A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

“To amma idan fa shi wanda kika kafe zaki aura din, shima yazo zai kara aure daga baya?”.

Nayi shiru cikin tunani, lokaci zuwa lokaci ina irin wannan tunanin, sai dai har yau akan mafita daya nake sauka, “sai ya zaba ko ni, ko ita!”.
Maganar ta fito tun daga kasan zuciyata har cikin bakina, babu wata tantama ko fargaba.

Ta zare ido cikin mamaki, ta daga baki zata yi magana, nayi gaggawar katseta, “na san abinda kike kokarin yi Jan, maganar gaskiya zan fada miki, itace ki daina bata yawun bakinki. So kike yi kiyi provoking dina, ko kiyi convincing dina, koma dai wannene daga ciki ba zai yi aiki a kaina ba. Kin san hali na sarai. Zama da kishiya daya ma bai cikin tsarina, Allah ya gani, balle kuma mai mata har biyu? Not a chance! Ba wai ba zan yi bane, ba zan iya ba! Don haka gwanda ma kiyi hakuri kawai, mu canza magana, kafin rayukanmu su zo su baci a banza!”.

Maganar da nayi ta sosa mata rai, sai dai tasan kamar yadda nace, idan ta kafe akan wannan maganar, lallai rayukanmu zasu baci. Don haka ta girgiza kai kawai, “Allah ya ganar dake” kadai ta iya furtawa.
Nayi murmushi ina kai gorar yoghurt din dake hannuna baki, “Ameen”.
Ban nuna mata na kula da kallon da take min ba na takaici da ban haushi, abu daya na sani, ba zan taba canza magana, ra’ayi, ko tsari na ba. Ba zan taba zama da kishiya ba!!.

Janan ta juya taci gaba da tunkarar pediatric ward bayan wannan, na bi bayanta da sauri tare da sankala hannuna bayan wuyanta, ina kallonta cikin kokarin ganin na dan yi lifting din mood dinta.
“Come now Jan, kada ki bari wannan maganar ta shiga tsakaninmu mana, shi yasa seriously maganar nan does not appeal to me that much. Haka kike so inje in auri yayan naki, idan muka yi fada ki dinga goyon bayanshi?”.
Na fada cike da tsokana.

Janan tayi dan murmushi kawai, “Na’ilah kenan. Ni nasan ko hakan ta faru babu ta yadda za ayi in juya miki baya, ko mai zai faru kuwa… Yanzu mu bar wannan maganar, yaushe kike ganin yakamata mu tafi?”.

Na dan sauke ajiyar zuciya cike da jindadin ta bar maganar, nace “kin san fa da kyar ne su bari mu tafi har na kwana hudu Janan”.

Tayi yar dariya, daidai lokacin da muka shiga cikin ward dinmu muka wuce nursing station kai tsaye, tace “mu masu uwa a gindin murhu? Ango guda fa garemu a cikin wajennan, Allah na tuba ko wata ne ai ba zamu samu wata matsala ba”.

Na jefa mata harara cikin wasa, nace “amma kinsan bana using mutane to my advantage ko?”.

Tana shirin bani amsa, muka ji gyaran murya a gefenmu, muka daga kai. Dan halas dinne a tsaye a gefenmu, ni da Janan muka gaida shi ya amsa da murmushi akan fuskarshi from ear to ear, idanunshi a kaina yace “amaryata!”.

Yadda kasan saukar aradu haka naji kalmar, wani irin vile feeling dana ji ya taso min daga can cikin cikina ya makale min a makoshi, yadda kasan zanyi amai. Na daure na hadiye shi, na kakaro murmushi duk da ni a karan kaina ban ji alamun murmushin ba. Nace “Dakta!”.

Ya dan girgiza kai, “gaskiya zamu zauna muyi magana akan wannan sunan Na’ilah dear. Amma wannan zama zamu yi na musamman, ya kike?”.

Na amsa a tausashe, duk da cewa can kasan zuciyata ji nake kamar ana tafasa min ita. Lallai idan aka cigaba da tafiya a haka, akwai matsala.

Ya jima anan muna yar hira dashi, Janan tashi tayi ta bamu waje. Rabin hirar sama-sama muka yi ta saboda hankalina baya tare da ni. Har sai daya kai ga tambayata lafiya? Na mishi karyar kaina ne yake ciwo. Nan da nan ya rikice, ya fara watso min tambayar ina bukatar ganin likita ne? Nace mishi a’ah, nagode.
Ranar da wuri muka tashi saboda ciwon kan da nace mishi ina yi, hasalima a motar shi ya kaini har gaban hostel dinmu, ya hado ni da tulin magunguna da yoghurts. Sai dai duk abinnan da rawar jikin nan da yake yi, ban ji wannan so da kaunar da nake ji ba a duk lokacin da Yaya ya nuna min kulawarshi ba.

