A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Na girgiza mishi kai da sauri, “a’ah, ba wani abin damuwa bane. Ina ga yanayin weather dinne kawai”.
Ya bini da kallo kamar bai yarda da abinda nace ba, kafin ya gyada kai. Mota ya tarar mana, muka hau muka wuce masaukinmu.

Magana ta gaskiya Yaya bai kula da kyau ba, tun muna gida nake irin wannan jirin sai dai bai kai irin wanda nake yi yanzu karfi ba. Gashi tunda azumin wannan ya kama ban sha azumi ko daya ba, tun ina jiran al’adata yau ko gobe, har na hakura saboda lokacin yin ya wuce.

Ina so in yarda da zuciyata da take rada min ko dai? Kusan kullum. Amma ina tsoron disappointment. Ina tsoron kada in sanyawa raina abinda bashi bane, daga karshe ni kadai zan ji ciwon hakan. Don haka na kasa yarda da zuciyata, duk da signs din da nake gani.
Musamman idan na tuna abinda likita tace lokacin da nayi bari, cewa saboda yadda cikin ya fita ta karfi da tsiya, mahaifata ta dan samu matsala. Saboda haka samun ciki a gareni zai yi wuya, ko zan samu to gaskiya ba a shekarun nan na kusa ba.
Abinda yake kara sanya min sanyin jiki kenan.

             *☆⋆49⋆☆*

Washegarin ranar da aka yi sallah muka dira a Kaduna da yamma, nan muka kwana washegari muka wuce Zaria da safe. Kafin mu isa Yaya ya sa an share bangarenmu an gyara shi sosai. Tunda muka isa na lalubi gado nake zuba barci, sai can bayan azzuhur na tashi.
Nayi mika a kwancen da nake, kasusuwan jikina suna amsawa suna tuna min gajiyar dana kwasa a cikin yan kwanakin wadannan. Abu na farko daya fara zuwa raina shine abinci. Kada ma dai cikina da yake ta kugin yunwa yaji labari.

Na samu na mike da kyar na zauna tare da jingina da jikin allon gadon. Kamar tana jirana, ina tashi Anty Sarah ta turo kofar dakin ta shigo. Tayi murmushi ganina a zaune, nima na mayar mata da murmushin.
Tace “har kin tashi ne?”.
Sai dana ja wata doguwar hamma na sauke sannan na amsa mata da ‘ehh’.

Tace “sallah zaki yi kafin ki ci abinci ko kuwa?”.
Na girgiza mata kai ina yar dariya, “barni dai in fara cin abincin. Irin yunwar da nake ji ai bana tunanin zan iya kara minti daya a zaune ba tare da wani abu ya shiga cikina ba”.
Tayi yar dariya, “abincin yana falo, ko zan kawo miki shi nan ne?”.
Na girgiza mata kai da sauri, “a’ah, ki barshi zan fito in ci. Bari in wanke bakina”.
Ta gyada kai, “to shikenan. Ina falon”, ta juya ta fita.

A hankali na zuro kafafuna daga kan gadon, sai dana dan tsaya a haka, jikina ya waye da jiri-jirin daya zame min jiki cikin wannan yan kwanakin, sannan na tashi tsaye. Na shiga bandakina da yake ta tashin kamshin freshner da antiseptic, na wanke bakina.

Falon na fita, kamar yadda tace, a falon na sameta zaune akan kujera. Rabi’ah na ta guje-gujenta a cikin falon. Ga kulolin abinci nan shirye a kasa an shimfida ledar cin abinci. Babu bata lokaci na zauna na fara zubawa, tun kafin in kai abincin bakina yawu ya fara tarar min a baki.
Anty Sarah tace “Yaya Bilal sun riga sun ci shi da Abban Mimah. Sun tafi can babban gida tun dazu”. Kai kawai na gyada mata, yadda gabadaya hankalina ya tafi kan abincin da yake gabana ai bana tunanin zan iya saurarar komi.
Anty Sarah tayi murmushi ganin yadda na dage ina cin abinci hannu baka hannu kwarya, babu sassautawa. Zuba shi kawai nake yi kamar wadda aka ce za’a kwacewa. Tace “ci a hankali, kada ki kware”. Na sake gyada mata kai.

Bata sake cewa komi ba, har na gama ci da shan abubuwan data ajiye min. Na ture kwanukan gefe tare da komawa na jingina bayana da kujera saboda jin yadda cikina ya cika tam.
Nace “ina Mimah kuwa?”, tunda muka iso sai yanzu muka samu damar gaisawa sosai. Saboda mutane da yadda idanuna suke a rufe da barci lokacin da muka iso, a tsaitsaye muka gaisa.

