NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:26 – ????????????: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA HAIYYU YA KAIYUMM, , , ,

GA MASU BUKATAN LAYIN KIRA ZAKU IYA KIRAN 08036959257 KO 09026931792 .
DON TURA KUDI SAYA ZAKI IYA TURAWA TA WANAN ACCOUNT DIN KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN KIRA NA DARI UKKU KACAL NAGODE

Bayan watanni sun shude sun bada baya abubuwa sun faru dama a wanan lokacin ciki harda rikici sosai da merry da yaya umar sukayi akan yar shi har wurin hukuma.
Inda hukuma taba uwar daman rike yarta akan addinin ta har zuwa lokacin da yar zata kai shekara sha bakwai ko takwas a lokacin tana da daman zaban addinin da take so a rayuwan ta.
Wanan matsalan shi ya kara ja baya da alakan su sosai suna haduwa don yarsu saidai ba kamar baya ba da ko yaushe suna like da junan su cikin so da kulawan juna irin na family din dake cikin farin ciki a rayuwan su.
Ga Allah yasawa yar son mahaifin ta a ranta ita zata matsa sai uwar ta kira mata uban sunyi waya ko ta tursasa mai yazo tana son ganin shi.
Zuwan bai haifar da wani jin dadin rayuwa a gare su don a karshe zasu kare da fadane don uwar bata taba yarda ya ya koyar da yar wani abinda ya shafi addinin shi can.
Wanan kan hada su fada sosai har yai fushi ya bar masu gidan ganin ya matsa akan sai yar ta koyi addinin shine yasa yanzu ma ta daina zuwa birnin London din sosai.
A rayuwa irin nasu na turawa nacan hakan da farko bai wani damay ta ba don tasan zai gama fushin shi na dan lokaci ne ya dawo gare su don baida wata ya da yake gani a duniya bayan faith din ta.
Da wanan tunane ta watsar da zancen shi tana jiran dawowan shi gare su a duk lokacin daya kare fushin shi dasu din .
Don iyayyen merry din suna tsaye sosai a kan yarsu don sun tabbatar da basu taba yarda ya ja ra,ayin ta zuwa wani addini haka yasa ko yaushe suna manne da yarsu don kada kewan hakan yaja ra,ayin ta ga mijin ta.

Yau Friday bamu dadewa a school kamar sauran ranaku wasu na tasowa da goma wasu zuwa sha biyu a ranan jumma,a din ina cikin wa yanda suka bar school din tun goma da wani abu na safe.
A gajiye na dawo ina cikin shigana na musulunci da ban yarda in yarda shi ko kadan don ganin irin rayuwan wasu a can .
Duk da makaranta yawanci duk diyan musulmai ne a cikin shi amma muna dan gauraye da wasu addini masu daukan karatu din haka bai hana rayuwan wayewa sosai ga wasu daliban.
Wanan bai taba darsuwa a zuciyana ba nidai abinda ya kaini nake yi kawai gashi yanzu nayi nisa sosai ga karatuna saura kiris mu karasa ba wani matsala irin ta kasata da muke samu indai zaka tsaya kai abinda kaje nema a wurin.
Tsakanina da yaya yanzu sai abinda ya karu a tsakanin mu na bangaren kula da junan mu a cikin aminci da yarda da juna.
Ban taba yarda nayi wanin abinda ya haneni yin shi ba zancen yarshi da matar shi kuma ban sa kaina a cikin zancen su ba ina zamana a inda ya ajeni ne .
Tun lokacin da sukai kotu nayi gigin fadin magana ya hayayakoni tun lokacin naje bakina a kansu tare da kawar da idona ga matsalan su mai daki shiya san idan ruwa ke masa yoyo.
Na sauka taxi don nauyin cikin dake jikina da yai min yawa yanzu ban iya tafiya mai nisa sosai hakan yasa nake hawa taxi zuwa da dawo daga makarantan.
