A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Na bi wayar hannunshi daya ajiye bayan ya kashe wayar da kallo. Zuciyata na rada min wani abu sounds off da matar nan. Tunda muka bar gidan, kullum sai ta kira waya, ayi hira da ita faram-faram ayi sallama. Duk yadda zuciyata take rada min kan cewa kila ko tayi karatun ta nutsu ne, zuciyata ta kasa kwanciya da hakan. Nasan dai koma menene, tunda gidan zamu koma, idanunmu zasu gane mana.
Yaya bai ma kula da yanayin tunani dana shiga ba saboda yadda hankalinshi yake kan iPad dinshi, tun ma kafin mu koma gidan har ya fara aikinshi. Sai na maida kaina na kwantar akan seat tare da lumshe idanun, babu bata lokaci barci yayi awon gaba da ni.

Ban farka ba sai da muka shiga garin Abuja, sannan. Na gyara zamana ina taba bayan wuyana da naji ya dan rike. Yaya ya kashe hasken wayar hannunshi, da alama shima tunda muka dauki hanya bai ajiye wayar ba, ya bude gorar ruwan sona ya miko min. Babu musu na karba na kafa kai, sai dana shanye shi tas. Ya karba ya rufe gorar.

Balarabe yayi horn, maigadi ya taso da sauri ya bude gate din. Muka gangara da motar ciki, shi kuma ya juya ya maida gate din ya rufe kafin ya kwararo da gudu zuwa inda motar take kokarin yin parking. Ya budewa Yaya kofar motar yana ta zuba mishi ruwan sannu da zuwa, ni kuma Balarabe ya bude min. Duk muka fito daga cikin motar.

Su Balarabe da maigadi suna ta kokarin fito da akwatunanmu da tarkace daga booth, ni da Yaya kuma muka tasamma kofar shiga gidan.

Haka kawai naji gabana ya fara faduwa kamar ana buga ganga, muna tsayawa a kofar falon kuwa naji kaina yana wata irin juyawa kamar zan fadi.
Samuel wanda yake ban ruwan fulawowi da gyaran garden ya bazamo daga bayan gidan hannu rike da tsintsiya, da alamu shara yake ya taho gaisuwar ban gajiya.
Hakan ne ya dakatar damu daga bude kofar falon, muka tsaya suna gaisawa da Yaya. Bayan ya mana sannu da zuwa, ya juya.

Idanuna suka sauka akan matakalar dake manne da kofar wasu irin abubuwa kamar har da danko da lema, babu mamaki wani abu ne ya zuba a wajen. Da sauri na kira sunanshi, ya juyo yana kallona.
Nace mishi “don Allah dan sa tsintsiya ka share wajen nan, kamar yayi datti”.
Babu musu ya matso tare da sanya tsintsiya ya fara shara wajen, “to Haji…”.

Bai gama rufe baki ba aka turo kofar falon da sauri kamar za’a ballata, Raheemah ta fito a sukwane kamar wata sabuwar kamu tana ihun “kada ka share! Kada ka share!!”.

Amma ina! Aikin gama ya gama, tuni ya gama sharewa.

Ta ja tayi turus, muna kallon-kallo. Mu na mamakin abinda ya sanyata yin haka, ita kuma fuska cike da alamun tsoro.
Yaya yace “lafiya?”.
Ta kalleshi a dan firgice, kafin ta girgiza kai da sauri, “me? A’ah, babu komi. Dama turaren wuta ne na zuba a wajen”.

Yaya ya karya kanshi gefe guda yana kallonta, kafin ya tabe baki, “well, to ina ma amfanin sanya turaren wuta a waje? Muje ko?”.

Ya tura kai zuwa cikin falon na bi bayanshi. Strangely, babu wannan faduwar gaban da nayi ta ji dazu. Har Yaya ya gama shigo da kayanmu Raheemah na inda muka barota a tsaye. Sai da na kai akwatina daki na dawo daukar jaka sannan na ga ta shigo falon jiki a sanyaye.
A dan lokutan da muka yi bamu hadu ba, babu abinda ya canza daga jikinta. Ta sha kwalliyarta cikin wani tsadadden paper Swiss lace, daya daga cikin wanda Yaya ya dinka mana na sallah. Babu laifi kuma, sun matukar karbarta.
Kai tsaye dakinta ta wuce da sauri, kamar zata fadi, ni da Yaya muka bita da kallo cike da mamakin wannan halayya. Wa zai yi zaton irin tarbar da zamu samu kenan a yadda take ta faman dokin mu dawo dinnan?.
Yaya ya taimaka min na gama kai kayana daki, shi dama daga brief case dinshi babu abinda ya riko. Daga nan ya wuce dakinshi, ni kuma na fada bandaki don in watsa ruwa ko na warware gajiyar jikina.

