A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Ban ankare ba, naji an fara kiran assalatu.
A hankali naji Yaya Bilal ya fara motsi, ba’a jima ba ya bude idanunshi, bakinshi dauke da addu’ar tashi daga barci.

A hankali ya dago kanshi ya kalleni, mamaki ya kama shi daya ga idanuna biyu.
Yace “tun yaushe kika tashi?”.
Na daga kafada sama, “ban jima da tashi ba”.

Ya kura min idanu kamar wanda bai yarda da abinda nace ba, na dauke kaina daga kallonshi kamar wadda take tsoron zai karanta tsantsar damuwar dake dankare a cikin raina. Sai dai ban tserewa hakan ba, ina jin ya karanci hakan, ko kuma ya fahimce ni.
A hankali naji ya sake janyoni cikin jikinshi, ya sake nutsa kanshi a kirjina kamar wani karamin yaro. Muka jima dashi a hakan, babu wanda yake kwakkwaran motsi, sai numfashinmu dake shiga kawai yana fita.

A hankali, daga can kasan makoshi, naji yace “am sorry baby!”.
Na dan kalleshi in confusion, nace “saboda me?”.

Ya tashi zaune sosai yana kallona, ni kuma nayi amfani da wannan damar na gyara zaman riga ta a jikina.

Ya kai hannunshi na dama ya kamo nawa dake kan ruwan cikina, ya damke cikin nashi yana murzawa a hankali, yace “for all of this, Na’ilah. Komi ma, tunda muka yi aure I was not able to… you know…!”, ya ma kasa fadin kalmar, sai gesturing da yayi a tsakaninmu. Nima naji kunya, nayi kasa da nawa kan.

Yace “kawai ina so ki san cewa ba haka nake ba, ban san me yasa sai dake kadai bane hakan take faruwa, amma ina kan neman magani, don haka don Allah ki kara yi min hakuri, kinji baby na?”.

Irin yadda yayi maganar da tambayar, helplessly, yasa naji wani irin tausayinshi ya rufe ni, haka naji wata irin soyayyar shi ta kara lullube min kirji.
Na kai hannuna daya na dora akan nashi hannun da har yanzu yake cikin nawa, a hankali, (don kunyar yin maganar naji sosai), nace “to ni menene na bani hakuri, laifin me kayi? Ko kuwa kaji ni ina complaining ne?”.

Ya dan zare ido, idanunshi na nuna alamun mischievousness, yace “baki damu ba fa kika ce? Kenan ni kadai ne na damu, ina ta so inyi ajiya a nan!”.
Ya kai daya hannunshi yana taba kasan marata. Na kai hannuna da sauri ina bige hannunshi, na kama idanuna na rufe, a lokaci guda kuma na juya fuskata na binneta cikin filo, “kai Yaya!”. Na fada shrieking.

Ina jin sautin dariyar daya saki, ya mike tsaye yana cigaba da dariyar, “zaki sani ne yarinya, gwanda ma ki shirya tun da wuri, jikina yana bani soon, I mean very soon, wannan kunyar taki zata bar idanun nan naki da jikinki!”.
Ban ce mishi komi ba har ya shige bandaki, sai da naji ya maida kofar ya rufe sannan na mike zaune ina ajiyar zuciya. A can kasan zuciyata kuwa, sai naji wani sanyi ya ziyarce ni. A raina nace ‘at least dai lafiyarshi lau, sai dai mu kara kaimi wajen yin addu’a, idan ma wani abu ne, Allah ya yaye mishi’.

Yana fitowa daga bandakin, ban jira komi ba na fada ciki a sukwane.
Ina fitowa na ganshi akan abin sallah ya gama yin nafila, na dauki zanin dana shigo dashi saboda dorawa akan rigar barcin dana sanya idan zanyi sallah, na kalleshi, “yau ba zaka je masallacin da wuri bane?”.

Yace “ina tunanin tsayawa muyi sallar mu ne a daki kawai yau”.
Nace “ni dai na yafe, ka tafi masallacin ka kawai”.
Yace “wai korata kike yi ne, baby?”.

Na kama baki ina dariya, “ni ban wani koreka ba, kawai dai na fada mata ka tafi masallaci kaje kayi sallar ka ne a can, kasan yafi lada”.

Ya mike tsaye, “ai shikenan, tunda abin ya zama haka, baby na ta fara gajiya dani har wani korata ma take yi daga daki”.
Ban ce mishi komi ba, har ya fita daga dakin, sannan nayi murmushi na fara nafila kafin a kira sallah.

