A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Yaya ko kallon mu bai kara yi ba, ya dai jefo mana “ku zauna ku jira ni, ina zuwa!”, bai jira jin ta bakinmu ba, ya ciccibi amaryarshi suka shige daki. Na kama baki na bi bayansu da kallo, a zuciyata ina kara tausayawa Janan. Idan har haka ake treating dinta a gidan Yayanta, Allah kadai yasan halin da take ciki gaskiya.

Ta ja ni zuwa dakinta inda yake can cikin falon, can karshe kusa da wani karamin daki da suka mayar dashi kamar store. A gefen katifa duk muka zauna, na titsiyeta sai data bani labarin abinda yake faruwa a gidan, tun daga farko har karshe.
Matar Yayanta irin matannan ne da idan Allah ya hada ka kishi dasu, taka ta kare. Babu boka babu malam, zasu dafa ka cikin ruwan sanyi ka kankare. Irin matannan ne masu dan banzan kissa.
Tace a bayan idon Yaya Bilal, ita, Janan din da sauran dangin shi har ma da Ummansu, basu maraba da kayan wanki a wajenta, amma idan a gabanshi ne sai tayi ta tattalinsu tana ririta su.

Ameerah irin sangartattun yaran masu kudin nan ne. A wannan shekarar ta gama karatunta. Bata aikin komi a gidan wannan sai zama, kallo da nanikewa miji. Tana da yan aiki kala-kala, don ma dai ba kwana suke yi a gidan ba. Da masu girki, masu sharar waje, masu wanki, har da masu gyaran daki, kuma duk mahaifinta yake biyansu. Tace yanzu haka garar da aka kawota da ita tana cike da store, ko alamun tabata ba ayi ba, saboda bata yin girki. Watarana ma daga gidansu takanas ake dafo abincin a kawo mata. Kai hatta da wutar amfani wannan ta gidan, mahaifinta ne yake biya. Yayan yayi magana game da hakan, amma mahaifanta suka nuna duk cikin son da suke yiwa diyarsu ne.

Tunda Janan taje gidan, take gasa mata aya a tafin hannu cikin ruwan sanyi. Bata da bakin korafi saboda koda wasa bata bar hanyar da Yaya zai yi suspecting dinta ba. Spare makullin gidan da Yaya ya bata, ta amshe, kullum sai ta buga mata gida idan ta dawo daga makaranta, kuma sai ta wulakantata kafin ta bude mata gidan, store din abinci a kulle yake, wani lokacin sai dai ta saka kudinta ta sayi abinci. Idan Yaya baya gidan to ita da babu duk daya suke, duk kokarin Janan akan su daidaita abin yaci tura. Ita cewa ma tayi gwanda ace fada suke yi akan wannan zaman doya da manja din.

Ita kuma tayi-tayi dashi akan ya bari ta koma wajen Anty Sa’a tunda suna Zaria yanzu, ko basa nan akwai kanwar mijinta da suke zaune tare a gidan sai ta zauna dasu, ko kuma ya kama mata gida a samaru, ko ma dai a ina ne, amma yayi fir ya ki. Ita kuma bata so ta takura mishi da maganar kada yace ko bata son zama da matar shi ne ko wani abu.

Sai a ranar naji cewa ashe ba mahaifinsu daya da Yaya Bilal ba. Mahaifinsu Yayan ya jima da rasuwa, bayan nan ne ta auri wani mutum a Kaduna, shine mahaifin Janan din. Sai lokacin na fahimci komi, ina ta mamakin dalilin da yasa Ummarsu take zaune a Kaduna bayan duk danginsu suna Zaria, nayi zaton ko aikine ya kai baban su Janan din Kaduna. Amma nayi mamaki, koda wasa basu taba nuna mata banbanci ba, ita ko su Harira diyar kishiyar Umma, basu taba nuna mata wani ki ko kyama ba.

Janan kuka take yi sosai lokacin da take bani labarin wannan, na rungumeta ina bata hakuri, don shine kadai abinda zan iya yi a lokacin, har ta gama kukan. Daga nan muka fito da littafanmu muka cigaba da karatu har aka kira sallah muka tashi muka yi, muka koma muka cigaba da karatunmu. Muna nan sai ga Anty Ameerah ta leko, tace muje mu debi abinci, Janan ta fita zata zubo mana abincin, sai gata ta dawo wai Yayan yace muje muci tare dasu. Tace haka yake, in dai yana gidan tare suke cin abinci. Na dauki hijabita na saka muka fita.
A falon sai na daga baki ina kallon ikon Allah, gabadaya mata ta rikide, ta koma kamar wata salihar kirki, kamar ba wannan matar da take amsa mana magana da dai-daya ba.
Sai nan-nan take yi damu, abinci kamar zata zuba mana a baki yadda take ta turo mana plates na varieties din abinci gaban mu. Tsabar mamaki ma ni kasa yin magana nayi. Lallai an saka Janan a cikin tsaka mai wuya. Idan har haka take mata, to lallai kuwa babu wanda zai yarda da cewa idan an saka mata yatsa a baki zata ciza, sai dai idan har tayi hakan a gabanka.

