A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

*☆⋆25⋆☆*

Ga duk wata diya mace da take jin ta cika ‘ya, mai cikar halitta da kamala, wadda zata shiga ko’ina ne a fadin duniyar nan kanta a tsaye, ta kuma amsa cikakken suna na ‘ya mace, to ta cancanci gwarzon namiji kamar Yaya Bilal.
Irin mazajen nan ne da ake kira mazajen duniya. Wadanda Allah yayi wa ilhama da kuma rufin asiri ta kowane fanni.

Tun bayan rasuwar mahaifinsu, a lokacin yana ajinshi na shida a makarantar firamare, yayin da babbar yayarsu Yaya Sa’a take aji na biyar a sakandire, Jameel kuma yana primary three, duk da kankantarshi, Bilal bai yi kasa a gwiwa ba wajen zagewa tun karfinshi wajen ganin cewa ya tallafa musu. Wannan duniya da muke ciki ta riga ta zama abinda ta zama. Mutane basu san kowa ba daga kansu sai iyalansu, wasu ma iyalan nasu sai na kurkusa kawai. Mahaifinsu mutum ne mai rufin asiri daidai gwargwado, bayan rasuwarshi kuma sai rayuwa take nema ta zamar musu wata aba mai tsananin wahala.
Ummansu ta fara sana’o’i na hannu iri-iri domin ta samu ta tallafi ci da shan ‘ya’yanta da karatunsu. To shima Bilal bai zauna ba, kananun sana’o’i na hannu babu wanda bai kama ya taba ba, kanikanci, dinki ne, bude karamar tired, da dai duk wata hanya daya san zata sada shi da samun halaliyarshi.

Duk da cewa yan uwa na iyaka bakin kokarinsu, sai dai kamar yadda nace, wannan zamani da muke ciki yanzu ya zama naka sai na naka. Koda suka fara abin daga farko kamar abin arziki, sai suka zo suka watsar. Shi kuwa yau a duniya, babu wani abu da yafi saurin zubar da mutunci da kima irin yawan bani. Ko iyaye gajiya suke yi balle kuma wadanda alaka ce kawai da bata kai ta kawo ba ta hada. Don haka suka kama kansu, idan an kawo musu abin amfani ko na tallafi, su karba suyi godiya, idan basu dashi, suyi kama-kama su rufawa kansu asiri.
Wannan gida da suke zaune, shi kadai mahaifinsu ya bar musu a matsayin gado, su ukun da kawunsu daya kasance kanin mahaifin nasu. Sai kuwa wata karamar gona da aka sayar da ita lokacin da Yaya Sa’a zata zana jarabawar fita daga babbar makarantar sakandire.
A cikin wannan lokacin ne mahaifinsu Janan ya fara neman Ummansu, lokacin matarshi bata jima da rasuwa ba. Kuma abokin mahaifinsu ne kafin ya rasu. Aka daura aure ta tare a Kaduna abinta.

Nan ya hade Bilal da Jameel din ya saka su a makaranta tare da sauran ‘ya’yanshi suka cigaba, ita kuma Yaya Sa’a ya shige gaba, aka daura mata aure da wanda yake nemanta a lokacin bayan ta gama sakandire, taci gaba da karatunta a gidanta.
Bayan ya gama secondary, ya taho nan ABU Zaria yayi degree dinshi akan mass comm. Allah ya taimakeshi da taimakon Baban yara, ya gama degree dinshi da offer dinshi ta aikin jarida a hannu. Ya fara aikin a gidan jaridar Daily Trust da kafar dama, cikin dan kankanin lokaci ya samu karin matsayi, nan da nan yayi kaurin suna. Ya saye gidansu da suka gada a wajen kawunsu, itama Yaya Sa’a ya sayi nata ya bata kudinta. Yaje aka warewa Jameel nashi, ya tada gini abinshi. A cikin dan lokacin aka yi aurensu da Ameerah. Sun jima suna soyayya da ita, tun yana karatu a abu.

Har gashi a matsayin da yake tsaye a yau. Magidanci ne dan kimanin shekaru talatin da hudu, wanda ilimi na musulunci da zamani ya gogar dashi. Yana fara aikinshi da Daily Trust, ya cigaba da neman kwalin masters dinshi ta online, bayan wannan bai dakata anan ba, yayi kwasa-kwasai da dama da suka kara mishi experience akan aikinshi, da kuma taimakonsu ne da taimakon Allah yake akan matsayin da yake yanzu a wajen aikinshi, Deputy Manager din Daily Trust.