Bayan na fito falo na sake fita. Ina zama, Yaya ya fito daga nashi falon sanye da jallabiya baka. Yadda fatar jikinshi tayi wani kyau, da yadda rigar ta bi jikinshi ta lafe kamar second skin, yasa ban san sanda na saki baki ina kallonshi ba har da karkace kai gefe guda. Yadda sajen fuskarshi ya kwanta mishi sosai…
Ban san ya iso kusa dani ba, sai dana ji iskan daya hura min ya sauka a fuskata, na lumshe ido ina murmushi yayin daya zauna a gefena da yake akan two seat nake.
Yace “wannan kallon fa baby? Na nawa ne kuma?”.

Na kyalkyale da dariya ina jingina da jikinshi, “yanzu don na kalleka har sai na wani biya?”.
Yace “ehh mana!”.
Na daga kai na kalleshi, “halalin nawa?”.
Shima ya kalleni, tare da sanya hannu yana dan jan hancina, “zakin baki ne zaki yi mun yanzu?”. Na sake yin wata dariyar ina kara kwanciya a jikinshi.

Raheemah ta fito daga dakinta, ba kamar dazu da take a hargitse ba, yanzu ta warware duk da daga gani zaka fahimci cewa murmushin dake kan fuskarta bai kai can ciki ba. Lullube yake da damuwa.
Bakinta washe da murmushi kamar zai tsage biyu, “marhabun lale sannunku da zuwa. Ya hanya? Kun sauka lafiya?”.

Bata nuna alamun tado zancen abinda ya faru dazu ba, don haka babu wanda ta tayar mata a cikinmu. Muka ce “lafiya lau”.
Tace “abincin ku yana kan dinning, ko nan zan kawo muku?”.
Yaya yace “sai na dawo daga masallaci”.

Ta kalleni, “ke fa Na’ilah?”.
Da fari kallonta nayi cike da mamaki da kuma alamun tambaya, banyi tunanin dani take ba. Da sauri na girgiza mata kai, “a’ah, nima sai anjima”.

Ta zauna akan kujera dake gab data Yaya, ta fara tambayarshi abinda ya wakana yayin zuwanmu umrah, nan suka cigaba da hirarsu.
Ni kuwa kallo kawai nake binta dashi, mamakina ya kasa boyuwa. Shi kanshi Yayan nasan ba karamin kokari yayi ba wajen boye nashi. Bansan abinda ya tsirar da wannan sabuwar halayyar tata ba, koma dai menene nasan raina baya gaya min da dadi. Nasan hakan baya rasa nasaba da yadda na saba da halayyarta ta mita da tankawa duk wani abu daya dangance ni.

Ana kiran sallah duk muka mike, Yaya ya wuce masallaci, mu kuma muka wuce dakinmu.
Bayan nayi sallah na kunce tsarabar da nayi, na dauki turaren kaya, na miski da ruwan zam-zam na leka har dakin Raheemah na mika mata. Ta amsa da fara’arta tana godiya. Na jima a kofar dakinta bayan ta amshi kayan ta rufe kofarta ina kallon kofar, kafin na juya na koma dakina.

Abinci ma a tsaitsaye na ci shi saboda cikine a cike yake. Dambun kifi dana nama Anty Sarah ta hado ni dashi cike da wasu manyan plastic rubbers. Shi nake ta ci tunda muka iso abina.
Muna gama cin abincin na musu sallama na wuce dakina, nasan yau dai Raheemah ce take a turaka. Kayan jikina kawai na cire na saka na barci na kwanta. Ina kwanciya kuwa barci ya daukeni, ban tashi ba sai da asubahi da Yaya ya shigo ya tashe ni sallah.

Da wuri na shirya shiga asibiti. Jakata dam da kananun turaruka da robobin zam-zam na tsaraba. Ina kan dinning ina hada ruwan shayi, Yaya da Raheemah suka fito. Hannunta daya rike da jakar shi ta wajen aiki, dayan kuma ya sarkafo daya hannunshi. Na kauda kaina gefe ina kokarin danne wani abu mai daci da yake kokarin taso min. Idan nace bana jin irin haka a duk lokacin da naga wata daga cikin matan Yaya tayi kusanci dashi, kamar haka, kai koda bai kai haka ba, to nayi karya. Ina ji, sai dai karfin zuciya da tsananin iya danne zuciyar tawa ne yasa nake iya kauda kaina gefe guda.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button