A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Cikin ihu tace “lallai ma! Wato kuma yanzu zagina zaka fara yi akan karatu ko? Wato saboda matanka suna da digiri, ni bani dashi, shine zaka fara zagina har matanka ma su raina ni ko? To wallahi ba’a isa ba!!”.

Yace “zagi dai ke kika ji shi don ni dai ban daga baki na zageki ba. Karatu kuma bani nace ki barshi ba balle yanzu ki zo ki fara tada jijiyar wuya ki nemi ki tara min mutane ba. Wai ina dalili? Ba zaki taba barin rayuwata ta huta bane? Daga yanzu ki tado wannan, anjima sai ki kirkiro waccan?”.
Tace “to saboda meye na katse karatun nawa? Ina jin saboda aurenka ne?”.

Yaya yace “haka dai kike tunani, ni ban sani ba. Maganar direba ce dai, yana nan, kuma ai ba ita kadai na ajiyewa ba ko? Kema zaki iya aikenshi, zai kuma dinga kaiki duk inda kike son zuwa idan zaki tafi unguwa, don haka maganar wannan ta mutu!”.
Ya bude kofar dakinshi a fusace ya shige, ya barta a falo tana masifa da mita, ni kuwa da nake kwance a daya daga cikin kujerun falonshi na kara lafewa akan kujerar, babu wanda ya kula dani.

Idan na tashi da safe ranar girkina, na kan hada abin kari mai rai da lafiya, idan muka ci, wani lokacin tare muke fita ni da Yaya, kowa ya wuce wajen aikinshi, watarana ya riga ni fita, ko kuma in riga shi. Karfe biyu na yamma nake dawowa, sai in dora abincin rana, shi Yaya baya cin abincin rana a gidan sai na dare, na kuma yi dashi akan in dinga dafawa ana kai mishi wajen aiki amma yaki, yace suna cin abinci acan.
Idan na gama abubuwan da nake yi da yamma, sai in dora abincin dare.

Sai ta fara mitar bana dafa musu abincin rana da wuri, ranar kuma da nake aikin rana ina dafa musu abincin rana da wuri, kafin lokacin ci yayi, abincin ya huce, ko ya saki, wasu irin excuses dai da daga jin su ma kasan rigima ce take nema kawai. Yaya yace to daga yau kowa ya dinga dafa nashi abincin da rana kawai.
Ba haka taso ba, maimakon ta bar maganar, sai ta fara masifar ita fa ta gaji da irin rashin adalcin da Yaya yake gwada mata, ya maidata saniyar ware a gida, ya biye min muna wulakantata, duk muka mata shiru dai. Data gaji da fadan, ta wuce dakinta fuu.
To yanzu dai a haka muke, yanzu ina cikin satina na biyar da dawowa Abuja kenan.




Dare ne sosai, baka jin motsin komi a cikin dakin, sai karan ac da kuma labulaye da suke kadawa sakamakon iskan da yake kadawa mai sanyi. Dakin babu haske, sai hasken farin wata daya ratso ta cikin tagogi da labulayen dakin.

Na sauke wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya a karo na barkatai, ni kaina bansan lokacin dana dauka a cikin wannan halin ba.
A hankali idanuna suka sauka kan sumar gashin dake saman kirjina. Tattausan numfashin da yake ja yana shaka yana sauka a saman fatar kirjina, rabin rigar barcin dana sanya yana saman ruwan cikina. Tun dazu numfashin ya fara saukar min da wani irin kasala, ya kuma haifar min da goosebumps a ilahirin sassan jikina. Sai dai duk yadda naso, na kasa samun zuciyar ture shi daga jikina, duk da ihun da zuciyata take yi min kuwa.

