NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

NOVEL DIN KUDINE DON ALLAH A KULLA NIDAI NA FITAR MAKU DA HAKKINA NA FADA MAKU.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:24 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM IHHIDINAS SIRATAL MUSTAKIN, , , , , , , ,

Sannu a hankali ya umar ya kowa min shakuwa dashi da sake jiki inyi komai a gaban shi ba tare danaji nauyin shi ba kamar yadda muke da farko dashi.
A cikin yan kwanaki wani shiri da kaunan juna muke gwadawa junan mu a gidan duk da shi bagwanin son surutu bane amma haka takan biye min ina bashi labaran gida wani guri yayi dan murmushi wani gun yace baki ko kyauta ba zarah shiya ake cewa baki da kunya din tun ban dawo na ganki ba nake jin labaran ki a nan .
Sai dai da na dawo nayi nazarin zaman ku dasu salma na dan fahinci wasu abubuwa game daku a baki daya.
Nace yaya mai ka fahinta daka fara ganina yace ai kin san kece na farko dana fara haduwa da ita ranan dana dawo ko ?
Dan tunane nayi kafin ince haka ko akayi sai na dan turo baki nace ni ai banga kayi kama da hjyn kun bane yasa na tsayama gardama.
Zarah wai kinsan a sanadin ki na bata da hjyna da dacan baya nine dan gaban goshin ta kowa ya sani amma yanzu kin sa komai ya lalace a tsakanin mu da ita.
Yanayi na yadan canza lokacin da yake wanan magana sai ya ban tausayi ko wanan zuwan danayi duba daddy na dauka abin zaiyi sauki zuwa lokacin ta hakkura dake amma sai na samu abin ba haka yake ba a gurinta haryanzu.
Cikin sanyin jiki nace abinda nakewa gudu tun farko ke nan yaya gashi yanzu shakuwa da , , , sai nayi shiru yace damay fa ki karasa mana kinyi shiru ?.
Barshi kawai yaya na fada yace ai baki isaba ba kince baki da kunya ba sai kin fadamin shaku damay ya shiga tsakanin mu yanzu ganin ya tsatsareni da manyan idanuwan shi nan nace sabo dan murmushi naga yayi yana fadin ashe kina da saura ke nan tunda kin kasa fadin abinda kikai niya.
Tambayan dana jefo mai yasa ya dago don duk hiran da mukeyi kanshi a laptop din shi yana aiki a ciki nace yanzu yaya ana nufin zaka sakeni ne idan mun koma gida ko may ?
Da sauri ya dago kanshi yana fadin wanan banzan tambayan ina ya fito maki haka ni ba namiji bane mai sakin mata hakkuri mama zatayi ta barmu tare.
Ke dai abinda nake son ki dashi shine kada ki yarda da duk abinda mama ko yan uwanta ko nawa yan uwan zasuyi maki kimasu rashin kunya don ba zan iya lamuntan hakan ba ga matata ta raina min yan uwa ko iyayye don haka ki kula da wanan .
Komai nisa da mama da nakeyi a yanzu nasan wata rana haduwa zamuyi dani dake da ita a lokacin abubuwa da dama nasan zai faru so ba zanso ace wai matana tanawa uwana rashin mutunci ba ko kadan.
Shiru nayi kamar mai nazari lalai va karamin so yakewa mahaifiyar shi da yan uwanshi nasha jin Amma na fadin haka akwai shakuwa sosai a tsakanin hjy jummai dayaran ta.
Wanda har hakan yasa kowa ya jaye ya barta dasu don ita din bazata bar wani ya fadi laifin diyan ta ko kadan ba a gaban ta.
Shiru nayi ina cigaba da nazari a raina nasan akwai aiki babba a gabana kan zama da yaya umar nan gaba ta bangaren mahaifiyar shi da wurin matar shi merry da a yanzu na gama fahintar akwai matsala a tsakanin su do merry din banjin tana kiran shi shima hakan bai kiranta kamar da da mintuna kadan zanji dayan su ya kira daya a waya koda a ganane suna soyewar su.
Shin hakan na nufin damata ke nan ta hanyar batawan shi da merry shine silar kulawan da nake samu a wurin shi yanzu.
