A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Tsananin mamakinshi ya dankarar dani a zaune, na kasa motsi. Bakina nake motsawa ina so inyi magana, in maida mishi martani ko yaya ne, amma kamar ansa zare da allura an dinke min shi, na kasa buda shi.
Ganin haka yasa ya cigaba da magana babu kakkautawa, “meye bana miki? Meye bana baki?? Idan ma abinda nake miki ne bai isarki, kema kinsan ai ba sai kin zauna kina wani shan kwana ba, ki fito ki fada min mana ki ga idan ban baki ba yanzu take! Meye na roki ki min? It’s just a kiss fa! Meye a cikinshi?”.

Sai lokacin naji bakina ya motsa, saboda tsananin bacin ran da maganganunshi suka haifar min yasa naji jikina yana wani irin rawa, nace “sau nawa kake so mu yi wannan maganar da kai? Jikina ba jikim banza bane da zan sakar maka shi kawai saboda kana yi min hidima. Na fada maka ina bukatar abubuwan da kake yi min ne? Na taba daga baki na tambayi wani abu a wajenka? Ko kuma na taba furta maka ina bukatar irin rayuwar da kake son yi? Kawai saboda kai kana ganin irin wannan rayuwar itace wayewa, ni a ganina ba hakan bane. Ba zan taba yin rayuwar zubda mutunci ba, ba zan taba zubar da mutunci da kimata ta ya mace ba akan mata’ul hayat, abubuwan da zasu kare cikin dan kankanin lokaci, saboda haka ka bude min kofa in fita!”.
Cikin saurin magana da bacin rai nake maganganun, nasan da kyar ne idan ya fahimci duk abinda na fada.

Ya sauke ajiyar zuciya, “come on Na’ilah! Ni fa ban ce ki bani kanki ko wani abu ba, kawai kananun abubuwa nan da can ne fa, what’s the harm in it? At least ki dan dinga appreciating dina mana!”.

Na galla mishi harara, “kai a wajenka ba komi bane, saboda shaidan ya riga ya rufe maka idanu, amma ni a wajena it’s a big deal. Kada ka manta, mun taba yin wannan maganar da kai, na fada maka idan kasan wani abu kake bukata daga wajena yafi mana sauki mu yanke alakarmu, don babu abinda zan iya maka. Ba zaka taba taking advantage dina ba Umar, ba zaka taba yin amfani da kayan banza ka yaudare ni ba wallahi, in Allah ya yarda nafi karfin haka. Don haka ka bude min kofa in fita tun muna shaidar juna ni da kai wallahi. Kuma ga wayar ka nan, bana so, kai bana so in kara ganinka ma!!”.

Na hau kici-kicin bude kofa da sauri kamar wadda ta fita daga cikin hayyacinta. Ina ji yana kiran sunana amma nayi banza dashi. Ban tantance ba naji saukar hannunshi yana dafe min hannu, banyi wata-wata ba na wancakalar da hannun nashi can gefe. Bai daddara ba dai ya sake dafa kafadata, wannan karon dana kama hannunshi, twisting nayi da karfina duk da nasan ba lallai yaji zafin hakan ba, duba da yanayin aikinshi.
Cikin tsananin bacin rai da tunda muke dashi bai taba ganin kwatankwacinsa ba, daga murya da tsawa nace “kada ka sake taba ni!! Kada ka sake kuskuren taba ni!! Kuma wallahi ka cuce ni da kayi tunanin zaka iya saya na da kyale-kyalin banza, in shaa Allahu sai Allah ya saka min. Ka bude min kofa nace!!”.
Tsananin ihun da nayi ni kaina ya bani mamaki balle shi. Ina jin hakan ne yasa bai ma san lokacin da hannunshi ya danna madannar ba, ina jin na taba murfin ya bude, na fita daga motar da sauri. Ko sakan biyu ba ayi ba naji shima ya fito, ya hau auna min kira. Babu ko waiwaye, na shige gida da sauri.

Jikina rawa yake, hannu, kafa, baki, kai, komi nawa rawa yake yi. A daidai parking space dinsu na tsaya, na dafa wani pole ina haki kamar wadda tasha tseren rai da rayuwa. Kodayake kusan hakan ne.
Tunanina daya a lokacin, da ace yaki bude kofar fa? Me zai faru da yaki bude kofar? Me zai faru idan bai daina taba ni ba? Me zai faru idan wajen da muke babu mutanen da zasu ji ihuna idan ina ihun neman taimako? Tambayoyin suka yiwa zuciyata yawa. Ban san lokacin da gwiwoyina suka saki ba, na zube akan gwiwata a wajen. Allah kadai yasan iya lokacin dana dauka a wajen, ban ma san a wani hali nake ciki ba. Kai ban ma san ina hawaye ba sai da naji lema da alamun gishirin hawaye akan lebena sannan na ankara. Sai kuma vibrating din da wayata take tayi babu kakkautawa. Na daga na ga sunan Umar yana rawa a jiki, tsaki na ja nayi declining, yana katsewa wani kiran ya sake shigowa. Wayar na dauka gabadayanta na kashe.

