A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Na kalli kayan jikina, kafin na sake kallonshi ina sakin murmushin saye zuciya, na manna mishi peck a kumatu tare da rada mishi thank you a kunne.
Sai dana juya zan fita sannan na kalli inda Anty Ameerah take, nace “oh oh! Anty Ameerah an tashi lafiya? Ashe kina dakin?”.

Dan murmushin da yake kan fuskarta ya yaye, kafin ya sake dawowa, “lafiya lau Na’ilah. Wai ina dan taya shi hira ne ganin shi kadai ne a dakin”.

Na girgiza kai cikin murmushi nima, idan duniyanci ne, gidan shi tazo, nace “babu komi wallahi, kin kyauta. Abinci ya kammala idan zaki ci”.
Ta gyada kai tana murmushi, ni kuma na bude kofar dakin na fita.

Nayi zaton zata biyoni ne, amma shiru har na gama zubawa Yaya abincinshi, bata fito ba. Zuwa can sai gasu sun fito tare, hannunta damke cikin nashi. Na ciza baki cike da takaici da kuma mamakin matar, ina kula da lokacin da Yaya ya zame hannunshi daga cikin nata, amma duk da haka sai data sake yunkurin kamo shi, yayi saurin zama kusa dani. Ni kuwa na fara tura mishi abincinshi gaban shi.
Abincin dana zuba daidai wanda zamu iya cinyewa ne ni dashi, ina kallon yadda ta fara raba kallo tsakanin kulolin dana ajiye a bude babu komi a cikinsu, da kuma plate din gaban Yaya.

Ganin bata da niyar barin wajen, yasa nace mata “abincin a babban falo na ajiye”.
Ga wani mutum daban, ko kuwa shi Yaya dake zaune yana durawa cikinshi abinda na girka mishi, zai yi zaton cewa tuni ne kawai nake mata, amma ita ta sani, nima nasan cewa ce mata nayi ta bamu waje.

Na kura mata idanu ina son tace wani abu, kamar tana son taci gaba da zama anan taga yadda ake fadin ‘bar nan wajen’, gatsar. Kowa yasan cewa ranakun weekend, har azuhur mai girki tana tarr da maigidanta suna hira ko duk ma abinda suka ga dama. Duk sai idan Yaya ya dawo daga masallaci sannan muke haduwa a babban falo, watarana kuma a falonshi, wani lokaci ayi hira, watarana kuma kowa yayi abinda yaga yafi mishi. To meye nata na wani zuwa ta dinga neman batawa mutane jindadin safiyarsu?.

Murmushi itama tayi, daga ganinshi bai kai ciki ba. Ta kalli Yaya tana wani firirita da rangwada, “babyyy… Kasan fa bana jin dadin cin abinci ni kadai musamman idan ina ganinka, gaskiya ni dai bari inje in zubo nawa sai inzo nan mu ci At least idan ina jin motsinku a kusa dani zan fi jin dadin abincin”.

Yaya ya danyi hesitating, da alama shi kanshi bai yi maraba da hakan ba, sai dai sanin halin Yaya na rashin son disappointing mutane, ba zai iya cewa a’ah ba.
Ban ce komi ba, kaina a kasa ina tura abincin cikin bakina kamar bana ma jin abinda suke fada, sai dai gabadaya hankalina yana kansu ina jiran abinda Yayan zai ce mata.
Kallona yayi, yace “babu matsala?”.

Na daga mishi kafada kaina a kasa, “wai ni? Noo, babu komi. Meye a ciki?”.

Yaya bai fahimci yadda nayi maganar cike da dacin rai ba, yace mata “to ki je ki zubo din”. Ta kuwa juya ba musu ta fita daga falon.

Na bita da kallo ina sake-sake a cikin raina, wata idea ta sauka a cikin raina. Nayi murmushin mugunta.

A hankali na matsa kusa da Yaya, na tabbatar kamshina yana kaiwa cikin hancinshi yadda na kamata, cikin salo na karairaya, ina kada idanu nace mishi “kasan wani abu Yaya?”.

Ya dago kai a hankali ya kalleni, ina kula da yadda ya lumshe idanu yana kara shakar kamshin turarena, nayi murmushi. Kai kawai ya iya dagawa ba tare da yace komi ba, daga haka ma kadai nasan cewa ya shiga cikin wani yanayi.

Na kara matsawa saitin kunnenshi, “yanzu nayi wanka”, na rada mishi a kunnen nashi.
Kallon daya watso min cikin zare ido yasa na kusa shekewa da dariya, na dai daureta, nayi murmushi, “da gaske?”, ya tambaya breathless, kamar wanda yake dambarwa da numfashinshi, na gyada mishi kai.

