A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Lokacin dana fito waje ban ga kowa ba, da alamu a can wajen gate ya tsaya, don haka na fara kai kayan hannuna wajen da zamu zauna na ajiye su, sannan na taka a hankali zuwa wajen gate din. Idan wani ya kalleni a lokacin, nasan babu bata lokaci zai ce tafiyar yanga ce nake yi, sai dai a zahirin gaskiya, tsananin fargaba da tsoro ne suka sa nake tafiya kamar wadda take jan kafarta. Ban san dalilin wannan sudden tsoro da naji ya dirar min ba, amma nafi danganta hakan da cewa kila saboda kawai haduwarmu ta farko kenan yau.

Na fita daga gate din, idanuwana suka fara karade ilahirin wajen da kallo, ina duba gefena na dama, na hango shi. Jingine da motar rav4 baka kirin, sanye yake da wata jikakkiyyar danyar shaddar getzner ruwan kasa mai haske, ta sha dinkin surfani na zare shima ruwan kasa amma mai duhu sosai, takalmin kafarshi shima ruwan kasar ne irin flats dinnan na maza, ko ba’a fada maka ba kasan ba karamin kudi da daraja zasu yi ba. Daga inda nake, babu abinda zan iya karaswa game da features dinshi, kawai dai nasan dogo ne, ya danyi min nisa, ban hangi komi a fuskarshi ba, musamman da yake a daidai wannan lokacin ya nutsa wayar tashi cikin wayar hannunshi. Sai hular kanshi kawai.

Na samu kaina da takawa a hankali zuwa inda yake, kaina a kasa ban iya dagowa na kalleshi ba saboda wani irin nauyinshi da naji ya dirar min, amma duk da kan nawa a kasa yake, ina jin zafin kallonshi a cikin jikina. Sai dana fara ganin kyawawan jerin dogaye kuma zara-zaran yatsun kafarshi da suka yi matukar kyawu cikin kyakkyawan takalmin kafarshi, sannan na iya daga kaina a hankali.

‘Assalamu Alaik…”, sallamar da nayi niyar yi mishi, ta makale a makoshina lokacin da na dago kai a lokacin, muka hada idanu hur-hudu dashi.
Fuskarshi bata nuna mamaki, al’ajabi ko rikicewar tunani kamar yadda na tabbatar suna zane akan fuskata ba baro-baro. A tsaye take kyam, maimakon hakan ma, sai wani tattausan murmushi daya bayyana akan fatar bakinshi.
Yace “wa alaikumussalam wa rahmatullah… Har kin fito?”.

Na tsinci kaina da karkata kaina gefe guda cikin tsananin mamaki, can kasan zuciyata kuma ina maimaita kalmar ‘har kin fito?’, ko me yake nufi da hakan?.

Na dan duka cike da girmamawa nace “Yaya Bilal ina yini?”. Gabadayan idanunshi fuskata suke karewa kaina kallo kamar yau ya taba ganina, yace “lafiya lau Na’ilah! Ya kike?”.
Na gyada kai kawai, zuciyata cike da tambayoyi, yayin da a gefe guda kuma naci gaba da dube-dube ko zan hango Muhammad. Ya nake ganin kamar mu kadai ne a gaban hostel din? Ko kuma bai zo ba yace min yazo?.

Na furta tambayar da take ta ci min rai tunda naci karo da Yaya ne, nace “ko kazo wajen wata ne anan ko wani?”, a raina nace ko dai wani auren yake nema ne? Na danyi shivering lokacin da tunanin abinda hakan yake nufi ya darsu a cikin raina.

Ya cigaba da jefa min irin wannan kallo da tunda muka hadu dashi yake jefa min, yana kuma gyada kai a hankali, “wata”.
Na dan zare ido cikin mamaki, kafin nayi kokarin maida mamakina na kulle, sai anjima Janan zata sha labari, nace “uhmm, to. Dama nima akwai wanda na fito gani ne dama, tunda bai zo ba kuma bari in koma, ka samu wadda kazo ganinta ne ko kuma kana bukatar in dubo maka ita ne?”.

Idanuwanshi na fitar da wasu alamu, awe and mischief, yace “a’ah, no need. Nagode. Na ganta ai, gata nan a gabana!”.
Na dan juya bayana cikin tunanin in hadu da wadda take nufi din, sai naga wayam. Na girgiza kai kamar wadda take kokarin shaking din wani feeling, gabadaya abinda yake faruwa yanzu yana da matukar daure kai, na kasa banbance tsakanin karya da gaskiya. Ina bukatar in ganni a cikin dakina, in kwanta akan katifa inyi tunanin abinda yake faruwa.

