A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Daidai bayan gidanmu, na hangi wata yarinya Lubah, yar dakin Ramata ce. Anan cikin unguwar take, duk wata gulma da tsegumi daya taba gidanmu, daga gidansu yarinyar yake fara fita.
A durkushe na ganta, kamar tana tona kasa ko kuma wasa take yi? Sai waiwaye take yi da kalle-kalle, kamar dai wadda take tsoron wani ya ganta. Na dan yamutsa fuska in suspicion, kamar zan karasa in ga abinda take yi, sai kuma naga hakan ba hurumina bane, tunda ba shiga harkarta ko ta mutanen gidansu nake yi ba. Muka wuce ta.

A tsakar gidan su Kulsum muka zube ni da ita akan tabarma, muka cigaba da tattaunawa. Mun yanke shawarar zata je ta samu Kawunta tayi mishi bayani, zai je ya samu iyayen Mukhtar din sai suyi mishi magana. A cewar Inna, hakan zai fi kawai, in yaso idan ta tashi yin aure, ko kuma Muneerah din ta fara mallakar hankalin kanta, sai ta koma din. Tunda dai duk inda za aje a dawo, gidan mahaifin nata dai nan ne mutuncinta. Da wannan na musu sai da safe na wuce gida.

Washegari Laraba, nayi sa’ar samun Baba kafin ya tafi wajen aiki. Na gaida shi, ya amsa yana kora shayin da Alawiyya ta hada mishi, yayin da Ramata take gefenshi zaune a hakimce. Yadda nayi zaune a gabanshi, nasan cewa yasan dalilin yin hakan, amma ya basar dani.
Ban yi fushi ba, na kaskantar da murya, nace “Baba zancen registration dina?”.

Daga farko shiru yayi kamar ba zai yi magana ba, can kuma yayi gyaran murya, yace “kudin nan naki fa sai dai kiyi hakuri sai zuwa satin da zai kama. Ranar litinin zan biyawa kaninki kudin waec da neco, abubuwan zasu yi min yawa!”.

Wani abu daya kusa bani dariya shine, jarabawar waec da neco zata iya jira har nan da watanni biyar zuwa shida masu zuwa, tunda dai ba’a fara zancen yin ta ba balle akai ga saka deadline din wadanda basu biya ba zasu rubuta jarabawar ba da sauransu. Naso in tunatar dashi hakan idan ma mantawa yayi, yadda naga ya zubo min ido ne yana jira yaji ta bakina, Ramata ma da Alawiyya sun zubo min nasu suna jira inyi magana, kila dalilin haka Baban ma yayi fushi, satin samar ma yazo yace bashi da kudi, yasa na hadiye duk takaicina da kududun daya makale min a makoshi, nace “to babu laifi, Allah ya hore!”. Na tashi na kara gaba. Banyi kuskuren ganin yadda suka bini da kallo baki a dage ba.

Magana ta gaskiya ita ce, na gaji da takaicin da suke guma min. Daga Baban har su. A kullum, kuma a kodayaushe, hidimar kansu data ‘ya’yansu ita ce ta farko a idanunsu, koda tawa matsalar tafi bukatar agajin gaggawa, haka za ayi shagulatin bangaro da ni da lamarina, har sai an biya musu nasu bukatun. Idan kuma nayi magana, sai cibi ya zama kari. All tables will turn, and bets will be off. Sai laifi ya dawo kaina, ace na cika bakin ciki, su ce bana son cigaban su ko na ‘ya’yansu, su ce bani da godiyar Allah, daga karshe kuma su zo suyi sanadin wannan abin ba za’a yi shi ba kenan. Idan ma anyi, to a kurarren lokaci ne.
Saboda haka naga, meye amfanin yin maganar? Babu abinda hakan zai karas dani sai bacin rai. Meye kuma amfanin sanya maganar a cikin raina, again, sakamakon hakan dai bacin rai ne. Don haka nayi wurgi da maganar cikin kwandon shara, naci gaba da harkokina cikin kwanciyar hankali.

Sai dai Baban yana fita, sai ga Ramata ta fiddo dankareren Swiss lace daga daki, ta fito tsakar gida tana ba danta Aliyu da bai je makaranta ba, labarin jiya Baba ya bata kudin, dubu ashirin da biyu ta sayo, ya kara mata da dubu uku kudin dinki. Tace yayi maza-maza yazo ya kai mata shi wajen telanta ya watsa mata dinki na rashin mutunci, na shiga taron manya.
Nasan duk don inji haushi take yin hakan, sakonta kuma ya shigeni yadda yakamata, naji haushin. Sai dai wannan karon ma maimakon magana, sai na kada kaina na shige daki. Ai sai ina wajen sannan zata yi tunanin tsokano ni ko? Sai dai ga yadda na ga fuskar Alawiyya, to ta shaka da yawa. Nasan a cike take dam, kiris take jira ta fashe. Nasan kuma da Baba ya dawo zata tare shi da maganar, idan Allah ya taimaketa, ya dorata a kanshi itama ya siyo mata lace din ko ya bata kudin yace ta dinka. Wanda kuma da kyar ne, hakan sau daya yake faruwa a gidanmu a shekara.