Bai ce komi ba, ya ture plate din abincin can gefe, bai ankare ba naji an daga ni sama cimak, sai dakinshi. Na sheke da dariya ina kokarin zamewa, amma ina, ya maida kofar dakin baram ya rufe kamar tashin duniya. Bai min masauki a ko’ina ba sai akan tattausan gadonshi.
Tun ma kafin in gama tantance abinda ya faru, naji an fara zame min kayan jikina. Dariya kawai nake kyalkyalawa, gefe daya cikin farinciki, ganin yadda mijina ya rikice bayan dududu kwanaki shida ne kawai muka yi ba tare da juna ba, gefe daya kuma ta mugunta ce. Ina ta picturing yadda fuskar Ameerah zata kasance idan ta dawo cikin falon nan taga babu kowa sai kwanukan abinci kawai. Ko zata biyo mu taga abinda yasa muka tashi kuwa? Na sake sakin wata dariyar ina tunanin abinda zata yi idan ta shigo ta ga halin da muke ciki yanzu. Watakila daga yau ta shiga cikin hankalinta.

                             ⋆⋆

Lokacin da muka sake fitowa daga dakinshi, tuni wasu masallatan suka gama sallar azuhur. Falon babu kowa sai kayan abincin da muka bari dazu, nayi murmushi ina girgiza kai. Yaya ya min sallama ya fita zuwa masallaci, ni kuma da yake na riga nayi tawa sallar a dakinshi, na hada kayan na wuce kicin.
Dukansu suna babban falo a zaune, Raheemah na kallo, Ameerah kuma tana wasa da kan wayarta. Na musu sannu na wuce kicin, babu wadda ta amsa min, sai Raheemah data bini da kalmar ‘jarababbiya’, ban ma nuna naji abinda tace ba na fada kicin.
In dai akan farantawa mijina rai ne, babu abinda ba zan iya yi ba, ban damu da duk abinda zasu ce ba, duk wadda taga zata iya jerawa dani, sai ta biyo bayana mu buga.

Yinin ranar haka muka yini, yau mu duka hudun muka hadu a falo ana ta hira, wadda yawancinta ni da Yaya ne muke yin ta, Raheemah bata saka mana baki sai idan harkar korafi ta taso, dama nan tafi auki, ita kuwa Ameerah, kokarinta kawai taga ta janye hankalin Yaya daga kaina, wanda ban bari hakan ta faru ba. Tana bukatar kara zage damtse sosai kafin hakan ta faru. Bata san cewa zaman nan da muka yi dasu ba, don dai ya zame min dole bane? Ni a son samuna, mu zauna mu biyu daga ni sai shi kawai, amma duk da kasancewarsu anan wajen, hakan ba zai taba hana ni yin abinda zai sanya mijina cikin nishadi ba. A haka dai yinin namu ya kare.

Yau ma da dare irin jiya ce ta faru, sai gata ta kwaso kwalliya, wai tazo taya mu hira. Sai dai maimakon wannan karon inji haushin haka, sai kawai nayi murmushi. Naci gaba da yiwa Yaya tausa a kafafunshi kamar yadda ta shigo ta same mu, muka cigaba da hirarmu dashi. Babu jimawa ma Yayan ya tashi yace zai je ya kwanta, muka mata sallama muka shige daki bayan mun bar mata sakon ta kashe wutar falon idan zata fita.

Washegari na fita daga girki, Raheemah ta amsa. Wani abin mamaki, sam Ameerah bata yi abubuwan data fara yi ba lokacin da nayi nawa girkin. Kenan hakan yana nufin ni ce dai take yiwa wannan shirmen? Idan kuwa haka ne, a shirye nake. Wannan shi na kira ‘kishi’.
Kodayake, ban ga laifinta ba, Raheemah dai ba ruwanta da wani kula da tarairayar miji. Idan ta dafa mishi abinda ta dafa, wani lokaci yini take yi tana kallo a falo ko kayan da aka ci abinci bata dauke ba, watarana kuma gidan ma take bari. Saboda haka nafi kyautata zaton Ameerah gani take yi kwace miji a hannun Raheemah ba wani aiki bane, kuma da gaskiyarta. Sai ni kenan.

*

To rayuwar haka taci gaba da tafiya dai. Zaman da muka yi dasu a waje daya ya bani ikon fahimtar su sosai.

Ita Raheemah, tana da wani irin hali na daukar zuga da shawara. Babu abinda zata aikata ko ta gudanar, sai ta nemi shawarar kannenta. Sai ya zama kamar sune ma suke juya mata rayuwar aure gabadaya. Bata tsinanawa miji komi sai dan banzan mita, yawo da lalaci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button