A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Daga nan muka shiga wajen Anty Sarah. Nan kam tarba muka samu ta mutunci, aka gaisa a mutunce, aka bada amana suka karba, daga nan muka koma sashen na.

Muna shiga na yaye gyalen kaina na haye can kuryar gado na lafe. Abinda ya faru a sashen Raheemah, ta tabbatar min daga cewa lallai sai na kara daure damara a cikin wannan gidan. Ina cikin wannan sake-sake su Janan suka shigo, dole na mike zaune muka kafa sansanin hira dasu.

Da dare ina daki na jiyo shigowar Yaya Bilal nan sashen, ina ji suna gaisawa dasu Anty Halima da suke falo suna hira. Na zauna a gefen gado sosai, ina jiran ya shigo ciki inji da kalar wadda yazo. Ba’a jima ba na ji hayaniyar gaisuwar ta ragu, sai hirarsu da suka cigaba da yi da kuma karar tv, wato fita yayi babu ko leke? Na kuta tare da komawa na kwanta abina.

Ba’a jima ba suka leko, wasu suka mana sai da safe suka koma daya dakin suka kwanta, wasun kuma kamar su Janan, suka kwanta tare dani anan dakin.

F.W.A

          *☆⋆35⋆☆*

Washegari muka karya da abinci mai rai da lafiya wanda aka kawo daga gidan Anty Sarah. Bayan mun ci munyi nak, muka yi wanka muka shirya.
Ina gaban mirror ina shafa man lebe a bakina, Maryam ta leko kanta dakin, “Yaya Na’ilah motar da zata maida mu tazo”.
Na kalli agogo naga karfe goma, naji jikina yayi sanyi sosai. A sanyayen nace “tun yanzu? Nayi zaton zaku kai ko gobene”.
Tace “haba, daga kawo amarya kuma? Mu daya kamata mu kauce tun jiya, mu ba ango damar cin amarcin sa?”.

Na mike tsaye ina harararta, “yarinyar nan kin baci da yawa wallahi, baki da kunya yanzu”.
Tayi dariya tare da maida murfin kofar ta fita bayan tace “kiyi sauri ki fito ke dai muyi sallama”.

Na saka kaya a gaggauce na fita falon, ganin Anty Halima da kaya a gaba nayi turus, nace “kema yau zaki tafi?”.
Tace “ehh mana, ko zaman daki kike so in zauna in miki?”, duk suka kwashe da dariya.

Nayi narai-narai da ido kamar zanyi kuka, nace “yanzu ba zaku dan kara kwana bane?”.

Huleirah tace “nop, not happening. Gwanda mu tafi tun ana ganin girma da mutumcinmu. Ko kuwa so kike angon ya kai ga korar mu ne?”.
Na jefa mata harara, “dallah can yi mana shiru, waye ya sako bakinki anan?”. Suka sake kwashewa da dariya.

Na shiga inda akwatuna suke, na cicciro kaya na fita na kai mika musu, Anty Halima tayi kir tace babu abinda zata amsa, “ce miki aka yi kyauta ake yi da kayan lefe ne? Mijinki kawo miki yayi don ki mishi kwalliya dasu ba wani abu ba”.
Nace “to ai sanya albarkarku ne nake nema, don Allah ki amsa Anty”.
Da kyar ta amsa, sannan suma su Maryam suka amshi tarkacen kayan kwalliyar dana basu, suna zuba godiya da sanya albarka.

Da yake a hannuna akwai kudin da Janan ta bani tace Yaya yace inyi hidimar biki dasu bayan an daura aure, babu abinda nayi dasu ma sai jikin jaka dana saka su. Na dauko na basu dubu dai-daya, Anty Halima kuma na bata biyar.

Tace “a’ah, har da kari? Kai Allah dai ya sanya albarka. Allah ya baku zaman lafiya ke da mijinki da zuriya dayyiba”.

Na dan yamutse fuska cikin alamun tambaya, “karin me kuma?”.
Tace “au, ashe fa kina barci lokacin daya shigo. Ai dazu da safe ya shigo muka gaisa shine ma ya sanar damu za’a zo a maida mu gida. Bayan haka kuma ya kara mana da kudin mota bayan shi ya bada motar da za’a kawo mu”.

Naji wani abu a cikina ya tsinke. Yaya ya shigo dazu da safe? Kenan hakan yana nufin guduna yake yi ne ko menene? Sanyin jikina ya karu.

