A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Ai lokacin amarya Na’ilah babu ita. Tunda ya furta kalmar sunan Bilal, naji duk wata dauriya ta rike kafafuna su tsaya a tsaye ta bar jikina, karshe dai sai dana kai ga silalewa kasa.
Abu na karshe dana gani, shine confused fuskokin mutanen da suka yo kaina a rikice, suna kwala min kira, duhu ya mamaye ni gabadaya…!

*

Ban tuna komi ba lokacin dana tashi. Mutane hudu ne a kaina lokacin dana farfado daga suman da nake kyautata tunanin nayi. Janan da Anty Halima kadai na iya ganewa, sauran biyun tare suka zo da Anty Haliman daga Gashua, ban gane su ba.

Na tashi zaune, Janan tayi saurin tara filo a bayana yadda zan ji dadin jingina duk da protests dina na cewa kada ta damu.
Dakin da muke ciki daga gani babu tantama asibiti ne, ko kuma karamin clinic.
Janan ta bude gorar ruwan faro ta tsiyaya a cikin kofi ta miko min, na amsa na kafa kai na sha tare da mika mata, ta amsa ta ajiye.

Na dafe kaina da yake sarawa tunda na tashi, ina kallonsu.
“Me ya faru ne?”. Na tambaya cikin sarkewar murya, wincing lokacin da naji kaina ya kara sarawa kamar ana buga ganga.

Janan tace “Wanda zaki aura ne ya faru!”, duk yadda taso ta nuna tsana da venom a cikin muryarta, fuskarta dauke take da murmushi mai tsananin taushi.

Sai lokacin komi ya fara dawo min cikin kai daki-daki.

Na fara girgiza kai a hankali, kafin na fara da karfi ina ja da baya har sai da bayana ya hade da allon gadon. Na dora hannuwa biyu kai, ihu naso kurmawa, amma babu abinda ya iya fita daga bakina. Daga karshe dai na samu sautin, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Na shiga uku na lalace!!”.
Kafin naji na barke da wani irin kuka.

Anty Halima ta matso ta rungumeni jikinta ta fara shafa gadon bayana cikin alamun lallashi. Tace “ke ‘yar nan, ki kiyayi kanki ke kuwa, menene na shiga uku? Allah ya dube ki, ya baki miji na nunawa sa’a. Kowa yasan dama hakan da mamaki, ka auri wanda baka shiryawa ba, amma bai kamata kalma ta shiga cikin uku ta fita daga bakinki ba. Ki godewa Allah, Allah kadai yasan irin hikimar da take cikin wannan juyin lamari daya faru”.
Amma kuma kukan naci gaba dayi, har ma na yanzu yafi na dazu sauti.

Tun tana lallashi, har ta gaji, ta koma gefe ta zubawa sarautar Allah ido, tana kuma mitar ai sai inje inyi tayi, a kaina farau?, amma ban kulata ba.
Sai da nayi ya ishe ni, kuka share-share har da majina, ‘sai kace wadda aka aiko mata da sakon mutuwar uba, ba aure ba!’ a cewar Anty Halima bayan taga yadda fuskata ta baci da hawaye.

Janan tana gefe, kallona take daya bayan daya, babu alamun damuwa ko digo daya akan fuskarta sai ma amusement rather. Hakan ya kara tunzura ni.
Ta zari tissue ta miko min, na warta na share hawayen fuskata da majina, nayi jifa da tissue din can gefe guda.

Janan ta kasa danne dariyarta, tace “a’ah, baiwar Allah. Ba fa shi ya kar zomon ba, haka muma da kike wani huhhura mana hanci. Don haka idan ma zaki ware ne yarinya, ki warware”.

Na harareta tare da sake wartar wani tissue din na goge idanuna da suka cika da hawaye.
Nace “wane warwarewa kuma? Ai wallahi zuwa zasu yi su warware aurennan yadda suka kulla shi, don wallahi ba za ayi wannan kwamacalar dani ba! Idan kuma ba haka ba sai dai in bar musu garin wallahi!”.

Su duka suka yi shagara da baki suna kallona, kafin Anty Halima ta daga baki da niyar fara magana, “wannan wace maganar banza ce kike yi? Ke…”.

Maganar ta katse sakamakon kofar dakin da aka turo aka shigo, duk muka kalli kofar. Faduwar gaban data ziyarceni a lokacin da muka hada ido da ba kowa ba illa Yaya Bilal Allah kadai yasan irinta. Nayi saurin kauda kaina na kalli Yaya Mudatthir, daga ganin yanayin fuskarshi kasan cewa sun gama jin abinda na gama fada yanzu. Sai dai ban ji ko dar ba a cikin raina, hasalima can cikin raina cewa nayi gwanda da maganar ta shiga kunnen wanda aka yi dominta.
Fuskar Yaya babu yabo babu fallasa, ya cewa su Yaya Halima “Anty ko zaku dan bamu waje?”.