Da kyar muka samu suka barmu zamu tafi ranar Laraba, shima sai da Dr. Na Abba ya sanya baki sannan.

Ranar larabar, da kanshi ya kaini har tasha inda zamu hau mota, muna zuwa muka hadu da Janan itama zuwanta kenan.
Muka yi sallama da Dakta, ya hada ni da dubu ashirin, goma muyi kudin mota, goma kuma in ba maijego ta sai wa yara kwalli. Da kyar ma dai na amshi kudin sai daya fara nuna alamun bacin ranshi sannan na amsa na mishi godiya. Muka hau mota muka tafi.

Motarmu ta samu matsala can wajejen Hadejia, gyaran da aka tsaya akan yi yasa bamu isa cikin garin Gashua ba sai karfe tara na dare. Yaya Mudatthir ne da kanshi yaje ya dauko mu daga tasha kamar yadda ya saba a yawancin lokuta. A gidan Malam muka sauka.

A gurguje muka yi wanka muka dan ci abinda aka ajiye mana, daga haka muka bi lafiyar katifa.

Washegari muka yiwa gidan suna tsinke. Yara sun ci sunan Malam da sunan Mahaifin Sailuba din.
Yinin nan cur haka muka yi shi cikin kujiba-kujiba, da kai da kawowa. Mutane ne mu na dangi, wadanda suke da son zumunci da karah. Taron da sunan Sailuba yayi, da irin alkhairan da suka samu ita da ‘ya’yanta kadai ya isa ya tabbatar maka da hakan. A gidanta muka kwana ranar, saboda bayan watsewar yan taron suna, mun zauna gyara mata gidan har zuwa tsakiyar dare. Sai hakura ma muka yi muka bar wasu ayyukan zuwa washegari.

             *☆⋆30⋆☆*

Dogon salatin da Fatsu ta ja ne ya tashe ni daga dan barcin daya fara daukata. Sai da daren nan muka dawo daga gidan sunan, bayan mun ci abinci mun dan kimtsa, muka yi sallah. Muna gamawa Janan ta fita waje inda Fatsu take zaune tana sak’arta, ni kuwa na kwanta akan abin sallar muna waya da ango na to be, wanda bamu jima akan wayar ba muka yi sallama saboda ciwon kai, gajiya, da barci da suka lullube ni (don dai kawai ya kyale ni). Ban san ma barci ya daukeni ba sai da naji wannan salati.

Na zabura nayi waje a sukwane, dankwali a hannu. A tsakar gida na samesu zaune akan tabarma, hasken wuta da aka kawo da yammacin nan ya haskake wajen. Na kallesu a rikice, nace “lafiya, me yake faruwa ne?!”.

Fatsu da take tafa hannuwa, cikin salati har yanzu ta kalleni kamar na bullo wasu kawuna daga jikina. Na bisu da kallo ita da Janan cike da mamaki.

Sai data gama salatinta da sallallami sannan ta dakata, ta kama haba tana girgiza kai, tace “oh ni jikar su! Na’ilah wace irin shiririta ce nake ji haka? Kanki daya kuwa?”.

Na fara raba kallo tsakaninta da Janan, fuska na bayyana tsananin mamaki da nake ciki. Nace “wai me yake faruwa ne? Kin sanya ni a duhu!”.

Ta min dakuwa da hannuwanta biyu, “amshi nan ja’irar kawai! Ke dai wallahi baki ji dadin halinki ba. Dama wannan dan banzan ra’ayin rikau din naki yana nan? Nayi zaton duk yarinta ce ta janyo haka. To wallahi bari kiji, ba dani za ayi wannan haukan ba. Ina Yayan naki yake ne? Bari yanzu a kira min shi yazo!”.

Ta fara neman wayarta tana cigaba da mitar dana kasa fahimtar abinda take cewa.
Na daura dankwalina tare da zama a gefen Janan da tayi tsumu-tsumu.
Nace “wai ni akan menene kike ta wannan fada ne kam, Fatsu na?”.

Ta hararoni da duka idanuwanta, dama gasu tubarkallah, manya ne. Tace “gidanku nace! Wato ma baki san akan menene nake miki magana bane? To akan wannan yaro Yayan wannan yarinya da yake nemanki ne, kika badawa idanunki toka wai ke baki auren mai mata. Ba’a auren aka auri uwaki? Ko a gidanku don iyayenki mata nawa ne a ciki? To bari kiji in gaya miki, tun ma kafin tafiya tayi nisa, ki sallami wannan dan dukurkushin yaron da yazo nan. Ni dama tunda na ganshi naji raina bai kwanta dashi ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button