Na mike na kakkabe jikina tare da share hawayena. Sai dana tabbatar da na dawo cikin nutsuwata sannan na wuce cikin gida. Su duka suna falon suna kallo banda Janan, na musu sannu na wuce ba tare dana jira naji sun amsa min ko basu amsa ba.

Janan tana tsaye a tsakiyar daki da waya a kunnenta, ina shiga ta sauke wayar, “yanzu fa nake kiran wayarki, sai kuma naji ta kashe”.
Na kalli wayar kafin na kalleta, “kashe ta nayi”.
Ina tunanin bata kula da yanayin da nake ciki ba sai a lokacin, da sauri ta matso wajena, fuskarta dauke da alamun damuwa, “lafiyarki lau? Me ya faru??”.
Na girgiza mata kai, “babu komi fa!”.
Ban jira amsarta ba na yaye gyalena na rataye na shige bandaki. Alwala na dauro na fito.

Janan ta bini da kallo har na shimfida abin sallah, bata ce komi ba. Har na gama shafa’i da wutiri, na fara shirin saka kayan barci. Tasan ko ta dameni ma babu abinda zan iya gaya mata, sai ma karin bacin rai da hakan zai haifar min, don haka taja bakinta tayi shiru, tasan duk lokacin dana sauka don kaina, zan fada mata. Babu boye-boye a tsakanina da ita.
Instead sai tace “idan kin gama kafin mu kwanta, ki zo in danyi briefing dinki akan abubuwan da muka yi wannan satin”.
Kai kawai na iya gyada mata. Dana gama shiryawan, naje gefenta na zauna, ta dauko littafinta ta bude ta fara min bayani.
Zuwa lokacin da muka gama, na dan fara saukowa daga fushin, haka ma zafin zuciyata ya dan lafa, amma duk da haka abin yana makale a cikin raina.
Kai har lokacin dana kai ga kwantar da jikina akan katifar Janan da niyar inyi barci, abin yana makale a cikin raina. Nasan cewa shi da fita har abada.

  *☆⋆08⋆☆*

Da azumi muka tashi washegari, bayan munyi sahur, wanda ni ruwa kawai na iya sha, muka yi nafiloli har aka kira sallah, muka yi.
Janan ta tashi zata fita bayan gari ya fara yin haske kadan, lokacin na gama azkar dina kenan. Na dubeta cike da alamun tambaya, tace “breakfast zan je in hada, kiyi wanka kafin in fito”.
A zato na ko haka dokar gidan take, don haka naga bai kamata in barsu suyi aikin su kadai ba. Na tashi na saka karamar hijabi akan kayan barcina, duk da ba masu fitar da jiki bane, kuma Janan tace Yaya a gidan Anty Ameerah ya kwana, still ba zan dauki chances ba. Sai dai ina zuwa kitchen din nayi turus, ganin Janan ita kadai a tsakiyar madaidaicin kicin dinsu tana kokarin dora tukunya akan gas. Na shiga ina karewa kicin din kallo, “ina sauran?”.

Da sauri ta juyo ta kalli inda nake, ina tunanin bata tsammaneni a wajen ba shi yasa taji abin unexpected, “su wa fa?”. Ta tambaya lokacin da take kokarin zuba mai a cikin tukunyar.
Na kada idanuwa, “ina nufin sauran wadanda kuke zaune a gidan dasu, ba zasu fito kuyi aikin tare bane?”.
Ta danyi murmushi cikin girgiza kai, “ni kadai nake aikin dama can!”.

Na zaro ido, “say what??!”. Ta kwashe da dariya, na harareta, “wannan ba abin dariya bane Jan, this is serious! Ta ya za ace gardawan banza suna kwance sun saki baki da hanci suna barci, ke kuma zaki dage ki girka musu abinci? Wow! Ko da kike cewa suna sakar miki aikin gida, ban yi zaton har da wannan ba ai”.
Tayi yar dariyarta a sanyaye, “ni ban ga abin daga jijiyar wuya a cikin wannan lamari ba. Na riga na saba ne, har ya zame min jiki wallahi. Sannan yawanci kafin Yaya ya wuce Abuja yana biyowa ta nan yayi karin safe, shi yasa nake tashi in hada, sai kuma abin ya zame min jiki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button