A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Su Yaya Jameel suka mana addu’ar Allah ya tsare, Yaya Bilal ya tashi motar muka fita daga gidan.
Daga farko nayi tunanin ko zamu biya ta gidan Anty Ameerah ne mu daukota, amma sai naga Yaya ya dauki hanyar fita daga Zaria straight.
A raina na raya tunda ita din shafaffiya ce da mai, yar gaban goshi, tana da motar hawa ta kanta, kila da kanta ta tafi.

Tafiya muke cikin madaidaicin gudu, bayan sautin radio da take ta aikin yi, baka jin motsin komi a cikin motar.
Yaya ya fara katse mana shirun ta hanyar fara tambayata yanayin yadda tsarin internship dinmu zai kasance. Nan da nan hira ta barke a tsakaninmu. Muna cikin yin hirar, zaka ji Raheemah itama ta tsoma nata bakin a ciki. Duk da ba tamu hirar take sanyawa baki ba, tata kalar hirar daban. Na kula tun karfinta take kokarin janye hankalin Yaya daga kaina.
Daga karshe dai da abin ya ishe ni, sai na kwantar da kaina akan kujera na kyalesu suna ta hirar su kamar ina yin barci.

????????????

F.W.A

              *☆⋆38⋆☆*

Gidan Yaya Bilal babba ne, mai kyau na gaban kwatance. Lokacin da muka fara shiga Abuja barci ya fara daukata, haka na bude idanu ina kallon gari. Duk da cewa ba wannan ne karona na farko zuwa Abuja ba, amma kuma na jima kwarai rabona da garin. Shi yasa yanzu nake ganina kamar wata sabuwar zuwa.
Yaya yayi ta ratsa tituna da ginunnuka har muka isa wata unguwa da tun daga bakin gate naga an rubuta Maitama. Duk yawace-yawacena ban taba biyowa ta nan wajajen ba. Daga gani babu tambaya unguwa ce ta masu hannu da shuni, tun daga kan ginunnukan da kuma tsari da yanayin unguwar. Ba karamin burgeni tayi ba.
Yaya ya tsaya a kofar wani madaidaicin gida, yayi amfani da remote, gate din gidan daya kasance ruwan zuma mai cizawa, da wata irin raga-raga daga tsakiya wadda take baka damar hango tanfatsetsen ginin dake ciki, ya bude da kanshi. Yaya Bilal ya silala kan motar ta shiga ciki, muna shiga gate din gidan ya koma ya rufe.

Wajen ajiye motoci muka fara tararwa, waje na mai fadi da zai cinye motoci akalla guda biyar. Yayi parking din motar, muka fito muna karewa gidan kallo. Motoci biyu ne a garejin, rufe da tampol dinsu. Ya mana jagora zuwa gidan. Daga gefen garejin akwai karamin waje da aka yi shuke-shuken bishiyoyi da furanni da basu fara tsayi ba, da alamu sabon garden ne aka yi. Sai kuwa kofar gidan, kana shiga dogon corridor ne da zai kaika har tsakiyar wani babban falo, kana shiga corridor din zaka ci karo da wata kofa da zata sadaka da kicin.
Babban falon ya dauki saitin royal setting, daga kan kujeru, carpet, labulaye, da fenti, duk golden ne da ratsin royal blue. A cikin babban falon dinning room yake, sai kuwa kicin da kofar su daya da dinning room din, sai babban store.
Kana fita daga babban falon anan dakunan mu suke, suma dai tubarkallah manya ne, daya yana kallon daya, inda nan ne ya nunawa Raheemah daya a matsayin nata, dayan kuma a matsayin na Ameerah da bamu gani ba, kila ita sai anjima ko kuma washegari. Daga gaban nasu kadan nan nawa dakin yake, daga gefen nawa kuma akwai dakuna guda biyu, babu komi a ciki daga carpet sai katifa da labulaye, kila dakin baki ne ko kuma na yara. Daga nan ya jamu, muka bi ta gefen dakunan zuwa master bedroom, inda dakinshi yake. Shima dakine babba mai fadi sosai. Daga dakin nashi muka sake fita zuwa wani falon da bai kai wancan girma ba, shima dai saitin kujeru ne da madaidaiciyar tv, sai tagogin wajen da suka kasance manya, irin daga sama zuwa kasa dinnan na gilasai, kana hango karamin lambun daga nan. Wajen dai ya hadu kwarai, just spectacular. Da ya bude wata kofa daga nan falon, sai muka sake bayyana a babban falo.