Cikin sanyin jikin muka fita zuwa waje, suka shiga motocin da zasu kaisu destination dinsu. Su Maryam Katsina, su kuma su Anty Halima Kano za’a kaisu su kwana gidan yan’uwanmu dake zaune a can, sai su wuce Gashua gobe.
Sai dana ga sun shiga mota har an tayar, sannan naji hankalina ya tashi. Na fara zubda hawaye. Maryam da Kulsum na ganin na fara kuka suma suka fara, dama tunda muka fara sallama suke sharar hawaye.

Janan ta janyo ni gefen jikinta tana shafa bayana a hankali, har aka ja motar suka tafi muna daga musu hannu.

Sai da muka ga sun fita daga gidan, sannan muka juya, ni, Janan, Harira da Firdausi zuwa bangarena.
Muka yi clashing da Salama da Adi sun fito daga sashen Raheemah, sun yi shigar su ta Ala wadai kamar yadda suka saba. Siket din da suka saka a jikinsu ya matse su kam kamar idan suka yi motsi mai karfi zai yage. Adi tana ta taunar cingam. Suka watsa mana kallon taro da sisi, suka ja tsaki suka wuce. Ko kallo babu wadda suka isa a cikinmu.

Su Harira suka zauna a falo suka kunna kallo, mu kuma muka wuce wajen kayana ni da Janan. Ta taya ni muka cire kayan da za’a kai dinki wasu kuma muka ajiye su sai a hankali tunda yanzu kayana masu dinki basu da yawa. Bayan mun gama, ta taya ni daukar sauran kayan muka je dakina muka shirya su a cikin wardrobe.

Bayan mun gama muma falon muka koma muka biyewa su Huleirah muna kallo.

A hankali yinin ranar yaci gaba da tafiya, muna ta karbar baki yan ganin daki. Tun daga kan dangin Yaya Bilal din, abokan karatunmu dake nan cikin Zaria da kuma makota.
Da rana aka sake kawo abinci daga gidan Anty Sarah. Da kanta ta shigo ta kawo mana abincin.

Na karbi jaririyarta da taci sunan Rabi’atul Badawiyya a hannunta, na dorata akan cinyata, Mimah kuma ta zauna a gefena tana jan kumatun yarinyar.

Ko bayan ta kawo mana abincin, zama tayi cikinmu aka sha hira da ita, har muka gama. Su Harira suka wanko mata kwanukan tas, sannan ta karba ta fita.
Yanayin sabuwar halayyarta ya bamu mamaki sosai, canjin halayenta da yawan shiga cikin mutane da take yi yanzu ba abinda muka saba gani bane a tare da ita. Ko bayan first tata, maganar da muka dauko kenan muna yi.

Firdausi tace “kin san fa dama can basa shiri da matar Yaya, sai in ga kamar dalilin da yasa bata shiga cikin mutane kenan sosai. Tunda kinga ai idan harkar dangi ta taso tana shiga ciki sosai”.
Harira tace “nima na fi tunanin haka”.
Daga nan muka karkata hirar zuwa wata daban kafin mu kai ga cin namanta.

Da la’asar Janan ta fita ta kai min kayana wajen dinki. Tana dawowa su Harira suka shirya suka wuce Kaduna, ita Janan zata tsaya ta kara hade kan kayanta zuwa gobe. Nan muka yi sallama dasu, suka tafi suna godiya, nima ina musu da sakon gaisuwa wajen su Ummah.

Bayan sun tafi, muka koma falona ni da Janan. Na kwanta akan doguwar kujera, ita kuma ta zauna a kasan carpet, Mimah kuma tana kwance a gefenta tana barci. Muna ta hirarmu da ita har Mustafanta ya kira, ta dauki wayar ta koma saman kujera ta lafe suna ta hirar su ta soyayya.

Nayi shiru akan kujera ina sauraronta, ina tuno wasu lokuta da hakan ta dinga faruwa dani da Yayan. Lokutan da zamu zauna mu sha soyayyarmu kamar babu gobe, wadannan muhimman lokuta da babu kamar su a cikin rayuwata.

Yanzu fa? Me yake faruwa ne? Me ya faru da tarihin soyayyarmu? Me ya faru da irin alkawurra na tattali da amintacciyar soyayya da yayi min idan munyi aure? Me ya faru da wannan kallon soyayya da yake yi min a duk lokutan daya samu dama da? Da kalmomin soyayya da basu taba barin bakinshi?.

Gashi yanzu na kula ko kallom inda nake baya so yayi balle a kai ga maganar arziki da wani kallon soyayya.

Shikenan kenan? Wadannan alkawurran sun zama empty promises? Dama dai zakin baki ne irin na Maza yake min, tunda kuma yanzu ya ganni a cikin gidanshi, ai yana da damar ya wulakanta ni son ran shi.
Nayi concluding hakan cikin raina ina maida kwallar data tarar min a cikin idanuna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button