A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Duk muka gaida su cikin girmamawa suka amsa. Yaya Bilal ne yace “ina Yaya?”.
Firdausi ta tashi taje ta kirata, tare suka fito da ita, ta samu kujera dan nesa dasu kadan ta zauna. Suka dan zame daga kujerar suka gaida ta, ta amsa cikin fara’a, bayan sun gaisa suka ce mata wucewa Zaria zasu yi yanzu, tace “ba zaku hakura ku kwana ba ku kuwa? Dare ya fara yi, karfe tara fa!”.
Yaya Jameel yace “ai babu komi Yaya, in shaa Allah zamu isa lafiya, nan ne da Zaria fa”.
Tace “to shikenan ai, Allah ya tsare ya kuma kiyaye hanya. Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwa data iyali”. Duk suka amsa cike da jin dadi, suka mata sallama suka bar falon muma muna musu Allah kiyaye.

Suna tafiya muma duk muka tashi. Dakin mata muka wuce muka yi shirin kwanciya. Kananan kadajen kwatako guda uku ne a dakin, sai spare din katifa, ita nake shimfidawa ina kwanciya akai. Ni kam ina kwanciya na rufa da bargo har ka a kaina, ina jinsu har lokacin suna tafka mahawararsu naki motsi. Damuwar cikina na ma ta ishe ni. Shirun Muhammad ya tsorata ni, ko dai shima irin na Umar zai min??!.

*

Kwana biyu hidindimun sallah sun riga sun wuce, amma banda gidan su Janan. Har yau wannan gida a cike da iyali yake yini. Yau Assabar, kwana biyar da gama sallah kenan, gobe kuma muke shirin komawa Zaria. Har yau shiru babu labarin Muhammad, nayi text har na rasa abinda zan rubuta tunda wayar bata shiga, ina cikin damuwa. Wani laifi na mishi dana cancanci wannan hukunci haka?
Yau tare muka wuni da iyalan Yaya Hafiz, sai yau suka zo tasu barka da sallah din. Matarshi mace ce mai mutunci da sanin yakamata, haka ma ‘ya’yansu masu shiga rai.
Da yamma da kanta ta saka mu a mota dasu Harira muka shiga kasuwa tayi musu sayayyar komawa makaranta. A makarantar yanmata ta kwana ta FGGC Munjibir suke. Muma sai gamu mun shigo cikin sayayyar. Muna dawowa suka mana sallama suka tafi.

Washegari muma muka yi sallama da su Ummah, suma su Firdausi da safe aka tafi aka kaisu tasu makarantar. Mun fito daga dakin Baban Yara, mutum mai tsananin mutunci da kirki, yana ta mana addu’o’i da fatan alkhairi, muka samu su Ummah a falo. Tuni an fitar mana da kayanmu waje, nan muka musu sallama, har waje suka raka mu suma. Direban da zai kaimu yana tsaye a jikin motar gidan, yana ganin fitowarmu ya shiga ya tayar. Muka sake sallama dasu Ummah muka shige motar, direba ya ja muka fita daga gidan muka dau hanyar Zaria.

☆⋆20⋆☆

Tun da asubahi naji wayata tana kara babu kakkautawa, washegarin ranar da muka dawo kenan wadda ta kama litinin. Ko a cikin nisan duniyar mafarki, nasan kalar ringtone din, na kuma san ko waye mai kiran tun ma kafin in duba. Saboda haka duk da a cikin magagin barci nake, ban kasa rarumar wayata ba na latsa tare da kaita saitin kunnena na fara watsowa Muhammad tambayoyin da suka jima suna susar bangon zuciyata:
“Muhammad! Lafiya dai ko? Kayi rashin lafiya ne? Accident kuka yi a hanyarku ta dawowa daga Benin? Ko kuma wayarka aka sace maka ko ta lalace? Kayi welcome back ne? Ko kuma ka fara mantawa da ni ne?… Muhammad?!”. Na saurara da tambayoyin da nake jera mishi sakamakon jin shiru da nayi ta daya bangaren da yake.

Sai daya ji na saurara sannan naji ya saki murmushi mai sauti, yace “naji dadi da kika damu dani har haka baby na… Sannan na farko babu abinda ya sameni, waya ta bata lalace ba, sannan lafiyata kalau kamar dai yadda kike ji na!”.

Na hade fuska tamkar ina gabanshi, “shine kuma sati biyu cur ka dauke min wuta babu wani bayani. Kana ganin jerin texts din dana dinga turo maka a cikin wadannan kwanakin kuwa?”.
Yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, can kuma yace “kiyi hakuri, ina da dalili!”.

