A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Sai dana linke kayana na gyada su, sannan na sake fita tsakar gida, daidai lokacin yaran sun dawo, nan fa aka hau guje-guje da rige-rigen wanda zai riga zuwa wajena. Na taryo su gabadaya na rungume, sai da suka gama dokin su, sannan suka kyaleni. Na shiga bandaki na dauro alwala saboda yamma tayi sosai har rana ta kusa faduwa, na fito na sallami masu jiran tsaraba.
Na zauna kenan na fara shan zobon da Anty Alawiyya ta kawo min mai sanyi sosai, naji an fado kaina ta baya ana ihu. Muka fadi a tsakiyar dakin, gorar zobon tayi can nata waje, ni da Maryam da take kaina muma muka yi namu wajen.

Sai data ga barnar da tayi sannan ta tashi da sauri, ta fita ta dauko tsumma da mopper ta goge wajen da zobon ya zuba, sannan ta dawo ta sake rukunkume ni.
Tace “haba Yaya Na’ilah, ke kullum haka kike zuwa babu sanarwa? Me yasa ma kullum na kira wayarki bata shiga ne? Har a whatsapp bana samunki”.

Tun ranar da muka yi waya da Yaya Bilal ta karshe, washegari na sayi sabon sim card nayi register. Kafin in ba Janan lambar wayar, sai data sha jan kunne da gargadi iri-iri akan kada ta kuskura, koda wasa Yaya Bilal yasan da zaman wannan lambar.
Amsarta a lokacin itace, ‘kina tunanin zai damu da rashin samun wayarki ne bayan duk abubuwan da kika mishi?’.
Raina yayi rashin dadi da jin haka, amma sai na dake, nace “wani abu kuma na mishi?”. Bata amsa ni ba, taci gaba da kallonta da take yi a lokacin.

Bayan nan kwata-kwata mantawa nayi da zancen Maryam, yawancin sauran abokanmu ma sai daga baya idan mun hadu sannan zasu yi korafin sun daina ji daga gareni, sai dai kawai in kawo wani dalili can in basu, muyi exchanging din numbers.
Na bata hakuri tare da cewa sim din aka yi blocking, na bata sabuwar lambata tayi saving.

Na kalli gorar zobon data ajiye a gefena, babu komi a ciki duk ya zube, na harareta nace “kin ga kin zubar min da abu, bayan ko sha ban yi ba”.
Ta kyalkyale da dariya, “ai in dai ta wannan ne, baki da matsala Yaya. Ke da kika zo inda ake sarrafa zobon?”. Ta tashi ta fita da sauri, ta dawo da wata gorar ta miko min, na amsa na bude tare da kafa kai.
Muna nan a zaune muna taba hira da ita, har aka kira sallah. Ita ta dauki wayata zata yi game saboda bata yin sallah, ni kuma na tada kabbarar sallah. Bayan na gama na amshi wayar, na turawa duk wanda ya kamata sakon na sauka gida lafiya, na dauki Al-Kur’ani mai girma na fara karantawa har aka kira sallar isha’i.

Sai bayan na gama sallar ne sannan na bude mata tata tsarabar. Takalmi da gyale da jaka wadda ake yayi ta yanmata irinta. Murna wajenta har ta rasa inda zata jefa ni, gefe kawai na koma ina mata dariya.
Bayan na tabbatar Baba ya gama cin abinci na yiwa dakinshi tsinke. Yana zaune matan sun dabaibaye shi, Alawiyya na zuba mishi hira, su Ramata kuma ana gefe ana ta cika da batsewa. Da alamu kambun a hannun Alawiyya yake wannan karon. Abinda yake faruwa kenan a gidan, su ganin walwalar miji a wajensu juyi-juyi ne. Wadda ta samu ta shawo kanshi, ko ta tsibbunta ko ta malaman, ta fa ita da ‘ya’yanta su suke cikin jindadi, ita dayar kuma sai dai ta koma gefe ta kwashi takaici, kafin itama nata tenure din yazo.

Naja daga gefe na gaida shi, ya amsa fuska babu yabo babu fallasa. Nayi zaton zai yi min maganar Yaya Bilal, amma har na tashi na fita daga dakin, bai ce min komi ba. Duk da abin ya bani mamaki, amma naji dadin hakan.
Na shiga gidan su Kulsum, muka gaisa dasu Inna. Mun jima muna hira dasu, har wajen karfe goma, sannan na musu sai da safe na koma gida.

Kayan barci kawai na saka na lalubi shimfida na kwanta. Kamar wanda yake jira, ina kwanciya sai ga kiran wayar Dr. Na Abba ta shigo, dole na katse barcina ba don naso ba na dauki kiran.

