NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Kuyi hakkuri da wanan banda lafiya yau wallahi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:25 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM SIRRATAL LAZINA AN,ANTAALAIHIM, , , , , ,

Kewan kan naji shi na rashin yaya a gida lokacin sai na gane sabo yana da dadi ashe don abinda yai ta wahalal dani ke nan farkon zuwana kasan da ban ganin kowa na gida a tare dani.
Kaina daya damay da kaikayi yasa na shirya don kaina natafi gurin gyaran kai duk da ban son relaxer saida mai shagon ta sharwace da in saka saboda due din da kan nawa yayi sosai a lokacin.
Gyaran jiki akaimun sosai a shagon na biya na dawo gida da yamma sosai don ban fita gida da wuri ba.
Na dawo a gajiye sallah na gabatar saida na gama na dan saka wando da riga a jikina na sauko don neman abinda zanci.
Na gama ina zaune a falo wayana ya dauki kara mamu ce akan layin na dauka da sallama yau ba laifi don ta amsa min yadda ya dace don kwana biyu da suka wuce kona kirata bata wani amsa min a dadin rai.
Sayadi abinda nake fada maki ke nan yanzu ga yaron nan ya turo da kudi akai kakarki makka kinga kadan ke nan daga cikin aikin hakkuri gun mace riban shi yana fita ta inda mutum bai taba zato ba.
Mamu ban gane may kike fadi ba fa nace mata cikin zakuwa eh a jiya mijin ki ya turo min abokin shi ta hanyar bashi lamban wayana yai mi bayanin duk yadda umar din ke son abin ya kasance ba tare da kowa ya sani a gidan nan ba.
Mamu kawunane ya biya mata da sauri tace shi kadai ne mai zarahin yin hakan to wanda baki zatoba shinake nufi Umar mijin ki shiya biya mata.
Mamu kina nufin yaya umar ya biyawa manjo aikin hajji a banan nan tace kwarai kuwa sayadi abinda nake fada maki ke nan ai.
Wani ihun dadi nayi a lokacin mamu tace har yanzu kina nan da sakarcin nan naki ashe sayadi ?
Mamu dadine yai mun yawa tace bai fada maki ba ke nan nace baya ko kasan ya tafi America wurin matar shi satin biyu a can.
Tau kindai ji abin arzikin da yai maki saiki mai godiya nace cikin nuna jindadi na dajin wanan labarin mamu ba sai na barima yadawo ba zan kirashi in mai godiya.
Da kin kyauta don wanan ba karamin alheri bane gare ki shiyasa nake fada maki shi zaman aure mai karko ba komai bane ke kawo shi sai bari na bari ka tsaya iya inda mutum ya aje ka kada ki kai kanki ga harkan zaman shi da matar shi don a tare kika samay su tundai kema kina samun iya gwargwadon kulawan ki gare shi.
Nace mamu na gode ina kokarta yin abinda kike fada min a kullun kin kyata ubangiji Allah yai maku albarka nace amin cikin kunya.
Bayan mun gama wayan ne tunane yazo min wai hakan dama shine so ko kauna da nake ji ana fadi don dai nasan babu ko daya tsakanina da yaya .
Don shi da kanshi yasha fada min auren mu aure ne da akayishi a bisa kaddara ko dama zama irin hakan yakan iya rikidewa ya koma kauna.
Na gwada kiran layin yaya a lokacin saidai layin baya shiga ake fada min dole nayi hakkuri na dena neman shi har sai lokacin daya kirani kuma.
Ina shirin kwanciya sai ga kira sai dai alama ya nuna daga kasan chaina ake kirana lokacin nayi mamaki na dai dauki wayan.
Muryan yaya Umar ne naji yana fadin badai har kinyi barci ba ko don dare baiyi sosai ba yanzu na sani.
Ina dai shirin kwanciya ke nan yanzu yace to ya kike na sauke ajiyan zuciya nace lafiya kalau yaya ya queen da mamanta.
Suna lafiya na barsu tun satin daya wuce ina kasan china yanzu mamakin jin haka yasa nace Chaina kuma yace eh ba kince ba zaki tafi ba.
Ba haka bane yaya kaima kasan yin hankan kamar izzigiline a gareni ai ya isa yace min tare da fadin idan banyi hankali ba nan gaba sai kice zaki koya min komai akan addinina.