Lalai namiji abin tsorone ga mace gashi dai yanzu yaya ya mayar dani tankar wata sarauniyar ruhinshi zakace bai taba son wata mace ko sanin wani soyyaya da mace a baya sai wanan lokacin .
Zanbi a hankali har in gama nazarin in fahinci inda ya dosa dani a rayuwan shi don dole sai nayi taka tsamtsam so kada in fada a tarko daba zan iya fitar da kaina ba akanshi.
Ganin ya mike daga inda yake zaune yasa na dago kai a hankali ina kallon shi ki dubi lokaci magariba ya gabato kin zauna kina tunanen banza.
Mikewa nayi zuwa dakina inda na gabatar da salloli har da isha,i bayan nafila wanka nayi kafin in sauko kamar yadda ya koyar dani cin abincin dare a tare dashi.
Tun ina matakalan benen mai hawa daya ya kura min ido har saida hakan yasa na dan tsargu da kallon da yake min din.
Gaida shi nayi ya amsa yana lumshe idanuwan shi na wuce kitchen na hado muna abincin na kawo saida na gama aje komai na juya ina fada mai nagama hada wurin.
Mikewa yayi a cikin yanayin shi rashin kuzari ya tako zuwa table din ina duke ina zuba abinci a plate naji yakai hannun shi saman west dina.
Dan zabura nayi kadan bai damu da reaction dina ba yaja kujera ya kai zaune abincin ya kurawa idanu har na gama zuba nawa naja kujera na zauna.
Sai lokacin na dan dago na kalleshi da alaman lafiya a idona kai ya girgiza min yana fadin ba wanan abincin nake so ba yanzu.
Zarah na dauka zaki fahinci halin da nake cikine yau ki lissafa satin mu biyu cif da ki ban hakkina nayi hakkuri ko keda kanki zakiga dacewan hakan ki bani sai dai banga alaman hakan ba agare ki ko yanzu.
Tunda ya fara maganan shiru nayi ina dan cakula abincin dake gabana na kasa kaiwa a bakina jin yayi shiru na dan dago kaina kalleshi shi din ni yake kallo a lokacin.
Yace na dauka kinsan mu maza bamu da dauriya a wanan famnin gashi ni ban iya neman mata ba balle in nema a gurin wata waje.
Da sauri na dago kaina dan kalleshi jin abinda ya fada yanzu hakkuri na ya kare akan ki zarah ke kuma na fahinci raguwace a wanan fannin sosai ya zama dolr ki daure ki ban hakkina akoda yaushe don nima mutum ne mai jini ajika.
Ma,ana nidin namijine mai bukanta mace a tare dani yana daya daga ciki abinda yasa har na auri merry a lokacin don in kare kaina daga zina.
Ba don naso ba dole ranan saida na sadaukar da kaina a guri shi na hakkura na kyale shi yayi yadda yake so dani.
Duk iya daurewana na yishi amma a karshe saida nayi raki don na takura da yawa a lokacin tunda ban saba ba.
Banji jikiba kamar na ranan farko danaji wanan yadan bambamta kadan da wancan na farko.
Nasha albarka a wutin shi tare da alkawura idan har na daure ina faranta mashi rai kamar yadda yakeso dani.
Washegari shiya tayar damu da asuba don na kula ashe mutum ne mai yawan addini sosai shi din don wani lokaci saidai in falko a cikin dare inganshi yana sallah ko karatun alkur,ani maigirma a cikin dare.
Wanan shi ake ma karin maganan karka yiwa mutum shari da abinda kagani a fili don baka san zahiri shi ba koshi waye ?
Bayan mun idar da sallah na yana zaune yana karatu na nufi dakina na fara kimtsawa kafin in fito in gyara falo har zuwa kitchen da sauran wurare a gidan.
Dan tsamin da jikina yayi a lokacin baisa na biyewa haka ba ciki dauriya mayarda gidan tas cikin dan kankani lokaci.
Daki na koma nayi wanka na saka daya daga cikin rigunan daya sayo min daga tafiya rigan baida nauyi yana da dadin sawa don rashin nauyin shi soft yadi ne sosai.
Ban jima da fitowa daga dakin ba shima ya fito muka zauna mukai break yau sai satan kallona yake ina kawar da idona don kunyanshi nake ji a lokacin.