Na gyada kai a hankali, a hankalin dai nace “to shikenan, zan koma ciki ni, a gaida gida”. Kafin ma ya samu damar daga baki ya maido min amsa, maybe juya da sauri na daga kafata na fara tafiya.
Yace “Na’ilah, Muhammad ne fa!”.

Naji na tsaya cak, kamar wadda aka kafe. A hankali na juya, zuciyata tana bugu da karfin masifa, cikin idanunshi nake kallo directly, ina laluben wani alamu da zai nuna wasa yake yi a cikin idanun nashi. Tunani nake, ta yaya aka yi yasan zance na da Muhammad? Ko dai yana daga cikin abokanshi ne? Haba, babu mamaki. Kila ma Muhammad din abokinshi ne, kila shi yasa zai biyo shi su zo tare ko. Na dauke idanuna daga kanshi zuwa cikin motarshi, so nake inga ko akwai alamun mutum a ciki, amma duhun gilasan motar ya hana in hango komi.

Kallon-kallo muka fara yi dashi, ganin bashi da niyar yi mun karin bayani akan wannan katoton al’amari, yasa ni na bude baki kamar wadda take tsoron magana, nace mishi “a ina kasan Muhammad? Ka san shi ne?”.

Akwai wani nag feeling da yake damuna, daga can kasan zuciyata, wani bangarene yake jefo min tambayar, anya? Amma nake danne shi tun karfina, babu wata anya ko tantama, babu abinda yake faruwa. Yaya Bilal ba wani bane face aboki, ko kuma wani daya san zancena da Muhammad, and nothing more!.

Maimakon ya bani amsar tambayar daya min, sai ya daga kafa ya fara takowa a hankali har ya iso daf dani, ni kuma saboda tsabar rikici, na rasa ta yaya zan iya daga kafata inyi baya duk da cewa mun danyi kusanci dashi. A hakan ina iya shakar kamshin turaren daya fesa, kamar tufafin na nutsa a fuskata.

Ya daga yatsarshi manuniya yana nuna saitin kirjinshi, yace “ni nan, Na’ilah, nine dai Muhammad din da kike jira, Muhammad naki, wanda zai so ya ganki!”.

Na kura mishi idanu kawai, idan banda bugun zuciyata babu abinda ya canza daga yanayin motsin jikina. Kila ma sandarewa nayi a tsaye ban sani ba. Ban san me yasa Yaya Bilal zai ji bukatar yayi min irin wannan wasan ba, halayenshi na kamewa da rashin son wasa yasa kwata-kwata na kasa yarda da cewa tsokana ce kawai kamar yadda nake nanatawa kaina domin karyata abinda zuciyata take fada min tunda na bayyana a gaban Yaya Bilal yanzu.

Allah kadai yasan iya lokacin dana dauka a haka, kawai ina kallonshi kamar wata bakuwar halitta. Na rasa gane a duniyar da nake, shin duniyar mafarki ce ko kuma ta gaske?.

Na samu kuzarin daga baki da kyar, bayan dogon lokacin nan, nace “wane Muhammad kake magana akai, Yaya?”.

Ya saka hannu cikin aljihun rigarshi, ni kuma kamar sakara na bi hannun nashi da kallo har ya ciro wata kirar iPhone, fara kal da ita. Ina kallo yayi unlocking dinta ya fara danne-danne, ba’a dauki lokaci ba wayata ta hau kara da vibrating a hannuna. Sunan Muhammad ya fito baro-baro a jiki, yayin da a gefe guda kuma Yaya yake nuno min wayar hannunshi fuskata. Lambar wayata ce itama gata nan, da sunan ‘baby na’ a jiki, ga kuma hotona akai.

Yace “ko baki yarda da cewa nine Muhammad ba? Kina bukatar wata shaida ne daban?”.

Na rikice, na rasa abinda zan tunana a cikin raina, me ke faruwa ne wai?!. Mafarki nake yi ne? Ko kuma kwalwata ta fara samun matsala ne? Ko kuma kwalwar Yaya Bilal din ce ta samu matsala?”.

Kamar wata mahaukaciya sabon kamu, haka na fara ja da baya ina girgiza kaina, komi juya min yake yi, shi kanshi Yayan dake gabana bana ganinshi sosai. Da alamun hawaye ne suka ciko min idanu, naga lokacin da Yaya ya fara biyo ni shima, tun yana tafiya a hankali har ya daga kafa sosai ya tadda ni, ya kai hannu da niyar kamo ni yana mai ambatar sunana, “baby na!!”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button