A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Nan suka ja kujera suka zauna. Bayan mun gaisa, Ameerah ta zubawa Yaya nashi abincin. Ni kam ina gama ci, na dauki jakata na musu sai anjima. Sai dai tun kafin in kai ga tashi tsaye Yaya ya tsayar dani. Yace “bari in gama sai in sauke ki”.
Ban ce komi ba, na koma na zauna. Again, nayi zaton zata yi magana ko wani abu, nan ma ta bani mamaki da naji tayi shiru. Bai ma dauki wani lokaci ba ya gama cin abincin, nan muka mike muka fita.

A asibiti bayan na gama gaisawa da duk wasu wadanda muke gaisuwar mutunci, ganin babu aiki sosai yau a ward din yasa na yiwa ofishin Dr. Anita tsinke. Bayan mun gaisa da ita a mutunce kuma cike da girmamawa, na yi mata bayanin duk wasu signs da nake gani a jikina. Bayan tayi min wasu tambayoyi da kuma gwaje-gwaje, ciki sati biyar ya bayyana.

Ba karamin mamakinta ta nuna ba, cikin jijjiga kai tace “Allah kenan! Wannan abin mamaki da me yayi kama? A yanayin yadda kike dinnan, ban taba zaton zaki iya daukar ciki a cikin shekaru biyu masu zuwa ba wallahi. Kai congratulations!”.

Nayi murmushi ina jina kamar ina yawo a sararin samaniya. Duk da cewa nayi zargin haka, amma na kasa yarda da abinda naji yanzu gaskiya ne.
Tace “sai dai you’ll have to be extra careful gaskiya, saboda cikin jikinki yana bukatar kulawa da takatsantsan. Kin fahimce ni?”.
Na gyada mata kai. Nan ta zauna ta kafa min dokoki, irin ayyukan daya kamata in dinga yi, da wadanda yakamata in guda, irin abubuwan daya kamata in dinga ci, da dai sauransu. Nan na mata sallama na wuce pharmacy na sayi magungunan data rubuta min. Throughout jin jikina nake kamar ba nawa ba. Da an dan motsa kadan, sai in kai hannuna saman cikina ina shafawa.
Lokacin tashi yana yi, na koma gida.

Bayan na ci abinci na cire uniform dina, na zauna a gefen gado ina tunanin ta yadda zan sanarwa da Yaya maganar wannan cikin. A haka har barci ya dauke ni, sai wajen karfe hudu na tashi.
Nayi sallah na fita waje don samawa cikina abinda zan ci. Babu kowa a falon, sai dai daga jin sautin muryoyin dake fitowa daga dakin Raheemah, nasan baki tayi.
Na bude fridge na ciro fresh fruits da yoghurt na koma dakina. Har Yaya ya dawo ban fita ba.

*

Fiye da kwana uku kenan, amma na rasa ta yadda zan isar da sakon cikinnan wajen Yaya, na kuma rasa dalilin da yasa na kasa din.

Safiyar ranar juma’ah, na gama shirin tafiya wajen aiki. Na fita falo da dan saurina ganin cewa naso in makara yau.
Yaya na zaune akan kujera yana latsa wayarshi, babu alamun Raheemah wadda take yin girki yau, babu alamun kayan kari.
Na dan yi turus, kafin na karasa kusa da Yaya na zauna tare da gaida shi.
Ya amsa yana bina da kallo, nasan yadda na murmure da wata irin kiba dana fara yi ne yake kallo yana mamaki. Bai kai ga amsawa ba Raheemah ta fado wajen kamar an jefota. Tun kayan barcin jiya ne a jikinta bata cire ba. Kanta babu dankwali, gashin kanta ya cure waje guda.

Taje gaban Yaya tayi tsaye har da kama kugu, duk muka bita da kallon mamaki.
Cike da tsiwa da alamun dibar albarka tace “Bilal!”.

Ba Yaya kadai ba, ni kaina sai dana bude baki na bita da kallon mamaki. Bana tunanin ko Ummanmu tana ambatar sunanshi haka balle ayi maganar Yayye ko kannenshi, ayi zancen matar aurenshi. Nasan kila dai abokanshi na kiranshi haka.

Ya kalleta a dage, “lafiya?”.

“Lafiyar kenan, lafiya ce ta kawo haka. Sakina zaka yi!”. Ta furta hakan cikin saurin murya da mazarin jiki kamar wadda take shaking.

Yaya yace “ban gane ba? Ke lafiyarki lau kuwa? Me ke damunki ne?”.
Tace “ka ga bawan Allah, ba wasu maganganun banza na tambayi ka min ba, idan kana son arzikin kanka, to kawai ka miko min takardata in kara gaba. Dole ne? Nace auren naka dole ne wai?”.

