A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Wasa-wasa fa karamar magana sai ta fara kokarin zama babba. Shi kenan a wannan gidan yanzu babu wadda Yaya yake ganin tsakiyar kanta da gashi sai Raheemah kawai.
Lokacin da girki ya juyo kaina, sai dana kara raina kaina. Ranar Yaya bai shigo gidan ba sai can bayan isha’i. Na mishi sannu da zuwa ya amsa ciki-ciki, ya shige can kuryar daki.
Ban yi fushi ba, na bishi har dakin nace mishi ga abincin shi fa. Sai ce min yayi ai ya koshi.

Nace “ka ci abinci ne a waje ko kuma cikinka ne a cike?”.
Sai ya dago ya kalleni fuskarnan a cune, “to wai idan ma naci abincin ko kuma na kasa ci, menene matsalarki? Cikinki ko nawa?”.

Da yaga nayi shiru ina kallonshi ban ce komi ba, sai ya wawuri towel dinshi ya fada bandaki yana mitar duk na bi na tsangwame shi sai kace wani karamin yaro.

Na zabga uban tagumi har ya fito daga wankan ya sameni a yadda ya barni. Bai ce komi ba, ya fara shafa mai.

Nace mishi “Yaya, ko dai wani abu nayi maka ne? Idan ma haka ne, don Allah kayi hakuri. Ba da sani na nayi hakan ba”.

Murya ciki-ciki yace “to ni nace ne kin min wani abu? Ko kuwa don dai shi mutum bashi da damar yace ya koshi da abinci, sai a hau tuhumar shi. Wai ni karamin yaro ne, iye?”.

Gabadaya sai nake ga kamar Yayan an canza min shi da wani na daban. Wanda ban sani ba, wanda ban san komi nashi ba. Naji kwalla ta fara cika min idanu.

Sai ya dakata da abinda yake yi, ya kama baki yana kallona. Yace “to yanzu kuma me na miki da zaki sanya ni a gaba kina kuka?”. Na girgiza mishi kai alamun babu komi.

Yace “abinci ne dai ko? Bari in zo in ci, shikenan?”.
Na gyada kai ina dan murmushi, ina share kwallar data fara zubar min.

Bayan ya gama, muka rankaya zuwa falo, na zuba mishi abincin. Kadan yaci, hakan bai dameni ba, cin kadan din ai yafi rashin ci gabadaya.

Anan na barsu shi da matan nashi suna shan hirarsu. Har yanzu dai jiya i yau, bata sake zani ba. Ita kanta Ameerah na kula hakan ya dameta, bata fito fili ta fada bane kawai.
Dana koma falon, ban zauna ba, sai na shige can ciki nayi kwanciyata. Har Yayan ya shigo shima, ya gama duk abubuwan da zai yi, ya hayo kan gadon ya kwanta.

Ganin ya juya min baya ba tare da yace komi ba, yasa na gangara zuwa gefen daya kwanta. Nima na kwantar da kaina akan kafadarshi. Daga farko sak yayi kamar wanda lantarki taja, sai kuma ya saki jikinshi. Ana jimawa naji ya zame ya kara matsawa can gefe guda.

Wani irin makaki yazo ya takure min a cikin makoshina, wata kwallar ta sake ciko min idanu. Sai nima na juya mishi baya.

Zuwa can cikin dare na farka, na ganshi zaune a gefen gado, idanunshi kur a kaina kamar wanda yayi nisa cikin dogon tunani. Ban nuna alamun na farka ba, naci gaba da kallonshi ta cikin dan hasken dakin har barci ya sake kwasheni.

                         *☆⋆46⋆☆*

Har na fita daga girki na sake shiga wani, bata canza zani ba tsakanina da Yaya. Hankalina idan yayi dubu to a tashe yake. Wannan shine karo na farko dana taba fuskantar yace baya daga mijin aurena, bana kuma fatan hakan ta kara faruwa koda wasa ne. Yadda yake yi kamar duk duniya babu abinda yaki jinin ya gani kamar ni, shine yafi tayar min da hankali. Nan da nan nayi rama. Yanzu na samu yana cin abincina ba tare da bacin rai ba, sannan yana dawowa da wuri ranar girkina. Daga wannan shikenan, idan ma na samu ya amsa min gaisuwata da sannu, to naci sa’a.

Inda naji dadi daya ne, duk da dai ba abin jin dadi bane, ganin cewa ba ni kadai hakan take faruwa da ita ba, har da Uwargida Ameerah, duk da cewa dai ita yana dan daga mata kafa saboda cikin jikinta, amma dai babu gwara.
Hakan ya tabbatar min da cewa lallai da wata a kasa. Ta fannin addu’a da kula da jiki, ina iyaka kokarina dama, sai kara dagewa da nayi. Takanas na dauki kafa naje har Suleja wajen Malam Ali, da yake ya daina kawo mana rubutun da yake kai mana duk sati. Bayan mun gama gaisawa da mutanen gidan, aka min jagora zuwa inda yake karbar bak’inshi.
Mun jima muna hirar yaushe gamo, daga karshe dai na mike kafa na mishi bayanin abinda yake tafe dani, tun daga ranar da abin ya faru har zuwa yau.

