NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

INA MAI MIKA GODIYA GA DUK WANDA SUKAI MIN FATAN SAMUN LAFIYA DA WANDA NA GANI DA WANDA BAN GANI ALLAH YA SAKA DA ALHERIN SA DANI DA DUK WANI WANDA BAIDA LAFIYA UBANGIJI YA BAMU LAFIYA MASU SHI UBANGIJI ALLAH YA KARA MASU LAFIYA AMIN, , , , NAGODE NAGODE KWARAI DA KULAWAN KU GARENI INA ASIBITI KUN KIRA WASU BASU SAMU KIRABA DON LAYINA A KASHE YAKE , , ,

Zan iya cewa zaune kawai nake a cikin falon illahirin jikina sai rawa yake don ba abinda zan iya yi a lokacin banda addu,a.
Shi din kuma nake aikawa daga inda nake zaune don ko ina da lafiya iya abinda zan iya yi ke nan kawai neman tsari a wurin Allah.
Ban san ya sukayi ba ya samu ya turasu suka wuce naji tsit a kofan daya cika da hayaniyan su da farko.
Shiru shiru bai shigo gidan ba har tsawon wani lokaci haka yasa fargaba yasa na dauki waya na kira mamu a lokacin.
Kamar jira take in kirata ta daga wayan hankali a tashe nace mamu ke kadaice a wurin magana nake son yi dake.
Tace lafiya kike najiki a wani yanayi haka sake fadi nayi mamu idan ba a part din ki kike ba ki shiga daki muyi magana yanzu.
Kwantar da hankalin ki ina kuryan dakina yanzu haka kwance lokacin sallah nake jira inyi sai lokacin na sauke ajiyan zuciya.
Sayadi lafiya may ke faruwa dakene wai kin daga mi hankali haka mamu ina cikin tashin hankali a kasan nan yanzu matar yaya tazo gidan nan da tashi hankali don bata taba zuwa gidan nan ba sai yau mamu.
Kuma yaya ya fada mata yau cewa ni matarshi ce sun fita suna jidali dashi har yanzu bai shigo ba .
Kina nufin duk tsawon shekarun nan sayadi merry bata san alakan dake tsakanin ki da shi ba sai yau din nan mamu ta tambaya cikin mamaki ?
Nace hakane mamu a hankali yau ni maimuna naji abin mamaki a rayuwana shin wani irin zaman aure kuke da shine hakane sayadi ?
Shiru nayi na kasa bata amsa komai a lokacin don ban san mai zan ce da ita ba jin nayi shiru tace dani yanzu ke may ye naki na daga hankali a cikin wanan zancen sayadi ?
Ki kwantar da hankalin ki ki saka masu ido shi yasan yadda zai warware matsalan shi can ai namijine yasan yadda zaiyi da abinsa.
Ke nan muke namu hauka a nan ashe wata kila ko taraiyan aure baya yayi dake ke nan duk tsawon wanan lokacin sayadi ?
Shiru nayi ban iya furta komai ba sai ki abinda kikaga dama kin dai karanta kin san komai ba sai na tsaya fada kullun kan ki ba mijin ki hakkin ki ba daya dace.
Wai ace har tsawon wanan lokacin kina zaune sororo a gidan sa shi kuma daya fiki shirmay ya zauna ya zuba maki ido hakana ko tausayin ki yake ji waya sanar mai zanyi magana naji ta kashe waya a cikin takaici.
Wayan nabi da kallo ina mamakin ko yaya akayi ma nakira mamu da wanan haukan nawa ban sani duk tsabab rudewa ne ya kaini ga kiranta ko may oho ?
Har na gama abinda nake na rufe gidana na kwanta bai shigo ba har barci yafara daukata sai ga kiran mamu ya kara shigo min.
Uwa ke nan ashe hankalinta ya tashi sosai daga baya tana tunanen kada merry ta dauki wani mataki a kaina kuma.
Shine ta kirani tana rarashi tare da tambaya ko ya umar ya dawo naji yadda suka kwashe da merry bai dawo ba har lokacin na bata amsa.
