A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Nace “Aliyu!! Meye haka kuke yi?”.
Duk suka dago a tsorace suna kallona, sai dai idanun Aliyun kyar suke a kaina, babu ko dar a cikinsu.
Na harari abokan nashi da suka yi cirko-cirko a zaune, nace “ku tashi ku fita”. Babu musu suka mike sumi-sumi suka fita daga dakin.
Na maida kallona ga Aliyun, nace “kai yanzu abinda kake yi dama a cikin dakin kenan kai da abokanka? Shi yasa kullum kuke shiga ku rufo daki a rasa abinda kuke yi?”.

Ya mike tsaye yana wani muzurai, “to meye hadin mutum dani? Naga cewa dai rayuwata ce bata uban wani ba! Meye hadinki dani?”.

Nace “ko banza naci darajar kasancewa yayarka Aliyu. Wannan sam ba dabi’ar data dace bace, ka rasa a inda ma zaka sha shisha sai a gidan mahaifinka?”.
Caraf! Sai Ramata ta cafe maganar, “kinga kada ki sake cewa d’a na yana shaye-shaye. Gwanda ma shi an san abinda yake yi, kuma a gabanmu yake. Ke waya san wace tsiyar kike yi a can?”.

Na kalleta idanuna har juyawa suke yi saboda yadda maganganunta suka dake ni, nace “ke kan ki kinsan cewa nafi karfin yin wannan rayuwar da kike ambatowa, kuma karya kike yi kice saboda bana gaban iyayena zanyi rayuwar da bata dace ba!”.

Ai sai shima Aliyun ya hayyako min, “kada ki kuskura ki zagar min uwa fa!. Ba gaskiya ta fada ba? Ke har kina da bakin kirana dan shaye-shaye??”.
Nace “Aliyu ka kiyaye ni, kada bakinka ya sake kuskuren ci min mutunci!”.
Sai ya kara matsowa daf dani, “idan naki fa? Nace idan naki fa? Kashi zaki bani? Ke din banza! Ke har kin isa ki zauna kina gaya min kabli da ba’adi? Wallahi idan baki kiyaye ni ba sai in kwantar dake anan wajen!!”.
Ramata tace “yayi daidai da na. Yanzu na tabbatar da cewa nice na haife ka! Ka cika da!!”.

Inna data jiyo hayaniya da wata Assibi makociyar mu suka shigo, itace ta tari bakin Ramata din, tace “haba ke kuwa! Da girmanki zaki biyewa yara har ki goya mishi baya. Yanzu ko Na’ilah bata girmi Aliyu ba, ai tana da damar idan yayi abinda bai yi daidai ba ta kwabar mishi!”.

Sai ta harari Innar, tace “yo meye a cikin shishar? Uban wa yace miki kayan shaye-shaye ne ita?”.
Inna ta kama baki cike da mamakin zagin data yi. Assibi tace “amma kuma ai daga nan yara suke ganin hanyar shaye-shayen ko?”.

Sai Ramata ta kara kumbura, ta karkace daurin dankwali ta kawo shi goshi ta kafe. “ni fa dama ina sane da duk munafurcin da kuke min a cikin unguwar wannan musamman ma ke!”, ta nuna Inna. “Na’ilah tana zuwa gidanku kuna zagina da gulmata. To wallahi ta Allah ba taku ba! Kuma ni da ‘ya’yana nan gani nan bari. Idan ma wani kulli ake musu don su lalace to wallahi sai dai dan wani ya lalace don ni naci dubu sai ceto! Kuma bari uban Na’ilar ya dawo, sai ya gaya min in uban wani ne ya haifar min diyana ko ni!!”. Ta kama hannun Aliyu suka shige dakinta ta barmu anan a tsaye.
Assibi tace “to kuwa Allah ya kyauta miki gaskiya lamarinki sai du’a’i!”.
Tuni mutane har sun fara shigowa gidan jin hayaniya. Inna da Assibi ne suka kore su, bayan sun tafi suka lullube ni suna bani hakuri. Ban iya magana ba, na zame na shige daki.

Ina shiga daki jikina ya shiga rawa, na zame gefe katifa na zauna. Ban iya rigima ba ko kadan. Sam bani son rigima. Barni da tsiwa dai da mita, da kuma rashin barin ko ta kwana. Abin ya min ciwo kwarai da gaske, kanina wanda na bashi shekarun da suka fi yatsun hannu, zai tsaga tsakiyar idanuna yaci mutuncina a gaban uwarshi. Kuma nasan cewa ya zage ni a bulis, nasan cewa ko na gayawa Baba babu abinda zai yi akai.