Yana zaune don daren jiya ya dawo daga dubai tsaraba kan na sha su lokacin har irin kayan mu na yan Nigeria na samu a wanan tafiyan.
Yace yana son in rika amfani dasu don kada amma tace ya juya matani da wani akida ko kawuna.
Yau ma daya daga ciki na dauka na sa don yasan na yaba da kyautan haka nakan yi daya sayo min abu zan saka don ko gobe ya koma wani kasan kara kwaso min kayan su zaiyi irin da matan kasan musulmai ke amfani dashi.
Shiyasa zaka ganni da shigar mutanen kasa kasa don mijin daya kasance mai yawan shiga kasashen duniya ko yaushe.
Ina bude kofa ya dago ya kalleni tare da kallin lokaci yace may yasa baki kirani in daukoki ba kika dawo da kanki.
Kina son ku wahala ne zarah na rabaki da wanan tafiyan haka nidai ina cire takalman kafana don haka muke bamu manta da addinin mu da al,adan mu ba koda muke can sai daga bayan zan dawo in goge takalman in shiga dasu gurin da muke aje takalman mu.
Nufoshi nayi na zauna da kyat ta yadda jikin mu yake iya gugan na junan mu a lokacin ina sauke a jiyan zuciya.
Dan rugumoni yayi yakai min pick saman goshina yana fadin bakijin magana zarah ban san may yasa kike wanan tafiya ba.
Ya mike ya dauko min goran ruwan da baida sanyi gami da cup ya kawo gabana yana tsiyaya min ya miko min na gode dan uwa yace see you yana mikewa.
Duk na shanye ruwan na aje cup din a lokacin har yakai zaune shi hijjab din dake kaina nayi kokarin cirewa a hankali.
Sai lokaci nace bada kafa na tako ba yaya mota na shigo ai da kafane da yanzun ban kawo gidan nan ba ko.
Hanncina yaja yana fadin na sanki da kafiyan tsiya zarah ban san may kike son gani da kafa da kike bin hanya yiba.
Ki je ki rage wanan kayan yau fita zamuyi da yamma tare dake da sauri na dan kalleshi don nasan shi da kashin fitan dare gareni yana cikin dokan shi.
Yau kuma fita zamuyi yaya na tambaye da mamaki yace eh a kwai wani al,ada da musulman kasan nan keyi a ko wani shekara wurin wanan taro nake son mu tafi.
Allah ya kaimu na iya fada ina mamaki a raina wanan wani taro ne kuma haka mai muhinmanci da har ya yarda zamu tafi da yamma kuma ?
Ya sani gaba naci abinci a nan falon na kwanta tun muna hira dashi sama sama sai barci ya daukeni yaji shiru.
Bini bini yakan dago kai ya kalleni don shi tausayi nake bashi a ganin shi nayi kankanta da daukan ciki haka a lokacin .
Don haka ne baiko son tafiya ya kamashi zuwa wani kasa mai nisa yanzu ko a garin yake bai dadewa a waje muddin yasan cewa ina gidan ban fita ba.
Don hakane yake bani lokacin shi sosai tun abin na ban kunya har na gane haka rayuwan shi yake shi baida irin dabi,un al,adun mu na hausa fulani komai zai iya yiwa mace shi ba matsala bane gare shi hakan ya zauna sai nayi mai abu da kaina a a don in na kyale shi ina gidan zaice zai muna girki da kanshi.
Nakan zauna inyi tunanen ranan da muka koma gida Nigeria yadda rayuwan mu zata kasance a can da hjyn su.
Barci sosai na samu nayi nan kasa inda na kwanta a falon tun yana min fadan hakan har ya gajiya ya kyaleni don ko cikin darene sai ya falko ya samu na koma kasa na kwanta shiyasa ya gane ina jin dadin hakan da nakeyi ne.