Tace kin dai rufe gida eh na rufe na bata amsa ta dan shiga rarashina tana fadin kada ki soma sa masu baki a duk iya abinda zasuyi kada ki yarda aji wani zance a gareki kinji ko .
Ni dai tun ina amsa ta har barci ya daukeni lokacin jin ina barci ta kashe wayan ta ranan dai mamu ba wanda ya gane kanta bata kuma yarda ta fadawa kowa komai ba har amma ta dai bini da adduan neman tsari da rinjaye garesu.
Can cikin dare ya shigo gidan abuna farko daya duba shine ko naci abinci alama ya nuna tun abincin da mukaci dashi da rana ban kara girka komai ba naci.
Da sauri ya nufi dakina ya tura kofa a hankali ya samu kofan a bude ya tura ya shiga ina kwance na dunkule a wuri daya ina barci a takure.
A hankali ya hawo gadon ya kwanta ya sani tsakiyan shi yakai ma goshina kiss hakan da yayi yasa na bude idanuwana a hankali na sauke gare shi.
Dan murmushi na sakarmai cikin karfin hali ya kara rugumoni zuwa jikin shi yana fadin may yasa bakici abinci ba don ban nan , ?
Naci burglar na bashi amsa ya kalleni kamar bai gamsu da abinda nace ba naga ya mike ya fita yana fadin ina zuwa fita yayi zuwa kitchen ya dora ruwan zafi.
Wanka yayi koda ya sauko har heater ya kashe kanshi ya hado muna tea mai zafi ya nufo dakina dashi har lokacin ban iya komawa barcin dana fara ba .
Ya samu na tashi na kewaya na dawo ina zaune bakin gado nayi tagumi da hannu daya wanda ke nuna alaman ina cikin damuwa a lokacin.
Tun shigowan shi ya mayar da kofan da kafa ya rufe ya nufoni yana fadin mainene kuma ?
May ya same ki naga kinyi tagumi haka kuma gargadin da mamu taimun ne yasa da sauri nace babu komai.
Baiyi magana ba saida ya aje min tea din da bread din dayai toisting a gabana ya dawo gefena ya zauna ya dauki cup din ya mika min tare da fadin karba ki sha .
Kaina girgiza mai yace No no no kinsan bana son musu ki karba kawai ki sha nace maza bude bakin ki na baki yace ba yadda na iya dole na bude baki ya fara bani a hankali tare da dan guntsura min bread din ina ci har na shanye sai zufa sai lokacin naji yayi ajiyan zuciya ya aje cup din.
Ya dauki nasa ya fara sha a hankali ina zaune sai zufa nakeyi ina kallon shi har ya shanye ya aje cup din yana fadin tun dazun ina tunanen ki ina gidan Yusuf nasan dama haka zaki zauna da yunwa kiba kanki wahala kan dan maganan da baikai ya kawo ba.
Da mamaki na kalleshi har lokacin warning din mamu yana nan tana min yawo a zuciyata bandai iya furta komai ba sai shi naji yace dani kin tuna da wanan matar abokina da muka hadu da ita ranan wurin shiga taron nan ?
Na gyada kai a hankali yace itace ta bugawa merry waya ta ganni da wata sai dai ga haukan merry har yanzu ta kasa kwantar da hankalin ta tayi nazarin yaya alakana dake yake ne wai.
Ko da ya juyo yana wanan bayanin sai ya samu ina gyangyadi a wurin murmushi yayi ya sauke a jiyan zuciya tare da tayar dani na gyara kwanciyana.
Shikan ranan bai iya barci ba don irin rikicin da sukayi da merry da ya fada mata cewa ni din matarshi ce a yanzu.
Kuma har ina shirin haifa mai diya da zai iya juyasu yadda yake so ya sa su hanyar addinin shi sai ta fadi kasa a somay.
Sun kwashe ta zuwa asibiti bata yarda ta zauna ba tana farfadowa ta juya zuwa America ranan shine ya tsaya gidan yusuf suka shirya irin nasu don sun san tana kasa tana dabo a tsakanin su yanzu.
Washe gari bai tayar min da maganan ba nima haka na shirya zuwa school abina dan ban yarda na saka zancen a raina ba ko kadan.