Muna gama cin abincin muka koma daki. Muna shiga na fara zuba magana, tsananin mamakin matar ya hana ni hada maganganu masu ma’ana ma, Janan sai gefe ta koma tana min dariya. Sai dana nutsu sannan na iya zama muka yi magana akan haka da ita.

Sai bayan sallar la’asar can, sannan na mike ganin cewa Yaya bashi da niyar barin gidan. Janan tayi-tayi dani akan in tsaya Yaya ya fito, nace mata ina da abubuwan yi ne a hostel, dole ta kyaleni na tafi.
Daga wannan rana ban kara taka kafata zuwa gidan Yaya Bilal ba har yau.

Karatunmu yaci gaba da tafiya cikin nasara. Ni da Janan duk bamu dauki karatunmu da wasa ba, duk da bamu yin topping, amma dai Alhamdulillah, babu abinda ya taba dawo mana.

Muna shekarar mu ta uku, Yaya ya sake yin wani auren, ya auro Anty Raheemah. Yadda ya rikice akan wannan auren, yasa na kara tsurewa da lamarin maza. Lokacin bikinsu da Anty Ameerah yadda yake ta rawar kai da zakewa, kai sai kayi zaton babu wata ‘ya mace da zata sake yin daraja ko kuma a idonshi bayan ita, sai gashi tun ba aje ko’ina ba ya karo wani auren.

Janan tace ba karamin rikici suka yi da matar Yayan ba, har ta kai ga cewa ya fita ya bar mata gida, inda abin ya yiwa Yaya ciwo matuka. Ya karasa gyara gidan gadonsu, dama can ya fara gyarawa zai kai Ameerah din, iyayenta suka hana.

An dai yi biki lafiya, despite tashe-tashen hankulan da aka sha, amarya ta tare a gidan mijinta, Janan ma tayi kaura can.
Muna ta murna, a tunaninmu wannan zamu tafi da ita, tunda sa’ar mu ce ita, ashe yaudarar kanmu muke yi.

Raheemah da kannenta irin ‘ya’yan mace dinnan ne. Zaku yi mamaki idan kuka ji cewa suna da uba da yake raye, kuma auren iyayensu yana nan, amma suna zaune separately. Duniya da son abin duniya ya rufe musu ido daga su har uwarsu, mahaifinsu kuwa mutum ne mai wadatar zuciya da tsoron Allah.
Tun yarintarsu, bin bokaye da malamai shine amsar tambayarsu da komi nasu. Kodayake, wanene a garin Zaria bai san da zaman Hajja Ladidi ba? Shi yasa tashin farko da naji wai Yaya zai auri daya daga cikin diyanta, abin ya bani mamaki kwarai. Sam ire-iren su ba irin wadanda yaya yake hulda dasu bane.

Kannen Raheemah biyu da suka tare a gidan su suke kara rura wutar dake cikin gidan Yaya Bilal. Su duka biyun suna karatu a jami’ar Kongo. Saboda haka suka baro gidansu dake Hanwa, suka koma can saboda ya fi kusa da makaranta. Duk da a zahirin gaskiya ba hakan bane. Haleemo da Salama sune yan kanzagin ta, sune masu zuwa garuruwa da kauyuka amso mata magunguna wajen malamai da yan tsubbu yayin da take gida ta mike kafa.

Sai da na yiwa Janan fatan dama a wajen Anty Ameerah ta zauna, tace mugun fata nake mata. A cewarta zama dasu Haleemo, duk da gallazawar da suke mata, yafi mata sau dubu akan zama da Ameerah. Don haka na kawo idanu na zuba mata. Don haka ban taba ganin laifinta ba don tana zuwa wajen Umma weekend ba duk karshen sati, watarana ma nima ina binta.

To da yake ita rayuwa babu abinda hakuri baya maka, gashi yanzu har zamu shiga shekararmu ta karshe, ko ma in ce mun shiga. Duk da har yanzu dai babu abinda ya canza, sai ma karuwa da yake yi. Tun basa cin karfin Yaya akan Janan, har suka zo suka ci galaba a kanshi. Wasu lokutan haka zai birkice mata kamar ba Yayan nan nata mai son ta ba, sau tari sai dai ta kira ni tayi ta kuka, ni kam sai dai inyi ta bata hakuri. Rabin abubuwan da ake mata a gidan nan, ko Ummarsu bata sani ba, tunda duk cikin danginsu babu mai zuwa gidan balle yaga halin da take ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button