Nan ya bani wasu addu’o’i yace in lazimci yin su, shima kuma yace zai dinga taya mu. Ya kara da cewa “ku matsalar ku ta yan boko, sai ku ce baku yarda da sadaka irin wadda ake rabawa yaranmu suyi ayi yanka da sauransu ba. Ita kuwa sadaka abu ce mai kyau, koda wani abu mummuna bai faru da kai ba, ta kan kiyaye mutum daga munanan abubuwa da dama, haka kuma tana tsare shi daga kambun baka, sihiri da sharrin jinnu. Baka san bakin mutane ba, akwai wasu zababbu a cikinmu, da idan suka yi mana addu’a zaki ga kamar da bakin yan amin suka yi ta, Allah ya karba. Shi yasa muke rarrabawa, saboda bamu san inda albarkar take ba”.

Na gyada kai cikin alamun fahimta, nace “haka ne Malam. Muma din muna kwatanta yin hakan, amma zamu kara zage damtse in Allah ya yarda. Yanzu zan bayar da kudin sadakar kafin in tafi, in yaso sai ayi duk abinda yakamata dai”.

Ya girgiza kai, “kada ki damu ‘yar nan, babu abinda zai gagara da yardar Allah. Yaran nan namu ne, dan abinda ya rage kuma bai fi karfin aljihunmu ba, saboda haka za ayi duk abinda ya dace. Ke din ai diya ce a wajena, jinin Malam Audu tamkar jinina haka na dauke su”.

Nayi murmushi nace “nasan da hakan Malam, amma duba da cewa sadakar tawa ce, me zai hana ka barni in bayar da kaina?”.

Bayan je-ka-dawo dai, dole na sakar mishi, na mishi godiya tare da mishi sallama na tafi. A cikin gida nabi duk iyalan gidan da kyauta har ma da almajiran kafin na fita waje inda Balarabe direban gidanmu yake jirana, yaja muka koma gida.

Da yake aikin safe nake, sai na tashi da wuri tare da turawa Yaya sakon zan zo wajen Malam Ali wanda ya turo min da to kawai.
Akan hanya ya tsaya na sayi fresh fruits da vegetables, duk da ranar ba girkina bace, naji ina marmarin yin salad. Tunda na fara daukar albashina na daina jiran Yaya ya min, ko ya bani wani abu. In dai na ga babu abu kuma ina so ko kuma zanyi amfani dashi ranar girkina, bana kyashin cirewa in saya tunda dai Alhamdulillahi ina dasu, kuma shima Yaya Bilal din baya kyashin bude mana bakin aljihunshi. Wasu lokutan haka kawai zai kirgo kudi ya bamu, baya kuma banbancewa a tsakaninmu, duk da cewa ni ina daukar albashina, Ameerah ma kuma iyayenta na turo mata, amma hakan bai sa ya banbanta mu ba.
Kashi biyu na sanya Balarabe ya sayo komi, daya kawo nace ya dauki kashi daya shima ya kaiwa iyalanshi. Yayi ta godiya har muka karasa gida, ya zagaya da sauri ya bude min murfin motar na fito, ya biyo bayana da ledojin a hannunshi yana kara wata godiyar.
Yan aikin gidan na matukar girmama ni, kamar yadda nima nake girmama su, yawanci ko wani abu ya taso kafin kaji sun nemi Ameerah data kasance Uwargida sau daya sun nemeni sau goma, musamman idan wata bukata ce suke da ita wajen Yaya. Ban taba kyashin isar da sakonsu ba, tunda Allah yasa yana iyaka bakin kokarinshi wajen ganin ya kyautatawa mutane, kuma ya taimaka musu, meye a ciki idan na taimaka mishi ya cigaba da taimaka musu?.
Ranar nan Hasina wadda take mana wanke-wanke da shara, tace tana ta fadawa Raheemah ta taimaka ta yiwa Yaya tunin kudin albashinta, yace zai bata da wuri saboda aikin da za’a yiwa diyarta a hannu, amma har lokacin bai ce komi ba da alama ya manta. Tace ita fa tana zaton kamar bata fada mishi ba, don data sake mata magana sai ta hau ta da fadan wai ta takurawa mijinta. Nace mata kawai zan fada mishi da kaina. Sam ko sun kawo korafi kan wani halin rashin kirki da suka musu, bana biye musu mu ci namansu, yadda bana so ayi gulmata, nima bana yin ta wasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button