Munyi exam lafiya har lokacin tun ina sauraren zuwan merry naji shiru ranan ina zaune ya dawo yake ce min in shirya zan koma gidan Yusuf in zauna a can zaiyi tafiya har ya dawo.
Nadan so yin gardaman hakan sai dai ba fuska da zanyi hakan gurin shi .
Matar Yusuf din ita da mijin ta sukazo gidan suka daukan min duk wani abinda zan iya bukata a can dukda ba wani abu suka daukar min ba a gidan nidai na bar mamakin hakan a raina kawai.
Don na zargi akwai wani abinda suke boye min daga su har yaya din a lokacin wanda basu so in fahinta niko kwatar min da hankali da mahaifiya tayi dukda bata san halin da nake ciki ba yasa na fitar da komai a raina.
A kullun sai nayi in fadawa mamu zancen cikin dake jikina sai inyi tunanen yaya zan fada mata waini ina dauke da ciki a jikina wanan abin akwai kunya gaskiya.
Haka yasa naja bakina nayi shiru wanda shima yaya hakan yai mai dadi don har gashi ya kaini inda za a taimaka min in haihu batare da wani tashin hankali ba ko wani yasan da hakan don sun rigada sun gama shirin komai.
Nidai ba zance banji dadin zaman gidan yusuf ba ba don ko ba komai banda zaman kadaici ko kadan saidai kewan mijina da yakan damay ni don dan sabon da mukayi dashi a lokacin.
Ina sati daya da zuwa gidan ya dawo a wani safiyan nayi murnan dawowan shi kwarai da gaske har ban iya boye hakan a raina.
Ramla tana zolayana nidai sai murmushi nake mata kawai zuwa karbe biyu na idar da sallah ta shigo dakin tana fadin in shirya zamu fita inji mazan mu.
Ba wani shiri nayi ba dan hijjab dina kawai na dora a kaina karami muka fito baya muka zauna .
Tafiya mai dan nisa sosai da gidan mukayi zuwa wani unguwa sai dai unguwar yana da kama dana tallakawa a gaban wani gida yusuf ya tsaya da motar shi.
Saida yayi waya muka fito lokaci daya da wata mata da naji Ramla na kira da mummy tana kallona tace a masha Allah wanan ce yar tawa gaskiya sun dace sosai da maigidanta ta kamo hannuna zuwa ciki tana fadin yata sannun ku da zuwa.
Hausanta nakeji wani iri a raina nace oh nidai Allah ya kawo ni sun dan dade tare suna hira kafin su barmu gidan da sunan sai sun dawo daukan mu.
Hira sosai anty Ramla da dattijuwar matar suke keyi akan haihuwa har zuwa rainon yaya da sauran su ni dai ina sauraren su.
Tun ban kula da hiran su ba har yakai na mayar da hankalina gurin su kamar uwace ce ke koyar da yar ta abubuwa na fannin haihuwa.
Har ya kai ina masu tambayoyi suna ban amsa a tare cikin natsuwa nake fahintar su sai matar tace in miko hannayena ta gani na mika mata ta rike da hannunta bibiyu ta dade tana tsura masu idanu kafin tayi murmushi tace abubuwa ai zasu zo da sauki insha Allahu ke Ramla.
Wanan da kuke gani babu wani harin da zai samayta asalima ko sun jefota ba inda abin ke zuwa do itama ba a banza take ba gaskiya.
A kwata da yawan ibada ta fada tana murmushi sanan kuna kinganta nan tana tare da mutanen a kanta sosai.
Don haka mijin ta ya kwantar da hankalin shi insha Allahu cikin amincin Allah da yardan shi komai zaizo da sauki wanan mafalkin da sukeyi ba karya bane gaskiya.
Saidai duk abinda sukayi Allah bai yarda suyi nasara a kansu don makiya kan a kwaisu dana gida dana waje sai dai ta girgiza kai tace dasun sani dasun daina bata kudin su sukeyi ga banza wanan ta zama kainuwa dashen Allah a cikin zuri,an ta ko.
