SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL
SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Mun kashi rikici sosai da yaya da farko bai gane abinda nake nufi ba sai daga baya ya fahinci manufata din.
Kai ya girgiza tare da fadin baki da wayau yarinya karamace ke shiya har kikai tunanen hakan.
Banji kyamar merry da idan ta gama ba wankan tsariki takeyi ba sai ke da nasan kina wanka kina kula dashi yadda addini ya tsara zan kyamata ?
Ni lokaci ne banda shi kawai na zama gida saboda course din da mukayo a chaina muke gabatarwa a nan don karuwan na baya mu shiyasa nake kai wani lokaci a waje hakan.
Kunya ya rufeni gabadaya don yana fadi ya bar dakin ya tafi dakin shi abinshi.
Yanzu mai nayi haka na tambayi kaina waini nasan dadin namiji a kusa dani ko may ke nan nayi din.
Tunane nayi sai kawai na danna layin anty Farida a cikin daren nan na kirata kaf na kwashe abinda ya faru na fada mata tare da tambayanta abinda zanyi ?
Tace tawa kice min komai yai daidaita ke nan yanzu tsakanin ku har kin fara kishin mijin ki kuma.
Ba haka bane anty saukowan shi gareni da kuma matsin mahaifiyata daku yasa na yarda makaman yakina dariya ta tuntsure dashi tana fadin yanzu dai ki tashi ki shirya ki samu mijin ki a daki ki san kinyi gyaran da ba zai iya kawar da idon shi a kanki ba.
Godiya nayi mata bayan ta gama min bayanin komai na mike sai bandaki banda wani abin da ta lissafa min inyi don haka na dan zauna a ruwan zafi ina zaune ba a dauki wani lokaci ba naji na kara hadewa kamar ba wanda ya taba shigana.
Na zauna nayi komai kamar yadda ta umurce ni in yi manyatacen rigar baci na saka daga cikin wanda ya dawo min dashi da farko har ina zagin rigar dana dagashi naga harahara din shi yayi yawa sosai.
Zaune na samay shi a dakin shi ya harde kafa kamar mai tunane a lokacin sallamana yasa ya juyo ya kalleni.
Bai iya kawar da fuskan shi gareni ba har na karoso inda yake a hankali na tatare rigan cikin sallo na hauwo gadon jikin shi na dan fada ina fadin yaya har yanzu bakai barci ba ashe ?
Dan ajiyan zuciya ya sauke kafin ya kai hannin shi ya rungumoni da kyau yana fadin mamaki maganan ki nakeyi zarah kayi hakkuri nace ina kai kaina saman kafadan shi na kwanta da kyau.
Wani iska ya furzo daga bakin shi duk cikin sauke ajiyan zuciya ne hakan yace ban san yaya zan maki bayani ki gamsu dani ba.
Hakkuri na sake bashi na hana bayanin da yake son min din a lokacin ta hanyan hura iska a hankali zuwa cikin kunnuwan shi wanan abinda nayi ya jagula muna lissafin komai.
Sai da komai ya lafa a tsakanin mu na yunkura da niyar shiga bandaki da sauri naji ya rikeni sai da gaba ya sake faduwa a zatona wani abin zai sake min da wanan katon kan ihu sosai zan masa.
Amma sai naji yace dani not now ki bari sai dan anjima ka dan zaki iya kewayawa ba a wanan lokaci ba dan kallon shi nayi sai naga ya kawar da fuskan shi kamar bashi yai magana yanzu ba.
Kewayan da banyi ba ke nan sai a cikin dare na falka na samu yayi wanka ya gama sallah yana zaune yana karatu.
Nima wanka nayi daga gurin kewayawan na fito sai dai da yake ban zo da shirin sallah ba don haka na sake kwantawa da alwala a jikina kawai.
Sai asuba ya tayar dani sallah dakina nanufa na sake wanka tare da dauro alwala na fito na dade zaune ban daga ba ina addu,oi wani barci mai dadi ya dinga fisgana daga inda nake zaune dan kwance nakai a kasa gurin da nake zaune.
Shikuma samun kanshi da yayi da rage aiyukan dake gabanshi ya tuno wayan shi akashe yake duk wanan lokacin ya mayar da sim din nashi ya kunna waya.