Babu musu suka fita suka bar dakin, suka barmu mu kadai. Yayan ya kalleni fuska cike da warning tsantsa, kafin ya shima ya juya ya fita, har da maida kofar dakin ya rufe. Na harari kofar kamar ita ta min laifin.

A hankali ya tako cikin taku dai-daya, yazo ya tsaya min aka kamar wani tsohon soja, ya zuba min ido. Ni kuwa naci gaba da kallon kofar da Yaya Mudatthir ya bi stubbornly.

Ganin an dauki lokuta masu yawa ba tare dana sake ko jin motsin shi ba, yasa na daga idanu a hankali na kalli inda yake. Yana tsaye a wajen har lokacin, ko yanayin tsayuwarshi bai canza ba, idanunshi manya tubarkallah dasu kamar na Janan, a kaina. Na turo baki tare da sake dauke kaina.

Ina jin sautin murmushin daya saki, ya ja farar kujera dake can karshen dakin, ya ajiyeta a gefena ya zauna.
Murya can kasa, kamar mai rada yace “ya jikin?”.

Nan ma ban ce komi ba, na kurawa mayafin da aka lullube gadon da nake kai idanu.

Ya sauke ajiyar zuciya, “ko ki amsa, ko kada ki amsa, hakan babu abinda zai sa, kuma babu abinda zai hana Na’ilah. Abinda ya faru dai ya riga ya faru…”.

Nayi saurin katse shi, “bai riga ya faru ba, ni wallahi ban yarda ba, aurennan sai an zo an raba shi, dama tun farko ai sai dana ce ba zan aure ka ba!”.

Yayi wani kicin-kicin da rai, “wannan kuma sai ki samu wanda ya daura auren kiyi mishi bayani, sai ya warware. Tunda nima ina zaman zamana sai kiran waya kawai naji ance za’a karbi wakilcin aurena, in kawo sadaki. Kin kuwa ga nima daga sama na tsinci maganar kamar ke dinnan”.

Nace “to haka ake aure, babu tambayar wadda zata yi zaman auren?”.

Ya daga kafada sama, “kamar yadda nace ne, zuwa zaki yi ki tambayi wadanda suka daura auren. Amma a shawarce, zan baki shawarar ki ma sauke wani girman kai, jiji da kai da jan ajin da kike yi, kamar yadda nace, abinda ya faru dai ya riga ya faru sai dai kuma a tari na gaba. Yakamata ki san irin kalaman da zasu fito daga bakinki, saboda da da yanzu ba daya bane, idan kinyi da na kyaleki, ina mai tabbatar miki da cewa yanzu fa ba zan kyaleki ba saboda a karkashin Ikona kike, saboda haka ki kula”.

Kawai sai na sa kuka, yayi zaune a gefe yana kallona bashi da niyar furta ci kanki, nayi na gama na share hawayena, nace “to dama haka ake auren ne, tun kafin aje ko’ina ka fara cin zalina da gindaya min sharadi”.

Yace “watch it Na’ilah! Yadda fa baki shiryawa auren nan ba, haka fa nima. To meye ma amfanin auren idan babu doka da sharudda? Abinda nake so ki sani shine, lokacin lallashi da bin kai ya kare tsakanina dake, tunda ke kafiyar kai tasa baki fahimtar komi sai an biyo miki ta bayan gida, let’s bring it on then. Ta kowace hanya kika bullo, nasan ta yadda zan taro ki.

Ke yanzu hakan bai isheki ishara ba? Ki hakura ki saddakar, ki mika wuya ga hikima irin ta Allah ba? Ni din dai da kika dinga gudu Na’ilah, kina ihu da sanarwar ba zaki aure ni ba, ni din dai kika buge da aure bayan kin gama kewaye-kewayenki. Dama kin hakura tun farko, kin kauda wannan girman kan da kike ji dashi, da yanzu muna cikin farinciki gabadayanmu. Amma yanzu wa gari ya waya? Saboda tsabar son kai da taurin rai irin naki, kinga abinda kika janyo mana ai. Yaushe rabon da kici abinci ya cika miki ciki? Yaushe rabon da kiyi barci mai dadi? Yaushe rabon da ki samu sanyin zuciya da sukuni a cikin ranki? Yaushe rabon da ki samu wadataccen kwanciyar hankali? Ki duba kiga yadda kika bi kika rame, kika kare kamar kudin guzuri? Ni da kika dinga gudun ma dai sai da nazo na fiki kwanciyar hankali da jindadin rayuwa. Hakan bai isheki ishara ba Na’ilah? Me kuma kike bukatar gani da zai tabbatar miki da cewa ba’a taba tsallake abinda Allah ya riga ya tsara maka? Duk zullewarka, zaka yi ne ka gama. At the end of the day dai, sai ka komawa wannan kaddarar taka!”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button