A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Janan ce ta takura akan sai mun fita bakin titi mun sayo tangerine da mango.
Nace “wai ke ma ga Ahmad nan, ki tura shi mana?”.
Tace “ke zaki fita kiyi gadin gidan ko? Yadda Yaya zai dawo ya tadda baya nan ya tsige ni da raina ko?”.
Nace “to yanzu kina tunanin idan ya dawo yaga bamu nan, ba zai tsige ki da ran naki ba dai?”.
Tayi dariya, “sis, ki taso kawai mu fita, babu abinda zai faru. Ni fa bana jin dadin jikina wallahi, ai nayi kokari, kusan awanni na arba’in da takwas fa ba tare dana taka waje ba!”.

Na jefa mata harara, “da can kuma da kike fin sati ma ba tare da kin fita ba fa?”.
Tace “wannan ai ya banbanta, don Allah taso mu tafi kada mu bata lokaci har Yaya ya dawo”.

Duk da ban so ba, haka nan na tashi na bi bayanta muka fita. Har yanzu ina jin jikina ba daidai ba, duk da dai tunda nasha paracetamol da yammar nan, zazzabin ya sauka, amma har yanzu ina jin jirin kadan-kadan da kuma ciwon kai.

Can bakin titi muka fita, muka yi siyo duk abubuwan da idanunmu suka dora ido a kansu. Niki-niki haka muka juya gida hannuwa cike da ledoji. A hankali muke tafe akan titin, yanayin unguwarsu kamar G.R.A haka take, da rana ma baka cika ganin mutane suna shawagi ba balle da dare. Yanzu ma sai jifa-jifa muke ganin mutane, sai kuwa ababen hawa da suke ta wucewa. Wasu na fita wasu na shiga.

Gab da zamu shiga gidan naji nayi turus, sakamakon wata mota dana hango can gaba kadan da gidan. Idan da ba don wata sticker dake bayan motar ba, an rubuta ‘born to fight’, da cewa zanyi ba ita bace. Sai dai wannan babu tantama motar Umar ce, amma me zai kawo shi nan yanzu? Janan tana tambayata lafiya? Amma hankalina baya wajenta, wayata nake kokarin cirowa. A tunanina kila ya kira ni ban ji kiran ba, yanzu haka ma kila ni yake jira ko wani abu. Amma babu kiran Umar a wayata babu alamunshi.

Na kalli Janan ina nuna mata motar, da yake akwai hasken da kwayayen dake kofar gidajen unguwar suke badawa, take ta gane motar, tace “kai! Kamar motar Umar dinki fa!”.
Babu ko tantama nace “motar shi ce, amma me yake yi anan? Ko kirana fa bai yi ba!”.
Tace “ko dai bashi bane?”. Da sauri na hau girgiza mata kai, gabadaya na rasa akan abinda ya kamata inyi tunani a lokacin. Haka kawai naji jikina ya dauki wata irin rawa, ba kuma zazzabin da nake ji bane ya haddasa ta ba.

Ba tare da tunanin komi ba, naji na fara daga kafa ta zuwa wajen motar. Duk taku daya, rawar jikina karuwa take yi, haka bugun zuciyata yake ninkuwa.

Ban san tunanin me nake yi ba dana tunkari motar gadan gadan ba, amma ban shiryawa ganin abinda idanu na suka gane min ba. Ban shirya ba!.

Umar ne kamar yadda nayi zato, zaune a gaban motar, sai dai ba shi kadai bane kamar yadda nayi zato. Tare suke da ba wata ba illa Haleemo. A zaunen ma zama na rashin da’a, saboda kusancinsu kamar a kan cinyarshi take zaune saboda irin zaman da suka yi. Ba wannan kadai ba, daidai lokacin da wata mota ta danno cikin layin a sukwane, haskenta ya dallare gaban motar, daidai lokacin da bakinsu ya hade da kiss. Hannuwanshi na yawo a wuyanta da bayanta.

Naji kamar an katse duk wata magudanar jini a jikina, ban san lokacin da kayan hannuna suka zube ba. Innalillahi, me idanuna suke gani ne haka??! Da sauri na kauda kaina don bazan iya kallon irin wannan badala dake afkuwa a gabana ba.

Tunanin farko daya dirar min, shine in kwashe kayana da suka zube a kasa in wuce gida, tunda dai sam basu san da kalar wainar da muke soyawa ba, sai kuma naga inaa! Don haka kafin ma in sake tunanin yin wani abu, naji kafafuna sun daukeni zuwa wajen motar. Na tsaya a daidai wajen da direba yake zama na bubbuga.