Saboda tsabar mamaki Yaya kasa magana yayi, kawai zama yayi yana kallonta, kamar yadda nima na sankame a zaune.

Tace “ni fa bani da lokaci kaji? Ka sallameni don Allah”.
Yaya yace “ba zaki zo kai tsaye ba kawai ki ce in sallameki, akan me? Akan wani dalili?”.
Tace “saboda na gaji da zama da kai, zama da kai haukata zai yi. Kawai ka sake ni, ka sakeni nace!!”. Zuwa yanzu karaji kawai take yi. Tana rufe baki ta juya zuwa dakinta a sukwane, bata jima ba ta dawo hannu rike da takarda, ta jefa mishi jikinshi, “maza maza rubuta min in wuce Malam”.

Wani abu yayi snapping a jikin Yaya, kamar wani wanda aka yi possessing, kawai ya dauki takardar da biro ya hau rubutu, ko sauraren ihun kada ya aikata abinda ba’a so a aikata a cikin aure da nake mishi bai yi ba. Yana gamawa ya mika mata, ta warta tana karantawa cikin yatsina fuska.

“Saki biyu? Karya kake wallahi, wallahi sai ka cike min shi. An gaya maka wata tsiya nake kwasa a gidanka da zata sanya ni son dawowa gidan? Kai yau fa idan baka sallameni ba wallahi sai ayi yakin duniya a cikin gidannan! Kaji ma wani rashin mutunci!”. Ta hau wasu maganganu marasa kan gado da ma’ana.

“…Dama boka sai da yace kada in bari iska ta share wannan maganin, wannan shegen tsinannen mai sharar wannan yazo ya share shi. Dama sai da yace kaikayi koma kan mashekiya ne, kaina zai dawo muddin bata tsallaka shi ba. Saki uku yakamata ka mata, ni me yasa ba zaka min saki ikun ba?”.

Yaya ya tashi tsaye a hankali yana fuskantarta, “me kika ce? Me kike nufi?”.

Ta kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya kamar wata mahaukaciya, “to ina ruwanka da abinda nace? Abinda za ka damu dashi shine karashen saki na. Kasan wani abu? Boka ya bani wani magani yace in jika shi ya kwana uku, sai in tace in ba waccan sakarar matar taka data kunshi ciki, tana wani daga kai sama tana tutiya ita zata haifi magaji…”
Ni da Yaya muka zare idanu muna kallonta, saboda nasan inda maganar ta nufa. Bata damu da yadda muka yi ba taci gaba,
“kasan me nayi? Sirinji na sayo na zuki ruwan maganin, nawa mangwaron da zata sha allura. Hahhha!”. Ta sake wata dariyar. Tuni kwalla ta gama wanke min idanuna.
“Sakara, ina kallonta har wani rawar jiki take yi zata sha mangwaro, bata san cikinta zata fitar ba!”.

Na kai hannu bakina na rufe cikin kokarin danne kukan daya taso min, ita kuwa taci gaba da sheka dariyarta.
Karan marin da Yaya ya zuba mata, sai daya karade falon gabadaya. Yace “dama kece kika zubar min da cikina? Kodayake, I’ve had my suspicions tun daga farko. Saki kike so ko? To kije na karasa miki sakin na uku, meye amfanin zama dake dama? Tunda na aureki na rasa walwala a cikin rayuwata, ban ma san dalilin da yasa na aurekin ba, amma hakanan nake hakuri ina zama dake. Kuma abu dayan da yake sanya ni farinciki ki ce zaki raba ni dashi? Ki fitar min daga gida yanzun nan, kada ki kuskura in dawo gidannan in same ki don wallahi sai na wulakanta ki. Kada kuma ki daukar min ko allura daga cikin kayana!!”.

Yaya ya fita daga cikin falon da sauri kamar wanda zai tashi sama, ya barni sarkafe a tsaye ina kallon Raheemah da take ta dariya babu kakkautawa babu alamun zata daina.
Sai gashi kuma ya dawo, “kin san me? Fitar min daga gida yanzun nan, kada ki kuskura ki sake dawowa!”.

Sai lokacin ta dakata da dariyar da take yi, “yo dama ko baka ce ba fita zan yi. Gidanka da kayanka din banza dana wofi?”. Ta shige dakinta ta fito da gyale a hannu daya, purse da waya a hannunta daya.

Yaya ya saka ta a gaba kamar wata barauniya har bakin gate, sai data fita daga gidan sannan ya juya yana gayawa maigadi kada ya bari ko jingina da gate din gidan tayi balle ta kai ga shiga. Maigadi da rawar jikinshi yace “an gama Alhaji!”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button