Ni na isa ince zan koyar dakai abinda ka riga ka sani yaya ayi hakkuri idan rashin zuwana ya bata makarai ne.
Dan murmushi yayi tare da fadin kin wanke kanki yanzu ki kwanta ki huta sosai ki kula da kanki nace insha Allahu yaya zanyi magana akan abinda yaiwa manjo naji ya kashe wayan shi.
Wayan nabi da kallo na girgiza kaina tare da fadin shidai yaya bai mai da tafiya wani abu a rayuwan shi yau kaji yana nan gobe kaji yace can yake.
Tunane na yakai kan merry nace har ya gama da iyalan shi ke nan daya bulla wani kasan wani zama har yayi dasu a dan kwanakin daya tafi da har yai tafiya daga can.
Koma dai mainene ai sunfi kusa don sun saba da hakan kila tashi nayi na kashe komai na falon na nufi dakina.
Alwala na dauro nayi shafa,i da wuturri na dade a wurin zaune ina addu,a kafin in mike zuwa saman gadona.
Washe gari bayan na idar da sallah na koma saman godo don sanyi yayi yawa sai idan rana ya dan fito nayi aiyukan na gida.
Barci mai dadi ya daukeni lokacin ina tsaka da barciname karan bell din gida ya damay ni da ruri don har dakuna zuwa ko ina akai waring din shi.
A firgice na falka inda nake kwance ina wani irin mumanan mafalki da salma jin karan ya kara firgitar dani.
Duban lokaci nayi shida da wani abu na safe lokacin karan naji yayi yawa na daure na mike da sauri zuwa kasa ban bude ba saida na dan lekka dan kafan kofan.
Ya Umar na gani tsaye yana duban agogon hannun shi wata kila lokacin dana bata ban bude ba yake kallo.
Saye yake da wando da rigan jeans sai hulan da ya tare fuskan shi dashi da alama sanyi ya damay shi a lokacin don yadda yake takure kanshi a wajen da yake tsaye.
Da sauri na bude kofan mamaki karara a fuskana yana jin na bude kofan ya murza hannayen shi guri daya ya shafi fuskan shi sai kuma ya ware hannayen nasa.
A daidai lokacin da nake fadi sannu da zuwa yaya yadda ya ware hannayen nasa nasan nufin sa aladole dai sai yaya ya koya min rashin kunya gaban shi.
Nadan rausaya kai na fada kamar yadda ya bukata in mai ya mayar da hannayen ya rufe dani a tsakiya yana fadin I am home dear.
Dan sunar da kaina nayi saman kafadan shi ina fadin you’re wellcome yaya cikin jin kunyan shi dan dagoni yayi yana ja min hanci kadan na kara sune kawaina saman kirjin shi.
Can na dago nace yaya mun fayi waya dakai jiya baka fada min kana tafe ba ai.
Ina son in baki mamakine ya fada a lokacin da yake sakeni ya juya wurin kwalayen dake aje a kofa ya fara sukkutan su yana dauka.
Da sauri nace a a yaya ka baru ni zan kwashe kaida ka dawo yanzu yace no is my duty yin hakan ko baki sani bane.
Duk da ya hannani saida na dauko wasu daga ciki na shiga dasu nakai inda ya aje wanda ya fara daukowan.
Baki jin magana yace min nayi sauri fadin gaskiya ba zan iya kallo kana daukan kaya ba ina zaune ni .
Zaki saba da hakan ai kwana nawa yarage keda kanki zaki bari din ya fada yana ficewa.
Ban tsaya ba sama na hau na bude dakin shi yana a gyare tsab don koda bai gari ina gyarawa tun farko.
Ruwan wanka na hada na aje mai komai da zai bukata a wurin ina fitowa daga bayin lokacin ya shigo dakin.
Barin hada muna break fast da sauri nace ina fita daga dakin kina nan kina barci baki batun abinda zakici ba ko ?
Haka kike zama da yunwa idan bana nan ashe nace ban zama da yunwa don ni ban wasa da abinci kamar yadda kake fadan ban son cin abinci kullun.
Ganin yana shirin tube tufafin shi a gabana cikin ko in kula da ina wurin wai nayi saurin kawar da kaina na fita.
Dan murmushi ya sake kadan tare da fadin silly girl da sannu zan fitar maki da wanan kunyan tsiya haka.