Sai da aka dauki lokaci kafin aka yi kasa da tinted glass din da aka saka aka rufe motar, Umar ya zuro kanshi waje. Yadda idanunshi suka waro cikin gigita yasa naji wata irin tsanar shi ta cika min rai, me yasa zai yi min haka??

Da sauri ya fito daga cikin motar yana wani kame-kame, “hh-hheyyy… Sweetie. M-me kike yi… anan?!”, ya tambaya cikin rawar murya.

Na daure, na cije, na tattaro duk wani kwarin gwiwa daya rage min, nace “oh, wai zamu wuce ne sai naga kamar motarka, nace bari in tabbatar. Ashe kai dinne. Mai kake yi anan? Nayi tunanin kana Kaduna??”.

Ya fara shafa bayan wuyanshi yana wuri-wuri da ido, “wannan? Ai dazu na dawo, tunda na tafi ban dawo ba sai yau! Ai ayyuka ne suka yi yawa! Kusan satina daya ban daga wayata ba saboda aiki!! Yanzu…. Yanzu ma wani abokina ne anan unguwar nazo gani, ai ban ma gane layin gidan su kawarki bane saboda duhu. Me ma kike yi anan unguwar? Nayi zaton kina Shika??!”.

Ji nayi na gama sauraren kame-kamen da yake yi, rainin wayon yayi yawa. Banyi wata-wata ba na daga hannu na watsa mishi tafi…

F.W.A

☆⋆15⋆☆

Ba shi kadai ba, ni kaina nayi mamakin marin dana mishi, amma banyi nadamar hakan ba.
Ya dafe kuncinshi yana kallona cikin zare ido, “sweetie….!”.

Cikin tsananin tsiwa da balbalin masifa nace “idan ka sake kirana da wannan sunan, Allah ya isa ban yafe maka ba Umar!!”.
Yayi sararo a tsaye da baki a bude, ya rasa abin cewa. Nace “dama abinda kake yi kenan? Nayi tunanin cewa abubuwan da kake nuna min kawai kana yi ne saboda desperation, ashe halinka ne?”. Munafikin sai yayi shiru kai a kasa yana muzurai. Daidai lokacin Haleemo ta fito daga cikin motar, kai a kasa babu kunya babu tsoron Allah tana nukutu.

Na kalleta, wani tsabar takaici yana cina, ji nike kamar in kamata in hadata da bango ko motar, amma na cije don nasan shaidan ne yake so ya zuga ni. Na nunata da yatsa, “akan wannan abin ne ka yaudare ni? Akan wannan abin ka share ni tsawon watanni, ina bibiyarka kana yazga ni kamar wata mara aikin yi? Ba ni kuka cuta ba wallahi, kan ku kuka zalunta. Kuma ni babu abinda zan ce muku, babu kuma mummunar addu’ar da zanyi muku. Sai dai ku sani, za ku gani da idanunku, Allah ya kara muku dankon kauna!”. Daga haka na juya da sauri na wuce, babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu. Janan data tsaya ta tsince kayan da suka zube, ta biyo bayana da sauri, jerawa muka yi muna tafiya ba tare da dayanmu ya cewa daya ci kanki ba.

Muna shiga daki naji jikina ya dauki wata irin rawa, ba shiri na lalubi kujera na zauna. Na kai hannuwana duka biyu na dafe kaina ina girgizawa, dama abinda yake faruwa kenan, ni ina gefe guda na hangame baki ban san abinda ke wakana ba? Lallai, idan kana raye zaka sha kallo. Kallo ba na wasa ba kuwa.

Janan ta zauna a kasa tana fuskantata, babu wanda ya iya magana a cikinmu, har muka dauki lokaci mai tsayi a hakan. Can na daga baki, a hankali nace “me yasa? Saboda bana son shi ne ko me?”.
Janan ta dafa kafafuna da nake ta jijjigawa, cikin tausasshiyar murya tace “ko kadan, kawai son zuciya ne da rashin godiyar Allah. Kiyi hakuri, ban san hakan zata faru ba”.

Na kura mata rikitattun idanuna da nasan sun rine da jan bacin rai, nace “me kike nufi?”.
Tace “kamar sati biyu da suka wuce, na taba ganin hoton Umar din a wayar Haleemo, sai nake tambayarta a ina ta san shi, sai tace min abokin saurayinta ne. Ni kuma sai na share maganar. Ranar nan da nace miki kamar Umar, ni na tabbata na gan su su biyun, nasan banyi kuskure ba. Dana nuna miki kika musa sai naga babu amfanin fitowa gar da gar in fada miki, tunda ban tabbatar da alakar dake tsakaninsu ba… Don Allah kiyi hakuri!”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button