Abubuwa irin wadannan ba yau ne suka fara faruwa ba, kuma kowane lokaci haka abin yake, ya zageni, kuma bani da bakin ramawa ko na kai korafi, sai dai in shige daki in shaki kuka. To na gama kukan. Nayi alkawarin in dai akan Aliyu da uwarshi ne, to na daina kuka.

Wayata na janyo, banyi tunanin komi ba na dannawa Ya Mudatthir kira. Ina jin sautin muryarshi, naji na fashe da kuka. Take naji ya rikice, ya fara tambayata lafiya? Me ya faru? Duk yadda naso in daina kukan kasawa nayi, sai da nayi mai isa ta, sannan na fara zayyane mishi dukkan abinda ya faru tun daga farko har karshe. Nasan wasu abubuwan kawai yaji su ne ba don ya fahimta ba, saboda yadda muryata dama jikina suke rawa.

Bai katse ni ba har na gama mishi bayanin, sai dana gama sannan ya fara jefo min tambayoyi. “ita babar tashi me tace ne?”.
Nace “itama fada ta hau yi, tana cewa wai nace mishi dan shaye-shaye, kuma ni wallahi ban ce mishi haka ba. Kawai magana ce na mishi!”.
Yace “na sani Na’ilah, nasan ba zaki ce mishi haka ba. Zan kira Baban anjima, yana nan aka yi?”
Nace “a’ah, baya gida”.
Yace “to shikenan. Kina son zuwa nan ne?”.
Da sauri na hau daga kai kamar yana ganina, nace “ehh!”. Yayi yar dariya, “to shikenan, zan turo miki kudin mota. Idan zaki iya tahowa gobe, sai ki taho. Idan kuma baki samu dama ba, sai ki bari sai jibi”.
Nace “to Yaya, nagode. Allah ya kara girma”.
Muka yi bankwana dashi na kashe wayar.

Sau tari ina fata dama ace ni ce na samu damar da Yaya ya samu. Yana gaban danginmu lullube dasu hankalinshi kwance. Tun lokacin daya gama sakandire, Yobe ya koma yayi degree dinshi acan. Da Allah ya taimake shi ya samu aiki yana gama makaranta, sai ya zaune acan abinshi. Ni kam tsakanina dasu sai dai zuwa hutu, ko kuma idan wani daga cikinsu yazo, ko kuma wata sabga ta biki wanda Baba bai cika bari na naje ba.

Duk da hakan akwai shakuwa da kusanci a tsakaninmu dashi sosai. Yana so na kuma yana tattalina.

Ina gama sallar isha’i na hau hada kan kayana waje guda. Maryam da take kwance tana kallo ta kalleni, “wai garin zaki bari ne kike hada kaya?”.
Nayi dan murmushi, “wallahi kuwa”.

Ta tashi zaune, “ba dai akan rikicin dazu bane ba ko?”. Tunda aka yi abin ma ni babu wanda ya tuntube ni da zancen, sai naji abin ya dawo min sabo.
Na girgiza kai, “ko kadan. Dama ina son zuwa”.
Tace “to shikenan. Ki dai kara hakuri don Allah. Mama ta daure mishi gindi da yawa wallahi, ni kaina rashin kunya yake min, bani da yadda zanyi dashi kuma”.
Kai kawai na iya daga mata don bana ma son maganar tayi tsawo.

Washegari tunda safe nayi wanka na shirya tsaf, na fito da akwatuna na ajiye a kofar daki nayi sallama a kofar dakin Baba. Sai da aka amsa min sannan na shiga.
Yana zaune a kan kujera yana duba jarida, na durkusa a gefenshi na gaida shi ya amsa. Nace “Baba zan tafi Gashua!”.

Nayi zaton ma zai yi magana akan zancenmu da Aliyu, ga mamakina bai ce komi ba, sai tambayata da yayi, “shi wanda yace kije din, ya baki kudin mota ko? Don bani da kudin da zan baki”.
Na gyada kai, nace “ehh”.
Yace “to madallah. Allah kiyaye”. Daga haka ya maida kanshi ya cigaba da karatun shi. Na tashi na fita daga dakin.

Sai dana bi su daki na musu bankwana, Maryam ta taya ni daukar akwatina muka fita. Na shiga gidan su Inna su ma na musu sallama. Kulsum da Maryam suka raka ni har bakin titi kasancewar babu ababen hawa tunda safiya ce sosai, na tari adaidaita sahu na hau muka tafi tasha. Motar Kano na hau, tana cika muka dauki hanya.

           *☆⋆05⋆☆*

Tunda muka isa Kano da misalin karfe goma na safe, muka hau motar Gashua. Sai a tasha na samu yogurt mai sanyi da cake na ci. zuwa karfe sha daya muka dauki hanya. A Hadejia muka tsaya aka yi sallah tare da cin abinci, muka sake daukar hanya. Karfe biyar da yan mintuna muka shiga garin Gashua.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button