Tace “taje gida weekend”.
Bayan mun dan hiranta kadan, na tashi naje nayi sallah. Kafin in dawo har ta tattara kayan abincin dana bari.
Nace “da kin bari ma ai da na dauke”.
Tace “babu matsala wallahi, meye a ciki?”.

Na zauna akan kujera, wayata a hannu ina maidawa Janan sakon data turo min ina barci, bayan na tura mata muka cigaba da hira har take gaya min makota da wasu daga cikin ‘yan uwan Yaya da suka zo min sannu da zuwa ina barci.
A hankali naji zuciyata ta fara tashi, kamar zan amayo da abubuwan da naci. Nasan ba zan samu lemun tsami a cikin fridge dina ba tunda mun jima rabonmu da gidan.
Na cewa Anty Sarah, “ko zan samu lemun tsami a wajenki? Zuciyata take tashi”.

Anty Sarah ta kalleni cikin tunani, ko bata fada ba nasan ko tunanin me take yi. Nima sai ban tanka ba. Ta tashi ta fita, babu jimawa sai gata ta dawo da lemun tsamin.
Na karba na bare na fara sha. Kallona take tayi, kafin ta nisa tace “kin kuwa fadawa Yaya?”.

Na kalleta cike da alamun tambaya, “na fadawa Yaya me?”.
“Abin arzikin da muka samu mana”, ta fada fuska cike da murmsuhi. Kai na girgiza mata.
Take murmushin kan fuskarta ya bace, tace “me yasa?”.
Na daga kafada, “I just want to be sure. Bana son sanya mana rai akan abinda bashi bane”.
Tace “wata alama kike son gani bayan wadda ta fito baro-baro a jikinki?”.
Nace “na gansu nima, but we could be wrong!”.

Tana shirin dawo min da amsa, aka turo kofar falon aka shigo. Duk muka maida kallonmu ga kofar, ganin Yaya Bilal sai duk muka ja bakinmu muka dinke, daga ganinmu kaga wadanda suka sha jinin jikinsu.

Yaya yayi kasa-kasa da idanu yana amsa sannu da zuwa din da Anty Sarah take mishi, idanunshi kafe a kaina, ni kuwa na kara lafewa a jikin kujera kamar wadda aka kama ta nannaga karya.
Yace “Allah dai yasa ba gulmata kuke yi ba?”.

Anty Sarah tana dariya tace “haba dai Yaya, da girmanmu da komi? Kuma ma akan me zamu yi gulmarka? Kawai dai hirarmu ce muke yi irin ta mata”.

Ya zauna akan kujera tare da ajiye bakar leda a kusa dani, yana yar dariya, “to ina zan sani ne? Na ga daga shigowata kun kame baki kun dinke bayan kafin in shigo naji kuna hira. Idan ban tsammaci gulmata kuke yi ba, me zan ce?”.

Ta mike tsaye tana kade rigar jikinta, “to bari kuga inyi nan tun kafin magana ta zama babba. Na’ilah sai anjima”.
Cikin dariyar da nake yi na amsa mata. Ta sa kai ta fita.

Tana fita Yaya ya kalleni, “har kin tashi daga barcin?”.
Nace “ehh”.
Yace “fatan gajiyar ta sakeki? Don gobe nake so mu koma Abuja. Nasan ayyuka sun tarar min, kema kuma suna jiranki”.
Na gyada mishi kai, “zan iya maneji dai”.

Yasa yatsa ya shafo kumatuna cike da tsokana, kamar wata karamar yarinya, “sarkin langwabu. Ban san yaushe kika zama alangwaba ba wallahi baby, kwanannan kin cika son jiki”.

Na kuwa langwabe din, “kai Yaya!”.
Yayi dariya tare da mikewa tsaye ya fara tunkarar daki, “ga fruits nan hada mana. Bari in rage kayan jikin nan nawa”.
Ya wuce daki ni kuma na tashi na shiga kicin na dauko plate da fork.

Bayan anyi sallar la’asar, Yaya ya fita waje. Nima sai na kulle sashen nawa na tafi na Anty Sarah. Nan yan sannu da zuwa suka yi ta zuwa suna samuna har yamma sosai tayi. Muka shiga kitchen dinta muka dafa abinci. Anan muka yi dinner kafin muka koma sashenmu.

*

Sai wajen karfe hudu na yamma muka dauki hanyar Abuja, ko a wajen su Ummah bamu tsaya ba, kai tsaye can muka wuce.
Tunda garin Allah ya waye Raheemah take kiran wayar Yaya tana tambayar yaushe zamu iso? Akalla ta kira yafi sau biyar, yanzu ma muna daukar hanya sai data sake kira, yace mata yanzu muka taho. Cike da murnarta da doki tace “to Allah ya tsare hanya, Allah ya kawo ku lafiya”. Yace “ameen”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button