Zarah ki tashi anyi sallah kada ki makara yace dani da kyat na bude idanuwana saidana dan dauki lokaci kafin inyi yunkurin mikewa zaune kamar an nasa min mashe naji wanda hakan da sauri yasa na dan saki kara ina komawa a yadda nake.
Sai ganin shi nayi a kaina ya duka yana min sannu tare da dan bude cikin yana kallo a daidai lokacin da cikin ke wani irin motsi har zaka iya gani yadda yake motsawan a lokacin.
Ya dade yana kallin cikin yadda yake motsi yayin da idanuwana suke lumshe don wahalan dana sha hannun shi yakai saman cikin ya dan taba yana murmushi tare da fadin sorry my dear sai kuma cikin ya motsa fiye da farko ya shiga yin wani bul bul bul.
Shiko yana tsugunne yana murmushi sai can ya lafa ya bar motsi ya kara fadin sorry tare da miko min hannayen wai ya mikar dani na gyada mai kai alaman ya bari.
Na samu na mike da kyat ya bini da kallon tausayi na haye sama wanka na fara don inji dadin jikina lokacin na fito na tayar da sallah.
La,asar nayi na dora sai lokacin na fara shirin fitan da yace min zamuyi da yamma duk da bai fada min lokacin fitan ba dai.
Banyi tsammanin akwai wanda yasan da zancen cikin jikina ba har wanan lokacin don irin gargadin da yai min kada in soma in fadawa ko mamu ta san da zancen ciki a jikina balle wani in bar abin har Allah ya saukeni lafiya.
Sai dai na kula tsaye yake kyam da kanshi da karfin Allah wurin yin adduan Allah ya rabani da ciki lafiya ya bamu mai albarka.
Ban fada ba shi bai fadaba wa zai sani da yaya Aliyu mace ce da shi zai sanda hakan don shi kadaine na gida daya taba kawo muna ziyara ya kuma ji dadin yadda ya samemu zanzan da juna don lokacin ina cikin laulayin cikin yana sabo baikai wata biyu bama.
Yaso ya gane cikine amma sai yaya ya batar mai da tunane ya tsare da cewa haka nakeyi duk karshen wata idan ina Al,ada irin namu na mata.
Har yaya Aliyu ya koma bai fahinci komai ba a lokacin ne da zai koma naga irin makudan kudin dayake turawa mahaifan shi don a gabana ya bada su.
Nasu mamu dasu Amma da sauran yan uwa ya lissafa mai abinda zaibawa kowa idan yaje ba tare da ya bari mahaifiyar su ta sani ba.
Dakin ya shigo ina saman mirro zaune yace na dauka kin koma barcin ne na jiki shiru nace banyi barci ba don kada alwalana ya kare kiyi maza ki shirya kada mu rasa kujeran gaba don ina so mu isa da sauri gurin .
Ban tsayaba na tashi na dauko wata bakar jallabiya mai kwalliya kananan duwatsu har kasa da wuyanta an kewaye wuyan rigan da adon duwatsun kamar na gaban da ganin rigan ba sai an fada ma ba kasan an kashe kudi wuri sayen ta sosai gyalen ma nasa biyu ne zaka iya yafawa ko ka dora kamar hulan alkyaba a kai ko ka sake a bayan ka.
Yace mi tarone mai kamar buki na musulman kasan da sukeyi yasa nayi wanan shigar haka ba ta inda zakace kaga tsirencina waje sai tafin hannayi da fuskana ko kafana suna cikin sock saboda sanyi da ya fara,a lokacin kadan kadan .
Zamu kai safe kilafa a gurin ya fada daga bayana haka yasa na juyo da sauri ina kallon shi nace safe kuma yaya idan lalura ya kama mutum fa ?
Yace an fada maki wuri ne na wasa komai sun shirya don bukatan mutanen su sadaka fisabilillah bukatan su kawai idan dai kai musulmine kana kuma wanan kasan zaune ka samu halartan taro don wurin ya cika da jamma,a magoya musullunci.