Duk wani haushi da takaicin dana dinga tarawa ina makalewa a cikin raina na kwanaki masu dama sai suka zo suka tarar min a lokaci guda. Cikin tafasar zuciya nace “kana da dalili? Wane dalili?”. Yayi shiru. Nan na sake zuwa wuya, nace “kada ka ma damu da yi min wani bayani, na gane. Wato ka gaji kana neman hanyar da zaka bullo ka rabu dani ko? To menene na wani boye-boye da kashe waya? Ka fito kayi rayuwarka yadda kake so, ka fada min cewa ka gama dani, ba damuwa zanyi ba, ba kuma binka zan dinga yi ba, bai kamata ka wahalar min da zuciya ba. Kasan iyaka damuwar dana shiga a cikin yan satikan nan kuwa? Kodayaushe tunanina ya ta’allaka a kanka, gani nake kamar wani mummunan abu ne ya faru da kai, gani nake kamar zan rasa ka har abada! Shine yanzu har kake da bakin dagawa ka fada min wai lafiyarka lau?!”. Na karasa fada cikin dan karajin bacin rai, ban damu da cewa duku-dukun safiya bane, zan iya tashin sauran yan dakinmu. Bacin da raina yayi a lokacin ba karami bane.

Yace “baby…!”, muryarshi na nuna tsantsar nadama da damuwa, har sai dana kusa bude baki a take a lokacin ince mishi koma menene na yafe, amma na cije bakina. Nayi shiru ina jira inji abinda zai ce, amma shiru, daga wannan kalma bai sake maimaita wata ba. Kusan sakanni talatin tsakanin ni da shi babu wanda yake furta uffan, don haka nayi kwafa, nace “tunda haka ne sai anjima idan ka samu bakin magana sai ka kira ni!”. Na kashe wayar nayi jifa da ita can karshen katifata na mike zaune. Tashi nayi na fita naje na dauro alwala, na dawo daki na samu wayata na kara, na duba naga shine kawai na kashe karan wayar na tada sallah ta.

Koda na gama ina ganin yadda take ta haske tana mutuwa alamun ba’a hakura da kiran ba, don haka na tashi na dauki wayar tare da fita waje na amsa saboda kada in damu yan dakin. Na dauka nayi shiru kawai ina sauraron abinda zai ce.

Yace “baby please ki saurareni. Na rantse ba da gangan nayi hakan ba, ba kuma da son raina bane, please!”.
Duk da yadda magiyar ta shige ni, amma sai na dake nace “ina jinka ai”, cikin basarwa.

Yace “ina son ki Na’ilah, fiye da tunaninki wallahi!”.
Maganar tazo min a bazata, don haka na rasa abinda zan ce mishi, jin nayi shiru yasa ya cigaba da maganar shi.
“Tsorata nayi. Ina so in zo in ganki, ina so in bayyana miki ko ni wanene. Sanin cewa muna soyayya dake kuma har mun aminta da juna, amma kuma baki san ko ni din ainihin wanene ba, yana damuna sosai fiye da tunaninki. Saboda haka na fara tunanin sanar dake ko ni wanene, sai dai tsoron in fada mikin nake yi. Baby, ba zan juri kiyi rejecting dina ba don ba zan iya daukar hakan ba. Wadannan tunanika su ne dalilan da yasa na kashe wayata, saboda ina so in lalubar mana mafita daga ni har ke, wadda zata zaunar damu karkashin inuwar aure, ta kuma zaunar mana da soyayyarmu ni da ke”.

Na ajiye wani dogon numfashi, tuni naji zuciyata tayi sanyi, ta kuma yi haske kamar ya sanya soso da sabulu ya wanketa tas! Nace “haba dai, akan wannan ne dama ka tashi hankalinka nima ka tada min nawa?”.
Yace “ba zaki gane bane Baby”.
Nace “kaine dai ka kasa ganewa, kana da wata nakasa ne? Ko kuma kana tunanin baka da kyau ne, don nima ai ba kyawun gareni ba. Rashin aikin yi ne?”. Duk ya amsa min da a’ah, ya kara da cewa, “matsalar ta wuce inda kike tunani, ni dai fatana a duk yanayin dana bayyana a gareki, ki karbeni don Allah!”.

Nace “ni ai na riga dana gama karbarka, wace irin karba kuma kake so inyi maka ne?”.
Yace “dari bisa dari nake so ki karbeni!”.
Nace “tuni ka samu wannan karbuwar, believe me!”.
Yace “zamu gani ne dai, amma yanzu naga lokacin fita zai kure miki kada ki makara. Zan kira ki anjima. I love you!”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button