafin yace ko mu tafi asibiti ne a dubaki ?
Naji sauki na bashi amsa ba tare da na juyo na kalleshi ba na nufi kitchen din kai tsaye.
Abincine lafiyayu masu tsada da bazasu lalace ba kwalaye da yawa kala kala ya sayo ya aje a kitchen din ma,ana zan kwana biyu ban girka muna abunci bake nan.
Dan tsankwaro abincin nayi na fito ban nufi dining inda na tashi na zauna ina cakulan abincin a hankali.
Ya sake dago kai ya kalleni yana fadin wanan abincine ko shirmay wanan din zai kosar dake ?
Kinsan yanzu abincun da zai gina maki jiki mai kyau ya kamata kitche shiyasa naje halal store na sayo maki wa yan nan din don sune daidai kici kwana biyu don ki helling.
Ban dai dago kai na kalleshi ba ko in tanka mai naci gaba da cakulan abincin ina kaiwa baki a hankali.
Wayana ya dauki ruri na dan kalla ga mamakina mamuce ta kirani naso share wayan sai naga ya dago ya kalleni yana fadi bakiji bane wai ?
Wayan na kalla ina ya mutse fuska na dauka tare da sallama ciki ciki babu sauti ina fadin mamu ina wuni yayi saurin dago kai ya kalleni.
Sai kuma ya dukar da kai yaci gaba da zanen shi a board ya maigidan naki sayadi ta tambaya nace lafiya.
Bata saurareni ba tana fadin yanzun muke kallo aka nuna yadda kankara ke ta,adi a garin ku shine nace bari kiraku inji idan da sauki wurin ku ?
Nace ai kuwa kawai da ganin yadda ya dago kamar baiji dadin yadda nake amsawa din ba sai ta tambayeni waiko lafiya kike sayadi ?
Lafiya,lau na karasa da kuka da sauri ya dago kai yana fadin mainene haka a hankali ta yadda ba zata jiyoshi ba.
Mamu a cikin fada take fadin ki godema Allah, Allah baki miji salihi sayadi don da wanine wanan iya shegen da kikeyi na shagwaba da bai daukan maki shi ba wallahi.
Nasan Umar sosai nasan halinsa sayadi Umar mutum ne mai hakkuri da sanin ya kamata mutanen da basu sanshi bane suke ganin shi shu,umi.
Kawun ki yasan da hakan kullun yana godiya ga Allah kasancewarki matar umar kibi mijin ki sauda kafa sosai zaki ji dadin shi sayadi.
Banda shakkan komai akan auren ki don zuciyata ta yarda da wanda kike aure sayadi don haka ban yafe daki sabawa mijin ki ba ta hanyar aurataiya kinji na fada maki.
Sunkuyar da kaina nayi kasa lokacin sai hawayeb dake min ambaliya har yana diga daga cikin idona lokacin don haka ki natsu kiyi biyayyan aure don shi kikaje yi ba wai ki raja,a akan karatu ba kawai.
Nasan yaya na jin mu don shirun da falin yayi lokacin koda baiji duka ba yana jin wani abinda take fadi ta kare da fadin ni zan kashe ki gaida mijin naki idan ya shigo ubangiji ya kara albarka kice ina masa godiya don Allah.
Kamar in ce tamai mamu saidai babu halin yin hakan a lokacin tayi sallama ta kashe wayan har lokacin hawaye bai daina fito min a idanuna ba don takaici da dacin da nake ji na kowa har mamun dake yabon sa yana ji.
Saidai ban san hakan karin daraja uwata bane a idon shi don dana dan dago na saci kallon shi yana zaune ya bar abinda yake idanuwan shi a lumshe da gani yana cikin yanayin tunane mai zurfi a lokacin.
A raina nace ji munafuki kamar gaske kai namiji dai muna fukine ashe da gaske yanzu fa na gama jin sunayi dani da mahaifiyar shi.
Niko ga nawa uwar tana yabon shi kamar ya biya mata makka shidai yaya tunane zancen su da mahaifiyar shi yake ta yaya mama ke son in wullakanta masu ya ta gama zagin su uwarta kuma ta kira tana yabona da sa yarta ga hanyan daidai.
Sam ba zai iyaba yanzu ma ya fara zama da yarinyar nan idan mama bata sani ba yanzu ya fara sanin wacece zarah a shirye yake da ya saudakar da duk wani fitina da zai biyo baya idan an koma gida shi yasan irin shawaran daya yake a zuciyar shi ya kuma barwa cikin shi komai.
Bai kulani ba harna gaji nabawa kaina hakkuri don dole sallah ya tayar damu do lokaci yayi dakina shiga nanma sai dana dan gasa gabana don ruwan dumin dake min dadi idan na shiga.
Bayan na idar da sallah ban fito ba na haye gadona na kwanta sai faman tunane da nakeyi ni kadai a daki.