Cikin lokutan wadannan da muka yi munyi wani irin sabo ni dashi ba karami ba. Na sabar mishi da daddadan abinci mai rai da lafiya duk ranar girkina, tsabtar jikina da nashi, dakunanmu da kayan sanyawarmu, kamshin jiki, daki, da ma ko’ina, dadadan kalamai da sanyin hali. Ban taba daga sautin muryata tafi tashi ba a halin argument ko kuma hira kawai, ban taba tambayar dalilin wani umarni da zai bani ba koda kuwa ni abin bai yi min ba, shi yasa bana tantama yanzu har dokin zuwan ranar girkina yake yi, domin duk wani abu da zai sanya shi farinciki shi nake yi, bana yin abinda zai sosa ranshi koda wasa, sai dai cikin rashin sani. Sannan duk abinda zai yi ya bata min rai, ban taba confronting dinshi a gaban kishiya ba, kamar yadda naga tana yi ta kuma koya mishi, na kan bari sai mun shiga daki mu biyun mu sannan zamu kashe mu binne abinmu babu wanda ya sani.
Sannan duk runtsi, duk bacin rai, ban taba gigin raba mana shimfida ba, Anty Sarah tace kuskura na farko da mace zata yi wajen taimakawa balgacewa rayuwar aure mai armashi; raba shimfida da miji lokacin da ake cikin fushi.
Idan yanzu zamu yi fada, ko mu yini cikin fushi da juna, at the end of the day dai, zaka hangoni a dakinshi, akan gadonshi a kwance. Ko ban shige cikin jikinshi kamar yadda ya sabar min ba, zaka hangoni can karshen gadonshi. Sai dai da safe in tashi in tsince ni lullube cikin jikinshi, wasu lokutan daga nan zaka ga fadan ya wuce, watarana kuwa a nan kafin in fita dora abincin kari, zamu yi magana akan matsalar data taso mana, mu magance ta.

Matsalar daya ce dai har yanzu, mun kasa amsa sunan cikakkun ma’aurata. Tun yana kokarin yin wasanni dani a wasu ranakun, yanzu har ya ma daina attempting yin hakan.
Watarana haka na shiga dakinshi musamman, ciki da bai, har bayan dakin nashi, na fitar da komi na sharo har kasan gadonshi, true, na ciro layu, abubuwa iri-iri har cikin matashin kanshi naga abubuwa, naje can bayan gidan bayan Raheemah ta leka makotanmu gidan kawayen data fara yi, na kone su gabadaya.
Sannan cikin dabara da kissa irin tamu ta mata, na samu na lallabo kan Yaya Bilal, wani abokin Malam, babban Malami a cikin Suleja, yazo da dalibanshi suka yi saukar Al-Kur’ani Mai Girma a gidan, sannan duk sati yanzu ranar juma’ah yana bada rubutu a kawo mana, mu sha.
Sannan shi kanshi Yayan na dora shi akan hanyar sadaka ta ciyar da gajiyayyu, da marasa karfi. Yanzu haka duk ranar juma’ah, ana dafa abinci mai kyau a gidan su Ummah, a rabawa almajirai. Har Ummah sai data kirani a waya ta min godiya da haka, a cewarta hakan shawara ce mai kyau. Alhamdulliah, da alamun samun cigaba, tunda a hankali ya dawo da yan wasannin da yake min, duk da a yawancin lokuta na kanji dama kyaleni ya dinga yi, Yawancin darare haka yake barina cikin wani mawuyacin hali, darare da dama haka zan kare su cikin sharar hawaye. Sai dai ko a fuska, ban taba nuna mishi hakan yana damu na ba.
Yanzu dai ina cikin shakku ne, anya Yaya ba impotent bane? Musamman idan nayi duba da cewa, did shekarun nan da suka dauka da matan shi, basu taba haihuwa ba. Amma kuma ai Jan tace lafiyarshi lau, Allah ne bai kawo ba, but then, ba lallai Janan tasan yana da cuta ko baya da ita ba, tunda ba lallai ya fito ya fada mata hakan ba. Amma kuma da hakan ne, anya matan shi zasu yarda su zauna dashi? Ko kuwa? Abin har ya fara rikita ni.

Yau kam har na kwanta barci, wasu ayyuka ne suka sako shi a gaba a office kwana biyun nan, yanzun ma da kyar na janyo shi muka ci abinci, ya koma study room dinshi, wani dan karamin daki a cikin dakin nashi, nan yake gudanar da yawancin ayyukan shi. Har na gama duk wasu ayyuka da al’aduna, na kwanta yana kan desktop dinshi yana aiki.
Har wajen karfe sha daya na dare ina jiran ya dawo, naji shiru, na sake tashi na leka shi, he was so immensed a kan aikin da yake yi bai ma kula dani ba, don haka na maida mishi kofar na rufe, na kashe wutar dakin na kwanta abina.

Barci har ya fara daukata, ban san ko karfe nawa bane lokacin da naji ya hayo kan gadon finally, ya janyo ni cikin jikinshi.
Ina jin shi yana bin fatar jikina da shafa sensually, nasan dai karshen alewa kasa, wajen da muka saba tsayawa kullum dai nan zamu tsaya yau ma, amma kamar kullum, yau din ma kasa hana shi yin wani abu nayi. A haka ya taso ni na wartsake, ba’a jima ba naji nauyin kanshi a kirjina. A haka muka kasance tun dazun, na kasa koda motsa yatsa ne, na kuma kasa yin barcin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button