A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Dadina da Umar kenan, kulawarshi a gareni na matukar tafiya dani. Nace “lafiya lau fa, kawai nazo ganinsu ne!”.
Yace “good. Shine kuma sai yanzu kike fada min ko?”.
Nayi dariya sosai, rigimar Umar watarana tafi karfin mai rai.
Mun dauki kusan mintuna goma muna sa’insa akan ban fada mishi ba, daga baya dai ya saki zancen muka shiga wani kan yanayin aikinshi.
Sai dana fara jero hamma sannan muka yi sallama dashi, “goodnight dear, dream of me fa! Zan kira ki gobe ki bani labarin kalar mafarkin da kika yi”. Abinda yace kenan kafin ya kashe wayar.
Nayi murmushi kawai tare da ajiye wayar a gefen gado. Nayi addu’ar kwanciya barci tare da jan abin rufa zuwa jikina tare da rufe idanuna.

*

Funkasu muka ci a matsayin abincin kari. Ina gamawa nayi wanka na shirya na tafi gidan Yaya. Naci sa’a yana gida bai kai ga fita ba. Yana aiki ne da wani research institute. Na gaida shi ya amsa. Sailuba ta fito daga daki tana murmushi, “yanzu nake cewa ya kira ki kizo ki ci abinci”.
Na kalli inda take nuna min, kuloli ne a shirye akan ledar cin abinci. Na shafa cikina, “abincin nan sai dai ko anjima don yanzu dai kam cikina a cike yake”.
Tace “to ai shikenan”.

Yaya ya mike zai wuce, na mishi Allah kiyaye, ita kuma ta bishi zata mishi rakiya. Yace “kada dai a yi nisa Na’ilah, na san ki da yawo. Duk ranar da kika zo haka zaki ja matata ku shiga gari sai na nemo ku”.
Nace “Yaya sau daya ne fa ka taba nemo mu”.
Yace “oho dai. Idan dai kuka dade, babu fita gobe!”.
Nayi dariya “matar ka zaka ja wa kunne kuma wannan, ita ce mai son yawo bani ba”.
Yace “ni dai na fada muku!”. Daga haka ya fita.

Ina zaune a inda suka barni ina wasa da kan wayata ta dawo, tace “bari in shirya sai mu fita ko? Abincin sai mu tafi dashi gidan Yaseerah mu ci”.
Na gyada kai, “haka za ayi”.
Ta shige can kuryar daki ni kuma na cigaba da danne-danne na har ta fito sanye da riga da zani na atamfa, hannunta rike da jaka da hijabi. Na bita da kallo kafin inyi sequeling na fara tsalle akan kujera, “ke matar Yaya sai kice kin kusa sauke mana baby!”.

Tayi sauri ta ja rigarta kasa tana hararata kasa-kasa, “ni kada ki min ihu anan. Don mayuntaka har kin hango abinda ko wata uku bai rufa ba!”.
Na daga mata gira ina dariya, “haba mata, kada kiyi underestimating dina ta wannan fannin!”.
Ta shafa cikin tana dan murmushi, “ku dai taya mu da addu’a dai kawai, Allah yasa mai tsayawa ne”.
Murmushin tsokanar kan fuskata ya dusashe, sau biyu tana yin barin ciki, likitoci sun ce mahaifarta bata da karfin da zata dauki ciki ne, saboda haka aka mata daurin mahaifa.
Na dafa kafadarta ina murmushi reassuringly, nace “da yardar Allah babu abinda zai faru, zaki haifo mana babynmu lafiya lau, in samu takwara!”.
Hakan yasa ta saki dariya a tausashe, ni kuma nayi murmushi, tace “muje, Yaseerah har ta fara danno min flashing”.
Nayi dariya tare da ciccibar kwandon da ta saka abincin data ajiye mana, muka fita.

Yaseerah diyar Baba Adama kanwar Mama ce. Su hudu ne a wajen su Bako duka mata, Inna Talatu ita ce ta farko, tana aure a Damaturu, sai Mama na, Iya Lami da Adama, su duka suna nan Gashua ne. Yaseerah, ni, Sailuba, Ma’u kanwar Sailuba da Lawisa kanwar Yaseerah duk tare muka taso dasu, kusan duk sa’annin juna ne mu. Yaseerah a shekara daya aka aurar dasu ita da Sailuba. Yanzu har tana da yar diyarta Hafsat.

Gidan Yaseerah muka fara zuwa, a shirye muka sameta tsaf tana jiranmu. Bayan mun gaisa da yin yar hirar yaushe gamo, muka ci abinci, daga nan muka fita.
Gidan Iya Lami dake nan unguwar su Yaseerah muka fara shiga muka gaidata. Daga can muka biya gidan Marigayi Malam Mati muka yi gaisuwa.
Yinin ranar dai a haka muka gama shi. Shiga nan fita can, sai wajen karfe biyar muka koma gidan Sailuba.

