A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Na sake fashewa da dariya, wani lokacin haka take kamar wata sintacciya. Ina shirin bata amsa, naji alamun shigowar kira, na duba naga ‘Zhaujee’, kamar yadda ya kawo min wayar da wannan sunan a jikin lambarshi yana tsalle, nace “you are nuts wallahi. Bari in dauki wayar Yaya ya kira, ki gaida su Ummah”.

Ban jira ta gama fadin abinda ta dauko fada ba, na katse kiran tare da amsa na Yaya. Ina dagawa yace “ke da waye ne kuke yin waya tun dazu?”.

Nace “Janan ce Yaya”.
Yace “ok, ki fito mu ci abinci”.
Nace “to”. Na kashe wayar na tashi.
Wani tattausan silifas pink, na dauka a cikin kayana na saka. Na dauki turare na kara fesawa a jikina, na dauki wayar hannuna naja dakin na fita.

Suna zaune akan dinning table, da kwanukan abinci a gabansu na same su. Na musu sallama suka amsa, tare da jan kujera kusa da Yaya na zauna, ita kuma Raheemah tana kan wadda take fuskantar shi. Fuskar nan tasha make up har da na hauka.

Yaya yace mana “bismillah ko?”.

Na ga Raheemah ta ja plate ta bude ta zuba abinci a ciki macaroni ne aka yi jallop, an zuba kifi da nama a ciki. Maimakon in ga ta mikawa Yaya wanda ta zuba, sai naga ta ja shi gabanta zata fara ci.
Na kalli Yaya naga yana fama da cokali da plate, sai na dan matsa, na karbi plate din hannunshi na zuba mishi abincin, na tsiyaya ruwa a cikin cup shima na ajiye mishi, sannan na fara zuba nawa nima. Ya kalleni cikin dan murmushi, tare da furta “jazakillah”, a can kasan makoshinsa. Na maida mishi martanin murmushin.
Ina daga kaina, naci karo da idanun Raheemah tana watso min harara, ni kuwa na daga kafadata sama na fara cin abincin bayan nayi bismillah.

Ban wani ci da yawa ba, na ture kwanon gefe na ajiye. Ban taba cin girkin Raheemah ba tunda nake, don haka ban taba sanin yadda girkinta yake ba sai yau. Kodayake, zata iya yiwuwa yau din rana ce ta kufce mata abincinta yayi gishiri da yaji ya kuma dafe.

Na ci gaba da zama anan duk da cewa na gama, har suka gama cin nasu abincin. Yaya ya tashi ya wuce dakinshi, itama ta mike tayi nata dakin, ta bar kayan abincin anan, suka barni ina zare ido.
Da nima nawa dakin zan koma, sai na jiyo sautin karar talabijin a falon Yaya, don haka na karasa can. Baya cikin falon ma, na zauna tare da daukar remote na latso tashar mbc action na kunna, suna hasko film din Furious 7 kuwa, na gyara zama sosai don ina kaunar film din kwarai.

Ban yi nisa a kallon ba, sai ga Raheemah itama ta shigo. Tana zama, ta dauki remote ta canza tasha, na dan daga kai na kalleta kadan, sai kuma na dauke na maida kan tvn da take ta latse-latse da canza tasoshi. Idan tayi zaton magana zan mata akan haka, zata sha mamaki kam. Daga karshe ma sai na kunna wayata na bude wani document akan pregnancy issues ina dubawa.

Muka cigaba da zama a haka, babu mai ko tari sai sautin wakoki dake fita daga wata tasha data kunna. A haka Yaya Bilal ya fito ya same mu.

Ya umarceta data kashe kallon, yana so yayi magana damu. Nima sai na kashe wayata, na maida hankalina kan shi.

Yayi gyaran murya, ya fara da kara yi mana nasiha da kuma dokoki daya kafa. Yace babu yan aiki a gidanshi, daga maigadi, sai mai ban ruwan fulawa, sai kuwa wata mace da yace zata dinga zuwa tana tayamu da share-share da wanke-wanke, amma bai yarda da girkin yan aiki a gidanshi ba, mun fahimta? Muka ce mishi eh.
Sai kuwa zancen girki, ya tambayemu kwana nawa muke ganin zasu fi zama convenient a wajenmu? Ni dai nayi shiru ina jin suna muhawarar kwana daya ko biyu shi da Raheemag, har sai daya jiyo ya kalleni, Ya tambayeni ya nake gani? Nace ni duk yadda suka yanke daidai ne a wajena. Nan ma na kara karbar wata hararar dai, na nuna kamar ban gani ba. Daga karshe dai suka kare akan kwana biyu.
Yace tunda ita Ameerah bata da ranar dawowa, zamu cigaba da raba girkin a tsakaninmu har zuwa lokacin da zata dawo. Ya kara da cewa bai yarda da fada ba a gidanshi, babu fada kuma babu cece-kuce, yace duk wadda take da matsala game da wani abu, mu tunkari junanmu mu warwareta a tsakaninmu, ko kuma mu fada mishi, sai yasan yadda zai warware matsalar, muka ce to.

