A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Nace “ke dai kawai sai dai muyi fatan Allah ya hada mu dana kwarai ne kawai, amma fa wani gyaran jikinki da wasu karairayar ki, babu abinda zai sa balle ya hana wallahi”.
Tace “gaskiya ne, Allah dai yayi mana zabi mafi alkhairi, ya kuma bamu ikon zama dasu lafiya. Allah yasa mu cike ibadunmu lafiya”.
Nace “ameen”.

Tashi tayi ta shiga kicin tana fadin bari ta duba abinda ta dora akan wuta. Ni kuma na dauki wayata na turawa Yaya da yake kan hanyarshi ta dawowa daga kasar Germany, sakon Allah ya kiyaye hanya. Shekara guda kenan da aka maida shi Manajan gidan jaridar Daily Trust. Alhamdulillah, budi ta ko’ina muke samu. Tuni na haura matsayin da zan jira ayi min wata hidima komi girmanta kuwa, sai dai in yiwa wasu. Ko babu aikin da nake yi, Yaya Bilal ya kasance mijine mai tsananin kula da duk wata hidima ta iyalinshi.

Janan ta fito da kwaton bowl a hannunta, tun kafin ta karaso kamshin daddawa da tafarnuwa ya min iso, naja miyau na hadiya mukut!. Cikin da nake dauke dashi mai kimanin wata uku, ya sanya min tsananin son kwadayi da son ciye-ciye.
Ta ajiye farfesun kayan ciki dana sameta tana dafawa a gabana. Na shaki numfashi, dadin kamshin yana ratsa min har cikin kwanyata.

Nace “kyawunta abinnan ace har ‘yar uwata zata samu”.
Janan ta zauna a kusa dani tana zuba farfesun a cikin madaidatan plates, “ai fa, komi ‘yar uwa, ‘yar uwa. Na ajiye mata nata a microwave, don nasan kalar mitar da zan sha idan ban ajiye mata ba”.
Nayi dariya, “kin kyautawa kanki kuwa”, na karbi plate din data miko min na fara ci.

Ina cikin ci wayata tayi kara, hoton Hajara da aka dauka rungume da Muhaaseen ya bayyana, nayi murmushi, “kinga yar halas din ba”, na dauka.
Fada min tayi ta tashi daga wajen aiki, zata biya makaranta ta dauko yara sai ta biyo nan ta daukeni, nace mata sai tazo.
Muna yan hirarrakinmu, har suka iso gabadayansu. Yaran suka zo suka rungume ni, na dauki Suhaima da take rarrafe na dora ta akan cinyata.
Janan ta zubowa Hajara da sauran yaran, suka fara ci. Yaranta sun riga su Muhaaseen samun hutu, suna Kaduna.

Suna gamawa muka fara haramar tafiya, Al-Qaseem da muke kira Papa, yarona mai kimanin shekaru uku da rabi, ya dauki Suhaima ya fita waje da sauri yana cewa bari ya riga mu. Duk muka rufa mishi baya muna dariya.
Janan ta raka mu har gaban motar Hajara, dankareriyar Maybach GLS 650, shigen tawa ce. Ba’a jima ba da Yaya ya canza mana su, ni tawa ruwan maroon ce mai duhu, tata kuma ruwan hoda mai haske. Na shiga gidan gaba, ina zama Papa ya dora min Suhaima akan cinya data mishi tumbud’i, yana yatsinar fuska yana mitar shi fa shiyasa baya son daukarta. Ni da Hajara kam dariya muke ta mishi. Janan ta karbi tissue a hannun Hajara data yago, ta goge mishi gefen riga. Daga nan dai muka daga mata hannu muka harba kan titi.

Muna isa gida, muka tura yaran daki akan su je su shirya kafin lokacin zuwa islamiya yayi. Mu kam shirin tarbar maigida zamu shiga yi.
Hajara tace “Yaya, idan mun gama zan nuna miki wasu sababbin kayan daki, kila wadannan suyi naga suna da kyau”.
Nace “to shikenan”.

Bikin Maryam yana ta matsowa, wannan shekarar zata gama degree dinta akan chemistry a ABU, tana gamawa kuma za ayi aurenta ba da jimawa ba. Ni da Yaya Mudatthir aka dorawa alhakin kayan dakinta, hakan bai dameni ba ko kadan, hasalima naji dadin hakan. Ko babu komi an nuna mana cewa muna da wani gurbi a wajensu.
Shi yasa ni kuma na daurawa Hajara aikin nema mana kayan daki har ma da wasu daga na kicin, masu kyau na garari, tunda fanninta ne. Tana aiki da wani babban kamfani ne anan Abujar, sukan zana abubuwa iri-iri, kayan daki ne, gidaje ne, makarantu, masana’antu, da sauransu. Akwai ainihin kamfaninsu dake Saudi-Arabia, shi yake kera ire-iren abubuwan da suka zana din, a sayar.

