NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:25 – ????????????: BISSIMILAHI RAHAMIN RAHIM GAIRUL, MAGDUBBI ALAIHIM WAL DAALIIN, , , ,

Kamar yadda na saba kwana kin period dina har na gama yaya bai wani zauna a gidaba lokacin zuciya mai nashe nashe sai ta nasa mun ai kyamar jinin al,ada da nake yakeyi.
Wanan abu sai ya tunzurani ni kadai nake fada da kaina ina fadin ai Allah ya hallito mu da abinmu hakana idan ko hakan ne koda jinin ya dauke zai sha mamaki na sosai.
Dukda awanan lokacin na gujewa kwana dakin shi don kada inyi mistake yaji karni ko wani abu maka mancin hakan nasan komai na iya faruwa.
Amma bai hanashi wani lokaci ya shigo dakina ya dan zauna don har zaman falon a lokacin na gujewa hakan ko da yaushe ina dakina ina karatu.
Idan ya tambayeni nakan yi karya da marata ke yawan ciwo yasa ban dogon motsi a gidan ina zaune guri daya.
Duk da nasan wanan karon na samu sasauci sosai na ciwon maran da nakanyi idan ina period don sai wani lokaci yakan dan murda min kadan ya bari kuma.

KANO NAGERIA , , , ,

Duk da sanyin su ba nan bane saidai ko a can ana tsula sanyi gwargwadon yadda Allah ya tanadar wa kashen Africa dashi.
In zaki tuna na fada maki kawu baya fita sosai a irin wanan lokacin yafi zama a gida cikin iyalin shi balle yanzu da jikin nasa sai a hankali jefi jefi yakan leka kasuwa don ya dan motsa jkin sa da yai mai nauyi.
Yau hjy jummai zata fita girki mamu ta karba don girkin gidan a daidai yake tafiya basu hautsana shi ba don dokan hjy jummai ce hakan ko tafiya kayi ka dawo dole sai ka jira idan girka ya zagayo ka karba wanan dokane daga gare ta babu mai tayar dashi kuma a gidan.
Abu ga wanda tsufa ya fara hara a kaidan su karfe shidda ne fita gitkin mai girki a ranan sai dai zuwa biyar zaka iya zuwa kayi aikin daya dace a shiyan maigida kada yamma yayi ba,ayi ba.
Mamu ta dauki abin shara ta nufi sashen nasa a waje ta samay shi zaune yana shan iska duk da sanyi ya fara saukowa a lokacin kowa na haraman natsa kansa guri daya.
Gaida kawu tayi kamar yadda sukanyi idan yana gidan ta wuce zata shiga sashen nasa yace da ita.
Maimuna da zan samu ruwan dumi in jefa kafafuwana a ciki da zan so hakan yanzu dan jimm tayi kafin tace ko a dauko maka waya kakira hjy ta baka don ban son abin fitina ko kadan da saura lokacina yayi ka sani.
Da mamaki ya kalleta yace ruwan ma shi zai zama abin wani kishi a gare ku yanzu ?
Kamar tayi magana sai ta wuce zuwa ciki ta tara ruwan zafi a roban da suka tanadar mai don yin hakan.
Tana kawo mai yayi godiya wanan yana daga cikin dabian kawu godiya bai bata lokaci ba ya saka kafan nasa kamar yadda yake so don yana jin dadin hakan wani lokaci.
Tun data tunkaro wurin idon ta ya sauka akan roban gasa kafan dake gaban shi lokaci daya kishi ya ziyarci zuciyar ta.
Ta karaso a fusace tana fadin ya naga haka kuma waya rigani zuwa karasa min aikina ?
Kawu da idanun shi suke a lumshe saboda dadin ruwan da yake ji a lokacin kallon ta kawai yake don ya hango masifa a fuskanta lokacin.
Alh tambaya nake waya baka ruwan saurin da nakeyi ke nan yanzu nasan zaka bukaci ruwan a wanan lokaci.
Jummai zan zaunane ina jiran sai lokacin da kika fito ki bani ruwan mai yasa ke baki da tausayine a rayuwan ki ko kadan bani ruwan ma yanzu laifine a gurin ki ?
Amma kasan dai hakkinane yin hakan a wanan lokaci ko ?
Dama abinda take son hadawa ke nan mugun iri marasa asali gaba da baya masu abin kunya tatare a duwawon su.
Wai har wanan masu kashin tsiyan don son kai zaka dauko yar ta ka jefa a cikin iyalina don su bata min zuri,a da kashin tsiya irin tasu dasuka gada.
Wanan ba wani kike zagiba ni kakazo ki zaga dama, idan har wani yana da kashin tsiya a gidan nan to kece gaban masu shi arkin da kike kurin yaran ki nadashi nakine Jummai ?
