A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Muka karasa wajen da take, daidai lokacin da diyarsu mai kimanin shekaru biyar, Ruqayyah wadda suke kira Mimah, ta fito daga daya gefen mai zaman banza dauke da jakarta da lunch box.
A lokaci daya muka gaidata ni da Janan, ta amsa tana kama hannun Mimah da take kokarin isowa gareme, jininmu ya hadu da ita sosai. Halin mahaifiyarta na shiga part dinta ta rufe ta kuma hanata fitowa yasa bamu haduwa da ita sosai, sai lokaci zuwa lokaci.
Tana gamawa amsawa ta latsa key tasa motarta a lock, taja hannun diyarta suka tafi.

Duk da haka sai da Mimah ta juyo tana daga mana hannu, mu duka muka daga mata hannun muna murmushi har suka shige part dinsu, ta rufo. Ni da Janan muka kalli juna muka sake yin murmushi, kafin muma muka shige nasu part din.

Adi, da Haleemo suna kicin lokacin da muka shiga, Raheemah kuma tana zaune tana sana’ar kallo, ban san ina Salama ta shiga ba tunda bamu ganta ba. Mu dai muka musu sannu, muka shige daki ba tare da mun damu da kallon banza da aka bimu dashi ba.

Bayan la’asar muka fita waje ni da Janan muka sayo fruits a bakin titi. Muka zo muka hada fruits salad da kayan shan ruwa. Muna cikin soya yam balls, Salama ta shigo kicin din. Babu wanda ta yiwa ko sannu a cikinmu, ta dauki plate kawai sai ganin tana zuba yam balls din a plate din muka yi. Ta debi iya wanda zata dauka, ta fita daga kicin din. Duk kallo muka bita dashi har ta fita. Maimakon abin ya bani haushi, sai ya ma bani dariya. Na girgiza kai kawai, a zuciyata ina furta ‘Allah ya kyauta!’.

Sai bayan mun sha ruwa sannan na kunna wayata. Messages, missed calls, voice mails, messages din whatsapp da voice notes babu iyaka daga Umar, duk abu daya yake tambaya, ‘don Allah in daga wayata’, na harari wayar tawa kamar shine a gabana, in daga wayata in ce mishi me?!

 *☆⋆09⋆☆*

Har washegari Umar bai daina kiran wayata ba, nima kuma ban daga ba. Zuwa lokacin missed calls dinshi sun fi a kirga.
Da safe ina browsing din wasu procedures a wayata lokacin da nake jiran Jan ta fito daga wanka, don na rigata shiryawa. Wata bakuwar lamba ta min sallama ta whatsapp. Daga farko nayi zaton ko Umar ne, sai dana bi ta cikin description dinshi sannan naga kwata-kwata komi nashi bai yi shige da na Umar ba. Na farko dai Umar daya zauna ya zubo miki layi biyu a rubuce, ya gwammace kuyi awa biyu akan waya kuna hira. Shi yasa yanzun haka voice notes dinshi ne suka cika min waya.
Kamar wanda yake jira, ina amsawa ana maido da amsar ya nake? Fatan na tashi lafiya?.
Nace lafiya lau, ko wanene yake magana?
Sai aka turo, ‘ba lallai ki sanni ba gaskiya, amma ni na sanki farin sani. Ba tun yau ba nake ta so in miki magana, sai yau Allah ya yarda. Sunana Muhammad’.

Na rubuta, ‘to Malam Muhammad ko zaka iya sanar dani inda ka sanni? Don bana tunanin nasan wani Muhammad anan inda nake’.
Yace ‘in shaa Allah zaki sanni nan ba da jimawa ba, na miki wannan alkawarin. Magana ta gaskiya yanzu bana gari shi yasa, amma da zarar na shigo zan zo in same ki, nasan lokacin kuna shika’.

Na daga gira cikin mamaki, ta alama mutumin nan ya sanni fiye da yadda nayi tsammani. Nace ‘ta yaya aka yi kasan haka?’, ina tura mishi amsar Jan tana fitowa daga bandaki, na kashe datar na sauka daga kan WhatsApp din ina kallonta. Zama tayi ta gama shirinta a nutse. Tana gamawa muka ci pancake da muka yi da ruwan shayi, da muka gama muka dauki sauran da muka yi muka kai kicin muka wuce.

*

Yau sai yamma likis muka dawo daga asibitin. Da yake yau a bakin titi muka sauka, akan kafafunmu muka gangaro zuwa gidan Yaya.
A kofar gidan, Umar ne tsaye ya jingina da motar shi. Na danyi turus da ganinshi, gabana yana faduwa, kafin na dake muka cigaba da tafiya.
Da sauri ya tari gabanmu, “Na’ilah, sweetie, don Allah ki dakata, don Allah ki saurareni, wallahi na tuba, don Allah….”.