°•°•°

Ina kicin ina fama da yanka vegetables akan cutting board, Yaya yana dinning room akan daya daga cikin kujerun teburin, iPad dinshi ce a hannunshi, a cewarshi ayyukan jiya yake karasawa saboda a yau din ake so ya aika su, amma kuma hankalinshi baya kan wayar, duk motsin da zanyi idanunshi suna kaina.
Da yake yau ranar assabar ce, dukanmu muna gida.
Anty Raheemah har yanzu bata fito daga dakinta ba.

Har na gama hada abubuwan da zan hada, na kai kan table din na ajiye, Yaya yana zaune, sai dana gama hada komi sannan naje na buga mata kofa.
Ta bude kofar, har yanzu kayan barcinta ne bata cire ba, tana ganina ta hau wani yatsina, “menene?”.
Nace “Yaya ne yace kizo mu ci abinci”.
Bata ce komi ba, ta maida kofar ta rufe. Na tabe baki na koma inda Yaya yake.

Na zauna a gefenshi, na hau zuba mishi abubuwan dana dafa. A plate daya nake zuba mana komi, babu ruwana, tunda abinda yafi so kenan, to fa ni babu ruwana. Har muka fara cin abincin, babu alamunta.
Lokacin da tazo, daidai lokacin Yaya ya duka yana kwashe syrup din jam daya taba gefen bakina da harshen shi, sai sautin jan tsaki kawai muka yi.
Ta ja kujera ta zauna, babu ina kwana babu komi, ta mike kafa ta hau zuba abinci, shima Yayan bai ce mata komi ba, balle ni muka cigaba da cin abincinmu cikin shirun daya ratsa har muka gama. Ta tashi ta koma daki, shima Yaya ya koma dakinshi domin ya karasa aikinshi, ni kuma na dauki kayan da muka yi amfani dasu na wanke.

Tun jiya da dare Janan ta kirani a waya ta fada suna kan hanya ita dasu Harira da suka zo hutu. Da yake bikinta yana ta matsowa, nan da sati uku, suna ta aikin rabon katin gayyata da anko. Tace tunda aka kawo ankon, Yaya ya daukar mana ni da sauran abokan zamana, ina tunanin su ya basu nasu, don tace nawa kadai ya bada yace ta hada da nata a kai wajen dinki.

Tunda na shiga kicin din na hau hada musu abubuwan tande-tande da lashe-lashe da lemuka. Na saka lemuka cikin firjin domin suyi sanyi sannan na koma dakina ina jiransu.

Da wannna damar na samu na fara tunano maganganunmu da Yaya a daren jiya, nayi nisa cikin tunani, ban ma san lokacin dana dauko wayata na dannawa Sailu kira ba. Sai dana ji muryarta sannan. Nayi kamar in katse kiran kafin daga baya dai na daure na kara a kunne, muka gaisa da ita na tambayeta yan biyu, tace suna can gidansu.
Mun dan fara hira da ita, amma na kasa concentrating din komi. Da kanta ta fahimci ba lau nake ba, ta tambayeni lafiya? Da daga farko ce mata nayi lafiyata lau, kai tsaye tace karya nake. Ta fara watso min tambayoyi iri-iri, har sai data fara yin fushi, wai ban yarda da ita bane. Nace “wallahi ba haka bane Sailu, kema kin sani kuma”.

Tace “to menene idan ba haka ba?”.
Nayi shiru kamar ba zan ce komi ba, bata yi magana ba itama tana jiran taji abinda zan ce. In ina na fara, da kyar na iya rufe ido nayi summarizing din abinda yake faruwa damu tunda nazo gidan Yaya.

Tunda na fara take jan salati har na gama, tace “wannan ai babbar matsala ce Na’ilah! Kuma sai yanzu kike fada?”.
Nayi shiru ina hararar bango kamar itace a wajen, nace “dama kika samu na samu kwarin gwiwar fada miki ko?”.

Tace “kin taimaki kanki da kika fada da wuri kam, Allah kadai yasan abinda zai faru idan kuka cigaba da kasancewa a haka. Dole su Inna su ji labari!”.

Na zaro ido, “mene? A’ah, don Allah kar ki fada musu”.
Tace “to me amfanin fada min kenan? Ina dama don a nemo maganin matsalar ne a kuma maganceta?”.
Nace “to amma fa yace shima yana neman magani!”.

Tace “to sai me? Ba sai mu taya shi ba? Baki ji yan magana sun ce hannu da yawa maganin kazamar miya ba?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button