Tun ban fahintar ida maganan ta ya dosa har na gane inda Ramla da mijin ta suka kawo mu wanan dattijuwar matar malamace ko kuma wata mai magani irin namu na hausawa a gida.
A,uzubillahi nace har ya fito fili suka kalleni lokacin da nake bin gidan matar da kallo ina kara fahintar wani abu a gamay da ita.
Tayi murmushi tare da fadin bana shirka kamar yadda kike zato yar nan saidai Allah yaban mutane a kaina dake zama tare dani har yakai bana iya zama a cikin mutane dole na dawo nan bakin ruwa na zauna a kusa dasu.
Ba kowa nakewa haka ba sai wanda zuciyana ya aminta dashi matsalan ku babbane tun a gida yake faruwa har yanzu ba a daina bibiyan ku ba.
Da maishi zai gane hakan ya daina da zaifi sauki gareshi don abubuwan dake tare dake manyane sosai basu bari wani sheri ya samay ki.
Haka dai tayi ta surutun ta ina kallon su kawai ina murmushi don ni banji komai a raina ba kan abinda take fadi lokacin gamay damu.
Fita mukayi shan iska ta bayan ta sai lokacin ma kula da unguwar sosai ashe a bakin ruwa gidajen nasu yake sosai.
Tayi girki da wani irin kifi kato dan miya kamar miyar kasar hausa na danyen kifi tare da abinci mukaci.
Sai dare sosai suka dawo suka dauke mu bayan sun gama ganawa da ita tazo har inda nake tana min addu,an Allah ya saukeni lafiya.
Zuciyana cike da mamakin wanan matar ko maiye makasudin zuwa gidan ta da mukayi ban sani ba nu dai na dauki hakan da ziyara kawai muka kawo mata.
A zato na dauka zamu sauke su Ramla ne mu wuce gida sai naga sabanin hakan lokacin don har shi yaya din a gidan Yusuf din muka kwana ranan a dakin da aka ware mun gidan.
Sai lokacin da muka kebe ne naga irin raman da yayi sosai ya ramay yayi dan baki a lokacin da ya fito wanka.
Ya hawo gado inda nake lokacin ina fushin rashin maidani gidana da baiyi ba ina jin shi na kyaleshi .
Zarah na san idon ki biyu fushi kike danine haka komay ?
Sai lokacin na dan juya ina magana ciki ciki nace ban son zama a gidan nan da nakeyi yaya ka mayar dani gidana don Allah.
Sai naji ya sauke a jiyan zuciya tare da rugumeni a jikin shi kamar karamar yarinya yace nasan bakiso zarah amma hakan shine daidai dake a yanzu.
Don barin ki wancan gidan ke kadai hatsarine gare ki idan haihuwa yazo maki bana gidan ko wani yazo maki da tashin hankalin a wanan halin da kike ciki ban kusa kinga ai zaki shiga wani halin da ba a son mace mai ciki ta shiga.
Mutanen nan su suka bada shawaran in dawo dake nan kusa dasu don kina gab da haihuwa don sun san ni ba zama nake ko yaushe ba.
To ka maidani gida mana nace a dan shagwabe haba zarah in kin min haka baki min adalci ba baki fatan abinda zaki haifa ya taso cikakken dan kasan nan ne ?
Ko dai kina samun takurawane a nan din da sauri na girgiza kai alaman a,a kawai dai ni ban saba dasu bane har yanzu.
Ki daure ki saba dasu ya ban amsa nasan Ramla tana da hali mai kyau don hakanema na yarda da shawaran in bar ki nan din don hankalina zaifi kwanciya.
Shiru nayi ban bashi amsa ba yace da fatan kin daina yawan mafalkin ana binki da gudu yanzu jin tambayan da yai min yasa nayi magana a lokacin.
Na daina sai dai yanzu mata uku nake gani suna bina amma bada gudu ba kamar da kafin su cin mun wani abu yake dagani sama.
Bai kara magana a haka barci ya dauke mu washe gari tunda ya fita sallah bai shigo ba daga shi har mai gidan wurin matar gidan na samu labarin wai ashe suna case ne da merry matar shi ranan zasu zauna kotu.
