A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Hira muka fara da Aylah, tana bani labarin abinda ya faru a wajen bikin da taje ranar. Wai mutumin mace ta biyu ce zai aura, wadda ta kasance kawarsu ce. Shine a wajen lunch party, matarshi ta farko taje da tawagarta, aka yi rashin mutunci dai yadda ya kamata.

“Dama duka yaushe ne Yayan su Afrah kawata zai sake aure, amaryar ta hadu da uwargidan a shagon saloon. Wallahi tsiyar da aka yi a wajen sai ta baki mamaki. Kaca-kaca suka yi wa juna. Bayan anyi auren kuma da sati biyu, ya dankarawa uwargidan nashi saki. Naji ance kusan watannninta biyu a gida, sai kwanannan ta koma”.

Nayi ajiyar zuciya tare da girgiza kai. Abinda yawancin mata suke jin tsoro game da kishiya kenan, taje ta fitar dasu daga gidansu. Ko ta hana su zaman lafiya da miji. Ko ta zauna, haka zaka kare rayuwarka cikin tashin hankali, fargaba da takaici.

Aylah ta cigaba da cewa, “ni wallahi gani nake babu wani aibu game da wata kishiya. Ba abokiyar zama bace? Menene a ciki? Idan dai ka kwantar da hankalinka, tsaf zaku yi zaman lafiya da ita wallahi!’.

Na kada idanu, “baki san komi ba game da kishiya Aylah. Kiyi shiru kawai. Ina tunanin duk danginki babu wadda take zaune da kishiya ko?”.
Ta daga kafada, “Anty Hanifa ce kawai, kuma suna zaune da ita lafiya lau”.

A hankali murmushi ya subuce min, “to wannan sa’a ce tayi ba karama ba, ina gaya miki. Wallahi da tayi rashin sa’a, gabadaya sai ta girgiza family dinku saboda sanabe”.
Aylah ta girgiza kai, “naa. Bana tunanin haka. Kada dai kice min, baki son kishiya Na’ilah?!”.

Murmushi kawai nayi, na gyara kwanciyata tare da mata sai da safe.

Dare ya tsala matuka, yayin da barci ya gagari idanuwana. Zuciyata tayi wani irin nauyi, ji nake kamar an dauki wani gungumemen dutse an dora min a kai, numfashi ma sai da naji ya fara gagarata. A hankali na janyo wayata da headphone na hada, na kamo kira’ar Sheikh Malam Ahmad Suleiman na kunna. Idanuwa na lumshe a hankali, ina bin kira’ar a cikin raina.

To say that na tsani kishiya, is an understatement.

I despise her! Na tsaneta with all my being.

Tunanin zama da kishiya kadai a cikin raina, yana sa jinin jikina tafasa, zuciyata zafi kamar ana diga ruwan dafaffiyar dalma.

Allah Ya gani, bana son kishiya. Ina kuma da yakini a cikin raina, ko zan mutu tuzuruwa, sai dai hakan ta faru, amma ba zan taba zama da kishiya ba!!.

And why not, you might ask?!

A shekaru na bakwa a cikin rayuwata, na dandana zafin kaidi irin na kishiyar uwa, a wani unfortunate dare, da na kira ‘bakin dare’.

Ranar mahaifina yake sake aure, kyakkyawar bafulatanar mata, fara doguwa, tsayi wanda ta tafi gabadayanta ta mike, babu lankwasa ko duk’awa, har yau ina mamakin dalilin da yasa Baba ya aureta.

Idan kyawune, mahaifiyata tana daya daga cikin kyawawan cikin danginsu, kasancewarta ruwa biyu, shuwa-arab da barbanci, yasa ta kasance mace daya tamkar dubu. Kyawu, ladabi, biyayya, iya girki, kwalliya, kada ma ayi maganar tsafta, don gani nake duk duniya, babu na biyun mahaifiyata a tsafta.

Saboda haka, dalilin auren Babana da bafulatana Ramata, kazamiya mara kira, still remains a mystery, yet to be solved to me.

Bana taba manta ranar da aka kawota gidanmu, ina ta murna an kawo min wadda zan kira Anty na. Masu kai amarya sun shigo da habaici, suka tafi da bakaken maganganu a bakinsu, duk mahaifiyata da abokanta yan dannar cinya suna jinsu, amma suka kauda kai kamar basu ji ba. Wannan abu ya bakanta musu rai.
Wata daga cikin kawayen Mama da ta kasa kau da kai, ta tanka musu. Ba bata lokaci suka hau zage-zage, kamar dama jira suke yi, ko kuma da guzirin zagin suka shigo. Da kyar aka ba Iya Lami hakuri, su kuma suka tafi.