Kitchen na nufa cookerorth na hada muna don shi yafi min sauri a lokacin naga kuma yana son sha ko wani lokaci don wani bai kare ba yake sayo wani tun ban iya sha ba har nazo na iya sha daga baya.
Don ko a gida haka kawu yana son shi sosai ana yawan dama mashi shi lokaci lokaci ban iya sha sosao idan mamu ta zuba min har tazo tabar zubawa.
Ina aiki ina tunane shidai yaya ya zama mai irin dabi,un turawa koda yaushe akidan shi na daban ne motsin shi naji a bayana a inda nake duke .
Kafin in dago ya karaso gareni ya rikeni ta baya ya matse da jikin shi ajiyan zuciya muka sauke a tare kusan lokaci guda.
Juyo dani yayi a hankali muna fuskantan juna dani dashi yace may kika girka muna hakane shape shape.
Dan murmushi nayi nace abinda naga kana yawan sha da safe na hada ma don kada in bata lokaci.
Bude bowl din yayi yace ke a wanan yanayin da nake zaki kara dura min madara in sha kuma ?
I hope zaki iya daukan lalurana yau ba raki don idan kika bani wanan ehe yarinya zaki dandana kudan ki gidan nan yau.
Sam ban gane abinda yake nufi ba da zancen shi nayi saurin fadi yanzu ka daina shan shine kuma ?
Ina sha ya fada a lokacin da yake rabuwa da jikina yana zama yace indai kin shirya mun ai shike nan ko ?
Ban bashi amsa ba don har lokacin ba fahintar shi nayi ba wanka nayi na fito kwalliya nayi sosai don farauta mashi rai saboda ina son yi mai godiya kan abinda yaiwa kakata.
Ido ya kura min tun shigowan shi yake mamakin sauyawana goshina ya haskaka min fuskana nayi wani irin kyau dani don gyaran da nayi jiyan.
Wanan gyaran kan ya matukar karbe ki zarah yaushe kikayi shine na amsa da nagode sannan nace mai jiya ina zama naci gaba da fadin kan ya damay ni da kaikayi shine na tafi aka wanke min.
Sai an kwana biyu akwai wata yar ghana zanje tayi min kitso a bayan layin nan suke ita da mijin ta.
Gyaran ya karbe ki matuka daga haka bai kara fadan komai ba don na samu ya gama karyawa ko lokacin.
Ai gyara shine mace don komai tsabtan ka Amma na fadin idan baki gyara kai kin ragu dan murmushi yayi tare da fadin wanan ai komai kina ji a bakinta ita.
Sai lokacin na dan dawo kusa dashi na zauna na fasa nufar wurin karyawan da zani da farko ban kuma iya magana ba sai na dan zamo kasa na rusunna tare da fadin yaya Allah ya kara yawan arziki mai amfani yasa albarka jiya mamu ta kirani tana fada min abin arzikin da kaimuna na kakata.
Kallo na yayi da mamaki kafin yace may yasa ta fada maki nace ban son kowa ya sani don gudun fitina a gida nayi saurin fadin itama ta kwabeni da hakan fun farko fada min tayi in maka godiya kada a barni a duhu.
Kama kafadana yayi yana tayar dani kafin yace ba irin wanan godiya nike so ba yanzu a gurin ki kije ki karya sai ki dawo ki ban goron albishir din.
Na kallo shi da mamaki ina fadin goro kuma yaya a ina ni zan samu goro a wanan kasar kuma naga kai ba gwanin cin goro bane ai.
Baki san inda zaki samu goro ki ban ba ga abu ajikin ki aini gorona ba wani abu bane illa jikin ki zan mulka .
Kunyar maganan shi naji nayi saurin mikewa tsaye zan bar gurin naji ya riko min hannu daya yana fadin ba wasa nake na zarah nayi missing din ki .
Kunya naji sosai da abinda yake fadi lokacin ya dan lumshe ido yana fadin jeki karya ki dawo nan na wuce a sabule dakyat nake iya daga kafana zuwa dinning din na zauna.
Tunda na zauna ban juyo inda yake ba har na gama saida na gama na dan saci kallon shi kadan hankalin shi baya gurina yana kan wayan shi haka yasa naso gudu in koma dakina ba tare da ya farga da hakan ba cak naji ya rikoni ya dagani sai dakin shi ya dire ni saman gadi bai tsaya jiran komai abubuwa suka faru a tsakanin mu.