Bayan ya gama nuna mana gida da kuma ko’ina da ko’ina dai, sai duk muka wuce dakunanmu domin yin sallah da aka fara kira.

Dakina mai fadi ne, an sanya Italian bed, closet ta jikin bango, dressing mirror da shelves na littafai. Fentin dakin light orange ne, sai daga bangon gado da aka sanya wasu irin wallpapers masu tsananin kyau. Daga can gefe akwai study table da aka shirya, da dan karamin firjin a gefe, can gefe kuma nan ne bathroom yake. An zuba duk wasu abubuwan bukata a ciki. Sauran dakunan ma duk haka suke, hatta da kayan ma duk iri daya ne, kala ce kawai ta banbanta. Na sake bin dakin da kallo ina jinjina kai cikin jinjina namijin kokarin da Yaya yayi. Daga karshe dai na shiga bandaki na dauro alwala, ina fitowa na tadda abin sallah a shimfide yana facing din alkibla, don haka na hau kai na tada kabbarar sallah. Ban tashi daga kai ba sai dana yi sallar isha’i da shafa’i da wutiri sannan.

Kayana da aka taho min dasu na samesu a tsakiyar daki, na fara daga su ina fiddo su daga cikin akwatunan. Cikina ihun yunwa yake yi tun karfinshi, tunda yau na fita daga girki nasan bani da halin cewa zan shiga kicin in dora abinda zan ci. Nayi tunanin fita domin in ga abinda aka girka, daga baya dai kawai naga bari in dakata in gani ko za’a kira ni. Na daga fridge din dakin naga babu komi a ciki sai ruwa, shima babu sanyi saboda firjin din ba a kunne yake ba. Naja tsaki na maida firjin din na rufe. Na koma naci gaba da daddaga kayan.

Ina cikin fito da kayan Janan ta kirani, ni sai lokacin ma na tuna babu wanda na kira, na daga wayar cikin dariya saboda nasan korafi ta kira ta min. Illa kuwa, ina dagawa ta fara, “haba baiwar Allah, dokin sabon gida har yasa kin fara mantawa da mutane ne?”.

Nayi dariya nace “don mantuwa kam na manta dake, sai dai ba santin gida bane yasa na manta dake wallahi, gajiya ce da yunwa, gashi tunda muka sauka bamu zauna bane shi yasa”.

Tace “to sannunku. Nima tun dazu naji Yaya yana fadawa Ummah kun isa lafiya, shine na zauna ina jiran a kirani sai kuma naji shiru, shine na biyo baya. Kun sauka lafiya?”.

Nace “lafiya lau, ya su Ummah?”.
Tace “lafiya. Ya gidan naku?”.

Nan na mike kafa na fara labarta mata labari, har sai data fara cewa in dan saurara sannan na dakata ina dariya, “Allah don baki ga gidan bane Jan, ya hadu fiye da tunaninki. Bana tunanin duk shige-shigenki kin taba shiga gidan daya kai wannan wallahi”.

Tace “ai in Allah ya yarda zamu zo ganin gida ni dasu Yaya kila satin sama, tunda Yaya ya gama ginin kusan shekara nawa yanzu, babu wanda ya taba zuwa sai dai su Yaya Auwal da naji suna fadin haduwar gidan”.

Nace “haba? Dama ba’a taba zama a gidan nan ba?”.

Tace “wa zai zauna? Shi kadai yake zaune a gidanshi. Anty Ameerah dama bata taba zama a gidan ba saboda lokacin da aka yi aurensu tana karatu, kuma yana cikin yin ginin ne, bayan ya gama kuwa taki komawa. Ita kuma Anty Raheemah dama bai taba cewa zai kawota nan ba, don’t know why though!”.

Na jinjina kai, “lallai yayi kokari ba kadan ba. Zama a gidannan kai kadai duk girma da fadinshi?”.
Tace “to yanzu ba gaku nan ba? Dagewa zaki yi ki fara sauke mana yan digwi-digwi yadda zaki ga gidan ya cika nan da dan lokaci, sai ku daina ganin girmanshi”.

Wani abu ya dan ratsa zuciya da tace haka, amma sai na dake, na saki wata sarkakkiyar dariya nace “ke fa baki da kunya wani lokacin Jan, duka-duka yaushe aka yi auren?”.

Tace “tunda aka yi sati kuwa, ai lokaci yayi babe, yakamata zuwa yanzu ace koma menene ya gama shiga. Kin fara jin canje-canje a jikinki kuwa?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button