Jan ta kalleni, yadda na hade fuska kamar naga wani dan aiken mutuwata, yasa ta fara raba idanu tsakanina da Umar. Yaci gaba da zuba magiya yayin da na zagaya ta gefenshi na tunkari kofar gidan gadan-gadan. Janan ta riko hannuna, na juya ina kallonta, tace “meye haka Na’ilah? Ban san ki da wulakanta mutane ba sam”.
Nace “kiyi shiru Janan, baki san abinda ya faru ba, don haka kada kiyi kokarin shiga cikin wannan fadan”.
Umar yayi tsulum da bakinshi, “don Allah ki saurareni Sweetie, please…”.

Na kare mishi kallo, duk da kokarin dannewa da nake yi, da nuna kamar ban damu ba, amma nayi kewar shi. Kwana daya da yini daya kacal, amma nayi kewarshi.
Na kalli Jan data tsaya tana kallonmu, nace “ki wuce abinki kawai, zan shigo in same ki”. Babu musu ta shige cikin gidan ta barmu a tsaye.
Na harde hannu a kirji ina kallonshi, “me? Yanzu kuma mai kake bukata ne? Kana so mu kebe wani waje ne ko kuma ka kama mana daki ne a hotel?”.

Ya dafe kai, “Subhanallah, haba Na’ilah me ya kawo wannan maganar kuma? Kuskure ne nasan dana riga na tafka shi, amma ina neman afuwarki don Allah. Wallahi ban san abinda ya hau kaina ba, ok, na sani. Gajen hakuri ne irin nawa, amma wallahi na gane kuskurena, ba zan kara ba, don Allah ki bani dama Na’ilah, na miki alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba”.
Naji zuciyata ta fara yin sanyi da jin hakan, nace “how sure are you? Ta yaya zaka tabbatar da cewa nan gaba ba zaka sake tare ni a cikin mota, trying to touch me inappropriate ba?”.

Ya hau girgiza kai da sauri, “I assure you hakan ba zata sake faruwa ba, na miki alkawarin ba zan kara taba ki ba tare da izinin ki ba har auren mu!”.
Nace “idan kuma hakan ya sake faruwa fa?”.
Yayi shiru yana kallona, nace “magana daya ce Umar, idan abu makamancin haka ya sake faruwa, we are over! Dama kasan hakan ta taba faruwa, yazo ya sake faruwa yanzu, to babu na uku. Idan kuma muka rabu, mun rabu kenan, ka yarda?”.
Ya gyada kai, “it’s not as if zan sake maimaitawa, but yeah, na yarda. Fushin ki ba abu bane da zan yi marmarin sake gani ba koda wasa. Yanzu dai kin yafe min?”.
Nayi jim ina tunani, na yafe mishi? Ya riga yayi convincing dina, kuma yayi alkawarin hakan ba zata kara faruwa ba, saboda haka meye aibun yafe mishi a ciki? Don haka na gyada kaina, ya saki murmushi a tausashe wanda ya sanya ni sakin murmushin nima, “oh thank God! Wallahi baki ji yadda na damu ba, God, I miss you wallahi”.
Nayi murmushi kawai, yayin da naji wani sanyi yana kwaranya a cikin raina. Ban sani ba, na yafe mishi din da nayi ne, ko kuma na dawowa gareni da yayi bane. Kafin in sake daga baki inyi magana, muka ji kiran sallah, ya kalleni yana murmushi, “bari in wuce masallaci to, zan kira ki zuwa anjima”.
Na gyada mishi kai tare da shigewa gida.

Bayan mun ci abincin dare a dakin Janan, ta zauna a gefen katifa suna waya da Al-Mustapha saurayinta, ni kuma na shiga whatsapp chatting. Sakon mutumin nan na dazu shine abinda na fara gani, ni na ma manta dashi.
Amsar tambayar dazu dana mishi da safe ce ya turo min, “kamar yadda na fada miki, na san ki farin sani. Kuma ina matukar kula da lamuran wadanda suke very special a gareni, don haka ba wani abin mamaki bane”.

Na maida mishi da amsar ‘haba? Ta yaya aka yi na zama very special a gare ka?’.
Babu jimawa sai ga reply ya shigo, ‘oh, you are very very special in fact! Idan nace zan miki bayani zamu jima a haka, to cut it short, ina jin ki a cikin raina fiye da yadda kike tsammani’.
Haka kawai na tsinci kaina da darawa. Wani abu game da mutumin is very fascinating, yet so familiar. A karo na kusan biyar tunda muka fara chatting dashi yanzu, da naji a jikina duk yadda za ayi mutumin nan ya sanni fiye da sani na, kuma nima ko yaya ne na san shi. Sai dai duk hakan bai dameni ba, yadda naji hira dashi ta dauke min hankali, shine abinda ya bani mamaki ya kuma daure min kai a lokaci guda. It’s a first.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button