Kofan ba wani kara yakeyi ba idan an shigo dakin sai idan mutum ya kula sosai zai gane an shigo amma shi da yake shike da gidan sa yasa taba kofan ko wani lokaci aka taba din.
Ya dan tsaya tsaye yana kallon yadda na kwanta rub da ciki na lafe saman gadon ya dan yi murmushi yana fadin .
Nasan ba barci kikeyi kina jina ki tashi kici abinci mu kwanta tunda barci kike ji yau.
Shiru nayi ban dago ba daga yadda nake kwance dake fa nake magana zarah ya fada da dan karfi nace ni koshi ciki ciki to ki tashi mu koma dakina daga yau a can zamu dinga kwana tare don ba zan yarda inada mace a gida mu raba dakiba ba wani dalili mai karfi.
Cikin dan marairaicewa nace don Allah yaya ka barni nan yace gardama zaki mun tuno da ban yafe ban da mamu tai min dazu dazun nan yasa da sauri nace a, a yaya.
To ki tashi ina jiran ki a dakina ya fadi yana fita tun kan ya karasa fita nace ni kan yau na mutu na lalace a gidan nan.
Bai juyo ba saidai ya wuce yana murmushin magana ta a fili don shirmayna dariya ma ya koma bashi yanzu.
Na dade a kwance ina sake sake a raina kafi in daga a lalace na koma bandaki nayi tsarki da ruwan zafi tare da dauroyo kaina kamar yadda nake kula da mamu idan zata turaka tanayi don wani lokaci ina zaune muna hira zaitai ta faman lakace lakace da shafe shafe ina kallon ta ashe kallkn zai mun rana watarana ban sani ba.
Da kyat naja kafa na nufi dakin ina rabe raben bango na tura kofan a hankali na shiga ban samay shi a dakin ba haka yasa nabi dakin da kallo a hankali duk da dakin ba bakona bane saidai a kwai sauyi sosai ga dan kwana biyun da banshigo ba mamakine ya kamani sosai a lokacin.
Dan gyara muryan shi naji daga bayana inda hakan yasani nadan firgita kadan haunun shi dauke da plate da goran ruwa da cup.
Na gane nufin shi haka yasa na dan yamutsa fuskana kadan bai min magana saida ya aje abincin saman dan karamin table din gaban miro tare da jawo shi zuwa bakin gado ya aje goran ruwa a gefe daya ya kalkeni yana fadin oyo zauna kici kafin in fito.
Ni na koshi ina batarai don damuwa yayi min yawan da ba zan iya boyewa ba a lokacin ashe kina da aiki babba gamay dani.
Idan baki sani ba yau ki sani ba aimum mussu ga magana idan na fada final ne idan kuma kin ki bi kisha wahala .
Yana fadin haka naga yana kokarin sance igiyar dake daure a rigan shi duk rabin kitjin shi yana waje dama da sauri na kawar dakaina daga kallo abinda yakeyi din.
Nakai fuskana ga abinda ta aje min kazace taji hadi tana tururi gunduwa uku saidai manya ne yankan kwarai ko daya ba zan iya cinyewa yadda nakejin dandano bakina ya canza min.
Hakana na daure ina dan yaga a hankali ina hadewa da kyat duk so kazan da nake wanan yaimin ba dadi a baki.
Ya fito ya dan tsaya gaban mirro yana dan lakace lakace kamar mace kafin ya juyo gurina saida ya kalli plate din ya dago ya kalleni takowa yayi zuwa inda nake ya zauna daf dani kafin ya mika hannu ya dauki fork din ya da yuka ya yanko ya mika min kawar da kaina nayi gefe .
Sai naga yama mayar dani karamar yarinya a lokacin fuskan shi a hade yake dole na bude bakina ya sa min yanka na uku na dafe bakin sai hawaye naga ya girgiza kai kawai ya aje fork din da yukan kawai ya mike da kayan zuwa waje saida yakai kofa ya juyo yana fadin ki kwanta kawai.
Ban yarda na kwanta ba har lokacin daya dawo gani a yadda ya barni zaune ina dan wasa da yatsun hannu na yace cikin mamaki baki kwanta bake nan ?
Dan marauraicewa nayi da kaina da murya ina fadin yaya ka barni in koma dakina don Allah wallahi tsoro nakeji kayi hakkuri don Allah.
Shiiiii yasa yatsa saman bakin shi yana min alaman inyi shiru ya nuna min gado da hannun da sauri naja nakai kwance na kudundune a wuri daya idanu a runtse.
Ban san may ya tsaya yi ba saida ya dauki dan lokaci ya kashe din light din daya rage yana aiki a dakin naji ya hau gadon ya kwanta na kara runtse idanuna a hankali.
Saukan hannun shi saman jikina yasani dan zabura kadan zangudu ya rike ni gam a jikin shi yana sauke numfashin da ban san na maiye ba.