Ya Umar zaman turaine kawai amma bai yarda ya yarda addinin shi da al,adun malam bahaushe ba don idan ya tashi ya tashi kenan sai kuma wani daren zai zauna bayan ya gama addua ya duba sakoni a laptop din na mayarwa ya mayar wanda baida bukatan amsa ya barshi.
Ranan baisan ya akayi ba sai barci ya dan fisgeshi har yai mafalkin da hajiyan su ina gudu tana bina da sharbeben yuka ga yara ina ja acikin galabaita.
Innalillahi yace lokacin daya mike zaune daga ringinginen da yake kwance din yana mamakin yadda akai barci ya dauke shi da kuma tuna abinda ya gani a mafalkin nasa.
Addua yayi kafin ya mike ya shiga yai wanka ya shirya daya fito saukowa yayi sai jini gidan tsit kamar babu kowa a gidan lokacin .
Haka yasa ya gane banfitoba kamar yadda na saba fitowa inyi aikina da safe dakina ya juya ya kalla yana rufe ya nufi dakin ya tura a hankali ina kwace ina dan juye juye cikin wahala ina dan magana irin na mai mafalki takawa yayi yana kiran sunana ban amsa ba sai ya saurara da kyau yaji ina fadin salma mai nayi maki zaki kashe ni ?
Gaban shi ne ya fadi jin abinda nake fadi da sauri ya bugi filon da kaina ke sama ina kwance a kasa yadda na kwanta a wurin danayi sallah.
Mikewa nayi a wahalce na sauke idona a kanshi yana tsugene daidai saitin fuskana kamar yana min addua a lokacin.
Ki tashi yace yana mikewa tsaye kwanci a wanan lokacin baida kyau kin sani yana toshewa mutum hanyan alherin sa ne.
Dan mika nayi tare da salati ina fadin bansan nayi barci ba a nan saidaya juya yace wanan dabi,ar kine nasani ya kamata ki daina.
Ban fito daga dakin ba sai dana shirya na fito yana zaune a falo na gaida shi da kwana zan nufi kitchen naji yace ga abin karyawa nan na amso muna yana nuna min kwalin daya sayo din.
Dan jakkan kwalin na dauka na nufi danin dashi ina fitarwa a hankali pakege ne a ciki guda uku plates na dauko a kitchen na juye a ciki ina mamakin ko a ina ya sayo shi da wanan safiyan haka ?
Chip’s ne sai ganye da sauran tarkace irin abincin su na turawa na juyo ina fadin yaya ga abincin ya mike kamar dama ni yake jira in hada lokacin.
Har muka kareci ba wanda yai magana a cikin mu saidai ina kula da yadda yake tura abincin kamar yana da damuwa a ranshi lokacin.
Yana gamawa ya mike ya barni a gurin na dan dauki lokaci nima cikin damuwan ko may ya samai shi ya canza haka lokaci guda oho ?
Yana zama yaji sako ya shigo mai a waya kamar ya share sai yadai ya dauko wayan yana dubawa Aliyu ne yayo mai text.
Bros ina komai lafiya a wajenka mama tana neman layin ka bata samu akwai matsala a gida daya faru sai dai kabi hukuncin ta a sannu don Allah don ta dau zafi dayawa.
Iya abinda ya rubuta kenan ya dade yana maimaita sakon bai fahinci komai da sakon ke nufi ba iya abinda dai ya fahinta shine .
Akwai abinda ya faru a gidan wanda mahaifiyar su ke son daukan fansa a kaina kila kodai wani abin.
To ko shiyasa yayi wanan mafalkin dayayi da safe yasan dai shi ba gwwnin yin mafalki bane sosai hakan.
Idon shi a lumshe koda na fito yana tunane a ranshi rabuwa da zarah matsala ne gare shi yanzu kamar yadda mama ke nufi abin ya wuce nan yanzu.
Na nufi dayan kujeran zan zauna duk da idon shi suna rufe naji yace zo nan ki zauna yana nuna min gefen shi.
Sai lokacin ya bude idanuwan shi yana kallona na mike a hankali zuwa inda ya nuna min cikin kunya don munyi kusanci sosai da inda ya nuna min in zauna din.