A tunanina, idan mutum ya sai wa matarshi wani abu, itama dayar tana da hakkin ya sai mata irinshi, ko kuma ya bata adadin kudin daya batar wajen sayen abin? But no, banda gidanmu. Ban taba ganin haka ba, koda wasa.
Yawanci idan abu makamancin haka ya faru, sai dai hakan ya kare ga fada kawai. Ita Alawiyya bata hakura, kullum aka yi haka sai ta bukaci itama a bata nata kason, lokuta daidaiku ne Baban yake bata, basu fi a daga hannu a kirga su ba.
Wani lokacin tausayinta dana ‘ya’yanta yana cika raina, amma nafi tausayawa Ramata dana ‘ya’yanta.

Wunin ranar haka nayi shi smoothly. Da yamma ina kicin ina tuka tuwom dare, Maryam ta fado kicin din da sauri, wayata dana bata tayi kallo tana ringing a hannunta, ta miko min. Na duba naga mai kiran Janan ce, da sauri na daga ina murmushi.
“Hi…”, na furta a hankali, da niyar gaisuwa.
Tace “hii yourself, yaushe kike da niyar dawowa makaranta ne? Ni fa har na dawo Zaria”.
Na zaro ido cike da mamaki, “wow, lallai kina kaunar Zaria da yawa. Ni yanzu haka ban san ranar dawowata ba”.

Tayi dariya, “bana son shakiyanci wallahi, meye abin so a Zariar ne? Kinsan da maganar council exams dinmu ana tunanin kamar upper week fa za’a yi. Kinsan wasu lecturers har sun fara shiga aji kuwa?”.
Na dafe kai, “damn! Subhanallah! Daga dawowa?”.
Ta sake yin dariya, “exactly abinda na fada Saboda haka ki fara tattara naki-ya-naki, ki ciccibo kanki ki taho wallahi. Gobe in shaa Allah zan shiga in ga yadda ake ciki”.

Nayi shiru ina kallon wutar da take ci bal-bal a cikin murhu, da kyar na samu muryata, “ina tunanin kuwa sai dai inyi karatuna a gida. Ni da Zaria maybe sai upper week din”.
Tuni naji ta rikice, “ban gane ba, mai ya faru ne? Baki da lafiya ne? Ko wani ne a gida bashi da lafiya?”.
Nace “sam ba haka bane, ke da kika san banyi registration ba?”.
Tace “sai aka yi yaya?”
Banyi mamaki ba, nasan hakan zata fada, nace “sai bani da wajen zama. A kanki zan zauna in na dawo ba’a riga an bani daki ba?”.

Tace “ko baki zauna a kaina ba, kin zauna a dakina. Ki zo sai ki zauna dani kafin ki biya!”.
God!, wai komai ma sai nayi guessing dinshi daidai? Shima nasan abinda zata fada kenan, nace “nop… Nagode, amma zan jira a gida har sai na kammala komi sannan”.

Shiru ya biyo baya, again, nasan fada ne zai biyo baya, illa kuwa,
“wai Na’ilah, ni ce baki son zama dani ko kuwa me? Kada ki manta, last time ma abinda kika min kenan, hutun kirsemeti wannan na kwana hudu da aka bamu kin zuwa kika yi muyi a gidan Yaya, kika zauna ke kadai a daki kamar mayya. Yanzu ma kuma kina fada min wai zaki zauna a gida, baki son zama dani ne?”

Na kai hannu ina sosa bayan wuyana, ni dama nasan za’a rina. Nace “kamar ya bani son zama dake, ya ma zaki ce haka?”.
Wannan karon muryarta ta fara dagawa cikin alamun fada, tace “haka ne mana! Kada ki manta, duk lokacin dana miki tayin kizo mu zauna, ko wani abu makamancin haka, sai ki hau kame-kame kina wani kawo excuses. Me kike so in zata, idan ba haka ba?”.

Na girgiza kaina kamar ina gabanta, “wallahi ba haka bane Janan, ba haka bane. Kin san yadda muke sarai da matar Yaya da kuma kannenta, bana son harkar da zan je gidan mutane in zauna, wata magana da bata dace ba tazo ta fara fita. Ko kuma rashin hakurina yasa in zo inyi abinda zai janyo mana matsala, shine kawai”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button