Bandai gamsu da bayanin shi kodana fito falo ya gama shirya min komai a yar jakkar daya daukan min don shi ya tsaya rufe ko ina na gidan.
Motar daya canza ne wata irin rantsatsan mota baka ba sai an fada ma motar mai tsada bace ya dauko daga can gidan sa itace muka shiga zuwa wurin taron.
Mun bar unguwan mu kadan kiran merry ya shigo wayan shi inajin yadda suke hira na kawar da kai gefe har take gaya mai zasu jamaica a gobe yai masu Allah ya kai lafiya .
Bayan sun gama ya dan juyo ya kalleni hankalina yana ga kallon yanayin garin yace wanan unguwan baida nisa da unguwan mu muna kusa da gidan sarauniyar england yanzu.
Tirkashi tun dosowan wan mu gurin da ake taron tun daga nisa zaka gane taro ne wanda ya karbi sunan shi ashe.
Ban taba sani ko kawowa a raina ba cewa akwai musulmi haka da yawa a kasan America ba saida naga yadda maza da mata da yara suke dandazon zuwa wurin taron.
A ka,idance zaka nuna wani kati kafin shiga gurin mai nuna alaman tantance mutum tun farko .
An sayar da wanan katin shiga taron ne wata uku da suka shude aka fara sayarwa da sanarwa a lokacin ina fama da kaina sosai don laluran cikin jikina.
Ashe ban sani ba harni zan samu halartan wanan wurin taron da aka rubutawa London Muslims Forum Group.
Zakace a wata nahiyar labawa kake ko Africa ko Asian kasa dai iri ta musulmai.
Ina makale a hannun shi daya yana dauke da dan jakkan da ya dauko muna wanda har lokacin ban gama sanin ko maiye a cikin jakkar ba.
Na kula suna matukar mutanta mata masu ciki ga gaisuwa da ka hadu da mutum sai anyi ma sallama ana mutunta junan irin na addini.
A dai shigar mune muka hade da wasu mata da miji zakace ga yanayin su ba musulmai bane suna tare da yaran su mace dana miji .
Omar matar tace tare da nuna sanaya a gare shi sosai miji ma yazo suka gaisa ya dan shafa kan yaran nasu yana gaidasu yayin da yaran sukai mai sallama irin na addinin musulunci ina jin matar na tambayan shi matar shi yace tana gida.
Hakan da yayi ya dan so ya bata min rai yadda yai min din ya nuna ni din ba kowarsa bace a tare dashi.
Sai kallon mamaki da matar ta bini dashi har muka bar su shiko gogan nawa ya daure fuska babu halin ta kara mai wani tambaya a game dani.
Mukai gaba abin mu mun barsu suna sauwa yaran su abu a baya har lokacin matar tana bin mu da kallon mamaki sosai.
Duk saurin zuwa wurin da mukayi layi na ukku muka samu wurin zama saidai hakan ba wani matsala bane ga tsarin wajen ko wanda ke karshe baya kamar yana gabane zaune.
Tsaya fadan yadda wurin ya tsaru bata lokacine gare mu ga littafan addini ana rabawa da kashigo kofan shiga dana abubuwan da za a gudanar a wurin.
Gaskiya kasan Landon tayi wurin bawa kowa yancin da yadda ya dace dashi sai naji na kara son kasan da mutanen kasan a raina.
Malamai da dama na addini suyi wa,azi sunyi bayanai akan addini sosai kafin abawa masu bege su shigo suyi suma ba wani bambancin akida a wurin gabadaya an koma bai dayane.
Zanyi barci in falka ga gajiya zai ban abinci in ci mu fita muyi sallah magariba da isha,i ayin addu,oi sosai a gurin yadda ya dace.
Naji dadin wanan fitan da mukayi bamu dawo gida ba sai goshin asuba don dai yana son in dawo in dan mike kafana ne yasa muka bar wurin .