Ta tako a cikin tafiyana kamar na tarwada na zauna a hankali ajiyan zuciya naji ya sauke lokacin dana zauna din hannun shi ya dora sama kafada ya dan karyo kanshi zuwa wuyana yace zarah fada min mafalkin dana samu kina yi dazun dana shiga dakin ki ?
Dagowa nayi na dan kalleshi babu wasa a fuskanshi nace mafalkine kawai dai ba kuma yau ne farkon yin shi duk na kwanta kusan kullun ina wanan mafalkin ko yaushe .
Fada min akan mainene kike mafalkin nace sai nayi shiru na kasa magana yace fada min mana ke nake saurare inji ?
Dama dama sai na kasa fadi yace umhumm dama anty salma ce dai nakan gani tana son wai kasheni.
Tun yaushe kika fara wanan mafalkin ya tambaya kunya naji na kasa magana yace kinga fada min in akwai addu,an da zakiyi sai ki dinga yi don yanayin dama samay ki dazun ya daga min hankali sosai yau.
Dama dai ba wani abu bane sherin mafalkine kawai yaya ganin ta nake wai zata kasheni sai kuma wani lokaci zata jefani a rami.
Nace tun yaushe kika fara tambayan danayi maki ke nan yanzu ai ko ?
Ya fadi yana dagowa daga kafadana tare da tsura min idanuwan shi akaina nace tun lokacin daka fara saduwa dani na karasa a hankali.
Sai naga ya koma ya kwanta a makarin kujera ya dora kanshi yana lumshe idanun shi a hankali .
Bai faye yarda da mafalki gaskiya bane amma wanan din yana da bambamci tunda shima yayi kusan irin wanda nayi din ai to mai hakan ke nufi ke nan ?
Ganin yadda ya kwanta yasa na kai kaina a jikinshi na dan mike kafafuwana ga makaran kujeran ta gefe na lushe idanuwa hannunshi naji ya dora a kaina yana wasa da gashina a hankali.
Wayan shi ne ya dauki kara ya dauka muna a hakka yadda muke da kusanci da juna din naji yace mama barka da asuba.
Jin hakan yasa na mike da sauri zanbar wurin naji ya rikeni gami da yimin alama in kwanta abina.
Barkan mu tace mai yace lafiya mama da safen nan haka kallon lokacin da yake kira safe nayi lokacin sha dayan rana yana batun yi a London.
Babawo akwai matsala a gidan nan nayi neman layinka in sanar dakai halin da muke ciki ban samu ba.
Naji yace may ke faruwane mama a gidan wai kamanni Alh zaice ya dakatar da girki a gidan nan kan wanan shedaniyar matar kaddaran da ya aura maimuna harda hjy maryam laifin ya shafeta don bai son gaskiya .
Abinda nake so dakai yanzu shine ka rubutawa yarta takarda ka turota jirgi ta dawo masu gida tasan munfi karfin ta ta ko ina don hakan kawai za kaimun ka wanke min bakin cikina.
Shiru kawai yaya yayi bai tanka ba a lokacin ita kuma mama taci gaba da aibantani da uwana ina jin ta kaf don ina saman jikin shi lokacin komai na shiga kunnena.
Can ko taji haushin shirun da yayi mata din ne bai bata amsa ba tace wai kanajina kuwa babawo ina magana kayi shiru ko kana nufin bukatana ba zai yuyu bane na sani.
Na fadama ban yarda da karatun da kace in bari ta karasa ba yanzun nake son ayita ta kare ba kare bin damo inhar ta kare karatun ai taci riba damu ke nan daga ita har uwarta din don yarta ta samu madogara ta dalilin mu don haka ina duban hanyar ta zuwa jibi ta kashe wayan don baida niyar bata amsa a lokacin.
Yana jin ta kashe wayan ta naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin mamake nan laifin wani ya taba shafuwan wani ne ashe ?.
Ya dago daga yadda yake kushingide ya zauna da kyau nima mikewa nayi zaune gaba daya yanayina ya canza ga baki daya lokacin.
Sai addua nakeyi a bakina don abin ya firgitani sosai Allah kadai yasan tsawon lokacin da hjy ke binshi akan ya sakoni don maganan ta ya nuna ba yau bane farko.