Tuni magriba ta fara kawo kai lokacin da muka gama. Muka yi wanka, muka cancada kwalliya kamar masu zuwa fashion show. Dole Hajara ta koya min zana gira da yafa eyeshadow, haka nan nake shafawa duk da ba ko wani lokaci ba. Amma kuma duk lokacin dana yi din na kan sha yabo da kirari wajen wanda aka yi domin shi din. Suma yaran muka shirya su bayan sun dawo daga makaranta. Daga nan zuwa kowane lokaci Yaya zai iya dirowa, tun dazu Balarabe ya tafi dauko shi.
Muka zauna akan manya-manyan leather seats din dake cikin falon da muka canza, muna duba kayan dakin. Har dai muka tsaya akan wasu jajaye da farare da suka mana, tace zata saka su cikin oda, nace mata to. Daga nan muka koma dakinmu muka yi sallah. Tun kafin in gama na fara jiyo hayaniyar yara, hakan ya tabbatar min da cewa maigidan ya karaso kenan. Banyi gaggawar fita ba sanin cewa ba nice da girki ba. Nasan zai fara yin wanka ne kafin ya wuce masallaci sallah.
Ina dakin a zaune ina karatun Kur’ani ya shigo, na mishi sannu da zuwa muka gaisa, ya wuce masallaci.

Sai bayan sallar isha’i muka hadu gabadayanmu a falonshi muka ci abinci. Ni da Hajara muka fara jidar kayan muna maidawa kicin bayan mun gama, Papa da Muahaaseen kuma suka tafi daukowa Abbansu takardunsu na makaranta ya gani.

Na zauna a gefen Papa da yake gaban Abbansu yana duba nashi takardun cikin gyada kai, da yake yaron tubarkallah akwai ilimi, mawuyaci ne suyi jarabawa yaci kasa da casa’in a cikin dari.
Bayan ya gama dubawa, ya janyo yaron cikin jikinshi yana shafa kanshi, yace “good boy, kayi kokari sosai Baba na. A cigaba da kokari ko?”.
Yaron ya gyada kai cikin murmushi, yace “that’s my boy”, tare da bashi peck a kumatu.

Yaron ya wani yatsina fuska, Yayan yana dagawa yasa bayan hannu yana goge kumatunshi, yace “ewww Abba!”. Ni dasu Yayan me zamu yi idan ba dariya ba? Yaya ya kama kumatunshi duka biyun yana ja, yace “Babana har yanzu baka daina jin kyankyami na bane?”.
Na shafa kan yaron ina murmushi, haka Allah ya halicce shi da son jiki da kyankyami.

Ya maida hankalinshi ga Muhaaseen da tayi shiru a zaune tana kallonsu cikin dan murmushi. Ita kuma kunya da kawaici ne da ita kamar me, abinda wani lokacin nake cewa mai sunanta ta biyo.
Yace “Maama fa, ya ake ciki ne?”.

Awa daya da kusan rabi yana ta hira ne da yaran nashi, ya dauko tsarabar su ya kunce musu, kowa aka bashi nashi. Daga nan ne suka mana sai da safe, kowa ya nufi dakinshi. Suhaima kuwa tana kwance akan cinyar Yayan tana barci.

Bayan tafiyar su ne muma aka kunce mana tamu tsarabar. Kaya ne na ado iri-iri, dogayen riguna, takalma flats da heels da kayan su jikkuna masu kyau da burgewa, turaruka da sauran tarkace. Muka hau mishi godiya sosai, Hajara tace “Abban Maama mu kam kana shagawaba mu da yawa wallahi, mun gode, Allah ya saka da alkhairi Ya kara budi mai amfani”.

Yace “ai ban muku komi ba cikin abubuwan da kuke yi min, hadin kanku ma kadai ya isheni, balle kuma tallafawarku a gareni da kulawar da kuke bani. Allah dai yayi muku albarka, Allah ya kara hade min kanku gabadaya”.
Duk muka amsa da “ameen”, a tare.
Abinda ke kara mana kwarin gwiwar kyautata mishi kenan, Yaya baya kyashin yabonmu a ko’ina ne, a kuma gaban ko waye sai dai idan bamu yi abinda ya burge shi ba.

Bayan mun zauna, yace “yaushe yara zasu samu hutun makaranta?”.
Nace “nan da sati hudu muke sa rai”.
Yace “to ku shirya, umara zamu je gabadaya har yaran”.
Muka kalli juna ni da Hajara, kafin muka saki ihun murna muka dira jikinshi muna ihun murna da godiya. Aikin hajji kam mun je shi babu iyaka, mun fara zuwa ni da Yaya, muka koma har Hajara. Haka su Malam ma shekarar data wuce suka je suka sauke. Shi dama Baba yaje ya kai matanshi.
Ranar har wajen karfe sha daya da rabi muna falon ana ta hirar yaushe gamo, kafin na mike tsaye ina musu sallama.
Hajara ta kwashe kayanta ta kai daki bayan ta kai Suhaima ta kwantar a dakin Yaya, Yaya ya taya ni kwaso kayana muka kai dakina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button