Yana da wani irin hali na son yan uwanshi, zumunci da kyautatawa iyayenshi. Shi yasa har a kullum, Allah yake ta kara mishi budi da haske a cikin al’amuranshi. Allah ya wadata shi da haliita, zubi da kira irin na maza. Idan ka kalleshi sau daya, ba zaka so ka kauda kai ba. Irin halittar jikinshi halitta ce irin one in a million dinnan, kafin ka samu mai irinta sai ka dade. Sai kuwa alamun hutu da kasancewa cikin ni’ima ta rayuwa da suke kokarin boye yawan shekarunshi a duniya, wanda idan ba fada maka aka yi ba, mawuyaci ne ka iya cankar shekarun nashi kai tsaye.

Ta kowane fanni dai, Yaya Bilal irin mazan nan ne da idan mace ta samu irinsu, zata ce Allah ya karbi addu’arta, ya bata miji na kerewa sa’a. Idan kyawun ne, yana dashi, dukiya da rufin asirin ma dai Allah ya bashi, kyawun hali, kamala da nagarta, duk yana dasu. Duk dai wani abu da ake bukata a da namiji, miji na gari, kuma uban ‘ya’ya na kwarai, idan aka zo kan Yaya Bilal dole a diga aya. Sai dai me yasa ni nake kokarin guje mishi tun karfina?!.

A yanzu daya zagaye ni ta ko’ina, duk inda na waiga babu abinda nake gani sai faffadan kirjinshi sai kuwa fuskarshi da sai na daga kai sannan zan iya ganin zagayayyun lebunan bakinshi, ni kuwa banyi wannan gigin ba. Kaina a kasa yake, ina kallon yatsun kafata kamar duk duniya babu wani abu daya kaisu kyawu.
Tattausan kamshin turaren da yake yi a karan kanshi, seems very inviting. Ji nake kamar wani maganadisu ne yake kokarin janyo ni zuwa jikinshi, domin inyi ta shakar kamshin kamar ba zan daina ba, kada ma kuma ayi maganar wannan managarcin kirjin nashi. Da na fara dago da kaina naga zan sauke idanuna akan shi, sai inyi saurin kara dunkufar da kan nawa kasa sosai.

Gashi a bakin hanya muke, mutane suna ta wucewa wanda duk da cewa kaina a kasa yake, amma na tabbatar kallonmu suke yi. Nan da nan nayi narai-narai, idanuna suka kawo kwalla.

Ina tunanin ya kula da hakan ne, ko kuwa wani abu ne na daban? Saboda da sauri naga ya ja da baya kamar wanda wutar lantarki ta ja, hannu daya soke cikin aljihun riga dayan kuma yana shafa bayan wuyanshi sheepishly.
Yace “God, don Allah kiyi hakuri. Amma meye na guduna Na’ilah kamar wani makiyinki?”. Nayi shiru kaina a kasa.

Naji ya ja dogon numfashi ya ajiye, yace “ok…, na ji na kuma yarda ban kyauta miki boye kaina da nayi ba, sai dai bani da zabi ne Na’ilah, nayi tunanin wannan ita ce hanya mafi sauki da zata sa in saba dake. I was wrong ashe!”. Yayi shiru yana kallona, ni kuma dana kasa iya hada ido dashi saboda tsabar kwarjinin da yayi min, nayi kasa da kaina.
Ya sake cewa, “kiyi min alfarma daya mana, ki zo muyi magana a nutse. Kinga nan a bakin hanya muke, sannan mutane suna wucewa ba zamu samu muyi magana a nutse ba!”.

Gabadaya naji jijiyoyin jikina kamar an dauresu. Sai lokacin na dago muka hada idanu dashi, sanyin jikina ya karu, babu ma ta yadda za ayi in iya musawa wannan halittar da take gabana. Saboda haka na gyada kaina kawai, saboda a lokacin babu wata kalma da zata iya fitowa daga bakina.

Ya saki dan murmushi daya sa naji bugun zuciyata ya canza, na kara yin kasa da kaina. Yace “Masha Allah, bismillah!”. Yana yi min nuni da tsallaken titi inda ya ajiye motarshi, ni sam ban ma kula da ita ba sai a lokacin. A hankali na daga kafafuna da nake jinsu kamar babu laka a jikinsu, na bi bayanshi har zuwa inda motar take. Muka jingina da motar, kaina a kasa ina wasa da yatsun hannuna, shi kuma yana ta aikin kallona. Bai yi magana ba, har sai da naji kamar inyi fiffike in bar wajen saboda yadda idanuwanshi dake kaina suka addabeni. Nan da nan naji babu abinda nake so a lokacin kamar kasa ta tsage in shige ciki ta rufe ni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button