Asalima wai wanan gidan da nake zaune a cikin sa an rufe sai bayan kare case din mu yanzu ba a san inda nake zaune bane da har dani zamu tafi wurin case din.
Basu dawo gida tare ba gashi ina son tambayan shi sai dai ba zan iya hakan ba saboda nauyi da kunya itin namu na matan hausawa.
Sai bayan kwana biyu sai gashi ya kara ramewa sosai yayi duhu da ganin sa yana cikin yanayin damuwa.
Ina dan karamin falon gidan zaune idanuwa suna lumshe ina faman tunanen yanayin da na tsunci kaina a ciki kamshin shi ya daki hancina na bude idanuwana da sauri na sauke a kan shi.
Yana tsaye yayin da corth dinshi yake rike a hannun shi daya, dayan hannun na cikin aljihun wandon shi ya zuba min idanuwa cikin yanayin tausayawa gareni.
Kokarin mikewa nayi zaune sai na kasa da sauri ya karaso inda nake zaune yana fadin zauna abinki zarah.
Mai ya same kike zaune nan ke kadai kina tunane ko an maki wani abune ko kuma cikin na damun ki ne ya jero min wanan tambayotin kusan lokaci guda a jere.
Ban san yadda akayi ba sai ganin hawaye nayi sun soma zubo min a idona tun suna zuba a hankali har na soma a cikin sheshekan kuka.
Lokaci daya ya Umar ya rikice yana fadin fada min abinda ke damun ki yanzu ko muje asibiti ne dake ?
Ko gidan ne bakya so na rabaki dasu yau ganin ya rude har baisan abinda yake fadi ba yasa na dan rage sautin kukan nawa a hankali na bude baki da kyat nace yaya ka maidani gida don Allah wurin iyayyen mu.
Wani irin kallo yai min yace haba zarah baki tausayinane matsalan dake akwai a gida yafi wanan sau dubu a wurina yanzu kin sani.
Koda yake ba lalai bane ki san da hakan ke amma ina rokon ki zarah ki daure ki taimakeni ki kwantar da hankalin ki har zuwa lokacin da Allah zai saukeki lafiya ki haihu .
Izuwa lokacin komai zai kai karshe insha Allahu koba zaki iya min alkawarin komai ba na rokeki ki min wanan don Allah zarah for d sake of our urborn baby.
Na dago kai na kalleshi da sauri ni din yake kallo yana jiran amsan da zan bashi yana ganin na dago kai ya gyada min kai alaman in yarda da bukatan shi.
Ban bada amsa zancen ba don ba zan iya cewa eh ko a,a alokacin ba don irin yadda nake jin kaina.
Ganin nayi shiru ya mikar dani tsaye yana fadin muje daki in ja maki kafa ki ko zai maki dadi badon naso ba dole na bishi ya zaunar dani saman gadon tare da aje rigar jikin nasagefe daya.
Ya shiga matsa min kafan a hankali ina dan lumshe ido don jin dadin hakan da yake min din a lokacin.
Sai dai har lokacin ba wani magana don zuciyar kowan mu ba dadi a cikin sa shi yana ganin ya cutamin da yawa ga ciki ga rikicin daya taso tsakanin shi da merry.
Allah ya taimakeshi a kasan London suke ba a America ba don haka abin ya danzo mai da sauki ba kamar yadda merry din ta dauko zancen ba.
Don sam ta manta da yarjejeniyar su da sukayi kafin aure a rubuce dashi bata taba daukan wanan da muhinmanci ba don kamar da wasa sukayi shi.
Sai gashi wanan yar takardan ya rusa mata duk wani plain da alwashin ganin bayan shi tare da yan uwanshi a kan kara wasu hallita a cikin family din ta dashi.
Yayi barazanan bar mata dukiyan da take fadi akan zai bata takarda ta tafi har da yar tasu ya yafe mata.
Jin hakan har yan uwanta da iyayyen ta sun yarda da hakan daga baya merry din ta tubure masu akan sai tayi shawara da zuciyar ta ita kadai shinr aka kara basu lokaci.
Lokacin da suka fito cikin couth din dasshi da Yusuf ko kallon inda take baiyi ba ga Faith na kiran daddy daddy ya wuce ya barta a wurin zuciyar shi na masa kuna.
