A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Ranar nan ina jinsu ita da Raheemah suna gabzawa, ranar Adi tazo gidan ta wuni, a cewarsu itama ta samu wani house of rep dake zaune anan Abujar har an sanya musu ranar aure. Ina tunanin Adin ce ta fada mata kamar ba cikine da Ameerah ba.
Sai gata ta tsareta a kicin, ta kare mata zagi tas, tace “kuma idan karyar cikine zamu zuba ni da mutum anan gidan mu gani. Haba, biri yayi kama da mutum! Ke da kike da ciki, maimakon ki dinga yin kiba ko rama, amma kina nan a yadda kike? To wallahi mu zuba don uban mutum, zamu ga karshen karya!”.

Ta fita daga kicin din ta bar Ameerah tana ihun “tunda ita take bada cikin, ta riga ta san babu shi, ba sai ta fadawa Yayan ba?”.
Ban ce musu komi ba ni kam sai kai dana dinga girgizawa. Su dai suka sani ai.

Ranar assabar a Kaduna na wuni, Yaya zai shigo su gaisa dasu Ummah, don haka nima na biyo shi. A gidan su Ummahn muka fara sauka, duk da sunyi murna da ganina, hakan bai hana su min fadan mai ya kaini fara yawo yanzu ba, jikina har yayi karfin da zan fara yawo ne? Nace musu lafiyata lau, na warke.
Bayan mun gaisa dasu na huta, na tafi gidan Janan. Nan muka wuni muna hira da hirar yaushe gamo.

Lokacin dana mata zancen cikin Ameerah, dariya ta dinga kyalkyalawa har sai data kifa daga kan kujera. Na bita da kallo ina dan murmushi duk da bansan akan meye take dariyar ba. Sai data yi ta isheta, sannan ta dago idanu taf da hawaye don dariya, tace “yanzu kuma Yaya ya yarda da wannan crap din??”.

Nace “me zai hana shi yarda?”.
Tace “haba, tun yaushe suke zarya wajen likitoci ana cewa kwayoyin haihuwarta basu da kwari? Wace kasa ce basu je ba akan wannan matsalar amma magana daya, ba zata iya conceiving ba. Kila dai Yaya mantawa yayi, ko kuma tsabar son yara ne yasa idanunshi suka rufe. Amma daga ma jin labarin da kika bani, ko rantsuwa nayi nasan ba zata taba ci na ba, cikin karya ne!”.

Nayi shiru ina processing abinda tace, daga karshe na daga kafada, nace “kika san ko Allah ne ya dubeta da rahamar shi? Shi ikon Allah ai yawa ne dashi. Idan ma ba hakan bane, wannan matsalarta ce, ina zaune a gefe daya koma menene zai bayyana. Shi ciki ai ba’a boye sa, dole zai fito kowa ya gani”.

Janan ta gyada kai, “haka ne kam. Allah dai ya rufa mana asiri bakidayanmu”. Nace “ameen”.

Da yamma da Yaya ya gama ziyararshi, ya biyo muka juya bayan sun gaisa da Janan da mijinta Almustapha. Ashe har Zaria yaje, sai a hanya yake fada min.
Kafin mu karasa gida sai da muka biya wani fast food joint, ya sai roll cakes, tarkacen hamburger, ice creams dasu chocolate, sakon Ameerah. Muna komawa na kwashi kasona na fada daki saboda girkin Ameerah ne ranar. Sai ya zama wadannan su muka ci abinci matsayin abincin dare, saboda apparently bata da karfin yin girki ranar.
Sai abin yazo ya zama kamar al’ada Yawancin ranakun girkinta sai dai Yaya yayo odar abinci.
Nace mishi me zai sa maimakon yayi ta asarar kudi wajen siyo abinci, mu dinga girka kayanmu duk ranar da taji ba zata iya yin girki ba? Sai cewa yayi idan aka yi hakan, za’a bata mishi tsari da dokar gidanshi. Da na matsa, sai yayi kici-kicin da rai, yace “wai idan ma na batar da kudin, kudina ne ko naki?”.

Mamaki ya kama ni, na kama baki nace “daga maganar gaskiya? To Allah ya baka hakuri!”. Na tashi na koma dakina.
Can kuma sai gashi ya biyo bayana, wai inyi hakuri, kawai yaga yana kokarin dauke mana wahala ne amma kamar bamu gani, maimakon mu mishi godiya, sai mu hau korafi, waye da waye, nan ma dai na kara bashi hakuri aka wuce wajen.