Daga nan muka cigaba da kallonmu har dare yayi, sannan na tashi na musu sallama na wuce dakina.
Kayan da ban gama gyarawa ba, na gyara. Na ciro kayan barci na ajiye akan gado, sannan na shiga wanka. Wanka nayi, na wanke bakina da mouth wash mai kamshin berries, na daura alwala na fita.

Yaya Bilal yana bakin gadona a zaune da wayata a hannunshi yana dannawa, ya daga kai ya kalleni lokacin dana fito. Har naja kujerar da aka ajiye a gaban dresser na zauna, idanunshi suna kaina.
Na kauda kaina kamar ban san yana yi ba, na dauki lotion na fara shafawa a jikina. Ta cikin mirror na sake tsintar idanunshi a kaina, wayar ma ya ajiyeta a gefe guda, ya karkato da hankalinshi kaina kacokam. Naji gabadaya na fara takura da kallon kurillar da yake yi min, a gaggauce na karasa shafa man, na mike tsaye da niyar dauko kayan barcina dana ajiye.
Babban tawul ne a jikina wanda ya sauka har kasan gwiwata, na karasa gaban gadon na janyo kayan, ganin har lokacin yana zaune yana kallona yasa na juya na koma bandaki na sanya kayan.

Wannan karon dana dawo, yana tsaye a bakin gadon, hannuwana saye cikin aljihun sweat pant dake jikinshi, idanunshi kyam akan kofar bandakin yana dan murmushi.

Yace “meye na wani guduwa bandaki kuma? Menene ake boye min ne, wanda ban riga na gani ba?”.

Na kalleshi blankly kawai ban ce komi ba, na wuce kan gado kawai na ja bargo na rufa.
Ya matso ya janye bargon daga fuskata, “uh uh!! Shariyar menene ake min haka, baby na kamar baki gane ni ba?”.

Na sake yin banza na kyaleshi. Bai san tunda na baro su shi da Raheemah a falon nan ba wani haushin shi ya cika ni ba taf? Ji nake kamar in koma in janyeta daga kusa dashi, in jefata dakinta in kulle don ma kada tayi tunanin sake fita ta koma wajenshi, haka nan dai na danne zuciyata na dawo daki.
Yanzu kuwa da nake ganinshi a gabana, tunanin wajenta fa zai koma ba wajena zai dawo ba, naji wani irin matsanancin kishi ya rufe min idanu, kishi irin wanda ban taba jin shi ba.

Ya shafo gefen fuskata daga bayan kunnena zuwa kan lebuna na, cikin nuna damuwa yace “wani abu yana damunki ne? Ko baki jin dadi ne?”.

Wani haushin shi ya kara tuko ni, to ko ina ruwanshi ma da wata rashin lafiyata? Koma dai menene, daga karshe dai tafiya zai yi wajen matar shi ya kyaleni anan.

Nace “wai ina ka baro matarka ne ka taho nan? Ta ma san kana nan kuwa?”.

Ya daga gira cikin alamun mamaki, kafin wani murmushi ya subuce mishi, ya zauna sosai a gefen gadon.
“a’ah, bata sani ba, na taho yiwa baby na kuma amaryata sai da safe ne. Ko kuwa nayi laifi ne?”.

Nace “to ni sani zan yi? Sai ka bari sai ka tambayeta, sai kaji ko?”.

Yace “haka ne, bari inje in tambayeta inji kuwa”.

Bai jira ya sake cewa komi ba, ya duko ya bani peck a kumatuna, ya mike tsaye yana kallona cikin murmushi, “sai da safe baby na, kiyi barci mai dadi”.

Bai jira na amsa ba, ya juya ya fita daga dakin bayan ya kashe min wutar dakin. Na sauke ajiyar zuciya a hankali bayan fitar tashi, ina ji wani irin abu yana mintsinin can kasan zuciyata. Daga karshe dai nayi addu’ar kwanciya barci, na shafe jikina.
Cikin yan kwanakin nan shida, ba karamin sabo nayi da kwanciya a jikin Yaya ba, ban san nayi sabo da jikinshi sosai ba sai da barci ya nemi ya gagareni. Na dinga juyi ina karawa akan gadon, Allah kadai yasan iyaka tsawon lokacin dana dauka, kafin da kyar barci yayi awon gaban dani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button