Kowa dake wurin saida yai mamakin hakan har yan uwanta sun fara fadin kinga irin abinda muke fada maki ga wa yan nan mutanen ke nan.
Basu da tabbas akan addinin su zasu iyayin komai lokaci guda ki kyaleshi don dole ya dawo ko don yar shi gareku.
Ku rufa min baki gaba dayan ku banson jin maganan kowa daga cikin ku idan rayuwan aurena ya samu matsala kune silan hakan gareni da yata.
Don kun hanani bin abinda mijina keso dani kun hana mu zauna lafiya dashi ga baki daya kuna ganin zamu iya juyashi a lokaci guda.
Omar ya wuce hakan da kuke tunani don yana tsaye ga addinin shi sosai hakama iyayyensa basu zauna a kansa ba.
Nan ta barsu ta shiga mota ds yarta tabi bayan shi saidai bata samay su ba taje gidan data san Yusuf a da baya gidan yanzu.
Ta juya zuwa gidan da suka samay ni gidan yana rufe kamar yadda hukuma tace a rufe shi har lokacin zama tayi tana karewa gidan kallo.
Tana mamakin yadda Omar ya zauna wata mace macen ma yarinya karama kamar fatema da ta sani a matsayin matar auren shi.
May zai samu gun wanan yarinyar da bai samu a wurin ta ba har ya iya bin umurnin iyayyen shi kanta.
Ido ta runtse sai hawaye taja mota kamar an tsikareta ta nufi gidan su ko yana can sai dai tun a haraban gidan ta gane baya gidan a lokacin.
Duk wanan haukan da merry keyi har yan uwanta basu kai ga gane akwai ciki a jikina ba har wanan lokacin ita dai zafin ta shine cewa da yayi ya a zaman matarshi nake nima.
Duk wanan abinda suke ciki ni ban sani ba don bai zauna yai min bayani yadda zan gane ba har in fahince shi.
Ni dai zan iya cewa wanan hutun baizo min da dadi ba din ga laluran ciki gana wanan halin da muke ciki ina zaune a gidan mutane a takure duk kokarin da sukeyi dani sai ban gani don ina ganin da hadin bakin su komai ke faruwa.
Ga Anty Ramla bata kasa dani ba kullun zata shigo wurina mu zauna muyi hira ta kawo min wanan ta kawo wancan haka dai take dawai niya dani a gidan.
Ni da kaina na ba kaina shawaran in sake jiki da ita wanan fushin ba zai fishini ba don ba zan iya fahintar komai a haka ba.
Ranan tana kitchen da safe tana aiki na fito na samay ta kitchen din ta juyo tana fadin mai ciki kin fito na danyi murmushi zuwa inda take ina kokarin karban wanke plate din da takeyi.
Tace rufa min asiri kada mai gidan ki ya samu kina wanan yace zan halaka mar mata kin ko san yana can amma kunnuwan sa na nan zarah.
Ban taba zaton akwai wata mace da zatazo tayi tasiri haka a zuciyar umar ba sai gashi har naga abinda yafi ma tunanena.
Zarah ki godewa Allah mijin ki yana son ki sosai da ba haka ba duk wanan barazanar da matarsa keyi akanki ne zarah.
Kin san umar ya zabi ya sadaukar da dukiyan shi akanta da komai nasa ya zauna dake ?
Nace ni kuma anty ?
Tace ke kuwa zarah ko cikin nan naki a jikin sa yake ya tsaya hakan yanzu haka duk wani shiri ya kamala duk da wanan halin na barazana ga hukuma da yake ciki amma ya gama shiri akan komai na haihuwan ki da ya dawo daga wanan tafiyan zaki sha mamakin shi kwarai
Wanan maganan da mukayi yasa naji kunyan kaina da kaina na rashin kwantar da hankalina garesu bayan nasan suna cikin barazana duk kuma a kaina.
Sai na samu kaina da jin kunyan kaina da kaina don haka na yanke a raina yana dawowa kawai in bashi hakkuri sai wata zuciya tace min akan may zan bashi hakkuri din ?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button