Da bazarwa sukakai hakan da kike yanga wa mutane maimuna dai da kike zagi ina jininane idan kuma tana da kashin tsiya nima ina dashi ke nan don abu daya ya fitar damu duniya.
Ke har kina da bakin magana sananin kankine bantaba rike arzikin dana rike ba a lokacin auren maimuna a duniyan nan.
Wanan magana daya fada a karshe shiya harzuka zuciyar hjy ga baki daya tace may kake nufi da wanan magana yace kema kin sani ai.
Da can da kika matsamin in kai yaran ki waje ba durkushewa nayi kasa ba ga baki daya sai kama kama muke a gidan nan dan shago gudan dake gareni yana neman subuce muna.
Alh ya isheka haka kai bakaji kunyar fadan wanan maganan ba yanzu wanan hayaniyar da suka soma ya jawo hankalin yan gidan a baki dayan su suka fito.
A daidai lokacin da hjy ke fadi banda arziki ka dauki yar agolan ka ka jefa a zuria ta don kada ta wullakanta .
Kai amma jimmai zuciyar ki na kafiraine Amma ke fadi daga nayan ta wace tsofa ya tasata gaba yanzu tace mutumi na cikin wanan irin halin amma ke kishin ki bai barki kun zauna lafiya ba.
Hajiya fitina ya kawo dama ki duba yanzu karfe nawa tasan ina nan batazo ta ban ruwan dumin nan ba sai lokacin data kwatanci yar uwarta tazo ta ban tazo tana fitina sakarai wace bata kama girman ta ko yaushe.
Amma ita maman fauziya may ya kaita baka ruwan bayan tasan ba haka mukeyi ba inji hjy maryam ta fadi haka .
Wai sai a barshi a zaune da lalura yana jiran sai lokacin dataga dama tazo ta bashi bayan tasan ka,idan yadda kukeyi.
Kai ku rika maganan gaskiya don Allah ai kishi ba hauka bane don ma antaimake ta dama ke bugi sa bugi taikine aikinki a gidan ba fadan gaskiya kikeyi ba sai son kai don a yabe ki.
Hadiye kada ki fada min magana a nan don kawai na fadi gaskiya ai da gangan tai hakan don tasan yana cikin ka,idar mu yin hakan.
A daidai lokacin mamu ta bude kofa ta fito daga dakin dauke da tsitsiya a hannun ta maganan hjy maryam yakai kunnen ta.
Kallon kawu tayi tace na fadama wanan abin zai iya jawo matsala gashi ko ya jawo din.
Kai ni wanan abu ya isheni wallahi yau dai ku sheda na dakatar da jimmai da maryam girki a gidan nan abar mutum daya yai jinya ta har lokacin da Allah yaban lafiya.
Ina wuta su sakashi a lokacin har mamun fada take ita bata yarda ba a lokacin saresarin a sakata gaba da wani kullin ya fadi a tsawace yana mikewa tsaye wanan dokanane haka kuma na yanke a raina da kyat yabi bango zuwa ciki cike da bacin rai a tare dashi.
Amma ce tabi kawu ciki ita da mama hadiye mama hadiye na fadin hakanma yafi wallahi mutum a cikin lalura za a ce sai lokacin da akaga dama za a kula dashi wanan wani rashin imanine haka don Allah.
Wanan abin zaijawa maimuna bakin jini a gurin su kuma shi nake son ku kula maimuna mutum ce mai ruwan ciki sosai.
Hajiya don Allah ku barni dasu idan ba ta baya na fito masu ba nagane so suke su karasani da raina.
Tau gidan kane iyalin kane abindaka yanke daidaine amma a sasauta don Allah Amma ta fada tana fita daga dakin.
Ranan kan zagin tonon asiri da gori mun shashi sosai ga bangaren biyu kowa ya koma sashen shi zuciyar shi cike da bacin rai abinda ya faru.
Hjy maryam da tayi waya tana shedawa yar uwarta abinda ya faru sai yar uwan nata tace daidai ke nan yayi min daidai tunda ana rabaki da shiga sharo ba shanu kinki dainawa ta kashe wayan kawai ta barta dashi a hannu.
Ita gaiyyan aikin yaranta ta shiga kira tana labarta masu saidai tayi neman layin umar ta sheda mai halin da ake ciki saidai bata samu layin shi ba ya manta tunda ya dawo ya canza layi saboda busy da yai mai yawa.
Amma ce tayi wa mamu magana don da ta bijire akan ba zatayi ba saida daddy yakai karanta ta yarda akan zatayi din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button