Yaseerah da Ma’u suka koma gidanta, ni na tsaya wajen Sailuba. Sai da na taya ta tayi girkin abincin dare, sannan na mata sallama na tafi, lokacin har an gama sallar magriba.
Nayi sallama na shiga dakin Fatsu. Tana zaune akan abin sallah tana lazumi a tsakiyar daki, ta bini da kallo lokacin da nake ajiye hijabin dana cire akan gado.

Tace “wato Na’ilah kina nan da yawon nan naki ko? Yanzu saboda Allah ace kin fita tunda sanyin safiya amma sai yanzu zamu ganki? Saboda kin raina mu ne ko me? Idan a gaban mahaifinki kike kina wannan yawace-yawacen ne na babu gaira babu dalili?”.
Nace “haba Fatsu, ya zaki ce wai ina yawo? Ziyarar yan’uwa ce fa nayi, zumunci. Kuma a gida yawon me zanyi? Bani da kowa acan sai nan din dai, kin san haka”.
Tace “ai sai kiyi tayi, tunda bakinki bai iya bada hakuri ba balle ya iya amsa laifin da yayi!”.

Na koma gefenta na zauna ina yar dariya, “to naji Fatsu na, Allah ya baki hakuri, na tuba na bi Allah na bi ki. In Allah ya yarda gobe babu inda zan je, a kugunki zan wuni. Kinji dadi?”.
Ta dan harareni cikin wasa, gefe daya kuma tana kokarin danne murmushin da take yi, tace “Allah yasa, kullum ke dama maganar ki daya, amma baki cikawa!”.
Nace “in Allah ya yarda wannan karon da gaske nake, I’ll be all yours gobe!”.

Kamar yadda nayi alkawari, washegari a gidan na yini, ko nan da kofar gida ban leka ba. Da yake ba wasu ayyuka muka yi a gidan ba, na shiga dakin Malam na fiddo kayan ciki gabadaya na sharo dakin tas, na maida na sake mishi wani sabon shirin.
Da yamma bayan nayi wanka, na dauko littafaina da textbooks dana taho dasu ina bita. Nasan cewa nan da sati daya ne zasu fara zancen mu koma makaranta. Bana bari koda wasa in shantake a gida idan naje hutu, ina da lokuta na musamman da nake warewa, lokaci zuwa lokaci na kan dauko littafaina inyi bita musamman akan courses din da zamu yi a semester ta gaba ko kuma wadda muke cikin yi.

Da dare bayan isha’i muna zaune akan tabarma a tsakar gida. Bura-busko muka ci, (tuwon biski/tuwon tsakin masara ko na gero), wannan karon na masara ne muka yi, da miyar kuka da man shanu. Kamshin tuwon ma kadai ya isa yasa yawun mutum tsinkewa balle dadin da yayi. Malam yayi baki, tare suka ci abincin shi da bakin a dakin soro inda ya saba ajiye baki na nesa.
Bayan mun gama cin abincin, na koma na zauna ina taya Fatsu hade kayan sakar da tayi da zare, kasancewar babu wutar lantarki, hasken farin wata ne tar ya mamaye kafatanin tsakiyar gidan, sai kuma hasken wutar candle dana kunna daya kara taimakawa wajen kara haskake wajen.
Ita tana gaban murhu tana zubawa almajirai abinci. Malam ya dauki nauyin ciyar da kananan almajirai wadanda karfinsu bai gama kaiwa ba. Yanzu ya daina karbar almajirai na nesa ma, sai wadanda suke cikin Yobe kawai, kuma garinsu bai yi nisa ba.
Manyan tsofin almajiranshi kuwa tuni ya yaye su, wasu sun koma garuruwansu. Yayin da wasu suna nan cikin Gashua, wasu sunyi aure, wasu suna sana’o’insu, su da garuruwansu sai dai ziyara.
Da ta gama zuba musu, ta dawo gefena ta zauna muka cigaba da yin aikin tare.

Wani almajiri yayi sallama ya shigo, duk muka amsa mishi. Ya durkusa a gefen Fatsu, yace “wai ance ana sallama da Na’ilah a waje!”.
Nayi kasake da zare a hannu ina kallon yaron baki a dage, wa na sani da zai yi sallama dani a garin Gashua ne? Inna ce ta tambayeshi inji wa? Yace “yace wai ace Magaji ne”.
Sai lokacin naji na sauke ajiyar zuciyar da ban san dalilinta ba, nace “kace mishi ina zuwa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button