Bayan tafiyarsu babu jimawa, suma yan dannar cinyar suka mana sallama suka tafi, suna ta kara ba Mama na hakuri. Ni kam ina zaune muk’u a lokacin, ina jiran Mahaifina ya dawo. Bai dawo ba har barci ya daukeni.

Can zuwa cikin dare, hayaniya ta tasheni. Ba wai kuma normal hayaniya ba, kukan mahaifiyata ne ya tasheni wanda nake jiyowa yana tashi daga can dakin Babanmu.
Kasancewar gidanmu dakuna hudu ne, biyu suna kallon biyu. Dakin Mama shi yake kallon na amarya da Baba.

Daga tagar cikin dakin Mama na leka, ina hangen ta tsugune a gaban Baba. Matar da aka kai mishi a matsayin amaryarshi, a zaune a gefenshi kamar zata hau cinyarshi, tana ta wani firirita. Ban jiyo abinda suke cewa ba, daga karshe dai na ga Mama ta tashi ta fado daki da sauri.

Babu bata lokaci ta hau lalubar mayafi, ta yafa nata, nima ta miko min nawa. Ina tambayarta ‘Ina zamu je Mama?’, amma saboda tsabar kuka da take yi, ta kasa amsa min. Hannuna kawai ta kama ta ja muka fita daga dakin.

A bakin kofa, mahaifina ne a tsaye, kamar wanda yake jiran ta fito. Muna fita, ya kamo hannuna ya rike. Har yau ina tuna maganganun daya fada mata clearly,
“Kada ki kuskura kiyi tunanin zaki tafar min da diyata, yadda itama zaki je ki koya mata rashin kunya da rashin mutunci ko? To ba dani ba, yadda kika zo gidannan zikal, haka zaki tafi!”.

Wani kukan ya sake barkewa daga bakin Mama, cikin rishin kuka, magana na fita da kyar, tace “haba Malam, ta yaya zaka ce in bar maka yarinya yar shekara bakwai a hannun wannan azzalumar mata ta ka?”.
Ina tunanin hakan shi ya kara tunzira Baba, ya bude baki ya hau zazzagawa Mama masifa kamar wanda yake amayo kalmomin. Ban taba ganin tashin hankali irin na ranar ba.

Tunda aka haifeni, ban taba ganin sa’insa tsakanin iyayena ba. Tun tasowata, iyakarsu kawai: ‘Yana yi kaza, to. Yana kada kiyi kaza, to Malam’. Ganin wannan abu a ranar nan, was a first. And definitely not a good one.

Ina ji, ina gani, Mama tasa kafa ta bar gidan, Baba ya bita a baya ya rufo gidan. Bai ma kula da cewa ina kofar dakin Mahaifiyata daya gama ci wa mutunci a gabana ba, ya wuce dakinshi. Amaryarshi na tsaye a kofar daki tana jiranshi, yana shiga, aka maida kofar dakin aka rufe, ji kake garammmmm!!.

A hankali naja kafafuna da suke rawa, na koma cikin daki. Kan gadon Mamata na hau, na kwanta.
Karo na farko a rayuwata dana kwanta ba tare da na ji dumin mahaifiyata a jikina ba. Kullum sai na yi barci take tafiya dakin Baba. Sai dai kawai wani lokaci idan na tashi cikin dare, in ga bata nan.

Daren ranar barci sai barawo.

Washegari tun da safe na tashi, al’adar gidanmu ce. Na share tsakar gida tsaf, na kunna wuta a murhu na dafa ruwan zafi, kasancewar lokacin sanyi ya fara shiga. Na je nayi wanka, na koma daki na shirya.

Shiru ina zaune, ina jiran a fito a dora abincin kari, ban ga motsin kowa ba. Ganin karfe takwas tana neman shigewa, yasa na dauki jakar Islamiya ta na fita. Sai da na saka makulii na rufe dakin Mama, sannan na yi sallama a kofar dakin Babana.

Sai da aka dauki lokaci kafin aka amsa min, a hankali na tura kofar dakin na shiga. Baba yana zaune a gefen katifarshi, amaryarshi na kasa kusa dashi, tsabar kusanci har cinyarshi na gogar tata, nayi saurin yin kasa da idanuwana.
Karin safe ne a gabansu, shayi, libgegen biridi, soyayyen kwai, da indomie.

A nutse na gaidashi, ya amsa ciki-ciki. Ganin na ki gaida matarshi, yasa ya umarceni da in gaidata. Cikin tafasar zuciya na gaidata, ta amsa tana watso min wasu dogayen hakora marasa tsari, wai ita ala dole murmushi take yi. Bayan a hakikanin gaskiya, ko kare aka yiwa murmushinnan yasan cewa dole tasa aka kakaro shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button