Duk da barcin da nakeji sai da yasani gaba nayi sallah sannan na kwanta barci banda yunwa don ko a hanya haka yaita miko min tarkacen ban banza da wofi irin nasu na turawa shidai kada ya ganni ina cikin damuwa ko takura ko kadan.
Ban falko ba daga barcin da na samu wanda shima ya dan taba barcin sai sallah azahar ya tayar damu.
Wanka na shiga na fito na tayar da sallah a lokacin babu abinda nake so sai wanka hakane ke dan sa ina ji sanyi a raina duk da yaya yana fadan haka sosai.
Bayan mun gama cin abinci ya dan kalli kafata tare da fadin zarah tun lokacin dana dawo ina kula da kafafuwan nan naki kamar suna hawa idan kin huta anjima sai mu leka asibiti a dubaki.
Ba dama inyi gardama dashi bayan la,asar muka tafi ba laifi likitan ta dibani inda ta dan bada shawara in dinga dan yawatawa da kafa.
Ba wai dani suke bayani ba shike ganin su bayan sun dubani sukan mai bayanin komai don daukana da yakeyi yarinya har yanzu.
Washe gari ya fita dani da safe muka dan taka har zuwa karshen layin mu inda yake bina kamar wata jela can.
Bayan mun dawo nayi wanka abinci naci barci ya daukeni don akwai gajiya a jikina har lokacin.
Sai yaya ya koma yin danasani da fita zuwa sauraren wa,azin da mukayi har wani lokaci kwana biyun daya wuce.
A falo na sameshi shida kanshi ya debo min wani abincin na danci kadan yace in zauna saman kujera yandan matsa min kafata kadan kadan.
Na zauna namike kafafuwana yana matsa min wayan shi yai kara a daidai lokacin ya kai zaune a gefena yana sauraren wayan merry ce a kan layin.
Omar kana ina ne yace may ye matsalan ki na tambayana kuma tace fuck you tare da banko kofan gidan a daidai lokacin da hannuna ke saman kanshi ina dan mai tausa a hankali.
Gaba dayan mu kofan da aka banko muka kalla a lokaci guda mukai arba da merry da yarta da wasu kawayen ta biyu .
Da farko gabana ya fadi sosai da ganin ta sai daga baya zuciyata ta dake na bita da irin kallon da take min itama.
Kara mayar da kanshi yayi saman cinyana naci gaba da abinda nake mai a lokacin.
Mamaki ya hanata tsayawa ta fahinci ma jikina akwai ciki kamar yadda tsegumaman ta tsegunta mata ta ganmu din.
May zan gani haka da kaida blood sister din ka umar yace and so ?
Ta taba hannayen ta tare da fadin karatun da kake fadin tazo yi ke nan ashe ko yaushe kana wurin wanan yar ficiciyar yarinyar shiya baka damu damu ba ashe.
Dayan kawarta tace who is she ?
Tana kallona cikin harde hannayen ta itako merry tana takowa zuwa garemu a hankali da sauri yarta ta rigata tana murna tare da fadin daddy daddy.
Hannu merry tasa ta tare ta ta hanata karasawa wurin mahaifin nata ganin haka ya mike ya nufi hanyar fita yana nuna masu kofan fita ya fadi cikin kakausan murya su fice mai a gida kafin ransu ya baci ya fara neman layin police din su sun san sun taka doka dole suka koma daga kofa.
A gaskiya na tsorata sosai da ganin su tun dai lokacin data nufo inda muke zaune kada ta shakeni da dan cikin jikina.
Ina jinta sun musayar zance dashi tana kara tambayan shi ya amsa mata yes is my sister and my wife also .
Wani ihu ta fara tana turje turje a wurin yan uwanta na kamata ya mayar da gida ya rufe da karfi garam .
16/11/2021, 23:26 – ????????????: ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI TA,ALLA, WABARAKAT, TAHU YA JAMA,ATUL MUSULMIN JUMMA,AT MUBARAKAR, , , ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button