Ba zance ban wahala ba ranan a gaskiya naji jiki sosai wurin yaya umar don kanshi ya kyaleni yana fadin bari in barki kada anjima in tabaki kice baki san haka ba.
Na samu naja kafana da kyat zuwa dakina na gyara jikina sauko ba tare dana huta ba na nufi kitchen hada muna abincin rana.
Sai dai sanu a hankali nake jin marana yana dan murda min a hankali sai na dangata hakan da saduwan da ya gama danine da safe yajawo min ciwon maran lokacin.
Saidai ina kewaya na sami period ne yazo min a lokacin na tuna dama zan fara expecting din zuwan shi yau da gobe ko a cikin daren yau ya zo min.
Sallah da aka hutar dani ke nan banyi ba na kintsa na haye gado koda ya fito ya duba falo har kitchen ban nan ya koma dakina ya samu ina barci yasan ya wahal dani yau sosai anjima kuma yana da bukatana ya barni in huta.
Ban falkaba sai karfe hudu koshi yunwa ya tayar dani don naji cikina a lokacin kamar ban karya da safe ba.
Koda na fito bai gida ya fita a lokacin zama nayi nayi naci abinci sosai kamar mayunwaci na kora da ruwa don ni abin zaki bai damay ni ba gasu nan kala kala a gidan ban damu dashiba sai wani lokaci nakan sha idan ya biyo min a rai nakan sha.
Bai dawo gifan ba sai cikin dare sosai koda ya dawo ina dakina ina karatu ya shigo yana fadin sorry na fita kina barci dazun kada in tayar dake in lalata maki barcin ki.
Na tashi ban ganka ba nasan ka fitane baka gidan kinci abincin ya tambaye a lokacin daya juya yana balle maballan riganshi.
Naci tun dazun danaga baka dawo ba da fatan banyi laifin yin hakan ba ina baki laifi ba kinma kyauta min dayin hakan kinsan mijin ki jarumine sosai a cikin mazaje.
Dariyana na kumshi don na fara fahintar maganan shi zuwa yanzu da yake mun a dunkule.
Wanka yayi ya sauka ya ci abincin ya dan jima lokacin na soma barci ya dawo dakin a hankali yakai hannun shi saman wuyana ya dan shafa.
Tare da kiran sunana a hankali kamar akwai wani a gidan da baison ya jishi lokacin da yake tayar dani din.
A hankali na bude idana na sauke a kanshi yana tsaye yace yau a nan kike bukatan mu kwanane zarah.
Dan fuska na yamutse kafin ince maratane ke min ciwo na kwata ashe barci ya daukeni ban sani ba.
Da sauri naji yace maine ? na kara maimaitamai abinda nace sai naka ya kai zaune yana sauke numfashi.
Can kuma ya juyo gareni yana fadin amma ai bai zubaba tukun ko nace tun da rana yazo min shiru naga yayi bai iya cewa komai ya mike yabar dakin na bishi da kallo.
Dan tabe baki nayi tare da fadin Allah ya rufa min asiri yau wai mutum kamar ba wurin matarshi ya fito ba yake wannan rawan kafa haka ?
Dama wai wanan abin ake nufi da aure namiji ko yaushe yana manne dakai yana jagula baiko isar shi.
Ban kara jin duriya shi ba bankuma je dakin nasa ranan dakina na kwana don sanin halin yadda period ke mun indan yazo zan dinga kewaya ga ciwon mara dake hanani barci da dadi da dare.
Washegari ina hada abin karyawa ya fito daga kofa ya tsaya yana fadin kada ki girka abinci dani fita zanyi.
Naji mamakin abinda yace din baima tsaya na fadi komai ba ya kama hanya yana kallin agogon hannun shi yadan yi tako biyu ya juyo yana fadin .
Ko akwai abinda kike sone ba komai na bashi amsa ina mayar da kaina ga abinda nakeyi.
Allah yasa ban zuba komai ba ruwa kawai na dora a wuta.
Rage gudun gas din nayi na juye ruwan tea kawai nasha a wurin wani tunane yazo min a raina.
Wai ko yaya yana cikin mazajen da suke kyamar matar su ne a lokacin da suke period din su su kama gudun su.
In dai hakane zan mayar da hankalina in kula da wanan hasashen nawa inko haka yake akwai matsala babba ke nan a tsakanin mu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button