A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Na sauke ajiyar zuciya tare da kurawa gadajen da patients suke kwanciya akai da suka kasance empty. Ban san lokacin dana dauka cikin tunani ba, sai da naji an dafa min kafada. Nayi firgigit! Na kalli gefen damana, Janan ce.
Murmushi na saki ina harararta cikin wasa, “wato tsabar shahara, yau sai karfe tara ma kika zo ko?”.

Tayi yar dariya, “to me yafi raina? Tunda an riga anzo anyi supervising dinmu, mun kuma yi presenting dinmu, ai babu abinda ya rage mana sai chilling. Yaya Bilal ne ma ya tsaida ni da jira, wai sai na jira shi ya karya sannan zai zo ya sauke ni. Kinsan na fada miki mun shirya dashi”.
Na gyada kai ina wasa da kan wayata, “yeah, haka kika ce. Yanzu idan muka gama ina kika nufa ne?”.

Tace “yo ni ina na sani? Watakila in tafi wajen Yaya Sa’a Funtua, ko kuma Kaduna wajen Umman mu. Ke fa?”.
Na harareta, “har wani tambayana ma kike yi? Bayan kin riga kin san komi?”.
Tace “to kizo muje wajen Umman mu mana kawai? Tunda dai ko kin je gidan ma ba wani jimawa zaki yi ba?”.
Nace “lallai ma, watanninmu kusan shida a makaranta fa, ban leka gida ko da wasa ba, kuma kinsan idan muka dawo hutu ma ba wani hutu zamu samu ba, gwara inje dai kawai”.
Ta kada kai gefe guda, “ai shikenan. In ka ki ji, ba zaka ki gani ba. Amma ai ba a goben zaki tafi ba dai ko?”.
Nace “a’ah, sai ranar assabar in Allah Ya kaimu”.

Kiran da daya daga cikin nurse din ta kwala mana, shine ya katse mana hirar da muke yi, muka tashi muka tafi wajen data kira mu.

Ranar ma karfe daya muka tashi. Janan ta sake ja na zuwa gidan Yaya Bilal, wai in taya ta hada kayan tafiya. Yau mun ci nasarar samun Anty Raheemah a gida. Tana zaune a falo sun kure kida ita da kannenta, wasu suna rawa, wasu kuma a zaune kawai suna kallonsu. Muka musu sannu da gida, suka amsa a kaikaice. Bamu kula su ba muka wuce dakin Janan abinmu.

Da yamma wajen karfe biyar, na mike ina rataya jakata. Janan ta shigo dakin hannunta rike da wasu ledoji biyu, tace “Yaya Bilal zai shiga Samaru yanzu, yace zai rage miki hanya”.
Na zaro ido, “what? No!! Kada ma ya wahalar da kanshi wallahi, zan bi bus kamar yadda na saba”.
Ta harareni, “jibe ta don Allah! To ya riga yace zai kaiki, yanzu haka yana jiranki ma a waje. Sauri yake yi, yau a gidan Anty Ameerah zai kwana, kuma dawowarshi daga Kaduna kenan, so yake yi yaje ya huta”.

Na dafe kai, “to menene na wahalar dashi akan cewa ya wani sauke ni a school? Da kin barshi yaje ya huta abinshi”.
Tace “sai kiyi kuma, tunda sabonki ne yin korafi. Yaya dai yana waje yana jiranki, idan kin tsaida shi, damuwar ki ce. Gashi Umma tace a kawo miki”.

Ta miko min daya daga cikin ledojin hannunta, na leka kaina cikin ledar. Turare ne, kayan biscuits da chocolates har da yan kunne da takalmi mai kyau. Umman su Janan tana yi min wani kallo ne kamar yadda take kallon Janan. ‘Diyarta, ‘ya kuma mafi soyuwa a gareta.
Duk wani abu da zata yiwa Janan, sai ta hada da ni. Ko ina nan, ko bana nan, ko ina sane, ko bana sane, zata bani da hannunta, ko ta bada a ajiye min.
Shi yasa nake matukar girmama matar. Ko ba don alkhairin da take yi min ba, don yadda take daukata kamar diyarta. Idan nayi wani abu da bai dace ba, zata kira ni ta zaunar dani, ta bani duk wata shawara da uwa ta gari ya dace ta bawa diyarta, ta tsaya daram, akan kafafunta, wajen dora ni akan hanya, duk da cewa bamu hada ko digon gumi ni da ita ba.
Ko a hakan kadai aka tsaya, wallahi ta gama min komi. Balle kuma ayi zancen irin alkhairanta a gareni.

Duk abinda zata yiwa Janan, ba ta taba bambanta mu, sai dai ko kala da tsayi.