Wayan shi yayi kara a daidai lokacin da muka kammala karyawa ya din ya dauka cikin basarwa muryan yarshi queen ne a wayan ban san ita bace sai lokacin da naji ya ambaci sunan ta din..
Dan dago kai nayi ina kallon shi ban dai ji may take fada mai ba sai murmushin danaga yanayi ne yasa nagane wani abu take mai albishir dashi.
Abinda naji yace yasa na mike don bashi guri suyi wayan cewa yayi I soon come to see you queen.
Ke nan zai tafi guri matar shi nace a raina ashe haka mata ke jin kishin abinda baikai ya kawo a fannin kishi.
Saida naje daki na kwanta ina ta sake sake a raina kafin in tambayi kaina a karshe ke yanzu kishi kike ko mai fatima.
Dan murmushi nayi a fili nace ke nan na fara kishin merry ko may a raina matar da nazo na samu da mijin ta har yaushe na fara kishin su a raina .
Lafiya kika dawo nan muryan shi naji a kaina nace ba komai ina dai son in hutane na dawo daki na kwanta .
Kamar bai yarda da abinda na fadi din ba don irin kallon danaga yana min a lokacin.
Zama naga yayi bakin gado nawa yana fadin queen ta kirani yanzu tace suna da buki a makarantar su da zasuyi tana kuma bukatana a wurin.
Allah ya kai lafiya nace ban bari yaci gaba da magana ba llokacin naji yace amma ai ba yau ko gobe nace maki zanje ba ko ?
Idan zan tafima ai tare zamu dake ko nace a,a yaya ba zan tafi ba gaskiya yace saboda may bani na gaiyace ki ba .
Gaskiya ba zan tafi ba don suma suna son kadaicewa dakai a lokacin in nai haka kamar na shiga hakkin su ne ai.
Wana kuma wani zance kike son kawowa tare zamu tafi don akwai abinda zanyi can idan muje yaya na katse shi ya juyo yana kallona don jin abinda zan fada.
Suma fa suna da hakki a kanka kasani don haka ne ba zanje ba don kada matarka ta zargeni da hana mata mijin ta ya basu kulawa.
Sannan kuma ka sani ita merry na kulla bata son kusancina da yarta don wani nata fahintar don haka ina rokon ka da ka barni nan Allah ya kaika lafiya.
Ido ya tsura min da nake magana azuciyar shi yana fadin yarinya saikace wata babba da iya jera kalamai haka.
Mikewa yayi yana fadin tunda nasaki abu har kin kai ki fara min mussu akai shike nan.
Yaya ba hakana bane gani dai nayi zan takura masu iyalin kane fa suna bukatan kulawan ka a yanzu.
Fita yayi daga dakin batare daya furta min wani abu ba ajiyan zuciya na sauke ina mai ci gaba da tunane a raina.
Na sani zuwana tare dashi zai iya haifar da wani fitinan a tsakani shi da merry duk da dai merry bata san akwai aure a tsakani na dashi ba amma tana zargina don bata boye min ba a ranan da mukai masu ziyara asibiti shine gani na karshe da ita harzuwa yanzu din bamu kara haduwa da ita ba.
Don a cikin fadsn su ranan merry ke fadin ta fahinci tu zuwa na kasan abubuwa suka canza a tsakanin su koda nake yarinya ai ya kamata in fahinci mai maganan take nufi dani.
Tun ina tunane har barci ya daukeni dama ga gajiya a jikina nan na samu na sauke gajiyana sai azahar na falka don alarm din dake kuka a dakin.
Har nayi sallah na idar na dan kara gyara jikina na sauko kasa banji duriyan yaya a gidan ba ashe ya fitane lokacin ina barci ya tafi gidan shi.
Don yana yawan zagayawa gidan ya duba ya bata lokaci a gidan yana gudanar da wasu aiyukan shi ban taba zaton ma yana zuwa office ba sai ranan da naji suna waya da wani abokin shi.
Tafiyan yaya America yasa na fahinci iri shakuwa da mukayi dashi a yanzu don sai naji gidan ya koma min ba dadi gabaki daya ko saukowa banson yi kasa .