To rayuwar fa kenan, yau dadi, gobe akasinsa.
Kamar yadda duk kokarin mutum wajen kaucewa kaddarar data riga fata, duk gudunka da fata da burinka, baka da wani katabus akan abinda Allah ya kaddara. Shi yasa ita yarda da kaddara take da matukar kyau. Ko babu komi, kowani irin abu ne ya kan zo wa wanda ya yarda babu abinda yake faruwa a doron kasa face da izinin Allah, da sauki.

Gabadaya yinin yau a kasalance nayi shi, tunda na tashi da safiyar yau nake ji na ba daidai ba. Jikina yayi min nauyi, da kyar na dinga gudanar da ayyukan dana saba yi.
Zuwa yamma, abin ya kara tsanani da kamari. Ina zaune ina yin azkar din dana saba yi, idanuna suna likewa saboda wani azababben barci daya mamaye min idanu. Duk yadda naso in daurewa barcin nan, kasawa nayi. Ban san lokacin daya kwasheni ba anan.

Sai gab da magriba na tashi a firgice. Nayi salati ina jan addu’o’i a cikin raina, ban saba barcin yamma ba, kai barcin rana ma gabadaya ban cika yin shi ba, balle na bayan sallar la’asar.
Mutuwar jikina har tafi ta dazu, na lallaba na fada bandaki nayi wanka da ruwan dumi. Kasancewar bana yin sallah, sai na gyada jikina kawai na fito.

Washegari, na shiga gaida Yaya. Yana zaune a falonshi, matan nashi sun zagaye shi yana karin safe. Ameerah da har yanzu ciki bai fara turowa ba, an ci kwalliya ta kece raini, fuskarnan baka ganin komi sai kyallin foundation, concealer da eye shadow.
Raheemah ma taci tata kwalliyar babu laifi.

Na duka a gefenshi na gaida shi, bai ko daga kai ya kalleni ba, ya amsa ciki-ciki kamar wanda aka takurawa, yaci gaba da cin abincinshi. Babu tambayar ‘ya kika tashi’ ko kuma ‘kin tashi lafiya?’. Wasu lokutan ma da yake cikin yanayi mai dadi, ya kan kara da ‘da fatan kinyi mafarkina?’.

Sai ban kawo komi a cikin raina ba, na juya na gaida matan nashi da suma suka amsa ciki-ciki, su dama sun saba, don haka ban damu ba. Yaya ne dai da ba haka ya sabar min ba, duk sai naji abin yayi min wani iri. Amma zata iya yiwuwa ko bai tashi cikin dadin rai bane yau. After all, mu dukanmu mutane ne, we all have our moments.

Ban jima ba, na koma dakina na gama shiryawa nima na tafi asibiti. Aikin safe nake yi wannan satin.

Koda na dawo daga asibitin, kasa zama dam nayi. Jikina tun jiya nan bai dawo daidai ba. Ji na nake yi kawai kamar ba ni ba. Ranar sai dana juya gabadaya tsarin dakina duk don in dan ragewa kaina zaman banza da tunanika marasa amfani.
Har zuwa can yamma ina abu daya, nayi wanka na sanya wata doguwar riga single, na dauki wayata tare da zura takalmi flat a kafata na fita falo.

Raheemah na kicin tana kammala girki, na zauna akan kujera, na dauki remote na kunno wata tasha suna karatun kur’ani. Na kwanatar da kaina akan hannun kujerar ina bin karatun a nutse. A hankali naji nutsuwa ta fara shigata.

Ina nan har Yaya ya dawo daga wajen aiki. Na tashi zaune ina kallonshi cikin murmushi, “Yaya sannu da…”.

Kafin ma in gama mishi sannu da zuwan, ya fada falonshi da sauri. Babu alamun ya kula dani a cikin falon da ya nuna, idan ma ya ganni din, ba karamin kokari yayi wajen share ni ba. Sai na bishi da kallo baki a dage.

Da dare kamar yadda aka saba, na tafi falon Yaya da niyar zuwa yin hirar dare. Suna zaune su duka ukun, Yaya da Raheemah suna hira, Ameerah kuma zaune a gefensu.
Na zauna a kusa da ita na musu sannu, Yaya da Raheemah suka yi shiru da hirar da suke yi suna kallona, babu wanda yace min ci kanki. Kafin suka komawa hirarsu.

Ko minti goma cikakke banyi ba, naji zaman wajen ya isheni. Yadda Yaya yayi kamar babu wata halitta a cikin falon face Raheemah kadai, abin ya sanyayar min da gwiwa. Ita kanta Ameerah din da idan da ne, duk wani motsi da zata yi zai yi ta binta da sannu, yanzu ko yunkurin tsoma baki tayi cikin hirar da suke yi, haka zaka ji yayi duf, sai kallo da zai yi ta binta dashi.
Da abin ya dameni, sai kawai na tashi na musu sai da safe don ba zan iya cigaba da zama a haka ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button