Na kalleta ina murmushi, “Madallah da wannan sako, lallai Umma ta gano ni. Bari in koma sai in latsa mata kira inyi godiya. Na gode kwarai”.
Tayi dariya, “ai fa! Yanzu ke dai mu tafi, kada Yaya ya gaji da kira”.
Kamar yana ji, sai ga kiranshi ya shigo wayar. Ta daga tana ce mishi gamu nan fitowa, ban san me yake ce mata ba, na dai ji tana cewa “minti daya!”. Ta ja hannuna muka tafi.
Sai da na leka ta dakin Anty Raheemah muka mata sallama, sannan muka fita ni da Janan.

Yaya Bilal yana cikin motarshi a zaune, ya zuro kafarshi daya waje. Kyakkyawan takalmin D&G baki, budadde na fata yana ta sheki a kafar tashi. Na gaida shi kafin na zagaya ta daya gefen na shiga gefen mai zaman banza.
Janan ta leko tana min Allah ya kiyaye, yayin da Yaya ya tashi motar muka fita daga gidan.

Tafe muke a cikin motar, babu wanda yake furta uffan. Sai sautin wakar “earned it’ ta weekend dake tashi a nutse. A hankali nake bin wakar, ba lallai ka sani ba sai idan ka kalli bakina sosai, inda zaka ga yana motsawa kawai ba tare da sauti ya fita ba.

Idanuna suna ta tagar gefena suna kallon cikin garin Zaria. Na dinga jin alamun idanu a kaina, nasan cewa zargin hakan ne kawai nake yi a cikin raina. Da abin ya girmama, sai na juya a hankali cikin dabara, na kalli inda Yaya Bilal yake, idanunshi straight suna kallon gabanshi. Na girgiza kai, dama sai da nace zargine nake yi.

A kofar Bitmas Bakery naga yayi parking motar. Ya kashe tare da fita daga motar yana muttering “excuse me!”. Wanda ba don na juya a daidai lokacin idanuna sun sauka akan fuskarshi, na ga bakinshi ya motsa ba, ba zan ji mai yace ba.
Na zaro wayata a cikin jaka ina dubawa don in rage kadaicin zama.

Bayan kimanin mintuna biyar da fitarshi, naji an kwankwasa gilashin tagar motar, gefen inda nake zaune.
Na daga kai, naga Umar a gefen a tsaye.

Nayi murmushi tare da sauke gilashin kasa, “hey handsome, me kake yi anan?”.
Shima yayi murmushin, “wai mun tsaya ne zamu sayi fruits fa, ina jiyowa kuma sai na ganki. Daga ina?”.
Nace “daga gidansu Jan. Tare muke da Yaya Bilal, zai sauke ni a makaranta”.

Ya gyada kai, “uhmmn… Ya shirye-shiryen tafiya gida? Jibi zaki tafi ko?”. Nace “ehh!”.

Yana nan a tsaye muna hira, Yaya Bilal ya dawo. Kwata-kwata ban ga wucewar shi ba, sai da ya bude motar ya shigo. Na kalli Umar ina murmushi, “handsome, bari mu wuce ko?”.
Ya gyada kai, “Ok Sweety, zamu yi waya ko?”.
Na jinjina kai, “in shaa Allah. See you!”.
Har ya juya ya tafi, sai kuma ya juyo da sauri, “hey, bari in miko miki fruits”.

Na daga baki da niyar cewa na gode, Yaya Bilal ya katse ni ta hanyar yiwa motar key. Ya kalli Umar, “ta gode, sauri muke”. Da wannan yaja motar. Ina hango Umar ta cikin gilashi yana daga kafada.

A main gate na kalleshi nace “Yaya ko zaka ajiye ni anan kawai, sai in karasa ciki?”.
Yadda kasan bango, haka ya maida ni. Bai ma nuna alamun yaji abinda nace ba, sai ma ya karawa motar wuta ya shige ta cikin makarantar.
A bakin hostel ya samu waje yayi parking din motar, na fara yunkurin bude kofar ina jera mishi godiya,
“na gode Yaya, a gaida Anty Ameerah”.

Sai da na fita, ina kokarin maida kofar in rufe, naga yana miko min leda mai dauke da tambarin Bitmas, na kalleshi fuskata dauke da alamun tambaya, kafin inyi magana ya riga ni, “karbi mana, kina bata min lokaci!”.

Nasa hannu biyu na karba, nace “nagode, Allah Ya amfana”. Yace “Ameen” a kaikaice, yawa motarshi wuta ya kara gaba. Ni kuma na shige cikin hostel.

Sai bayan sallar magriba dana gama komi, na bude ledar. Bread ne da roll cake da suke yi a wajen guda biyu, da ice cream biyu shima. Na dauki daidaya na mikawa Ayla, tana ta min tsiya, wai “lallai yau Umar ya tuna damu!”. Dariya kawai na mata na koma gefe ina cin nawa. Sai da na gama ci sannan na tashi na hau hada kayan tafiya gida.
Bayan na gama, na turawa Baba sako akan cewa zan taho ranar Asabar, ya turo min kudin motar tafiya gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button