Don ba karamin koyamin shakuwa dashi yayi a dan kwanakin da muke zaman gidan dole na kariya daga sanyi shi kuma yana more auren shi.
Merry tayi mamaki kwarai a yadda ta ganshi ya murje yayi kyau sosai ba wani alaman damuwan rashi a kusa dashi daya nuna hakan.
Abin ya dade yana bata mamaki a ranta inda ta fara zargin shi ko ya fara neman matane da har ya iya shareta haka na tsawon watani.
Taso fahintar wani abu tare dashi na yadda ya nuna mata in har zata kawo mai rigima ne zai iya komawa abinshi inda ya fito baizo don ta ba don yarsu yazo.
Wanan kalamin nasa ya dagawa merry hankali saidai bata yarda ta nuna mashi a fili ba ta barwa ranta abinda ta shirya yi kawai.
Ta samu ta lalabashi do itama tayi missing din shi sosai karfin hali kawai take da rashin su har lokacin dai rikici akidar yarsu yananan a tsakanin don yama samu yar ta kara juyewa ga baki daya irin abubuwan daya tanayi din.
Tun lokacin da ya isa kasan ya kirani don yaji lafiyata nace dashi ina nan kalau sai dai gidan babu dadi da baya nan.
Dan murmushi naji yayi yana fadi gidan ne babu dadi yanzu ke da kikan matsu na baki gidan ki a da can baya.
Nace ni ai ban taba fadin hakan ba ko lokacin yace zarah na amsa da naam yace in tambaye ki mana ina jinka ai yace in nace maki a yanzu sona kika farayi zaki yarda ?
Nace nidai ban sani ba naji yayi murmushi kadan yace ki yarda da maganata zarah kin fara sona ne har kike ganin gidan idan bani ba dadi a yanzu.
Nace ni dai ban sani ba ban ma san wani abu so bacen a rayuwats yayi murmushi tare da fadin zaki sani a sannu may so yake nufi.
Nace ban damu da in sani ba a yanzu tunda ban san yadda akeyin shi ba yace kin sanshi ai ko yanzu ada kin taba sanin aure yafi komai dadi a rayuwan bawa ?
Yaya zanyi in san haka yaya bayan ban taba aure ba sai yanzu to ki sani aure yafi komai muhinmaci a rayuwa bawa.
Kinsan may yasa nace hakan nace sai kafada min yaya wata kila in fahince ka yanzu.
Aure shine cikar kamalan mutum , aure shike haifarda fari ciki da natsuwa a ga uwa uba riban da aure ke haifarwa ta samun zuria,a ma,ana magada.
Zarah zanso ace kin cika mun gida da yaya kyawawa kamar ki idan haka ya kasance zanfi kowa alfahari da hakan .
Zarah a yau dana zo naga queen a cikin wani yanayi na akidar ahalul kitabi na yi bakin ciki da nadaman samuwar ta ta tsatson merry.
Da sauri na ce yaya kabar fadin haka addua bai bar komai a rayuwa wata kila har uwar ts gane hanyar gaskiya nan gaba.
Ba alaman hakan ga merry zarah merry iyayyen ta ba zasu barta ta musulunta ba da farko na dauka za iya juyar da merry zuwa akidana.
Sai daga baya na fahinci wani abu duk inda tasa kafa iyayyen ta ba biye da ita dkn kada ta sauya ba tare da sanin ta ba.
Tau sayi yaya ya bani da yake wanan maganan nayi tunane yaje ya samu wani abin bacin raine a gamay dasu a can tunda har ya zaunar dani yana min wanan magana haka lalai damuwar sa takai inda takai masa din sai ina ganin ban isa ba ban kaiba kuma.
Zarah yau idan daddy yaji wanan magana da wani ido zan kalle su yau nine na samar da yar dake bin mutanen littafi a rayuwan ta.
Kawu ba zai zarge kaba yaya yasan komai mukaddarine ga bawa don haka kabar wanan tunanen shiru naji yayi kafin muyi sallama ya kashe wayan.
A hankali na kai kwance daga inda nake ina tunanen magsnan mu da yaya ta yanzu yau nice da matsayin da har yaya zaiyi sharing din matsalan shi dani

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button