*

Washegari kamar yadda na saba, nayi duk wasu abubuwa da yakamata inyi da safen nan. Kasancewar yara sun samu hutun sallah daga makaranta, yasa ban dora abin kari da wuri ba. Wajen karfe tara na gama, kowa ya amshi nashi kason. Na hada kan kayan na wanke, na share kicin din, sannan na koma daki nima nayi nawa karin. Gobe in Allah ya yarda ake yin hawan arfah.
Ina cikin cin abincin, Aliyu ya fado dakin kamar an jefo shi, tunda na dawo gida sai yanzu na ganshi. Yace “babbar Yaya, to ya ne?”.
Nayi dan murmushi nace “lafiya lau Aliyu. Ya kake?”. Nan muka dan sha hira dashi ya bar dakin.

Da yamma bayan na gama duk abinda zan yi, muna tsakar gida a zaune ni da Maryam muna hira, tana bani labarin zuwan da Yaya Bilal yayi gida.

“Har nan cikin gida fa Baba ya shigo dashi in fada miki..” take fada. Wanda hakan ya tabbatar min da cewa ba karamar tarba Baba din yayi mishi ba. Idan kaga yayi baki ya shigo dasu cikin gida, to ba kananun masu muhimmanci bane.
“… Su Mamarmu dubu goma ya raba musu, muma ya bamu dubu goma muka raba, shi kuwa Aliyu aka bashi dubu biyar”.

Mamaki ya kamo ni, ban taba jin labarin hakan ba sai yanzu. Wato so yayi ya saye su da kudi ne ko me? Na godewa Allah daya kasance ba Gashua yaje yayi barin kudin nan ba.

Maryam ta dago ta kalleni, tace “amma da gaske ba zaki aure shi ba?”.
Ban san yadda aka yi labarin yaje kunnensu ba, amma nafi kyautata zaton Baba ne ya fadawa iyayen, su kuma suka basu labari. Ban iya ce mata komi ba sai kafada dana daga mata.

Tayi pouting, “amma Yaya Na’ilah mai yasa? Kinga da idan kika aure shi, sai in zauna a gidanki idan naje Zaria karatu, kinsan nima fa can zan je”. Na gyada mata kai.

Tsulum, sai ga bakin Ramata cikin maganar, da a daki take, bamu ma san lokacin daya fito daga dakin ba, “ke ja can sakaryar banza! Me ake da gidan mai mata? Ai wallahi kada ki kuskura ki yarda, kudin mutum su rufe miki idanu kiyi zaben tumun dare. Ke zaman nan gidan ma kadai bai isheki ishara ba? Kina dai ganin yadda muke fama, babu farinciki ko na anini sai akasinsa. Kullum cikin taraddadi da zullumin abinda makiya, makagauta zasu maka. Don haka wallahi ki auri dan saurayinki shi ya fiye miki kawai”. Ta saurara tana kallona, ko amsa take jira in bata da godiyar shawarar data bani? Ban ce mata komi ba, amma a can kasan zuciyata sai da nace ‘ishara ta nawa kuma?’.

Da dai taga bani da niyar tanka mata, sai ta kara gaba, tana fada tana kara nanatawa, ina amfanin auren gidan kishiya? Ina jin Anty Alawiyya daga daki tana ihun, “a hakan dai kuma ake zaune ake shuka rashin mutunci ba!”. Babu dai wanda ya tanka musu a cikinmu, sai ma hirarmu da muka cigaba da yi.

Washegari muka tashi da azumin nafilar arfah a bakinmu.
Washegari kuma Baba yayi yankan layya. Dama kowace shekara, ya kan yanka raguna guda uku, daya matan su raba, daya nashi shi da abokai da yake yiwa rabo kasancewar shi mutum na mutane, dayan kuma na yara ne.
Kwananmu biyu muna aikin suya, aka kammala aka raba kowa ya dauki nashi. Wanda ranar rabon ma sai da su Ramata suka raba hali kamar za ayi dambe, sannan da kyar suka hakura.
Ni dai naci gaba da jindadin hutuna kafin ya kare.

Bayan sallar da kwana biyu, su Dr. Na Abba suka kai kudi can Gashua, wanda Baba ne yace hakan. Gabadaya suka kai kudin, aka kuma sanya ranar aure. Nan da watanni uku masu zuwa. Wanda yayi daidai da lokacin dana gama exams dina kenan.
Ban san a cikin wani yanayi nake ba a cikin wannan lokaci, abu daya kadai na sani, shine zuciyata bata maraba da wannan biki koda wasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button